Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe!

  Karshen labarai da sharhin kasuwar musayar 'yan wasan kenan. Sai gobe.

 2. Dan wasan Liverpool ya koma wasan aro a Cardiff

  Dan wasan tsakiyar Liverpool, Marko Grujic, ya koma buga wasan aro a kungiyar kwallon kafa ta Cardiff da ke kan gaba a gasar Championship zuwa karshen wannan kakar.

  Amma dan kasar Sabiyar mai shekara 21 ya sha alwashin amfani da damar wasan aron ya samu ya shiga cikin 'yan wasan da Jurgen Klopp zai yi amfani da su a kaka mai zuwa.

  Marko Grujic
 3. Otamendi ya tsawaita zamansa a Man City

  Nicolas Otamendi ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejejniyar da za ta sa ya ci gaba da zama a Etihad har zuwa shekarar 2022.

  Dan wasan bayan na kasar Ajantina ya buga wasanni 22 cikin 23 da Man City ta buga a gasar Firimiyar bana kuma ya ci wa City kwallaye biyar a wannan kakar.

  Otamendi
 4. Dan wasan da Arsenal take so na fuskantar ladabtarwa

  Dan wasan da Arsenal take hako, Malcom, na fuskantar ladabtarwa a Bordeaux.

  An nuna dan wasan gaban mai shekara 20 tare da takwarorinsa Cafu da Otavio a wani bidiyon da aka wallafa a shafukan sada zumunta suna dariya bayan sun sha kaye daga kungiyar kwallon kafa ta Caen ranar Talata.

  Caen
 5. Barca ta yi watsi da tayin Inter Milan kan Rafinha

  Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta yi watsi da tayin da Inter Milan ta yi kan dan wasanta dan asalin Brazil, Rafinha, kan kudi fam miliyan 22.2.

  Barca dai tana neman fam miliyan 35.5 ne akan dan wasan, in ji Mundo Depotivo.

  Rafinha
 6. Mourinho ya kusa sabunta kwantiraginsa da Man United

  Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kusa cimma yarjejeniya da koci Jose Mourinho kan sabunta kwatiraginsa.

  Nan ba da jimawa ba ne Mourinho zai yarda ya zauna a Old Trafford bayan shekarar 2019, lokacin da kwantiraginsa na yanzu zai kare.

  Mourinho
 7. Napoli na son mai tsaron gidan Liverpool

  Kungiyar kwallon kafa ta Napoli da ke murza leda a gasar Seria A tana son sayen mai tsaron gidan Liverpool, Simon Mignolet, mai shekara 29, in ji Sky Italia.

  Simon Mignolet
 8. Borussia za ta bar Aubameyang ya koma Arsenal

  Kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta shirya domin kyale dan wasan gaban Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 28, ya koma Arsenal, kuma tana son maye gurbinsa da dan wasan gaban Chelsea da Belgium, Michy Bashuayi, mai shekara 24, in ji Bild.

  Aubamenyang
 9. Chelsea na son dan wasan Roma

  Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi tambaya game da dan wasan bayan Roma da kasar Brazil, Emersom Palmieri, mai shekara 23, yayin da kungiyar ke fuskantar matsala kan kokarinta na sayen dan kasar Brazil da ke Juventus, Alex Sandro mai shekara 26, in ji Evening Standard.

  Da alama fa Chelsea tana neman karfafa kulob dinta a kasuwar musayar 'yan wasa
  Image caption: Da alama fa Chelsea tana neman karfafa kulob dinta a kasuwar musayar 'yan wasa
 10. Dan wasan da Liverpool ke so ya koma Bilbao

  Inaki Williams

  Dan wasan tsakiyar Spaniya, Inaki Williams, mai shekara 23, wanda Liverpool ta nuna sha'awar sayensa, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Athletic Bilbao.

  Kwantiragin zai kai shekarar 2025, in ji Sun.

 11. Arsenal za ta rage wa Wilshere albashi

  Wilshere

  Dole dan wasan tsakiyar Arsenal da Ingila, Jack Wilshere, mai shekara 26, wanda zai iya barin kungiyar a wannan lokacin bazarar, ya yarda a rage albashinsa da kashi 20 cikin 100 bayan an gwada lafiyarsa kafin a sabunta kwantiraginsa, in ji Sun.

 12. Me ya sa Chelsea ke neman dan wasan gaba?

  Ko Andy Carrol ne zai fitar da Antonio Conte daga farin cin kwallon da kungiyarsa ke fama da shi?
  Image caption: Ko Andy Carrol ne zai fitar da Antonio Conte daga farin cin kwallon da kungiyarsa ke fama da shi?

  A karon farko a tarihin kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, kungiyar ta yi canjaras ba ci ko daya a wasanni uku a jere cikin dukkan gasar da ta shiga.

  Tun da aka shiga wannan shekarar kungiyar ba ta yi nasara a ko wasa daya ba.

  Da alama wannan ne ya sa kungiyar take son sayen dan wasan gaba, Andy Carroll.

  A baya dai Alvaro Morata ya ci kwallaye shida cikin wasannin gasar Firmiya shida, amma ya kasa cin kwallo ko daya a wasanni biyar na baya bayan nan da ya buga wa Blues.

  Morata
 13. Aubameyang yana son ya koma Arsenal

  Aubameyang

  Dan wasan gaban kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 28, ya bukaci kungiyar kwallon kafar da yake murza wa leda, Borussian Dortmund, ta kyale shi ya koma Arsenal, in ji Mirror.

 14. Henrikh Mkhitaryan na son karin albashi

  Henrikh Mkhitaryan
  Image caption: Henrikh Mkhitaryan

  Dan wasan tsakiyar kasar Ameniya, Henrikh Mkhitaryan, mai shekara 28, yana son a kara masa albashi domin ya koma taka leda a Arsenal daga Manchester United, in ji Mirror.

 15. West Ham za ta saurari tayin £20m

  Kungiyar kwallon kafa ta West Ham za ta saurari tayin fam miliyan 20 kan cinikin Andy Carroll, in ji Sky Sports.

  carroll
 16. Chelsea ta tuntubi West Ham kan Carroll

  Carrol

  Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta tuntubi West Ham game da sayen dan wasan gaban Ingila mai shekara 29, Andy Carroll, in ji Telegraph.

 17. Walcott ya yi shekaru 12 da Arsenal

  Walcott ya ci wa Arsenal kwallaye 65 kuma ya taimaka wajen cin kwallaye 43. Da me magoya bayan Arsenal za su rinka tunawa da wannan dan wasan in ya bar kungiyar tasu?

 18. Mene ne jaridu ke cewa ne?

  Kelechi

  Bari mu ga abin da wasu jaridu ke cewa. Da alama hatsarin da cinikin kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ke ciki ya fi yadda jaridar Times take nunawa.

 19. Everton ta yarda da lafiyar Walcott

  Walcott

  Kafar Sky tana bayar da rahoton cewar Everton ta tabbatar da lafiyar Theo Walcott, kuma dan wasan ya cimma yarjejeniya da kungiyar ta Everton, wannan na nufin za mu fara ganin dan wasan cikin riga mai launin shudin nan gaba kadan. Magoya bayan Arsenal, ya kuke ji da wannan?

 20. Iheanacho ya kafa tarihi

  Dan wasan Najeriya, Kelechi Iheacaho, ya kafa tarihi na kasancewa dan wasan da aka fara tabbatar da kwallon da ya ci da taimakon mataimakin lafiri mai amfani da bidiyo (AVR) a karawar da kulob dinsa Leicester City ta yi da Fleetwood town a gasar FA ta Ingila.