Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdulwasiu Hassan

time_stated_uk

 1. Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta sanar da wanda zai tsaya mata takara a zaben 2019

  Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta sanar da wanda zai tsaya mata takara a zaben 2019

  An zabi gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia a matsayin dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP a zaben da za a yi a 2019 bayan kuri'in da ya samu da suka kai 1,991, wanda jami'in hukumar zabe Raymond Dokpesiya bayyana. A wani labarin kuma, an daga zaben fitar da gwani na gwamna a jihar ta Abia zuwa ranar Litinin sakamakon rashin isar jami'an hukumar zabe daga Abuja zuwa jihar saboda matsalar jirgi.

 2. Sanwo-Olu ya mayar wa Ambode martani

  Mai neman takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam'iyyar APC, Babajide Sanwo-Olu, ya mayar wa gwamna Ambode martani kar zargin da ya masa na tarihin tabin hankali.

  A wani taron manema labaran da ya kira, Sanwo-Olu ya ce shi ba zai yi kaman gwamnan ba kuma jam'iyyar APC za ta bai wa gwmnan amsar zarge-zargen da ya yi masa.

  Shugabannin jam'iyyar APC ne suka daga hannun Sanwo-Olu a wajen taron manel labaran da ya kira
  Image caption: Shugabannin jam'iyyar APC ne suka daga hannun Sanwo-Olu a wajen taron manema labaran da ya kira
 3. An fara zaben fidda gwanin APC na bangaren Amaechi a Ribas

  An fara zaben fidda gwani na bangaren minista Rotimi Amaechi wadda uwar jam'iyyar APC ta amince da shi.

  Jami'an INEC da na APC suna sa ido a zaben da ake yi a Fatakwal.

  Cikin jami'an dai akwai Lawal Jafaru Isa.

  Porthacourt
 4. Wani bangaren APC a Kwara ya fidda dan takara

  Wani bangare na jam'iyyar APC a jihar Kwara ya fitar da dan takara a zaben fidda gwanin da ya yi yau.

  Wata sanarwa da jam'iyyar APC ta bangaren Balogun Fulani ta fitar ta ce kayode Abdulwahab ne ya yi nasara a zaben fidda gwannin da ka yi ranar Lahadi.

  Wannan bangaren dai yana da alaka da shugaban majalisar dattawan Najeriya, Bukola Saraki.

  Kwanan nan ne Saraki ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

  Kayode Abdulwahab
  Image caption: Kayode Abdulwahab
 5. Ana shirin fara zabe a Oyo

  A halin yanzu dai ana kan shirin fara zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar Oyo inda gwamnan jihar Isiaka Ajimobi da jami'an zabe suka isa wurin zaben a birnin Ibadan.

  Ajimobi
  Ajimobi
  Image caption: Gwamnan jihar Oyo Isiaka Ajimobi da sauran masu ruwa da tsaki a zaben sun isa wurin zaben
 6. 'Mai neman zama dan takaran APC a Legas na da tabin hankali'

  Gwamnan jihar Legas Akinwumi Ambode ya caccaki abokin gogayyansa wajen neman zama dan takaran gwamnan APC a Legas, Babajide Sanwo-Olu.

  A wani taron manema labarai da ya yi a Legas a yau, gwamnan ya ce Sanwo-Olu na da tarihin tabin hankali.

  Ya kara da cewa shi yana da bayanai da suka tabbatar da hakan.

  Sai dai kuma Sanwo-Olu bai ce komai ba tukunna game da wannan zargi da gwamnan ya yi masa.

  Cikin 'yan kwanakinnan dai 'yan majalisar dokokin jihar Legas sun nuna goyon bayansu ga Sanwo-Olu a zaben gwamna mai zuwa, maimakon gwamnan jihar da ke neman sake takaran gwamna a wa'adi na biyu.

  A ranar Litinin ne dai za yi zaben fidda gwani na APC a Legas inda Ambode da Sanwo-Olu za su kara.

  Ambode
 7. Wasu gwamoni sun fito zaben fidda gwani

  Akalla gwamnoni biyu ne suka fito zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da PDP da ake yi yau.

  Cikin gwamnonin da suka Fito zaben ne Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da kuma Okezie Ikpeazu na jihar Abia.

