Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Diego Costa
 2. Cristiano Ronaldo zai yi hutun dole
 3. Philippe Coutinho na tsaka mai wuya
 4. Liverpool za ta buga wasan neman shiga gasar zakarun Turai

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe

  Jama'a, abun da ya samu kenan yau. Sai kuma gobe in mai duka ya kai mu.

 2. Ba zan kara cewa komai kan Coutinho ba -Klopp

  Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce shi ba zai sake cewa komai ba kan Philippe Coutinho.

  Da aka tambayeshi game da Coutinho, sai kociyan ya ce: "Ba ni da abun da zan fada a kansa. Ina nan, amman in aiki da 'yan wasan da nake da su. Bana tunanin 'yan wasan da ba ni da su. Na fidi dukkan abubuwan da zan fada game da batun.

  Jurgen Clopp
 3. Southamton ta shiga yarjejeniya da wani dan China

  kungiyar kwallon kafa ta Southampton ta shiga wata yarjejeniya da wani dan kasuwa dan China, Jisheng Gao, da iyalansa, in ji wata sanarwar da mai kulob din, Katharina Liebherr, ta fitar.

  BBC ta gen cewar iyalan Gao sun saye kimanin kashi 80 cikin 100 na kungiyar.

  A watan Janairu ,kanfanin Gao ya cimma yarjejeniya da Saints, amman huldar yanzu ta zama jari na mutum.

  "Yau ne farin sabon tarihi mai cike da farin ciki ga kungiyar kwallon kafan," in ji Liebherr, wadda za at rike kashi 20 cikin 100 hannun jarin kungiyar kwallon kafan.

  sanarwa
 4. West Ham ta kusa sayan Carvalho

  West Ham ta kusa sayan dan wasan tsakiyar Sporting Lisbon, William Carvalho kan kudin da ake zaton zai kai fam miliyan 30.

  An ki wani tayin da Hammers suka yi kan dan shekara 25 din, kociya Slaven Bilic, yana fatan zai iya kammala cinikin.

  Carvalho na cikin 'yan wasan da suka yi wa Portugal nasara a gasar Euro ta shekarar 2016 kuma ya buga wasan neman cin na uku a gasar zakarun nahiyoyi a lokacin bazararnan.

  Ya ci kwallo daya a wasanni 37 da ya buga wa aksarsa.

  Carvalho
  Image caption: Carvalho ya fara taka wa Portugal leda ne a shekarar 2013
 5. Ga wasannin da Cristiano Ronaldo zai rasa

  Barcelona (a gida) - a gasar Spanish Super Cup - 16 ga watan Agusta

  Deportivo La Coruna (a waje) - a gasar La Liga - 20 ga watan Agusta

  Valencia (a gida) - La Liga - 27 ga watan Agusta

  Levante (a gida) - La Liga - 9 ga watan Satumba

  Real Sociedad (a waje) a gasar La Liga - 17 ga watan Satumba

  Ronaldo
 6. An dakatar da Cristiano Ronaldo na wasanni biyar

  An dakatar da Cristiano Ronaldo na tsawon wasanni biyar bayan an ba shi jan kati a wasan da Real Madrid ta yi nasara kan Barcelona a gasar Super Cup ta Spaniya da suka fafata ranar Lahadi.

  An hana shi buga wasa daya domin ya samu katin gargadi biyu a Nou Camp, ya samu daya domin ya tube rigarsa a wajen murnar shan kwallo yayin da ya samu dayan domin faduwar karya ta nuna cewar an masa keta.

  An kara dakatar da shi na tsawon wasannin hudu domin ture lafirin da ya yi bayan an kore shi daga filin wasa.

  Ba zai buga karawa na biyu da Real Madrid za ta yi da Barcelona ba ranar Laraba.

  Ronaldo
 7. Na fi jin dadi bayan na fara kwallo a PSG -Neymar

  Dan wasan gaban Brazil, Neymar, ya ce shi ya fi jin dadi bayan ya fara taka leda a PSG inda ya ci kwallo daya tare da tallafa wajen cin daya kwallon a wasansa na farko a PSG..

  Dan shekara 25 din ya zama dan wasan da ya fi tsada a tarihi a lokacin da ya koma PSG daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200.

  Shi ya tura wa Edinson Cavani kwallo na farko da ya ci wa kulob dinsa ranar Lahadi kafin shi da kansa ya ci kwallo na uku a nasarar da kulob dinsa ya samu da ci 3-0.

  "Mutane suna tunanin barin Barca zai sa mutuwa, amman akasin haka ne," in ji Neymar.

  Neymar
  Image caption: Neymar ya maye gurbin Javier Pastore a cikin 'yan wasan 11 masu fara wa PSG wasa
 8. 'Ba za ka iya watsi da tayin Barca ba'

  Dan wasan gefen West Ham, Michail Antonio, ya ce ya ji tausayin irin tsaka-mai-wuyan da Philippe Coutinho ke ciki a Liverpool.

  Coutinho ya mika takardar neman barin Liverpool sa'o'i bayan kungiyar ta fitar da sanarwar cewar dan wasan ba na sayarwa ba ne.

  "A matsayinka na dan wasa ba za ka iya watsi da tayin Barcelona ba," in ji Antonio.

  "Idan Barca ta kwankwasa maka kofa, sai ka je. Ina jin Liverpool na yin abun da ya kamaci kungiyar domin shi ne dan wasanta da ya fi iya taka leda, kuma yana taka rawar gani. Suna tsayuwa akan bakansu. Amman za ka so dan wasan da ba ya son tsayawa kulob din?

