Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. West Brom ka iya rasa Evans

  West Brom ka iya rasa keftin dinta, Jonny Evans, kan kudi fam miliyan 23 a lokacin bazara idan ba ta iya tsayawa cikin gasar Firimiya ba.

  An yi kiyasin cewa farashin Evans, mai shekara 30, ya kai fam miliyan 23 a hannun West Brom kuma Arsenal da Man City sun nuna suna sha'awar dan wasan.

  Jonny Evans
  Image caption: Jonny Evans
 2. Salah da Moreno za su buga wasan Liverpool

  salah

  Jaridar Liverpool Echota bayar da rahoton cewar Mohamed Salah da Alberto Moreno za su buga a fafatawar da kungiyar za ta yi da Swansea City a filin wasa na Liberty a daren Litinin.

  Rahoton ya kara da cewar Daniel Sturridge, wanda yake son komawa Sevilla, ba zai shiga cikin 'yan wasan Jurgen Klopp ba.

 3. Palace ta sayi dan Benfica

  Dan wasan tsakiyar Sweden, Erdal Rakip, ya koma Crystal Palace akan aro daga Benfica zuwa karshen kakar bana.

  Erdal Rakip
  Image caption: Erdal Rakip
 4. West Ham na son dan Lyon

  Clement Grenier
  Image caption: Clement Grenier

  Kocin West Ham, David Moyes, yana tattaunawa da dan wasan tsakiyar Lyon, Clement Grenier, in ji jaridar The Sun.

  Moyes ya tuntubi Grenier da kwantiragin shekara uku.

 5. Sturridge 'na son komawa Sevilla'

  Jaridar Daily Mail ta bayar da rahoton cewa dan wasan gaban Liverpool, Daniel Sturridge, ya nuna cewa shi zai so ya koma kungiyar gasar La Liga, Sevilla, kan aro a wannan watan.

  Sturridge, wanda damar murza ledansa ta ragu a karkashin Jurgen Klopp a wannan kakar, yana cikin 'yan wasan da Inter Milan take so.

  Dan wasan gaban Ingila da na Liverpool, Daniel Sturridge
  Image caption: Dan wasan gaban Ingila da na Liverpool, Daniel Sturridge
 6. Ana gwada lafiyar Henrikh Mkhitaryan a Arsenal

  Henrikh Mkhitaryan
  Image caption: Henrikh Mkhitaryan

  Sky Sports tana bayar da rahoton cewa dan wasan da yake kan hanyarsa ta barin Manchester United, Henrikh Mkhitaryan, yana arewacin Landan tare da ejen dinsa, Mino Raiola, inda ake gwada lafiyarsa gabannin musayar da za a yi masa da Alexis Sanchez.

 7. Hazard ya yi wa mahaifinsa gargadi

  Eden Hazard ya taka rawar gani a wasan da Chelsea ta lallasa Brighton 4-0
  Image caption: Eden Hazard ya taka rawar gani a wasan da Chelsea ta lallasa Brighton 4-0

  Eden Hazard bai ji dadin kalaman mahafinsa game da makomarsa ba.

  Rahotanni sun ce mahaifin dan wasan, Thierry Hazard, ya yi ikirarin cewa dansa ya yi watsi da sabon kwantiragi a Chelsea ne domin ya jira Real Madrid ta neme shi.

  Mahaifin Hazard ya yi wannan maganar ne a watan jiya kuma kalaman sun bata wa magoya bayan kungiyar ta Landan rai.

  An alakanta Real Madrid da dan wasan tsakiyar da dadewa kuma kwantiraginsa na yanzu zai kare a shekarar 2020, amma Chelsea na fartan za su cimma matsaya akan tsawaita kwatiraginsa kan kudi fam 300,000 a ko wane mako kafin dan wasan ya je ya buga gasar cin kofin duniya wa kasarsa Belgium a watan Yuni.

  An ambato shi yana cewa:.“Mahaifina ya fadi wasu kalamai mara kyau. Na mayar da hankali kan Chelsea. Kamar yadda na fada sau 10 a baya ina son in karasa wannan shekarar sannan za mu ga yadda za ta kaya. Amma ina jin dadi a nan.”

 8. An ga shugaban Gunners a Dortmund

  Aubamenyang

  An ga shugaban Gunners, Ivan Gazidis, a Dortmund yayin da yake kokarin kammala yarjejeniya kan cinikin dan wasan gaban Gabon Aubameyang, in ji Express.

 9. Arturo Vidal ba zai bar Bayern Munich ba

  Arturo Vidal
  Image caption: Arturo Vidal

  Arturo Vidal ya ce ba shi da damar barin Bayern Munich a watan Janairu. An alakanta dan wasan Chile din mai shekara 30 da komawa Chelsea,in ji Goal.

 10. 'Chelsea na iya sayen 'yan wasan Roma'

  Darakatan wasannin kungiyar kwallon kafa ta Roma, Monchi, ya ki ya kore yiwuwar Chelsea ta sayi dan wasan gaban Bosniya, Edin Dzeko, mai shekara 31 da kuma dan wasan bayan Brazil, Emerson Palmieri, in ji Metro.

  Yaya kuka ji da wannan labarin, magoya bayan Chelsea?

  Antonio Conte
  Image caption: Kocin Chelsea, Antonio Conte
 11. 'Ronaldo ka iya tafiya'

  Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da dan wasan gaban Portugal, Cristiano Ronaldo, cewar zai iya tafiya a lokacin bazara,yayin da Paris St-Germain da kuma Manchester United suke sha'awar sayen dan wasan mai shekara 32, in ji Yahoo.

  Ronaldo
 12. Madrid za ta taya Kane

  Kane

  Real Madrid za ta taya a dan wasan gaban Tottenham, Harry Kane, mai shekara 24, a lokacin bazara, kuma kungiyar kwallon kafar ta Spaniya ta shirya domin ta biya dan wasan gaban na Ingila fam miliyan 200, in ji Sunday Times.

 13. Da jirgi Sanchez zai tafi?

  Sako na baya bayan nan da Alexis Sanchez ya wallafa a shafinsa na Instagram wani bidiyo ne da ya nuna shi yana a hawa wani jirgin da aka ajiye dominshi.

  Kuna tunanin ina zai je?

  Ins
 14. Shehu Abdullahi zai bar Girka

  Dan wasan Najeriya, Shehu Abdullahi, zai bar kungiyar kwallon kafa ta Girka, Anorthosis Famagusta.

  Rahotanni na cewa zai koma kungiyar kwallon ka ta Bursarpor da ke kasar Turkiyya ne.

  A shafinsa na Twitter, dan wasan ya wallafa wani sakon bankwana mai sosa rai ga kungiyar ta Girka da magoya bayanta.

  View more on twitter
 15. Sanchez ya sanya kayan Man United

  Dan wasan gaban Chile, Alexis Sanchez, ya bayyana a wani hoto inda ya saka kayan man United a karon farko yayin da yake kara kusantar komawarsa kulob din daga Arsenal, in ji Metro.

  Sanchez