Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Takaitacce

 1. Shugaba Buhari ya yi alkawarin bunkasa Najeriya
 2. 'Zan ci gaba da samar da ayyukan yi da hada kan kasa'
 3. Talauci na da alaka da rashin tsaro, in ji shugaban
 4. Najeriya ta koma tafarkin dimokradiyya ne a 1999
 5. A bara ne aka sauya ranar daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga Yuni
 6. Shugabanni hudu ne suka mulki kasar a tsawon shekara 20

Rahoto kai-tsaye

Daga Naziru Mikailu, Umar Rayyan da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Karshe!

  Nan muka kawo karshen karshen labarai da rahotanni kai tsaye game da Ranar Dimokradiyya a Najeriya ta bana. Mun gode.

 2. Za mu ci gaba kamar China da India - Buhari

  Ranar Dimokradiyya

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu abin da zai hana kasar ci gaba kamar kasashen China da India ko Indonesia.

  "Tun da China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba," a cewar shugaban, wanda aka sake zaba karo na biyu a watan Fabrerun da ya gabata.

  Ya kara da cewa: "Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gaci".

  Shugaban na magana ne a ranar bikin murnar demokuradiyya, wacce a karon farko ake tunawa da ita a ranar 12 ga watan Yuni.

  An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma rage radadin alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993.

  Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.

  Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la'akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.

  Buhari
 3. Manyan baki

  Ranar Dimokradiyya

  Teburin manyan baki kenan ciki har da shugaban kasar Rwanda (na farko daga hagu).

  Eagle Square
  Eagle Square
  Eagle Square
 4. Ranar Dimokradiyya

  Karewar jawabin Shugaba Muhammadu na nufin an kawo karshen wannan taro na bikin dimokradiyyar Najeriya 'yar shekara 20 ba tare da katsewa ba.

  Yanzu haka fareti ne sojoji ke yi yayin da su kuma manyan baki ke ficewa daga filin taron.

  Fareti
  Fareti
 5. Post update

  Daga hagu zuwa dama, Aisha Buhari uwar gidan shugaban kasa da Sanata Ahemd Lawan Shugaban Majalsiar Dattawa da Femi Gbajabiamila Kakakin Majalsar Wakilai da Bola Ahmed Tinubu jagoran jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake rera taken Najeriya.

  Mahalarta taro
 6. Buhari ya gama jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  Shugaba Buhari ya gama jawabinsa, inda aka yi taken Najeriya.

  Yanzu za a ci gaba da faretin girmamawa ga manyan baki.

 7. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Daga yau na mayar da sunan babban filin wasa na kasa da ke Abuja Moshood Abiola National Stadium" - Buhari

 8. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Wannan gwamnati ba za ta yadda da aikin duk wanda yake so ya tsokani ko yi wa al'adunmu ba'a ba ko kuma ya kawo wa tsaron kasa cikas" - Buhari

 9. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Ina mika godiya ta musamman ga 'yan kasuwa wadanda suka gina wuraren kasuwanci kamar layukan wayar hannu da kuma sauran wurare wadanda suka bai wa matasanmu aikin yi" - Buhari

 10. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "A matsayina na shugaban komitin farfado da tafkin Chadi zan jagoranci zama na musamman don kawo karshen matsalolin tsaro a yankin" - Buhari

 11. Buahri na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Shirye-shiryenmu na habbaka rayuwar 'yan kasa (N-power da ciyar da 'yan makaranta) abin koyi ga sauran kasashen duniya" - Buhari

  Buhari
 12. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Ba mu tsorata da kalubalen da ke gabanmu ba sai dai ma sun kara mana kwarin gwiwa ne" - Buhari

  Buhari
 13. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  "Bambancin 2015 da 2019 dangane da harkar tsaro shi ne cewa a wannan karo muna yin aiki tare da jam'ian tsaro masu yawa da bayanan sirri da kuma kayan aiki," Buhari ya fada

 14. Buhari na jawabi

  Ranar Dimokradiyya

  Shugaba Muhammadu Buhari ya fara gabatar da jawabinsa, wanda dama shi ne babban abin da za a yi a yau.

  Buhari
 15. Ra'ayoyinku daga Facebook

  Ranar Dimokradiyya

  SMS Message: Muna tsammanin shugaba Buhari zai baiyana was yan Nigeria yadda gwamnatinsa zata sa gaba, kamar irin zubin ministocin da zaiyi aiki dasu, dakuma irin aikace-aikacen da zaisa agaba a wannan karon. from Yakubu Aliyu
  Yakubu Aliyu
  SMS Message: Babu wani sabon abu da shugaba Buhari zai fada, sai dai abinda muka saba ji daga gare shi! Allah ka kawo mana dauki! from Zubairu Adam Alejo
  Zubairu Adam Alejo
  SMS Message: Ina mamakin wasu da basu fadin alkairi abakinsu tir wlh da irin wannan mugun bakin nawasu insha Allah ta Allah batukuba from Rakiya Yusuf
  Rakiya Yusuf
  SMS Message: me zamu ji, banda karya DA kuma yaudara, sy ya Saba fada mana. from Adaraja Mata
  Adaraja Mata
  SMS Message: Uhm cewa zaiyi cikin kwanaki kad'an masu zuwa kowane d'an Nigeria zai yi dariya a zango na biyu. from Abdul Senior Babale
  Abdul Senior Babale
  SMS Message: DUNIYA kenan wai yau buhari ne TALAKAWA suke ganin makaryaci ne ba mutun bane mai cika alkawari from Sen Abdulrahman Omar
  Sen Abdulrahman Omar
  SMS Message: Karya Da karairayi Daya Saba Yiwa Yan Najeriya from Amina Abubakar Basheer
  Amina Abubakar Basheer
  SMS Message: Masha Allah.Allah yasa anshiga a sa a ameen. from Jamila Abubakar
  Jamila Abubakar
  View more on facebook
 16. BBC Hausa Facebook

  Za ku iya garzayawa shafinmu na BBC Hausa Facebook don kallon bidiyon wainar da ake toyawa kai-tsaye a dandalin Eagle Square wato inda ake bikin cika shekara 20 da komawa tafarkin dimokradiyya a Najeriya ranar Laraba.

  View more on facebook
 17. An fara fareti

  An fara fareti a dandalin Eagle Square bayan isowar Shugaba Buhari.

  A