Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Sanatoci 14 sun fice daga APC - 14 sun koma PDP - 1 ya koma ADC
 2. 'Yan majalisar wakilai 38 sun fice daga APC
 3. PDP ta yi maraba da su
 4. Da sanyin safiya 'yan sanda suka killace gidan Bukola Saraki a Abuja
 5. Tun karfe 06.00 na safe aka yi wa gidan Ike Ekweremadu kawanya
 6. 'Yan sanda sun musanta zargin
 7. A jiya 'yan sanda suka gayyaci Saraki kan zargin hannu a fashi da makami, abin da ya musanta

Rahoto kai-tsaye

time_stated_uk

 1. Sai an jima

  Jama’a a nan muka kawo karshen wannan sharhi da muke kawo muku kan dambarwar siyasar da ke faruwa a majalisar dokokin Najeriya.

  Sai a kasance da BBCHAUSA.COM domin samun karin bayani kan wannan da ma sauran labarai:

  Saraki
 2. EFCC ta gayyaci Ekweremadu

  Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta gayyaci matamakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu domin amsa tambayoyi kan zargin hannu a wata badakala da ta shafi kudi.

  Wannan na zuwa ne a lokacin da rahotanni suka ce jami’an EFCC da na ‘yan sanda sun killace gidan Mr Ekweremadu.

  Wani mai taimakawa Sanata Bukola Saraki ya wallafa takardar da ya ce EFCCn ta aikawa Mr Ekweremadu, sai dai BBC ba ta tabbatar da sahihancin wannan takarda ba:

  View more on twitter
 3. Atiku, Balarabe Musa sun mayar da martani

  Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Alhaji Balarabe Musa da kungiyar jam’iyyun adawa sun yi Allah-wadai da killace gidajen shugabannin majalisar dattawa da jami’an tsaro suka yi da safiyar yau.

  Sun bayyana lamarin da cewa hari ne kan tafarkin demokuradiyya.

  Rundunar ‘yan sandan kasar dai ta musanta wannan batu.

 4. Bidiyon Saraki bayan kammala zaman majalisa

  Wannan bidiyon na nuna yadda Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya fita daga zauren majalisar bayan hutun wani dan lokaci da suka yi.

  Daya daga cikin masu taimakawa Saraki ne ya wallafa a shafin Twitter:

  View more on twitter
 5. Na yi murna da fitar su Kwankwaso – Oshimhole

  Adams Oshiomhole

  Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya ce ya yimurna da sauya shekara da wasu ‘yan majalisun tarayya na jam’iyyar suka yi.

  Mr Oshiomhole ya shaida wa manema labarai bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari cewa wadanda suka fitan sojojin haya ne.

  Ya kara da cewa hankalin jam’iyyar bai tashi ba ko kadan, kuma hakan ba zai shafi nasararta a zabukan 2019 ba.

  A ranar Talata ne ‘yan majalisar dattawa 15 suka bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar APC, inda 14 daga ciki suka koma PDP.

  Hakan ne ya sa jam’iyyar PDP ta zamo mai rinjayea majalisar dattawan.

  Daga bisani kuma ‘yan majalisar wakilai 38 suka fice, abinda ya ragewa mata karfinta a karamar majalisar.

  Sai dai kalaman nasa sun sha ban-ban da wadanda mai magana da yawun jam’iyyar ya yi, inda ba su ji dadin ficewar ‘yan majalisar ba.

 6. Labarai da dumi-dumi‘Yan majalisar wakilai 38 sun fice daga APC

  Rahotanni daga majalisar dokokin Najeriya na cewa ‘yan masajilar wakilai 37 sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki.

  Hakan ya biyo bayan matakin da wasu sanatoci 15 suka dauka na ficewa daga jam’iyyar.

  Rahotanni na cewa akwai wasu karin ‘yan majalisar wakilai da na dattawa da za su fice daga jam’iyyar.

 7. Ba mu ji dadin abin da ya faru ba - APC

  Buhari
  Image caption: Kawo yanzu fadar shugaban kasa ba ta ce uffan game da abin da ya faru

  Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ba ta ji dadin yadda wasu ‘yayanta suka sauya sheka ba.

  A ranar Talata ne ‘yan majalisar dattawa 15 suka bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar APC, inda 14 daga ciki suka koma PDP.

  Hakan ne ya sa jam’iyyar PDP ta zamo mai rinjayea majalisar yanzu.

  Mai magana da yawun jam’iyyar Bolaji Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun yi iya kokarinsu domin ganin ba a kai ga wannan mataki ba, amma ba su yi nasara ba.

  Za mu ci gaba da daura damara domin tunkarar abin da zai biyo baya, a cewarsa.

  Ya kara da cewa har yanzu mu ke da rinjaye a majalisar wakilai, da kuma yawan gwamnoni.

