Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Rayyan

time_stated_uk

 1. A sha ruwa lafiya

  Ana muka kawo karshen labaran da muke kawo muku a wannan shafi, sai an jima, mun gode.

 2. Hotunan muhimman wuraren da ake gudanar da aikin Hajji

  Za ku ina samun cikakkun hotunan wuraren idan kuka latsa nan.

  Wannan shi ne dutesn Hajrul Aswad da ke jikin Ka'aba wanda ake so Musulmin da ya samu iko ya sumbace shi da zarar ya shiga harabar masallacin gabanin ya fara dawafi.
  Image caption: Wannan shi ne dutesn Hajrul Aswad da ke jikin Ka'aba wanda ake so duk Musulmi ya sumbace shi da zarar ya shiga harabar masallacin gabanin ya fara dawafi.
  Muna nan ne ainihin wajen da alhazai ke tafiya a ranar 8 ga watan Zul Hijjah don gudanar da aikin Hajji inda su kan shafe tsawon kwana hudu zuwa biyar. Waje mai matukar girma da aka gina tantuna don zaman alhazai.
  Image caption: Muna nan ne ainihin wajen da alhazai ke tafiya a ranar 8 ga watan Zul Hijjah don gudanar da aikin Hajji inda su kan shafe tsawon kwana hudu zuwa biyar. Waje mai matukar girma da aka gina tantuna don zaman alhazai.
  Wajen jifan Shaidan da aka fi sani da jamrah na daga cikin wuraren ibada masu muhimmanci lokacin aikin hajji.
  Image caption: Wajen jifan Shaidan da aka fi sani da jamrah na daga cikin wuraren ibada masu muhimmanci lokacin aikin hajji.
 3. Wata hajiya 'yar Nigeria ta haihu a Madinah

  Wata hajiya 'yar Najeriya ta haihu a birnin Madina ranar Laraba, kamar yadda Shugaban hukumar alhazan kasar NAHCON Abdullahi Mukhtar ya tabbatar wa BBC.

  Mahajjaciyar ta fito ne daga jihar Kogi, amma hukumar ba ta bayyana sunanta ba da kuma abin da ta haifa.

  Wadansu mahajjata mata
 4. Jami'an tsaro suna shirin ko ta kwana a Muzdalifah

  Jami'an tsaro suna cikin shirin ko ta kwana a Muzdalifah wurin da mahajjata za su yada zango idan suka baro filin Arafa.

  Hoto daga Saudi Gazette

  Jami'an tsaro
 5. Kamfanin DHL ya raba wa mahajjata 200,000 lema kyauta

  Kamfanin aikewa da sakonni na DHL reshen kasar Saudiyya ya raba wa mahajjata fiye da 200,000 lema kyauta, don su yi amfani da su yayin aikin hajjin bana.

  Adadin ya ninka wanda ya bayar a bara.

  A raba lemomin ne a Mina da kuma filin Arafat.

  Mahajjata da suka samu kyautar leman DHL
 6. Mahajjata sun isa masallacin Nimrah

  Mahajjata sun isa masallacin Nimrah da ke Arafat, inda Shekih Emad Baqree zai jagorancin sallar Azahar da La'asar.

  Hotuna daga Saudi Gazette

  Masallacin Nimrah
  Mahajjata a masallacin Nimrah
 7. Yadda ake sanyaya Jamarat

  Yadda ake amfani da na'urar zamani wajen sanyaya Jamarat wurin da za a yi jifan shedan gobe Juma'a.

  Bidiyo daga jaridar Saudi Gazette

  Video content

  Video caption: Yadda ake sanyaya Jamarat inda ake jifan shedan
 8. Kalli bidiyon filin Arafa da aka dauka ta sama

  Bidiyon filin Arafa wanda aka dauka ta jirgin sama yayin da mahajjata suke ci gaba da tsayuwar Arafa yau Alhamis.

