Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahya

time_stated_uk

 1. Post update

  A nan muka kawo karshen labarai da sharhin da muke kawo muku game da hawan Arfa da sauan ayyukan Hajjin bana. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu. Za ku iya ci gaba da karanta labarai da rahotanninmu a shafinmu na intanet bbchausa.com. Ni ne Nasidi Adamu Yahaya nake muku fatan alheri.

 2. An sanya wa Ka'aba sabuwar riga

  Hukumomi a Saudiyya sun sauya rigar da ake sanya wa Ka'aba ranar Litinin.

  Duk shekara ana cire rigar sannan a maye gurbinta da sabuwa ranar tara ga watan Dhu Al-Hijjah, wanda ya yi daidai a ranar Litinin 20 ga watan Agusta na wannan shekarar.

  Ana kiran rigar da suna "Kiswa" a Larabce - kuma launinta baki ne tare da ratsin ruwan gwal.

  Duk shekara ake sauya rigar Ka'aba
 3. Me alhazai suke yi a yau?

  Daga Yusuf Ibrahim Yakasai

  Ranar Arfa ita ce rana mafi girma da muhimmnanci a duka kwanakin aikin hajji. Ko a hadisi ma ya zo, Annabi SAW yace Arfa ita ce hajji.

  Don haka duk alhajin da bai shiga filin arfa ba har rana ta fadi a yau to ba shi da aikin hajji, sai ya sake.

  Hakan ta sa a kowane irin hali mutuum ya ke ciki sai ya je filin, hatta ma marasa lafiya ana kai su.

  Hukumomin Saudiya sun yi wani tanadi da ske daukar marasa lafiya da ke cikin mawuyacin hali a kai su filin a cikin motocin daukar marasa lafiya, domin su dace da samun ranar Arfa.

  Dole ne alhazai su kasance a filin Arfa har rana ta fadi.

  A Arfa dai alhazai suna hada sallar Azahar da La’asar, kuma raka’a biyu-biyu. Daga nan za su zauna suna ta addu’o’I da karatun kur’ani da zikiri har zuwa faduwar rana.

  Idan rana ta fadi kuma ba za su yi sallar magriba a filin Arfa ba, sai su kama hanyar tafiya Muzdalifa.

  Muzdalifa shi ma wani fili ne mai girman gaske da ke tsakanin filin Arfa da Mina a kan hayar zuwa Maka

  Kuma da zarar an fita daga Arfa, Muzdalifa za a shiga, kamar yadda ana fita daga Muzdalifa to an shiga Mina ke nan, inda nan ne alhazai kan yi kwanaki yayin aikin hajji.

  A muzadalifa

  Da zarar alhazai sun yi isa Muzdalifa za su hada sallar Magirba da Issha kuma Issha kasaru za su yi, wato raka’a biyu maimakon hudu.

  Daga nan babu wani abu da ake so su yi sai kawai su kwanta su yi bacci, saboda washe gari ranar 10 ga wata suna da wasu ayyukan ibada masu wuya.

  Idan gari ya waye za su tsinci tsakwankwani a Muzdalifa wadanda za su yi jifa da su.

  Tsakuwa 21 kowane alhaji zai tsinta, sai kuma a kama hanyar tafiya wajen jifa. (Jifan Shaidan)

  To sai dai wasu alhazan suna tafiya Mina wajen jifan tun cikin dare.

  A addinance dai an yi wanmata saukin cewa za su iya zuwa su yi jifansu na farko tun cikin dare, gabanin wayewar gari. Haka kuma an yi wa maza masu yi wa mata jagoranci ko rakiya irin wannan uzuri.

  To amma wasu malaman ma suna bawa maza fatawar cewa za su iya zuwa su yi jifan tun kafin gari ya waye.

  Hukumomin Saudiya dai sun tsarawa kowace kasa lokacin da za ta yi jifa, don gudun kada kowa ya tafi lokacin guda a samu cunkoso.

  Ba kamar filin Arfa da Mina ba da ake yi wa alhazai tanadin tantuna da dardumai na zama, da katifun kwanciya da abin rufe, a Muzdalifa ba a samarwa alhazai komai. Sai dai su kwanta a kasa, ko kuma su yi guzurin tabarma, ko darduma, ko kuma kwalin da za su kwanta.

  Ranar Sallah 10 ga watan Zul-hajj

  A kan shafe kimanin sa’o’I biyu ana tafiya a kafa daga Muzdalifa kafin a kai wajen Jifa a Mina. Don haka tafiya ce ba ta wasa ba.

