Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Buhari bai yi jawabi ba
 2. Yakubu Gowon ne kawai cikin tsofaffin shugabannin kasar da ya halarci taron
 3. Bukola Saraki da Yakubu Dogara sun halarci bikin
 4. Buhari ya fara mulki ne a 2015
 5. Buhari na APC ya doke Atiku Abubakar na PDP
 6. An rantsar da gwamnonin jihohi 29 na kasar

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Umar Rayyan

time_stated_uk

 1. Karshe

  Nan muka kawo karshen labarai da bayanai da muke wallafa a wannan shafinmu. Mun gode.

 2. Kaduna

  Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai na jam'iyyar APC bayan da ya sha rantsuwar fara mulkinsa a karo na biyu a dandalin Murtala Square da ke Kaduna ranar Laraba.

  A
  A
  Image caption: Mataimakiyar Gwamna Hadiza Sabuwa Balarabe lokacin da take shan rantsuwa
  A
  A
  Image caption: Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris ya halarci taron rantsar da gwamnan
  A
 3. Abuja

  Hotunan yadda aka rantsar da Shugaba Buhari a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

  A
  A
  A
  A
  A
  A
 4. Ra'ayoyinku daga Facebook

  SMS Message: To baba rantsuwa abu ce mai girma don haka ka dubi girman allah ka kamanta adalci ga al'umma da kasa baki daya dan ka samu tsira gobe lahira from Janaidu Auwal Gulumbe
  Janaidu Auwal Gulumbe
  SMS Message: Haryaban tausayi rantsuwa agoman karshe Allah yabaki Ikonyin adelci baba bahari from Amina Abubakkar
  Amina Abubakkar
  SMS Message: Allah swt ya bashi ikon cika alkawarin da ya dauka Allah swt ya mai jagora Amin from Fatima Abdulmalik
  Fatima Abdulmalik
 5. Abuja

  Tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) Nuhu Ribadu ya ce an yi nasarori a shekara hudun farko.

  Video content

  Video caption: Fatan Nuhu Ribadu a kan sabuwar gwamnatin Buhari
 6. Kano

  Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC bayan da ya sha rantsuwar fara mulkinsa a karo na biyu a filin wasa Sani Abacha da ke Kano.

  A
  A
  A
  A
 7. Jigawa

  Gwamna Abubakar Badaru lokacin da ya yake rantsuwar wa'adin mulkinsa na biyu a Dutse.

  A
  A
  A
 8. Sarki Sanusi bai je rantsuwar Ganduje ba

  Dukkanin sabbin sarakan wato Bichi da Karaye da Gaya sun halarci bikin rantsar da gwamnan amma ba a ga Sarkin Kano ba, Muhammad Sanusi a filin wasa na Sani Abacha ba, wato wurin da aka yi taron.

  Duk da cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta keta masarautar birnin zuwa hudu, al'amarin da wasu ke yi wa kallon wani yunkuri na yi wa Sarki Sanusi kora da hali. Latsa nan don karanta cikakken labarin.

  A
 9. Legas

  An rantsar da San Olu na jam'iyyar APC a matsayin sabon Gwamnan jihar Legas wa'adin mulki na farko ranar Laraba.

  A
  A
  A
  A
 10. Gombe

  An rantsar da Alhaji Inuwa Yahaya a matsayin sabon Gwamnan jihar Gombe.

  A
  A
 11. Abuja

  An tashi taron rantsar da Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo a Abuja.

  Buhari
 12. Abuja

  Mai bai wa shugaban kasa shawara kan kafafen sada zumunta Bashir Ahmad ya bayyana mana fatansa ga shugaban.

  Video content

  Video caption: Bashir Ahmad
 13. An fara shirye-shiryen rufe taron

  Ana shirye-shiryen rufe taron rantsar da Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo. Sai dai shugaban bai yi jawabi ba, kamar yadda ya yi a shekarar 2015 lokacin da ya dauki rantsuwar fara mulkin wa'adinsa na farko.

 14. Ana karanto tarihin Buhari

  Ana karanto tarihin Shugaba Buhari yayin da shi kuma yake ci gaba da kewaye dandalin Eagle Square a cikin wata mota yana jinjina ga jama'a.

 15. Yadda Buhari ya sha rantsuwa

  Shugaba Buhari ya sha rantsuwar mulki wa'adi na biyu yana rataye da gafakar Kur'ani a dandalin Eagle Square.

  Video content

  Video caption: Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar kama aiki
 16. Sojoji na fareti

  Sojoji na faretin ban girma bayan rantsar da Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo.

 17. Post update

  Jigawa

  Gwamna Badaru Abubakar na shirin shan rantsuwa

  BBC
  Image caption: BBC
  BBC
  Image caption: BBC