Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Wenger bai ji dadin fenaretin da aka bai wa Chelsea ba
  2. Mourinho zai tsaya ne ko zai tafi?

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe

Karshen labaran kasuwar musayar 'yan wasan kenan a yau. Sai gobe.

Daya zai tafi, daya zai tsaya a Everton ne?

Da alama Everton ta kusa sayen Cenk Tosun, amma me wannan ke nufi ga takwaransa a wasan gaba Sandro? Sam Allardyce ya ce: "kawo yanzu dai ba a taya Sandro ba. Idan wani dan wasa na son tafiya, dole sai farashin ya yi mana."

Sandro has one goal in 15 games for Everton this season
Getty Images
Sandro has one goal in 15 games for Everton this season

Dalilin da ya sa CAF ta soke kyautar gwarzon dan wasan da ke Afirka

Shugaban hukumar CAF Ahmad ya fuskanci wasu tambayoyi masu tsauri game da dalilin da ya sa hukumar ta soke kyautar gwarzon dan wasa da ke taka leda a Afirka a wani taron manema labarai a Ghana. An fitar da sunayen masu takarar gwarzon an wasan Afirka a karshen shekarar da ta gabata sai dai kuma CAF ta soke kyautar. Dalilin da Ahmad ya bayar shi ne CAF na son bunkasa kwallon kafa don ta yi fice a Afirka kuma kamata ya yi kyautar gwarzon dan wasa ta kasance daya tilo domin a kara gogayya tsakanin 'yan wasan Afirka.

Shugaban CAF, Ahmad
Getty Images

Mourinho na tattaunawa da United

Manchester United tana tattauna sabuwar yarjejeniya da koci Jose Mourinho. Yarjejeniyar kocin mai shekara 54 ba zai kare ba sai shekarar 2019, kuma United tana zabin tsawaita yarjejeniyar. Sai dai kuma, an ce ba a yi cikakken tattaunawa ba tsakanin mataimakin shugaban United da kuma masu bayar wa Ed Woodward shawara kan tsawaita zamansa a Old Trafford. Labarin na zuwa a lokacin da ake rade-radin cewar Mourinho na tunanin barin kungiyar kwallon kafar wannan lokacin bazarar.

Mourinho
Getty Images

Everton na da tantama a kan Keane

Sam Allardyce ya ce dan wasan baya Michael Keane zai iya zama a benci a wasan da za su fafata a Anfield. Keane na bukatar dinki a sawunsa bayan Everton ta sha kaye a hannun Manchester United kuma ba ya son ciwon da ya ji ya ta'azzara. "Ina ganin akwai hatsari tattare da saka shi, amma kowa ya shirya," in ji Allardyce.

Keane
Getty Images

Mourinho yana jawabi

Yarjejeniyar Mourinho da Manchester United za ta kare cikin shekarar 2019
Getty Images
Yarjejeniyar Mourinho da Manchester United za ta kare cikin shekarar 2019

Kocin Manchester United, Jose Mourinho, yana jawabi ga manema labarai a lokacin da ake rade-radin cewa zai bar Manchester United.

CAF ta gode wa Liverpool kan Mane da Salah

Mohamed Salah na cikin wadanda suka fiu zura kwallaye a raga a gasar Firimiya
Getty Images
Mohamed Salah na cikin wadanda suka fiu zura kwallaye a raga a gasar Firimiya

Shugaban hukumar CAF Ahmad gode wa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kan barin biyu daga cikin wadanda suke takarar zakaran kwallon kafa na nahiyar su kasance a Ghana.

Yana magana ne a kan dan wasan Senegal, Sadio Mane, da kuma dan wasan Masar Mohamed Salah - wadanda za su kasance a Accra duk da cewa suna da wasan da za su buga kasa da sa'o'i 24 a Ingila.

Wani jirgi na musamman domin su zai mayar da su. Shugaban ya nuna godiyar ne a wani taron manema labarai a Accra, Ghana.

An tsayar da yarjejeniya kan Cenk Tosun - Allardyce

Sam Allardyce ya fara jawabi kan wasan gasar cin kofin FA da za a yi ranar Juma'a kuma ya tabbatar da cewar Everton ta kusa sayen dan wasan Turkiyyar. "Mun cimma yarjejeniya kuma yanzu muna matakin cika sharudan da dan wasan ya gindaya ne. Muna fatan za mu iya yi masa rijista a kan lokaci saboda ya buga mana wasa a gasar cin kofin FA," in ji Allardyce. Yaya kuke ganin shigowar wannan dan wasan? Magoya bayan Liverpool, wannan ya tayar muku da hankali kuwa?

Sam
Getty Images

Cenk Tosun ya kusa komawa Everton ne?

Duk da cewa an dade ana magana kan wannan batun, da alamar za a gano bakin zaren. An ambato shugaban kungiyar kwallon kafa ta Besiktas Fikret Orman yana cewa: "Cenk na son komawa Everton. Muna son mu taka tamu rawar kuma muna neman wanda zai maye gurbinsa. "Ba a cimma yarjejeniya ba dai kawo yanzu, amma mun daidaita game da farashin. Mun kusa kai wa karshen lamarin. Za a kammala yarjejeniyar a karshen mako." An yi imanin cewar kudin da za a sayi dan wasan zai kai £27m. Magoya bayan Everton, ya kuka ji da wannan?