  Coutinho
 9. Na yi mamakin cewar Matic ya bar Chelsea -Mourinho

  Jose Mourinho ya ce bai taba tsammanin cewar Manchester United za ta iya sayan Nemanja Matic ba 'kafin wani abu na musamman ya faru' kan cinikinsa na fam miliyan 40.

  An ayyana dan wasan tsakiya Matic, mai shekara 29, gwarzon wasa bayan United ta lallasa West Ham 4-0 a wasansu na farko a gasar Firimiya.

  Tsohon kociyan Blues din ya ce: "Ban dame shi ba, ban dami Chelsea ba.".

  "Lamarin ya yi kaman wani abu na faruwa saboda ajen dinsa ya ce za mu iya sayansa, amman dole mu biya kudi."

  Mourinho
 10. Rico ya sabunta yarjejeniya da Sevilla

  Mai tsaron ragar Spaniya, Sergio Rico, ya sabunta kwatiraginsa da Sevilla, lamarin da zai sa ya ci gaba da zama a kulob din na gasar La Liga har shekarar 2021.

  Dan shekara 23 din ya buga wa Sevilla wasa tun daga farkon lokaci sau 129, kuma ya taimaka mata lashe gasar Europa sau biyu a shekarar 2015 da ta 2016.

  Rico
 11. Everton za ta sallami Gareth Barry

  Kociyan Everton, Ronald Koeman, ya ce shoi ba zai hana dan wasan tsakiya Gareth Barry, mai shekara 36, idan yana son tafiya a lokacin bazararnan, in ji Liverpool Echo.

  gareth barry
 12. Shin Coutinho zai koma Barca a wannan makon?

  Mundo Deportivo ta ruwato cewar Barcelona ta shirya domin yin shelar sayan Paulinho da Philippe Coutinho ranar Alhamis.

  Shin magoya bayan Liverpool sun shirya wa wannan rashin da bisa ga dukkan alamu ba shi da makawa?

  Coutinho
 13. Newcastle ta kusa sayan Joselu daga Stoke City

  Newcastle ta kusa kammala sayan dan wasan gaba na Spaniya Joselu daga Stoke kan kudin da aka ce ya kai fam miliyan 5.

  Tsohon dan wasan gaban Real Madrid ya koma Potters a shekarar 2015, amman ya kasa tabuka komai a kulob din. Ya koma Deportivo La Coruna ne a kakar 2016-2017.

  Joselu
 14. Barca za ta sayi Paulinho

  Barcelona ta cimma yarjejeniyar sayan dan wasan Brazil kuma tsohon dan wasan tsakiyar Tottenham Paulinho daga kungiyar kwallon kafa ta Guangzhou Evergrande da ke China kan kudi fam miliyan 36.4.

  Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke sayan wani dan wasa tun lokacin da ta sayar da Neymar ga PSG kan kudi fam miliyan 200.

  Paulinho, wanda a yanzu yana da shekara 29, ya koma Tottenham ne kan kudi fam miliyan 17 daga Corinthians a shekarar 2013 sannan ya koma China bayan shekara biyu.

  Za a yi masa gwaje-gwaje a Spaniya ranar Alhamis domin a kammala cinikinsa a ranar.

  Paulinho
 15. Liverpool na tunanin maye gurbin Coutinho da Insigne

  Kociyan Liverpool yana tunanin maye gurbin Philippe Coutinho da dan wasan gaban Napoli, Lorenzo Insigne, mai shekara 26, yayin da Barcelona ke zawarcin Coutinho, in ji, Express.

  Lorenzo Insigne
 16. Tottenham ka iya matsa kaimi kan zawarcin Keita Balde

  Tottenham za ta iya matsa kaimi wajen zawarcin dan wasan gaban Lazio, Keita Balde, mai shekara 22, bayan ba a saka shi cikin jerin 'yan wasan kungiyar da za su taka leda a gasar Supercoppa Italiana, in ji Mirror.

  Keita Balde
 17. Dan wasan PSG ya ki tafiya Fiorentina

  Dan wasan gefe na Paris St-Germain, Jese Rodriguez,mai shekara 24, ya yi watsi da tafiya Fiorentina kan aro, kuma a yanzu haka ya shirya domin komawa Stoke a wata yarjejeniya ta wucen-gadi, in ji Sun.

  Jese Rodriguez
 18. Chelsea na bukatar karin 'yan wasa -Cesar Azpilicueta

  Dan wasan Chelsea, Cesar Azpilicueta, mai shekara 27, yana tunanin cewar Chelsea na bukatar sayankarin 'yan wasa kafin a rufe damar cinikin 'yan wasa, in jiEvening Standard.

  Cesar Azpilicueta
 19. Juventus na son Naby Keita

  Jagoran Juventus, Beppe Marotta, ya ce kungiyarsa na sha'awar sayan dan wasan RN Leipzig wanda Liverpool ke nema, Naby Keita, dan shekara 22, in ji La Gazzetta dello Sport.

  Naby Keita
 20. Coutinho ba zai buga wa Liverpool wasan Hoffenheim ba

  Dan wasan tsakiyar Brazil, Philippe Coutinho, ba ya cikin 'yan wasan Liverpool da za su taka leda a wasan neman shiga gasar zakaraun Turai inda kulob din zai fafata da Hoffenheim a ranar Talata.

  Ba za mu iya tabbatar da cewa ya nemi kada a saka shi a wasan ne da kanshi.

  Ga jerin 'yan wasan da za su taka wa Liperool leda a wasan: Alexander-Arnold, Moreno, Lovren, Milner, Wijnaldum, Henderson, Can, Mane, Salah, Firmino, Kent, Solanke, Origi, Gomez, Klavan, Flanagan, Robertson, Matip, Grujic, Mignolet, Karius, Ward.

  Coutinho