  Da aka tambaye shi kan ko ‘yan majalisar za su yi yunkurin tsige Shugaba Buhari, sai ya ce:

  Ba na zaton haka zai yi wu domin abu ne mai wuya. Ko Amurka ma bai taba faruwa ba.

 8. PDP ta yi maraba da sanatocin APC

  PDP

  Jam’iyyar PDP ta yi maraba da sabbin ‘ya’yan da ta samu sakamakon sauyin shekar da aka samu a majalisar dokokin kasar.

  A ranar Talata ne ‘yan majalisa 15 suka bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar APC mai mulki, inda 14 daga ciki suka koma PDP.

  Mai magana da yawun PDP Kola Ologbondiyan ya shaida wa BBC cewa suna maraba da bakin nasu.

  "Wannan wani babban ci gaba ne ga tafarkin demokuradiyyar Najeriya," a cewarsa.

  Ya kara da cewa hakan zai ba su damar tserar da kasar daga manufofin "kama-karya na Shugaba Muhammadu Buhari" da kuma bai wa jama’ar kasar mulki mai inganci.

 9. 'Yan majalisar wakilai na shirin barin APC

  Wasu ‘yan majalisar wakilai da dama na shirin bin sahun takwarorinsu na majalisar dattawa.

  Wakilin BBC Yusuf Tijjani ya ce sama da ‘yan majalisa 40 sun sanya hannu kan ficewa daga jam’iyyar.

  Kuma ana ci gaba da tattara sunayen masu son ficewa daga jam’iyyar.

  majalisa
 10. Sunayen sanatocin da suka bar APC

  Sunayen sanatoci da suka koma jam’iyyar PDP da kuma ADC:

  Dino Melaye (Kogi)

  Barnabas Gemade (Benue)

  Ibrahim Danbaba (Sokoto)

  Shaaba Lafiaji (Kwara)

  Ubali Shitu (Jigawa)

  Rafiu Ibrahim (Kwara)

  Suleiman Hunkuyi (Kaduna)

  Isa Misau (Bauchi)

  Monsurat Sunmonu (Oyo)

  Soji Akanbi

  Usman Nafada (Gombe)

  Musa Kwankwaso (Kano)

  Suleiman Nazif (Bauchi)

  Lanre Tejuosho

  Abdulaziz Murtala Nyako (Adamawa) - ADC ya koma.

 11. Ra'ayoyin jama'a kan rikicin siyasar Najeriya

  Jama'a a shafinmu na BBC Hausa Facebookna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan abin da ke faruwa a majalisar:

  Haruna Umar Babanta: Alhamdulillahi gaskiya dokin karfe yanzu ta tabbata APC ba jam'iyyar adalci da son cigaban talakawa ba ce sun ga ana shirin bata musu suna wurin talakawansu shi ya sa suka yanke hukuncin kwashe kayansu. Up PDP

  Abubakar M Nura: Tarihi zai maimaita kanshi, an yi sakaci gaskiya don bai kamata ace PDP ke da rinjaye ba don yanzu ba wani abun da Buhari zai kawo musamman na ci gaba a amince da shi. Najeriya sai da addu'a.

  Majalisa

  Sa'eed Lambo Sokoto: Masha Allah ba komai a cikinta sai rashin adalci Bukola Sarakimuna tare da kai Allah ya dora ka kan makiyanka.

  Abdullahi Hassan: Da ma Buhari zai iya neman sulhu da Kwankwaso amma na yi mamaki siyasa kenan na dubi yadda yake nuna ba ruwanshi da kowa tunda yana ganin ya kama talakawa tofa aiki ya samu Buhari talakawa na kara kaucewa manyan 'yan siyasa na kara kaucewa. Allah ka kaimu 2019.

  Gali Mahammed Gali: Ko da suke a cikin APC, ai dama PDP suke ma aiki.

 12. Gwamnati ba ta ji dadi ba - Kawu Sumaila

  Mataimaki na musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan harkokin majalisar wakilai Kawu Sumaila ya ce ba su ji dadin abin da ya faru ba na sauya shekar da wasu ‘yan majalisa suka yi.

  "Batu ne na yawan jama’a a don haka ko mutum daya ka rasa, ba za ka ji dadi ba,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

 13. An dage zaman majalisar dattawa

  Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya ce sai a ranar 25 ga watan Satumba ne Majalisar za ta sake zama.

  Rahotanni sun ce hakan ya biyo bayan wani kudurin da aka gabatar a zauren majalisar wanda ya nemi majalisar ta dakatar da zamanta saboda dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi wa gidajen Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu.

  A yanzu sun tafi hutun awa guda domin su samu damar amincewa da matakin da aka dauka a yau din.

 14. Kwankwaso bai ji 'maganar Buhari ba'

  Buhari da Kwankwaso

  Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa kwankwaso na cikin sanatocin da suka koma jam’iyyar PDP a yau.

