Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Zidane yana fargabar aikinsa a Real Madrid
 2. Ross Barkley ya fara taka wa Chelsea leda

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Sai gobe!

  Abin da ya samu kenan a shafinmu na labarai da sharhi game da yadda kasuwar musayar 'yan wasa ke ci a Turai.

 2. 'Dembele ba na sayarwa ba ne'

  Kocin Celtic, Brendan Rodgers, ya ce Moussa Dembele yana nan daram a Celtic, kuma kulob din ba shi da niyyar sayar da dan wasan.

  Moussa Dembele
  Image caption: Moussa Dembele
 3. Mourinho ya jinjina wa Sanchez

  Mourinho
  Image caption: Mourinho

  Kocin Manchester United, Jose Mourinho, ya jinjinawa sabon dan wasan kulob dinsa Alexis Sanchez yana mai cewa dan wasan ya 'bar kulob mai kyau zuwa gagarumin kulob.'

  'Muna tare da daya daga cikin manyan 'yan wasan gaba a duniya kuma yana da muhimmanci gare mu saboda muna bukatar fitattun 'yan wasa," in ji Mourinho.

  sa
 4. Man City da Atletico Madrid za su yi musaya

  Sergio Aguero
  Image caption: Sergio Aguero

  Manchester City za ta iya cimma matsaya da Atletico Madrid wajen musayar dan wasan Ajantina, Sergio Aguero, da dan wasan gaban Faransa, Antoine Griezmann, mai shekara 26, a wannan lokacin bazaran. City ta sayi dan wasan mai shekara 29 daga kungiyar ta Spaniya a shekarar 2011, in ji Sun.

 5. Dan Feyenoord na son New Castle

  An yi imanin cewa dan wasan Feyenoord, Nicolai Jorgensen, yana sha'awar komawa Newcastle United bayan 'yan Magpies sun taya shi kan kudi fam miliyan 14 a makon jiya, in ji Chronicle.

  Nicolai Jorgensen
  Image caption: Nicolai Jorgensen
 6. Julian Brandt ba zai je Barca ko Liverpool ba

  Julian Brandt
  Image caption: Julian Brandt

  Dan wasan Jamus, Julian Brandt,mai shekara 21, zai yi watsi da sha'awar Bayern Munich da Liverpool da Barcelona domin ya ci gaba da zama a Bayer Leverkusen, in ji Sport Bild.

 7. Aston Villa za ta sayi dan Man United

  Aston Villa ta kusa sayen dan wasan Manchester United mai shekara 20, Axel Tuanzebe, in ji Express.

  Axel Tuanzebe
  Image caption: Axel Tuanzebe
 8. Barca ba za ta sayi dan wasan baya ba

  Javier Mascherano
  Image caption: Javier Mascherano

  Kocin Barcelona, Ernesto Valverde, ya ce kungiyar Spaniyar ba za ta kara sayen 'yan wasan baya ba, duk da da komawar Javier Mascherano, mai shekara 33, kungiyar gasar Super League ta China, Hebei Fortune, in ji ESPN.

 9. An gwada lafiyar mai tsaron gidan Spaniya a Palace

  Vicente Guaita
  Image caption: Vicente Guaita

  An gwada lafiyar mai tsaron gidan Getafe, Vicente Guaita, mai shekara 31, a Crystal Palace, amma ana tattaunawa kan ko zai koma Palace a yanzu ne ko kuma a lokacin bazara, in ji Mail.

 10. Roma za ta sallamar wa Chelsea Edin Dzeko

  Edin Dzako
  Image caption: Edin Dzeko

  Kungiyar kwallon kafa ta Roma ta yarda da tayin fam miliyan 44 da Chelsea ta yi wa dan wasan gaban Bosnia mai shekara 31, Edin Dzeko da kuma dan wasan Brazil, Emerson Palmieri, mai shekara 23, in ji Guardian.

 11. Locomotive Moscow na son dan Liverpool

  Lazar Markovic
  Image caption: Lazar Markovic

  Lokomotiv Moscow ta tuntubi Liverpool kan dan wasanta, Lazar Markovic, mai shekara 23, in ji Mirror. Dan wasan na Sabiya ya yi wasan aro a Sporting Lisbon da Hull City a kakar da ta gabata.

 12. Arsenal za ta iya sayen Aubameyang kuwa?

  Aubameyang
  Image caption: Aubameyang

  Arsenal ta taya Pierre-Emerick Aubameyang kan yuro miliyan 50 jiya, amma nan-da-nan aka shaida wa Gunners cewa 'albarka.'

  Borussia Dortmund za ta sayar da dan wasan Gabon din, amma Arsenal tana bukatar kara kudi sosai idan tana son ta sayi dan wasan.

  Duk da cewa akwai rahotannin da ke cewa Dortmund na son Giroud, ba ya cikin tayin da Arsenal ta yi jiya.

 13. West Ham ta kusa sayen dan Portugal

  West Ham ta kammala yarjejeniyar aro kan dan wasan Portugal Joao Mario.

  Akwai wata yarjejeniyar komawar Mario, mai shekara 25, Hammers kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar 31 ga watan Janairu, duk da cewa ba a kammala samar da takardun cinikin ba.

  Joao Mario
  Image caption: Joao Mario
 14. 'Neymar ya yi da-na-sanin komawa PSG'

  kafar watsa labaran Spaniya Marcatana ikirarin cewa Neymar ya yi da-na-sanin komawa PSG kuma yana kewar La Liga.

  Marca ta yi wannan rahoton ne bisa rahoton da aka yi a Faransa game da ikirarin cewa dan wasan ba ya jin dadain zamansa a can.

  Shin dan wasan zai iya komawa Real Madrid? Shin akwai mai iya sayen dan wasan a Ingila?

  Neymar
  Image caption: Neymar
 15. Arsenal na da kwarin gwiwar sayen Aubameyang

  Har yanzu dai Arsenal tana da kwarin gwiwar sayen dan wasan gaban Borussia Dortmund, Pierre-Emerick Aubameyang, duk da cewa an yi watsi da tayi na biyu da kungiyar ta yi kan dan wasan.

  Kazalika kocin Gunners, Arsene Wenger, ya fara shirye-shiryen lokacin da dan wasan zai fara taka leda a kungiyarsa, in ji Bild.

  Aubameyang
  Image caption: Aubameyang
 16. Man City na da kwarin gwiwar sayen dan Athletic Bilbao

  Manchester City tana da kwarin gwiwar kammala sayen dan wasan Athletic Bilbao, Aymeric Laporte, kan kudi fam miliyan 57.

  Kocin City, Pep Guardiola, ya shafe lokaci yana sha'awar sayen dan shekara 23 din kuma ya shirya domin biyan kudin fansan dan wasam daga kwantiraginsa.

  kawo yanzu dai ba a cimma matsaya ba kan dan wasan bayan Faransan, amma ana tsammanin a kammala tattaunawar kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ranar Laraba.

  Aymeric Laporte
  Image caption: Aymeric Laporte
 17. Zidane na fargaba game da makomarsa

  A iya cewa harkar wasanni ba ta tafiya wa Real Madrid yadda ya kamata a wannan kakar.

  Komabayan da kungiyar ta fuskanta ta baya-bayan nan ita ce kayen da kungiyar ta sha a hannun Leganes a gasar Coap Del Rey a daren Laraba.

  An tambayi Zidane bayan wasan kan ko makomarsa ta ta'allaka ne kan iya nasara a karawar Real Madrid da PSG a gasar zakarun Turai.

  ESPN ta ambato shi yana cewa "Haka ne".

  Zidane
  Image caption: Zidane