Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

  1. Naby Keita zai koma Liverpool kuwa?
  2. Everton ma tana neman Theo Walcott
  3. Dan wasan tsakiyar Real Madrid ya ce zai tafi

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

Sai gobe!

Karshen labaran kasuwar musayar 'yan wasan kenan. Sai gobe!

Ina son West Ham ta yi wasa kamar Chelsea

Moyes
Getty Images

Kocin West Ham, David Moyes, ya ce yana son kungiyar kwallon kafarsa ta taka leda "kamar Tottenham, kamar Chelsea" in har ya ci gaba da kasancewa kocin kungiyar bayan wannan kakar.

Huddersfield za ta sayi dan wasan tsakiyar Norwich City

Kungiyar kwallon kafa ta Huddersfield Town za ta sayi dan wasan tsakiyar, Alex Pritchard.

Dan wasan mai shekara 24 ya koma Canaries ne kan kudi fam miliyan 8 daga Tottenham Hotspur a watan Agustan 2016 kuma ya ci kwallaye bakwai a wasanni 38.

Alex Pritchard.
Getty Images

Mourinho zai kai Kluivert Ingila

Kluivert
Getty Images

Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya nemi dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Ajax, Justin Kluivert, mai shekara 18, ya tsaya a kungiyar kwallon kafar da ke Netherlands a wannan watan domin yana fatan kawo shi Ingila a lokacin bazara,in ji Sport.

Tottenham za ta rubanya wa Dele albashi domin Real Madrid

Dele Alli
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham za ta rubanya wa dan wasan tsakiyar Ingila, Dele Alli, mai shekara 21 albashi domin kawar da saha'awar sayensa da Real Madrid da Paris ST-Germain ke yi, in ji Mail.

Liverpool za ta bai wa Firmino wani kwantiragi

Firmino
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana shirin bai wa dan wasan gaban Brazil, Roberto Firmino, mai shekara 26, wani kwantiragin da zai sa ya karasa murza ledarsa a kulob din, in ji Telegraph.

Man United za ta bari Mkhitaryan ya koma Borussia

Henrik Mkhitaryan
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta iya bari Henrik Mkhitaryan, mai shekara 28, ya koma Borussian Dortmunda cikin wannan watan idan za a iya cimma matsayar da bangarorin biyu suka amince da shi. Ana ganin albashin da dan Ameniyan ke karba ka iya kasancewa wani kalubale ga cimma yarjejeniya, in ji Independent.

Barcelona za ta sayi dan Colombia daga Palmeiras

Yerry Mina ya ci kwallaye 9 cikin wasanni 49 wa kungiyar kwallon kafa da ke kasar Brazil
Getty Images
Yerry Mina ya ci kwallaye 9 cikin wasanni 49 wa kungiyar kwallon kafa da ke kasar Brazil

Barcelona ta shirya domin ta sayi dan wasan bayan kungiyar kwallon kafa ta Palmiras, Yerry Mina, kan kudi fam miliyan 10.44.

Kungiyar da ke saman teburin La Liga ta bayar da sanarwar cewar dan wasan mai shekara 23 ya amince da yarjejeniyar shekara biyar da rabi.

Crystal Palace za ta sayi dan Senegal

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace za ta iya kammala sayen dan kasar Senegal Diafra Sakho, mai shekara 28, daga West Ham zuwa karshen mako, in ji Daily Mirror.

Sakho
Getty Images

Everton ma tana son Theo Walcott

Theo Walcott
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ma ta na son sayen dan wasan gaban Arsenal, Theo Walcott, mai shekara 28.

Kulob din dan Ingilan na farko Southamton shi ma yana son dan Ingilan yayin da Arsenal ta shirya domin sanar da fam miliyan 30 a matsayin farashinsa, in ji Liverpool Echo.

Dole sai Man United ta biya miliyan 27 kan Leander

Dole Manchester United ta biya har fam miliyan 27 in har tana son sayen dan kasar Belgium mai shekara 22 Leander Dendoncker daga Anderlecht a watan Janairu, in ji Manchester Evening News.

leander
Getty Images

Tottenham ta fara tattaunawa da Dele Alli

Dele Alli
Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara tattaunawa da Dele Alli. An ce kulob din yana da kwarin gwiwar cewa zai cimma sabuwar yarjejeniya da dan wasan Ingilan mai shekara 21, in ji Daily Mirror.

Liverpool za ta iya kuwa?

Ana raderadin cewar Jurgen Klopp zai iya biyan RB Leizig karin fam miliyan 13 domin sayen Naby Keita a wannan watan.

Shin Klopp zai iya biyan wannan kudin kuwa?

Naby Keita
Getty Images

Valencia za ta sayi dan wasan Arsenal

Kungiyar kwallon kafa ta Valencia ta shirya domin sayen dan wasan tsakiyar Faransa, Francis Coquelin daga Arsenal, kamar yadda Arsene Wenger ya tabbatar.

Dan wasan mai shekara 26 zai tafi Spaniya kan wata yarjejeniyar da ake ganin za ta kai fam miliyan 12.

Francis Coquelin
Getty Images

Dan wasan Real Madrid ya ce zai tafi

Dani Ceballos
Getty Images

Dan wasan tsakiyar Real Madrid, Dani Ceballos, ya sanar da kulob din cewar yana son ya barta yayin da ake bayar da rahoton cewar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana son sayen dan kasar Spaniyan mai shekara 21, in ji Diario Gol.

Wenger ya ce yana son Sanchez ya tsaya da Gunners

Sanchez bai auna mai tsaron gidan Chelsea ba bayan ya shiga wasan
Getty Images
Sanchez bai auna mai tsaron gidan Chelsea ba bayan ya shiga wasan

Kocin Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ajiye Alexis Sanchez a benci da farkon wasan Arsenal da Chelsea da aka yi ranar Laraba ba shi da wata alaka da raderadin tafiyar dan wasan da ake yi, kuma ya jaddada bukatarsa ta cigaba da rike dan wasan gaban a kulob din.