  Kwankwaso ya yi hakan ne kwana guda bayan ya yi wata ganawa tare da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa.

  Sun gana tare da Gwmanan Jigawa Abubakar Badaru da shugaban APC na kasa Adams Oshimhole.

  Sai dai daga dukkan alamu bayannan da suka yi wa sanatan ba su gamsar da shi ba, a don haka bai fasa daukar matsayar da ya yi niyyar dauka ba.

  Buhari da Kwankwaso
 15. Jam'iyyar APC ta kauce hanya - Buba Galadima

  A kwanakin baya ne jam’iyyar APC ta rabu gida biyu inda wasu ‘ya’yanta suka kafa nasu shugabancin karkashin jagorancin Buba Galadima.

  Sun kira kansu rAPC ko kuma gangariyar APC.

  Alhaji Buba Galadima ya shaida wa BBC a kwanakin baya cewa jam’iyyar ta gaza, a don haka suke son kawo sauyi:

  Video content

  Video caption: Shugaban sabuwar APC Injiniya Buba Galadima
 16. Wadanda suka fice daga APC a kwanan nan

  Tun kafin batun na yau dai, wasu ‘ya’yan jam’iyyar ta APC suka fara ficewa daga cikinta.

  • Bangaren Akida da Restoration a jihar Kaduna wadanda ke rigima da Gwamna Nasir el-Rufa'i

  • Suna dai samun goyon bayan Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi

  • Bangaren rAPC na Buba Galadima ya kulla alaka da PDP domin kayar da APC a 2019 - wasu na ganin su ma sun kama hanyar ficewa daga jam'iyyar

  • Sanata Abdul-Azeez Nyako da Dan majalisar Wakilai Rufai Umar daga Adamawa - kamar yadda Daily Trust ta rawaito

  • Hakeem Baba Ahmed - shugaban ma'aikata a ofishin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki • Usman Bawa - mataimaki na musamman ga Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

  aaa
  Image caption: Masu zanga-zanga sun hallara a gaban ginin majalisar
 17. Sunayen sanatocin da suka koma PDP

  Shugabn majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya bayyana wasikar da sanatocin suka rubuta inda suka bayyana aniyarsu ta komawa jam’iyyar PDP.

  Sanatocin sun hada da Rabi’u Kwankwaso, Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da Isa Hamma Misau da Abdul’aziz Nyako da kuma Dino Melaye.

  Ga dai yadda shafin Twitter na majalisar ya lissafa su:

  View more on twitter
  View more on twitter
 18. Saraki ne yake jagorantar majalisa

  Sanata Bukola Saraki ya fara jagorantar zaman majalisar dattawa nay au tuk da yunkurin da ya ce jami’an tsaro sun yin a hanashi isa ofishin nasa.

 19. 'Yan sanda sun yi wa 'gidan Saraki kawanya'

  Yan sanda

  'Yan sanda sun tare duka hanyoyin shiga layin da gidan Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Saraki ya ke a Abuja.

  Mataimaki na musamman ga Mr Saraki, Bamikole Omisore, ya wallafa hotunan da ya ce jami'an tsaro ne lokacin da suka tare duka hanyoyin zuwa gidan sanatan, wanda ke unguwar Maitama.

  Daya daga cikin masu taimakawa Saraki ya shaida wa BBC cewa tun da sanyin safiya ne 'yan sandan suka mamaye titin Lake Chad inda gidan sanatan ya ke, kuma suka hana shi fita duk da cewa ya shirya tun tuni.

  Sai dai daga bisani BBC ta fahimci cewa Mr Saraki ya fice daga gidan saboda ya samu bayanan cewa 'yan sanda za su yunkurin hana shi ficewa.

  Bayanai sun nuna cewa Sanata Saraki ya yi niyyra zuwa ofishin 'yan sanda ne domin amsa gayyatar da suka yi masa kan zargin da suka ce wasu 'yan fashi da aka kama a jihar Kwara sun yi, na cewa shi ne mai gidansu.

  Mr Saraki, wanda ya musanta zargin, ya ce ya samu bayanan da ke nuna cewa gayyatar tasa na da alaka da yunkurin hana wasu sanatoci da 'yan majalisar wakilai na jam'iyyar APC mai mulki sauya sheka.

  Tun da asuba ne kuma 'yan sanda da jami'an EFCC suka killace gidan mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Ike Ekweremadu da ke unguwar Apo, a Abuja, kamar yadda wani na hannun damarsa ya shaida wa BBC.

  Jaridar Daily Trust ta rawaito kakakin rundunar 'yan sandan kasar Jimoh Moshood yana cewa ba shi da masaniya kan batun killace gidan shugaban majalisar da mataimakinsa.

  View more on twitter