  Bidiyo daga jaridar Saudi Gazette

  Video content

  Video caption: Bidiyon mahajjatan masu tsayuwar Arafa da aka dauka ta sama
 9. Abin da ake so wanda bai je hajji ba ya yi

  Ana so wadanda ba su samu damar zuwa aikin hajji ba su yi azumi a ranar Arafa.

  Hakazalika su ciyar da abinci, kuma su yi sadaka.

  Sannan su yi wa Allah godiya, su yi wa 'ya'ya da iyaye addu'a da sauran jama'a baki daya, kamar yadda Sheikh Tijjani Bala Kalarawi ya shaida wa BBC.

  Wata wadda ba ta je aikin hajji ba
 10. Abin da ake so mahajjata su yi a yau

  Wani malamin addini a Najeriya wanda yanzu haka yana kasar Saudiyya, Ustaz Tijjani Bala Kalarawi, ya shaida wa BBC irin abubuwan da ya kamata mahajja su yi a wannan rana:

  Ana so mahajjaci ya rika yin kabbara yana cewa Labbaikallahumma labbaika la sharika labbaika.

  Ya yawaita yin istigifari da salatin manzon Allah (SAW) da kuma tasbihi.

  Ba a so mahajjaci ya yi azumi a wannan rana.

  Har ila yau ba a so gari ya waye mahajjaci bai yi tsayuwar Arafa ba.

  Mahajjata
 11. Ana sauya rigar dakin Ka'abah

  A yayin da alhazai ke tsayuwar arfah a Makkah, ana can ana sauya rigar dakin Ka'abah da ake kira da Kiswah wanda ake yi duk shekara a daidai wannan lokaci. http://saudigazette.com.sa/article/516322/SAUDI-ARABIA/Holy-Kaaba

  Hotuna daga Saudi Gazette

  Ka'aba
  Ka'aba
  Ka'aba
  Ka'aba
 12. Alhazan Nigeria bakwai sun rasu

  Alhazan Nigeria bakwai sun rasu a Saudiyya, kamar yadda hukumar alhazan kasar ta bayyana.

  Hukumar ta ce mahajjatan sun fito ne daga jihohin Kwara, da Katsina da Kogi da kuma Kaduna.

  Sai dai hukumar ba ta yi karin haske ba kan abin da ya yi ajalinsu da kuma sunayensu ba.

  Akalla akwai 'yan kasar kimanin 90,000 da suka halarci aikin hajjin bana.

  mahajjata
 13. An tsaurara matakan tsaro a Makkah

  Dubban jami'an tsaro ne suke sintiri yayin da mahajjata suke tsayuwa a filin Arafat.

  Akwai babura da motoci da kuma jiragen sama masu saukar ungulu wadanda ake amfani da su wajen tafiyar da aikin samar da tsaro.

  Rahotanni sun ce al'amura na tafiyaa cikin kwanciyar hankali.

  Jami'an tsaro Saudiyya
 14. Kun san wanda zai ja sallah a filin Arafa?

  Ana sa ran Sheikh Sa'ad Shathri ne zai gabatar da Khuduba a Masallacin An Namirah, da ke Arafat. Yayin da shi kuma Sheikh Emad Baqree (ladanin masallacin Al Haram) shi zai kira sallah, inda za a hada sallolin Azahar da La'asar.

  Sheikh Sa'ad Shathri da Sheikh Emad Baqree
 15. Mahajjata sun fara tsayuwar Arafa

  Kimanin mahajjata miliyan biyu ne suka fara tsayuwar Arfa, wani ginshiki a aikin hajji a ranar Alhamis.

  Mahajjatan sun nufi dutsen Arfa ne bayan sun kwana a Mina.

  Za su kwashe yinin yau ne a filin Arfa inda za su rika yin addu'o'i da karatun Alkur'ani.

  Wani mahajjati
 16. Barka da Hantsi

  Jama'a barkarmu da saduwa a wannan shafi wanda za mu kawo muku labarai kan al'amuran da suke faruwa a filin Arafa, wurin da Musulmi kimanin miliyan biyu suke tsayuwa a ci gaba da aikin hajjin bana.