  Washegarin arfa, wato ranar sallah, alhazai suna yin wasu muhimman ayyuka uku zuwa hudu.

  1. Jifan Aqba, wato babban jifa. Alhazai suna zarcewa wajen jifan ne bayan sun bar filin Arfa sun kwana a Muzdalifa. Wajen Jifan dai yana can karshen Mina a hanyar Makkah idan an taho daga Muzdalifa.
  2. Yanka dabbar hadaya. (Ga wadanda za su yi hadaya)
  3. Aski. Ana so maza su yi kwal-kabo, ko saisaye, Mata kuma za su dan yanki kadan ne kawai daga gashinsu.
  4. Dawafin aikin hajji (Dawaful Ifada) da safa da Marwa. Amma wasu suna barin dawafin sai an gama zaman Mina an koma Makkah, sai su yi kafin su bar Makkah.

  Idan Alhazai suka yi ukun farko ko kuma biyu daga ciki, to za su iya cire haramin da ke jikinsu, su yi wanka su sa kayansu na gida, su fesa turare, su yi farauta, da ma sauran duka abubuwan da aka hana mai aikin hajji yinsu, in bada saduwa da iyali, har sai alhaji ya yi Dawafin aikin hajji, wato Dawaful Ifada. Daga nan mutum ya kammala aikin hajji.

  Bayan kamala wadancan ayyukan gudu uku ko hudu, alhazai za su koma masaukansu a Mina su yi kwanaki biyu ko uku, kamar yadda aka basu zabi.

  A cikin kwanakin za su dinga zuwa suna yin jifa.

  Daga nan kuma shi ke nan sun kammala aikin hajji, sai dai ga wanda bai yi dawafin Ifada ba, shi wannan zai yi da zarar ya koma Makkah kafin watan Zul-Hajj ya fita.

  Abu na karshe da mai aikin hajji ke yi gabanin barin Makkah shi ne dawafin ban kwana.

  Abu na karshe da mai aikin hajji ke yi gabanin barin Makkah shi ne dawafin ban kwana
 4. 'Yan Najeriya na yi wa kasarsu addu'a

  Mahajjatan Najeriya na can sun taru wuri guda a filin Arfa domin gudanar da addu'a ta musamman ga kasar.

  Za a yi cikin Turanci, Hausa, Igbo, Yoruba, Fulfulde, da Kanuri.

  Manyan malamai tara na kasar ne za su gabatar da addu'o'in.

  Daga cikin su akwai Ustaz Ahmad sulaiman, Ustaz Tijjani Bala Kalarawi da Sheikh Bala Lau.

  Za a yi addu'ar ne don nemawa Najeriya zaman lafiya saboda tarbarbarewar tsaro da take fama.

  Hukumar alhazan kasar ce ta shirya yin addu'ar.

  Jakadan Najeriya a Saudi Isah Dodo na cikin mahalarta wurin addu'ar.

  Ana yi wa Najeriya addu'a
 5. 'Jaririyar farko da aka haifa a filin Arfa a bana'

  Fitaccen Malamin nan Shaykh Mohammed Aslam ya wallafa hoton wata jaririyar a shafinsa na Facebook inda ya ce ita ce jaririyar farko da aka haifa a asibitin da ke filin Arfa kuma ranar Arfa.

  A cewarsa, sunan jaririyar Wadah, yana mai cewa Hajiya ce.

  View more on facebook
 6. Mahajjatan jihar Kano

  Hotunan wasu daga cikin mahajjatan jihar Kano da ke arewacin Najeriya a filin Arfat.

  Fiye da mutum miliyan biyu ne dai ke halartar aikin Hajjin bana.

  Wasu mahajjatan jihar Kano
  Wasu mahajjatan jihar Kano
 7. Masallacin da ake budewa sau daya a shekara

  Masallacin Nimra da ke filin Arfat da ke Makkah, nan ne Annabi Muhammad (SAW) ya gabatar da hudubarsa ta karshe.

  Ana gudanar da hudubar aikin Hajji kowacce ranar tara ga watan Dhul Hajji a cikin masallacin.

  Ana bude masallacin ne sau daya a shekara.

  Kazalika a masallcin mahajjata ke yin sallar Azahar da La'asar, dukka dai a ranar.

  Yana da matukar wahala ga dukkan mahajjata su je masallacin lokacin aikin Hajji saboda cunkoso.

