Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Haruna Shehu Tangaza

time_stated_uk

 1. Allah Ya jikan Shehu Shagari

  A nan muka kawo karshen bayanai kai-tsaye da muke kawo maku game da jana'izar tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari wanda ya rasu a ranar Juma'a 28 ga watan Disamban 2018.

  An binne shi ne a mahaifarsa garin Shagari a jihar Sakkwato.

  Marigayi tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari
 2. Kalli bidiyon kabarin Shehu Shagari

  Mutane da dama ne ke zuwa suna wa kabarin tsohon shugaban na Najeriya addu'a.

  Video content

  Video caption: Kalli bidiyon kabarin marigayi Shehu Shagari
 3. Yadda gidan Shagari ya cika da mutane

  Gidan marigayin a garin Shagari ya cika makil da mutane da ke zuwa gaisuwar ta'aziya.

  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
 4. Sakon da muka samu

  SMS Message: Ina tunawa da marigyayi Shehu Shagari a duk lokacin da naga ko naji an ambaci sunan wani mutun dan asalin garin Shagari. dafatar Allah ya jikansa da rahama ameen. from Sako daga Nafisa Nasiru Aliyu Bukkuyum
  Sako daga Nafisa Nasiru Aliyu Bukkuyum
 5. Sakon da muka samu

  SMS Message: Hakika Najeriya tana cikin alhinin rashin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari, muna addu'a Allah Ya ji kansa Ya ba wa iyalansa hakurin rashinsa. from Fiddausi Ibrahim Na'ibawa
  Fiddausi Ibrahim Na'ibawa
 6. Inda aka binne Shehu Shagari

  An binne gawar tsohon shugaban na Najeriya a mahaifarsa garin Shagari a jihar Sakkwato bayan ya rasu a ranar juma'a 28 ga watan Disamban 2018 a asibitin kasa a Abuja.

  Kabarin Marigayi Shehu Shagari
  Kabarin Marigayi Shehu Shagari
 7. Bidiyon yadda aka yi wa Shagari Sallar Jana'iza

  An fara sallar jana’izarsa ne da misalin karfe uku na rana a gidansa da ke Shagari.

  Dubban masu alhini ni ne daga sassa daban-daban suka yi wa gawar addu’a a yayin sallar ta tsawon mintuna biyu.

  Daga cikinsu akwai tawagar gwamnatin kasar wadda ta kunshi ministoci da kuma sakataren gwamnatin kasar Boss Mustapha wanda ya jagorance ta.

  Haka ma gwamnonin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara na daga cikin wadanda suka halarci jana’izar.

  Daga nan aka dauki gawar domin binne ta a wani kabari da aka haka a wani bangare na katafaren gidansa a yayin ‘ya’ya da jikokin da makusanta ke sharbar hawaye.

  Lokaci ne dai mai sosa rai ga wanda ya gani.

  Bayan da aka kammala binne gawar tsohon shugaban wata tawagar sojojin kasar ta zagaye kabarin domin yi bankwanan ban-girma. Sun yi harbi sau ukku a sama zagaye da kabari tsohon shugaban wanda ya shugabanci kasar a shekarun 70-80.

  Video content

  Video caption: Yadda aka yi wa Shagari Sallar jana'iza
 8. Kalli bidiyon yadda aka shiga da gawar Shagari

  Yadda aka shiga da gawar marigayi Shehu Shagari domin sallar Jana'iza a mahaifarsa da ke Shagari

  Video content

  Video caption: Yadda aka shiga da gawar Shagari don Sallar Jana'iza
 9. Yadda aka yi wa gawar Shagari sallar Jana'iza

  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
 10. Sakon da muka samu a Facebook

  SMS Message: Rai Bakon Duniya Allah Jikan, Tsohon Shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Usman Shagari. from Sako daga Mustapha Salisu Gusau
  Sako daga Mustapha Salisu Gusau
 11. Kalli bidiyon yadda gawar Shagari ta iso Sakkwato

