Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Dangote zai kori Wenger
 2. Tottenham za ta taya Suarez
 3. Man Utd ta fasa zawarcin Rose
 4. Napoli ta yi watsi da tayin Barcelona

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Wenger ya ce za a iya sayar da Sanchez da Chamberlain

  Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya yarda cewar za a iya sayar da Sanchez da Oxlade-Chamberlain a kasuwar lokacin bazara, in ji jaridar Daily Star.

  Chamberlain
 2. Suarez zai kwashe mako biyar bai yi wasa ba

  Dan wasan gaban Barcelona, Luis Suarez, ba zai buga wasa na sati hudu ko biyar ba saboda ciwon da ya ji a guiwa, in ji hukumar kwallon kafa ta Uruguay.

  Tsohon dan wasan Liverpool din ya ji ciwon ne a lokacin da Barca take karawa da Real Madrid a gasar Super Cup ranar Laraba.

  Ba zai buga wasannin da Uruguay za ta fafata da Argentina da kuma Paraguy ba a ranar 31 ga watan Agusta da ranar 5 ga watan Satumba.

  Kazalika, ba zai buga wasannin da Barcelona za ta kara da Real Betis da Alaves da Espanyol da kuma Getafe ba.

  Suarez
 3. Muna da karfin guiwa kan karawarmu da Man Utd -Swansea

  Kocin Swansea, Paul Clement, ya ce kungiyarsa za ta tunkari wasan da za ta fafata da Manchester United ranar Asabar ne da karfin guiwa domin tarihin karawarsu ya nuna cewa Swansea ba ta da fargaba.

  Swansea
 4. Coutinho ba zai yi wasa a wannan makon ba -Klopp

  Kocin Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce Philippe Coutinho ba zai buga wa Reds wasan karshen mako ba.

  Da yake bayani a ranar Alhamis, kocin ya ce yana tunanin ciwon baya ne zai hana dan wasan taka leda.

  Ya kara da cewar Daniel Sturridge zai taka leda a karshen mako.

  Daniel Sturridge
  Image caption: Amman kocin ya ce Daniel Sturridge zai yi wasa.
 5. Kocin mata: 'Yar Najeriya na iya yin zarra

  Kociyar tawagar matan Najeriya, Super Falcons, Florence Omogbemi, za ta iya cin lambar yabon hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta wanda ya fi kwarewa a kociyan mata.

  Sunanta na cikin sunayen mutum 10 da hukumar ta fitar ranar Alhamis.

  Sunanta ya samu shiga cikin jerin sunayen ne, domin ta ci kofin kwallon mata na Afirka a lokacin da take taka leda da kuma bayan ta zama kociya.

  View more on twitter
 6. 'Barca ta yi wa Real Madrid kadan'

  Dan wasan bayan Barcelona, Gerard Pique, ya ce Real Madrid ta fi karfinsa a karon farko bayan Madrid ta lallasa Barca a gasar Super Cup.

  Zakarun La Liga da na Turai sun ci wasan da aka yi a daren Laraba 2-0, lamarin da ya sa jumullar sakamakon wasanni biyun da kungiyoyin suka yi ya zama 5-1 .

  Pique, mai shekara 30, wanda ya kai shekara tara a Barca, ya ce: "Wannan lokaci ne mara kyau ga kungiyarmu."

  Barca
 7. Man Utd za ta nada Ibrahimovic koci?

  Manchester United ta shirya domin ta bai wa dan wasan gaba Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 35, aikin koci a wani mataki a kokarin kulob din na sabunta yarjejeniyar dan wasan, in ji Independent.

  Ibrahimovic
 8. Tottenham za ta taya Suarez

  Tottenham tana shirin taya Denis Suarez na Barcelona kan kudi fam miliyan 27. Da alamar cewa dan shekara 23 din na kan hanyarsa ta zuwa Napoli, in ji Metro, wadda ta ruiwato daga Mundo Deportivo.

  Denis Suarez
 9. Me ya sa Chelsea ta fasa sayen dan PSG?

  Chelsea ta janye daga yarjejeniyar sayen dan wasan tsakiyar Paris St-Germain, Grzegorz Krychowiak, mai shekara 27, domin PSG ta shagaltu da tarbar Neymar daga Barcelona kamar yadda Daily Express ta ruwato daga L'Equipe

  Grzegorz Krychowiak
 10. Zan kori Arsene Wenger - Dangote

  Attajirin dan kasuwar nan na Najeriya, Aliko Dangote, ya ce abin da zai fara yi da zarar ya sayi Arsenal shi ne ya kori kocin kulob din, Arsene Wenger.

  Dangote ya ce zai taya kulob din da zarar ya kammala matatar man da yake ginawa a Legas, in ji Bloomberg.

  Dangote dai ya dade da kasancewa mai goyon bayan kulob din tun shekarun 1980.

  Wenger
 11. Juventus za ta sayi Blaise Matuidi

  Juventus ta cimma yarjejeniyar biyan fam miliyan 18.2 kan dan wasan tsakiyar PSG, Blaise Matuidi, mai shekara 30. Dan Faransan zai kasance dan wasa na 10 da kulob din na kungiyar da ke gasar Serie A ta saya a wannan bazarar, in ji jridar Guardian.

  Matuidi
 12. Gabriel zai koma Valencia daga Arsenal

  Dan wasan bayan Brazili, Gabriel, ya shirya domin komawa Valencia daga Arsenal a wata yarjejeniyar fam miliyan10. Gabriel, mai shekara 26, ya koma Gunners ne a wata yarjejeniyar kudi fam miliyan 15 a watan Janairun shekarar 2015, in ji jaridar Daily Mirror.

  Gabriel
 13. Manchester City ta taya Alexis Sanchez

  Manchester City ta taya dan wasan gaban Arsenal Alexis Sanchez kan kudi fam miliyan 60, yayin da Real Madrid take sha'awar dan wasan Chilen mai shekara 28, Don Balon, via Daily Star.

  Arsenal ta riga ta yi watsi da tayin fam miliyan 45 da City ta yi kan Sanchez, kamar yadda Daily Express ta ruwaito daga El Mercurio, wadda ta ambato wakilin dan wasan Fernando Felicevich yana tabbatar da hakan.

  Sanchez
 14. Barcelona ta kusa kammala sayan Dembele?

  Jaridar Daily Express ta ce Barcelona ta kusa kammala da sayan Ousmane Dembele, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund bayan da hoton dan wasan yana kwashe jakunkunansa ya bayyana.

  Dembele
 15. Barca ta taya Coutinho

  Barcelona ta ce za ta bai wa Liverpool fam miliyan 118 kan dan wasan tsakiyar Brazil mai shekara 25 Philippe Coutinho, in ji Goal.com.

  Coutinho
 16. Chelsea ba ta hakura da sayan Alex Sandro ba

  Chelsea ba ta hakura da son sayen Alex Sandro, mai shekara 26, daga Juventus ba, amman tana jiran dan wasan Brazil din zai mika takardar neman sauya kulob, in ji jaridar Evening Standard.

  Amman jaridar Daily Star ta ruwaito daga Calciomercato cewar Juventus ta yi watsi da sabon tayin fam miliyan 73 da Blues ta yi kan Sandro.

  Alex Sandro
 17. Man Utd ta fasa zawarcin Rose

  Manchester United ta fasa zawarcin Rose,duk da cewar dan wasan Ingilan ya matsu da son komawa Old Trafford, in ji jaridar Daily Star.

  Rose