Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. West Brom ta sayi dan Zamalek

  Ali Gabr
  Image caption: Ali Gabr

  Kungiyar kwallon kafa ta gasar Firimiya West Brom ta sayi dan wasan Zamaleck ta Masar, Ali Gabr,

 2. Watford na tattaunawa kan dan wasan Barca

  Gerard Deulofeu
  Image caption: Gerard Deulofeu

  Watford tana tattaunawa domin sayen dan wasan Barcelona, Gerard Deulofeu, amma Inter Milan da Napoli su ma suna son dan wasan mai shekara 23, in ji TalkSport.

 3. Dan wasan Chelsea zai je Dortmund?

  Michy Batshuayi
  Image caption: Michy Batshuayi

  Dan wasan kwallon kafa na Chelsea, Michy Batshuayi, mai shekara 24,ya shirya domin koma buga wasan aro a Borussia Dortmund- lamarin da zai bai wa dan kasar Gabon mai shekara 28 Pierre-Emerick Aubameyang ya koma Arsenal daga kungiyar kwallon kafar ta Jamus, in ji, Mirror.

 4. Giroud zai koma Chelsea?

  Olivier Giroud
  Image caption: Olivier Giroud

  Arsenal za ta kyale dan wasan gaba Olivier Giroud ya koma Chelsea idan kulob din ya iya biyan fam miliyan 35 kan dan wasan dan asalin Faransa, in ji Mail.

 5. Sakho ya koma Rennes

  Sakho

  Dan wasan gaban West Ham Diafra Sakho ya koma kungiyar gasar Ligue 1 ta Faransa, Rennes.

 6. Man United na son dan Bayern Munich

  Manchester United ta shiga jerin masu neman sayen dan wasan Bayern Munich, Arturo Vidal, mai shekara 30, in ji Mirror.

  Arturo Vidal
  Image caption: Arturo Vidal
 7. Ayew zai koma Swansea?

  Andre

  Andre Ayew ka iya kasance akan hanyarsa ta barin West Ham yayin da Swansea take fatan kammala yarjejeniyar sayen dan wasan Ghana din mai shekara 28 kan kudi fam miliyan 18, in ji Sun.

 8. Arsenal ta kusa kammala sayen Aubameyang

  Arsenal ta kusa cimma yarjejeniyar sayen dan wasan gaban Gabon Pierre-Emerick Aubameyang daga Borussia Dortmund kan kudi fam miliyan 60.

  Amma ba za a tabbatar da cinikin ba har sai Dortmund ta sami wanda zai maye gurbinsa yayin da dan wasan Arsenal Oliver Giroud yake daya daga cikin 'yan wasan da ake sa ran za su maye gurbinsa.

  Dortmund ta riga ta yi watsi da tayi biyu da Arsenal ta yi akan dan wasan.

  Aubameyang
  Image caption: Aubameyang
 9. 'Chelsea na bukatar 'yan wasan gaba uku'

  Kocin Chelsea, Antonio Conte, ya jaddada cewar yana bukatar karin 'yan wasan gaba uku a cikin 'yan wasansa domin ya sami damar lashe wani kofi a wannan kakar, in ji Express.

  Conte
  Image caption: Conte
 10. Shin Ibrahimovic zai koma Amurka ne?

  Dan wasan gaban Manchester United, Zlatan Ibrahimovic, ya kusa komawa kungiyar kwallon kafa ta LA Galaxy da ke wasa a gasar MLS ta Amurka. Dan wasan mai shekara 36 zai koma atisaye a mako mai zuwa bayan ciwon da ya ji a watan Disamba, in ji ESPN.

  Ibrahimovic
  Image caption: Ibrahimovic