Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. 'Yan takara biyar ne suka fafata a muhawarar Sokoto
 2. Tambuwal na PDP ya hadu da tsohon mataimakinsa na APC
 3. Gwamna Tambuwal ya ce Buhari da kansa ya jinjina ma sa
 4. Ahmed ya bar PDP ne saboda rashin gamsuwa da mulkin Tambuwal
 5. Aliyah ta Kowa za ta magance talauci ta hanyar rokon Allah
 6. Sadiq na SDP ya ce zai kori malamai marar inganci
 7. Abba Sidi na NCP zai tabbatar da kowa ya samu ilimi
 8. Za ku iya ci gaba muhawara a twitter ta maudu'in #BBCgovdebate

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

 1. Sai wani lokacin

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  A nan muka kawo karshen bayanai kai tsaye da muke kawo muku a kan muhawarar da 'yan takarar gwamnan Sakkwato suka tafka. Muhawara ita ce ta karshe da BBC Hausa ta gudanar a jihohin arewacin Najeriya bayan ta Nasarawa da Gombe da Kano. Awwal Janyau da Mustapha Kaita da Abdulbaki Jari da Umar Mikail ke cewa a yi zabe lafiya.

  Muhawarar 'yan takarar
 2. Bayanin 'yan takara na karshe

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  • Ahmed Aliyu na APC ya ce a zabi cancanta.
  • Aliyah ta Kowa ta ce kada a mayar da hankali kan 'yan takarar da ke alkawura amma zabi wanda ya dace.
  • Sadik na SDP ya yi kira da kada a zabi masu bayar da sabulu da man shafawa
  • Tambuwal na PDP ya yi kira ga Sakkwatawa su yi zabe ba tare da zage-zage ba yana mai cewa Allah ya riga ya zabi wanda yake so.
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 3. An kammala Muhawara

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Shugaban sashen Hausa na BBC Jimeh Saleh ya yi jawabin godiya ga 'yan takara da suka samu lokaci har suka amsa goron gayyata da kuma dimbin mutanen da suka halarci muhawarar.

 4. Da me za a tuna Tambuwal a Sokoto?

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  An san gwamnonin Sakkwato da gine-ginen gidajen ma'aikata, Me Tambuwal zai bar wa jihar Sokoto a matsayin abin da za a tuna da shi.

  Ya ce babban abin da za a tuna da shi shi ne sha'anin ilimi da lafiya da raya karkara da ruwan sha.

  Zai inganta makarantu da samar da ilimi da tarbiya. Ya ce idan ka ba da ilimi ka gama komai. Tinkahonsa shi ne bai wa al'umar Sokoto ilimi.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 5. Aliyah ta ba wata mukamin kwamishina

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Aliyah ta soma rabon mukamai inda ta ce za ta bai wa wata mata mukamin kwamishinan harakokin mata bayan ta yi tambaya kan yadda za a inganta rayuwar mata.

  Muhawar Sokoto
 6. Na samar wa matasa dubu 50 aiki - Ahmed

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Ahmed Aliyu na APC ya ce ya samar wa matasa fiye da dubu hamsin sana'a lokacin da yana kwamishina matasa.

  Muhawarar Sokoto
 7. Ba zan sake sauya sheka ba - Tambuwal

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Aminu Waziri Tambuwal ya ce ba zai sake fita daga PDP ya koma APC ba domin gwamnatin tarayya ba ta yin harka da jiharsa.

 8. An fara amsa tambayoyi

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  An fara amsa tambayoyi musamman na mahalarta muhawarar da kuma na shafukan sada zumunta da kuma tambayoyin da aka nada a garin Sokoto.

  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
 9. Ma'aikatan BBC da ke kawo bayanai kai-tsaye

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Awwal Janyau ne da Mustapha Musa Kaita da Umar Mikail da Abdulbaki Jari ne ke kawo ma ku bayanai kai-tsaye daga Abuja.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 10. Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
  Ma'aikatan BBC a wajen Muhawara
 11. Ni ba dan koren siyasa ba ne - Sadiq

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  An tambayi Sadiq Abubakar na jam'iyyar SDP, ko da gaske yake takara ba turo shi aka yi ba?

  Ya amsa cewa da gaske yake takara da kudinsa na kasuwanci, babu wanda ya turo shi.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 12. Masu bukata ta musamman sun hallarci muhawara

  Wasu daga cikin masu bukata ta musamman ke nan da suka hallarci muhawarar 'yan takarar gwamna a jihar Sokoto.

  Bukata ta musamman
  Bukata ta musamman
 13. Shin Ahmed na iya fita APC idan da matsala?

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Da aka tambayi Ahmed Aliyu na APC ko zai iya sauya idan har ya samu matsala a jam'iyyarsa musamman uban gidansa. Sai ya ce amsa da cewa yana siyasa ne don ra'ayin al'umma ba don son rai na ba

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 14. Ni na fara nada mata kwamishina - Tambuwal

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Gwamna Tambuwal na PDP ya ce gwamnatinsa ce ta soma bai wa mata kwamishina da kansiloli masu yawa.

  Tambuwal ya ce ya kamata a sani cewa tsarin mulkin jihar Sokoto ne ya hana kananan hukumomi gashin kansu kuma aikin 'yan majalisa ne su yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 15. Da yawa wasu ba su samu shiga zauren muhawara ba

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Jama’a da dama ne da ba su shiga zauren muhawarar ba amma suna sauraro a waje ta hanyar radiyon wayoyinsu a kafofin da ake watsa muhawarar kai-tsaye a jihar Sokoto.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 16. Zan magance talauci ta hanyar rokon Allah - Aliyah

  Aliyah ta ce za ta magance talauci ne ta hanyar rokon Allah sannan za ta gayyaci masu ba da agaji daga waje.

  Ta ce idan mata sun fito takara ana cewa ba su da ilimi da tarbiya, tana mai cewa hakan bai dace ba.

  Aliyah
 17. Ku kalli hotunan Hubbaren Dan Fodiyo

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Hubbaren Shehu Dan Fodiyo
  Hubbaren Shehu Dan Fodiyo
  Hubbaren Shehu Dan Fodiyo
  Hubbaren Shehu Dan Fodiyo
 18. Zan karfafa masana'antu

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Abba Sidi na NCP ya ce zai karfafa masana'antu yana mai cewa da ma taken jam'iyyarsa shi ne kawar da talauci.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto
 19. Zan daina dogaro da kudin tarayya - Sadiq

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto

  Sadik na SDP ya ce zai yaki talauci domin kawar da harkar daba. Zai tattauna da iyayen 'yan daba domin a ba su dama su samu horo domin kama sana'a.

  Zai ba matasa Naira dubu hamsin domin kama sana'a.

  Ya ce a matsayinsa na dan kasuwa, cikin shekara biyu zai daina dogaro ga kudin gwamnatin tarayya.

  Muhawarar 'yan takarar gwamnan Sokoto