  Masallacin Nimra
 8. Hotunan wasu daga cikin mahajjatan bana

  Wata yarinya da ta halarci hajjin bana dauke da kaninta.
  Image caption: Wata yarinya da ta halarci hajjin bana dauke da kaninta.
  Wata mahajjatiya tana karatun Qur'ani a filin Arfa.
  Image caption: Wata mahajjatiya tana karatun Qur'ani a filin Arfa.
  Wani mahajjati yana karatun Qur'ani a filin arfa.
  Image caption: Wani mahajjati yana karatun Qur'ani a filin arfa.
  Wata dattijuwa a filin arfa rike da lema.
  Image caption: Wata dattijuwa a filin arfa rike da lema.
 9. Jaruman Kannywood sun sauke hajjin bana

  Wasu daga cikin jaruman fina-finan Kannywood na cikin mahajjata sama da miliyan biyu da ke sauke hajjin bana.

  Ga hotunan wasu daga cikinsu wadanda suka hada da Ali Jita da Aminu Saira da kuma Naziru Ahmad.

  Wasu daga cikin jaruman Kannywood da ke halartar hajjin bana
  Image caption: Wasu daga cikin jaruman Kannywood da ke halartar hajjin bana
  Wasu daga cikin jaruman Kannywood da ke halartar hajjin bana
  Image caption: Wasu daga cikin jaruman Kannywood da ke halartar hajjin bana
 10. Ina kewar wannan babbar rana

  Yusuf Ibrahim Yakasai

  Bara warhaka ni ma na kasance cikin alhazan da suka tsaya a filin Arfa tare da miliyoyin Alhazai.

  Kasancewa a wannan fili na Arfa ya sanya ni jin wani farin ciki na kasancewar na sauke daya daga shikashikan musulunci biyar.

  Ba kamar sauran lokutan zaman aikin hajji ba, a filin Arfa ba a fiya hira ba. Kowa yana dukufa ne wajen ibada da addu’o’I, don haka ina kewar wannan babbar dama.

  Ina tuna cewa babu wani wuni da ya kai Ranar Arfa, kuma kasancewarka a filin zai sa ka dinga jin cewa kana cikin wadanda Allah ya yi wa alfarmar kasancewa a wajen.

  A yanzu haka ina tuna irin zaman da na yi a wannan fili bara, da mutanen da muka zauna da su, a bana sun koma, suna maimaita irin wannan zama na ibada da addu’o’i da farin cikin kasancewa a wajen.

  Ina kewar irin addu’o’in da ake yi a filin Arfa, da yadda jama’a ke dukufa wajen ibada da addu’o’I wanda kaima zai kara maka karfin gwaiwar zage dantse.

  Ina kewar irin walwala da farin ciki da za ka ga alhazai a ciki a filin Arfa.

  Ina kewar yanda ka ke ganin masu hali ke kokarin kyautawa alhazai, ta hanyar rabon dubban madara, da lemuka, da kayan marmari, da ruwa, da lema da duk wani abu da alhazai ke bukata.

  Ina kewar yanda alhazai ke kara zagewa da addu’a da yamma sosai, kafin faduwar rana. A lokacin ne za ka ga alhazai sun mike tsaye sun fuskanci alkibla sun dukufa da addu’a. A lokacin za ka ji filin kamar ba mutane, saboda yadda kowa ya shagala da addu’a.

  Ina kewar yadda ake fadakar da jama’a muhimmancin ranar da yanda ake tunawa alhazai irin addu’o’in da ya kamata a yi wa kasa da ‘yan uwa.

  Ina fatan Allah ya ba wa wadanda ba su taba zuwa ba ikon zuwa, mu kuma Allah ya sa mu samu damar komawa.

  Yusuf Ibrahim Yakasai a Hajjin bara
  Image caption: Yusuf Ibrahim Yakasai a Hajjin bara
 11. Sojojin Najeriya sun sauke farali

  Wasu daga cikin sojojin Najeriya na cikin Mahajjatan bana.

  Maza da mata Musumi na rundunar sojin kasar na can sun bi sahun sauran Mahajjatan duniya domin hawan Arfa.

  Ga hotunan wasu daga cikinsu.

  Sojojin Najeriya a Hajji
  Sojojin Najeriya a Hajji
  Sojojin Najeriya a Hajji
  Sojojin Najeriya a Hajji
 12. Amurka ta jinjina wa Saudiyya kan Mahajjatanta

  Wani babban jami'in diflomasiyyar Amurka da ke Saudiyya, Christopher Henzel, ya bayyana matukar godiyar kasarsa ga mahukuntan Saudiyya saboda karamcin da ake nunawa Mahajjatan Amurkar.

  Dubban Amurkawa ne ke halartar aikin Hajjn bana.