Cenk
Getty Images

An kori Sinisa daga Torino

Sinisa daga Torino
Getty Images

Torino ta kori koci Sinisa Mihajlovic bayan kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta cire ta daga gasar kofin Italiya da ci 2-0. Sinisa zai bar kungiyar kwallon kafar a mataki na 10 a gasar Serie A inda ta lashe wasanni 19 a wannan kakar, ciki har da canjaras shida a wasansu takwas na baya bayan nan a gasar Seria A din. An ganin tsohon kocin Watford Walter Mazzarri ne zai maye gurbinsa.

Shin Robbie Keane zai koma Wolves?

Kamfanin dillancin labaran Press Association Sport ya ba da rahoton cewa Wolves tana son ta dawo da Robbie Keane kungiyar kwallon kafar, shekara 21 bayan ya fara wasa a Molineux . Keane ya fara wasa ne a Wolves kafin ya murza leda wa kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Tottenham da Liverpool da Celtic da kuma LA Galaxy. Yana taka leda ne ATK ta India.

Robbie
Getty Images

Ko Theo Walcott zai bar Arsenal?

Jaridar Daily Express na ikirarin cewar kungiyoyin kwallon kafa hudu - ciki har West Ham da Southampton - suna son sayen dan wasan Arsenal Theo Walcott.

Daily Express
Daily Express

Ana yi wa Morgan gwaji a Celtic

Ana yi wa dan wasan gefen St Mirren, Lewis Morgan, gwaji a Celtic. Ana tsammanin zakarun Scotland din su biya kimanin £300,000 domin sayen dan wasan mai shekara 21. Dan wasan tawagar 'yan kasar da shekara 21 na Scotland din zai kasance dan wasa na biyu da Celtic za ta saya bayan zuwan dan wasan Marvin Compper daga RB Leipzig.

Morgan
Getty Images

Costa ya zura kwallonsa ta farko a Atletico Madrid

Tsohon dan wasan gaban Chelsea Diego Costa ya ci kwallo bayan minti biyar da fara wasa bayan ya sake fara taka wa Atletico leda a daren Laraba. Shin zai iya taimaka wa Chelsea a wasanta da Arsenal kuwa? Kuna ganin zai iya cin daya daga cikin damarmakin kwallo da Alvaro Morata ya barar?

Diego Costa ya bar Chelse ne sannan ya koma Atletico
Getty Images
Diego Costa ya bar Chelse ne sannan ya koma Atletico

Mirror ta jinjina wa Hector Bellrin

The Mirror
Getty Images
The Mirror

Jaridar Mirror ta ce Hector Bellerin ne ya ceci Arsenal kuma ta yi ikirarin cewar Liverpool na son sayen dan wasan Monaco Thomas Lemar domin ya maye gurbin Philippe Coutinho. Magoya bayan Liverpool, za ku ji dadin wannan labarin?

Jose Mourinho zai tsaya ne ko zai tafi?

Mourinho zai tsaya ne ko zai tafi?
Getty Images
Mourinho zai tsaya ne ko zai tafi?

Wannan dai ya dangata ne da jaridar da kake karantawa a wannan safiya. Jaridar Daily Mail ta bayar da rahoton fargabar cewa Jose Mourinho ba zai kasance a kulob din ba a kaka mai zuwa, yayin da jaridar Daily Telegraph ta yi ikirarin cewa United ta tattauna da shi kan tsawaita kwataraginsa. Magoya bayan United ya kuka ji?

Ashley Cole ya tsawaita kwantaraginsa a LA Galaxy

Tsohon mai tsaron gidan Ingila Ashley Cole ya sanya hannun kan kwantaragin karin shekara daya a kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Galaxy.

Cole, mai shekara 37, ya koma Galaxy ne a watan Janairun 2016 kuma ya buga wasa 55 a kakar wasa biyu.

Tsohon dan wasa na Arsenal da Chelsea ya buga wa Ingila wasa 107 sai dai ya daina yin tamaular duniya bayan an ki sanya shi cikin tawagar da ta buga gasar cin Kofin Duniya ta 2014.

Cole ya buga wa Los Angeles Galaxy wasa 55
Getty Images
Cole ya buga wa Los Angeles Galaxy wasa 55

Arsene Wenger bai ji dadin fanaretin da aka bai wa Chelsea ba

Arsene Wenger
Getty Images

Wasa ne da aka samu damarmakin cin kwallaye 33 da wani fenareti mai cike da ce-ce-kuce. Kocin Arsenal, Arsene Wenger, bai ji dadin fanaretin da aka bai wa Chelsea ba. Ya shaida wa Sky Sports cewa: "Abin takaici a gare mu shi ne hukuncin da aka yanke (na fanareti)."