  Shehu Shagari ya rasu

  Video content

  Video caption: Kalli bidiyon yadda gawar Shagari ta iso Sakkwato.
 12. An kammala sallar Janaiza

  Ana shirin binne marigayi tsohon shugaban Najeriya Alhaji Shehu Aliyu Shagari a mahaifarsa garin Shagari a Sakkwato

 13. Yadda mutane suka cika gidan Marigayi Shagari

  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
 14. Sakon da muka samu daga Facebook

  SMS Message: Hakika Mutuwar Alhaji Shehu Shagari babban Rashi ne Ga kasar Nigeria Baki Daya. Ya Allah Ka gafarta wa Alhaji Shehu Shagari. Sannan Muma Idantamu Ta zo Ya Allah Kasa Mu cika Da kyau Da Imani from Sako daga Haris Alkanawii GoranMaje
  Sako daga Haris Alkanawii GoranMaje
 15. Sakon da muka samu a Facebook

  SMS Message: Halin mutum jarin sa: hakika dukkan al'ummar Najeriya na cikin alhinin mutuwar Shehu Shagari saboda kamanta mulkin adalci da ya yi a kasar nan, Allah ya jikansa ya sa mutuwa hutu ce a gare shi. from Sako daga Adamu Aliyu Amo Katsina
  Sako daga Adamu Aliyu Amo Katsina
 16. Gawar Shagari ta isa mahaifarsa garin Shagari

  Daruruwan mutane ne suka taru suna jiran isowar gawar tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari domin yi ma sa Sallar Jana'iza a mahaifarsa garin Shagari.

  Jana'izar tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari
  Jana'izar tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari
  Jana'izar tsohon shugaban Najeriya Shehu Shagari
 17. Sarautar Turakin Sakkwato

  Shehu Shagari ya rasu

  Wani matsayi da Alhaji Shehu Shagari ya rike har karshen rayuwarsa shi ne na Turakin Sakkwato.

  Babban wakili ne a majalisar koli ta fadar Mai martaba sarkin Musulmi .

  Tun a shekarar 1962 ne aka ba shi wannan mukamin wanda kuma ya rike har ranar da ya koma ga mahaliccinsa.

  Malam Bello N. Junaidu, shugaban cibiyar bincike da adana tarihin daular Sakkwato ya yi wa Haruna Shehu Tangaza Karin bayani game da sarautarsa ta Turaki da kuma irin gudummuwar da ya bayar ga ci gaban masarautar ta Sarkin musulmi:

  Ya ce an ba shi sarautar ne a matsayin jagoran ilimi, kuma garkuwa ga ilimi a masarautar Sarkin Musulmi.

  Sannan ya ce Turakin Sakkwato Alhaji Shehu Shagari ya bayar da gudunmuwa wajen bunkasa ilimi a lardin Sakkwato inda ya hada kan 'yan boko da kuma tabbatar da mutane sun tura 'ya'yansu zuwa makaranta

  Shehu Shagari
 18. An tafi da gawar tsohon shugaban zuwa mahaifarsa Shagari

  Bayan isowar gawar marigayin tsohon shugaban Najeriya daga nan an saka ta cikin wata mota mallakar rundunar sojin sama ta kasar inda ba da bata wani lokaci ba ta zarce zuwa garinsu na Shagari inda za a yi masa jana’iza.

  Gawar tsohon shugaban Najeriya shehu Shagari
  Gawar tsohon shugaban Najeriya shehu Shagari
 19. Gwamna Tambuwal ne ya jagoranci karbar gawar

  Gwamnan jihar Aminu waziri Tambuwal ne ya jagoranci sauran fitattun mutane a jihar da kuma iyalan marigayin wajen karbarta daga sojojin kasar a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III.

  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
 20. Yadda gawar Shagari ta isa Sakkwato

  Gawar ta iso da karfe daya na ranar Asabar cikin wani jirgi mallakar gwamnatin kasar mai lamba 5N FGZ.

  e

  Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari
  Jana'izar Shehu Shagari