  Abia
  Ganduje
 8. Bangarori biyun da ke zabe a PDP ta Zamfara

  Zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Zamfara dai ta rabu gida biyu ne tsakanin bangare Injiniya Ibrahim Shehu Bakauye da na Alhaji Bello Mohammed Matawalle.

  PDP
 9. An kama wadanda ake zargi a Inugu

  An kama wasu da ake zargi da kai samame wurin da ake zaben fidda gwanin APC a Inugu kuma an ci gaba da zaben kamar yadda aka shirya.

  Enugu
 10. An wurga bam a sakatariyar APC

  An wurga wani abin fashewa a sakatariyar APC ta jihar Ribas.

  Wakilin BBC ya ce abin fashewan ya yi karan gaske.

  Tun daga farko dai 'yan APC na bangaren Sanata Magnus Abe ne suka fara zaben fidda gwaninsu na 'yar tinke a rumfunar zabe.

  Su kuwa 'yan jam'iyyar na bangaren Rotimi Amaechi, sun hallara ne a sakatariyar jam'iyyar ta jihar.

  Video content

  Video caption: Kalli yadda wani bangaren APC ya yi zabe a Ribas
 11. Ana zaben fidda gwanin PDP a Zamfara

  An fara zaben fidda gwanin wani bangare na jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Zamfara.

  Zamfara
  Zamfara
 12. Ana hatsaniya a wurin zaben fidda gwanin Inugu

  Ana hatsaniya a wajen zaben fidda gwanin APC a jihar Inugu. Wakiliyar BBC ta ce da wasu 'yan bindiga suka shiga wurin da ake zaben sai mutane suka tsere.

  Cikin wadanda suka tseren ma har da jami'an tsaro
  Image caption: Cikin wadanda suka tseren ma har da jami'an tsaro
 13. Wakilai masu zabe

  Wasu wakilai masu zabe a zaben fidda gwanin APC a jihar Kano suna nuna katin zabensu na jam'iyya.

  APC Kano
 14. 'Yan PDP na dakon zabe a Bauchi

  A jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, 'yan jam'iyyar PDP suna jiran a fara zaben fidda gwani.

  Zaben fidda gwani
  Zaben fidda gwani
 15. Kalli yadda aka yi rububin shiga wurin zabe a Ibadan

  Kalli yadda aka yi ta rububin shiga wurin zaben fidda gwanin APC a birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

  Video content

  Video caption: Yadda 'yan jam'iyyar APC suka shiga wurin zabe a Ibadan na Najeriya
 16. PDP ta gama tanatance masu zabe a Kwara

  A jihar Kwara jam'iyyar PDP ta gama tantance masu zabe a zaben fidda gwaninta na jihar.

  PDP kwara
 17. An samu rarrabuwar kawuna a Inugu

  Wakilai

  Wakiliyar BBC ta ce an samu rabuwar kai ne wajen zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar Inugu.

  Wakilan APC din dai sun rabu gida biyu, suna goyon bayan masu neman takara daban-daban.

  An hana wakilan jam'iyyar masu shudin kati shiga wurin zaben
  Image caption: An hana wakilan jam'iyyar masu shudin kati shiga wurin zaben
 18. APC na dakon kayayyakin zabe a jihar Oyo

  APC Ibadan
  Image caption: Daruruwan 'yan jam'iyyar APC suna kokarin shiga wurin zaben a Ibadan

  'Yan jam'iyyar APC na dakon kayayyakin zabe a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

  Wakilin BBC ya ce 'yan jam'iyyar suna kokarin shiga filin wasan Lekan Salami da ke Adamasingba a birnin Ibadan.

 19. APC ba ta fara zaben fidda gwani ba a Gombe da Bauchi

  Bauchi

  A jihohin Bauchi da Gombe jam'iyyar APC ba ta fara zane fidda gwani ba don rashin isowar jami'an zabe da kayayyakin zabe.

 20. PDP na shirin fara zabe fidda gwani a Abia

  Abia

  A halin yanzu dai jam'iyyar PDP tana shirin fara zaben fidda gwani a jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.

  Wakiliyar BBC da ke wurin ta ce a wakilan jam'iyya masu zabe suna jiran a fara zaben, yayin da jami'ai ke shirin farawa.

  Abia
  Abia