  Jaridar Saudi Gazette ta ambato wata sanarwa da Henzel ya fitar, inda ya ce kokarin da mahukuntan Saudiyya ke yi wajen ganin sun kula da Mahajjata abin godiya ne.

  Amurka ta ce mahukuntan Saudiyya sun yi kokari
  Image caption: Amurka ta ce mahukuntan Saudiyya sun yi kokari
 13. Hotunan yadda ake aikin Hajjin bana

  Mahajjata na can kasar Saudiyya inda suke ci gaba da gudanar da ibada da addu'o'i a wani bangare na aikin Hajjin bana. Ga karin wasu hotunan mahajjatan:

  Hajjin bana
  Hajjin bana
  Hajjin bana
 14. Wasu mahajjatan Nigeria a tantunansu

  'Yan Najeriya sama da 55,000 ne suke aikin Hajjin bana, cikinsu har da wadannan matan da ke cikin tantunansu.

  Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
  Image caption: Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
  Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
  Image caption: Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
  Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
  Image caption: Wasu mahajjatan mata Najeriya a tantunansu
 15. Za a sauya rigar da ake rufe Ka'aba

  Hukumomi a Saudiyya sun ce ranar Litinin za su sauya rigar da sanya wa Ka'aba.

  Duk shekara ana cire rigar sannan a maye gurbinta da sabo ranar tara ga watan Dhu Al-Hijjah, wanda ya yi daidai a ranar Litinin 20 ga watan Agusta na wannan shekarar.

  Ana kiran rigar da suna "Kiswa" a Larabce - kuma launinta baki ne tare da ratsin ruwan gwal.

  Video content

  Video caption: Hukumomi a Saudiyya sun ce ranar Litinin za su sauya rigar da sanya wa Ka'aba.
 16. An kirkiro manhajar da za ta rage batan alhazai lokacin Hajji

  Hukumar kula da aikin Hajjin Najeriya ta ce ta kirkiri wata manhaja da za ta taimaka wajen rage batan alhazai yayin zaman Mina.

  Hukumar ta ce manhajar ta GPS za ta dinga nuna wa alhazai taswirar wajen da suke da kuma inda suke nema.

  Manhajar tana dauke da shafin intanet kuma an saya ta a dukkan shemomin jihohin kasar, ta yadda za a iya latsa duk wacce mutum ke nema daga ko ina, kamar filin Arfa da Muzdalifa da wajen jifa.

  Manhajar za ta yi aiki ne kawai a kan wayar komai da ruwanka
 17. An yi ruwa da iska mai tsanani a Makkah

  An yi iska mai karfi da guguwa da kuma ruwan sama da aka dauki lokaci ana yi yayin da alhazzan ke shirin fita filin Mina da ke wajen garin Makka, inda daga nan suke wuce wa zuwa filin Arafat.

  Hukumar kula da yanayi ta Saudiyya ta yi hasashen cewa za a yi matsanancin zafi a ranar Litinin da ake hawan Arafat, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

  Jaridar ta ce hasashen ofishin kula da yanayi na Saudiya ya nuna sai zuwa yammacin Litinin za a yi iska da kura da kuma ruwan sama a Makkah saboda matsanancin zafin da aka maka.

  Iska da aka yi dai ta lalata wasu runfunan alhazzai a Mina, yayin da aka bukaci alhazzai su kiyayen umurni da shawarwarin da hukumomi suka bayar kan yanayin.

  Iska da aka yi dai ta lalata wasu runfunan alhazzai a Mina
 18. Yau ake hawan Arfa

  Ranar Litinin ne Musulmi fiye da miliyan biyu daga sassa daban-daban na duniya ke hawan Arfa, inda za su shafe ranar suna gudanar da ibada da neman gafara ga Allah (SWT).

  Wadanda suke da iko da koshin lafiyar hawa dutsen Arfa kan yi kokarin aikata hakan domin koyi ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

  A filin Arfa Musulmai za su sallaci Azahar da La'asar a matsayin Kasaru, sannan a ci gaba da ibada da zikiri da karatun Al-Kur'ani.

  Mutum miliyan biyu ne ke aikin Hajjnin bana
 19. Post update

  As salamu alaikum. Barkanmu da saduwa a wannan rana mai albarka, wato ranar da ake hawan Arfa wanda shi ne kololuwar aikin Hajji. Ku kasance tare da ni, Nasidi Adamu Yahaya, inda zan kawo muku labarai da rahotanni da hotuna da bidiyo kan abubuwan da ke farua a filin Arfa da ma wasu yankunan Saudiyya.