Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Karshen rahotannin

  Kotu ta yi watsi da karar Atiku da PDP

  Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin. Muna godiya da kuka kasance tare da mu.

  Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

 2. Ra'ayoyinku daga Facebook

  SMS Message: Ai Buhari ba Obasanjo ba ne in mutum yana nasara a kan OBJ kar ya zaci PMB ma haka ne ko Obj din ma dan bashi da gaskiya ne. Doɗar!! from Ibrahim Shuaib Baba Kula
  Ibrahim Shuaib Baba Kula
  SMS Message: Haba wannan aikin banza ne, dole mu 'yan PDP da Atiku mu daukaka kara zuwa kotun koli. Insha Allahu tarihin da ba'a taba kafawa ba a Nigeria Atiku zai kafa shi. from Umar Musa
  Umar Musa
  SMS Message: Haba Atiku kaman de ba dan Nigeria ba,ka taba ganin anyi zaben shugaban kasa a nigeria kotu ta soke. from Jabir Abdulrahman
  Jabir Abdulrahman
 3. Mataki na gaba ga Atiku

  Shari'ar Buhari da |Atiku

  Zuwa yanzu ba a samu martani ba daga Atiku Abubakar ko jam'iyyar PDP game da hukuncin kotun.

  Jam'iyyar PDP da dan takararta suna da damar daukaka kara a kotun kolin Najeriya.

  Atiku
 4. Buhari: Kotu ta yi watsi da karar Atiku

  Kotun sauraron kararrakin zabe a Najeriya ta yi watsi da karar da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar, ya shigar a gabanta, yana kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari.

  Kotun mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari'a Muhammad Garba ta tabbatar da Shugaba Buhari na jam'iyyar APC mai mulkin kasar a matsayin halastaccen wanda ya lashe zaben watan Fabrairun 2019.

  Sakamakon da hukumar zaben kasar, INEC, ta fitar ya nuna cewa Shugaba Buhari, mai shekara 76, ya samu kuri'a miliyan 15 da dubu 200 yayin da Alhaji Atiku Abubakar, mai shekara 72, na jam'iyyar PDP ya samu kuri'a miliyan 11 da dubu 300.

  Buhari
  Image caption: Buhari
 5. An yi watsi da sakamakon zaben rumbun intanet na PDP

  Shari'ar Buhari da Atiku

  Kotu ta yi watsi da ikirarin Atiku da PDP cewa su ne suka samu mafi yawan kuri'u a zaben shugaban kasa na 2019 bisa sakamakon da suka tattara daga rumbun tattara sakamako na intanet.

  Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce a dokar zaben Najeriya "ana aikewa da sakamakon zabe ne kawai a fili ba ta intanet ba a kowane mataki tun daga jiha har zuwa kasa baki daya".

  Ya kara da cewa: "Babu wata doka da ta bai wa INEC ko wani jami'i damar tura sakamakon zabe ta intanet. Sannan kuma babu dokar da ta bai wa INEC damar yin amfani da na'urar card reader wurin tattara sakamakon zabe."

  Na'urar card reader
 6. Ra'ayoyinku daga Facebook

  Shari'ar Buhari da Atiku

  SMS Message: Muna fatan shugaban kasa baba Buhari fatan samun nasara a kan Atiku Aabubakar insha Allahu from Alhaji Mai Hula Askira
  Alhaji Mai Hula Askira
  SMS Message: To muna fatar shugaba Buhari zai rungumi ƙaddara da zarar kotu ta ayyana Atiku a matsayin halattaccen shugaban ƙasa! from Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Ɓaure
  Ashiru Lawal Nagoma Ruwan Ɓaure
  SMS Message: Kotu gidan raba gardama da fatan hukuncin da wannan kotu za ta yanke ya zama alheri ga al'ummar Nigeria from Alh Mele Yusufari
  Alh Mele Yusufari
 7. Labarai da dumi-dumiBuhari ya cancanci ya yi takara - Kotu

  Shari'ar Buhari da Atiku

  Kotu ta ce babu wata hujja da ke tabbatar da cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai cancanci ya tsaya takara ba saboda bai je makaranta ba.

  Daya daga cikin korafe-korafen da PDP da Atiku suka gabatar a gabanta shi ne cewa Buhari ba shi da takardun shaidar zuwa makaranta sabda haka bai cancanci ya yi takarar ba baki daya.

  Kotun ta ce dokar zabe ba ta tilasata wa dan takara ya hada da takardun shaidar kammala karatunsa ba yayin mika fom mai lamba CF001 kafin a tabbatar da cancantarsa.

  Mai Shari'a Muhammed Garba ya ce Atiku da jam'iyyarsa ta PDP sun gaza gamsar da kotu cewa takardun da Buhari ya gabatar ba na gaskiya ba ne.

  Sannan kuma sun yi zargin cewa Buharin ya yi karya game da takardun shaidar kammala karatunsa, abin da kotun ta yi watsi da shi domin, a cewarta, tun kafin zabe ya kamata a duba shi ba bayan zabe ba.

  Buhari
 8. An dawo daga hutu

  Shari'ar Buhari da Atiku

  Zaman kotu ya ci gaba bayan dan gajeren hutu da aka tafi.

  Yanzu za a gabatar da hukunci ne kan korafe-korafen da suka shafi kafin zabe.

  Mai Shari'a Muhammed Garba shi ne shugaban rukunin alakalan da ke sauraron karar, kuma a nan gaba ne za su bayyana hukuncinsu kan zaben da INEC ta ce Muhammadu Buhari na APC ne ya lashe shi a watan Fabararairun 2019.

  Lauyoyi
 9. Anya Buhari ya ta da hankalinsa kuwa?

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya jagoranci zaman majalisar ministocinsa a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.

  Ya yi hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zaman shari'arsa tsakaninsa da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar a kotun sauraron kararrakin zabe.

  A
  A
  A
  Image caption: wasu daga cikin ministocinsa
  A
 10. Buhari bai yi karya ba kan shaidar karatu

  Kazalika, kotu ta yi watsi da batun cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi karya game da takardar shaidar karatunsa, inda ta ce abu ne da ya shafi harkoki kafin zabe.

  Tun farko ita ma INEC ta ce ya kamata ne a gabatar da korafjn tun kafin zabe, yanzu kuma kotu ta goyi bayan hakan.

  Muhammadu Buhari
  Image caption: Muhammadu Buhari
 11. Kotu ta yi watsi da ikirarin cewa Atiku dan Kamaru ne

  Game da batun da lauyoyin jam'iyyar APC suka gabatar a gaban kotun cewa Atiku Abubakar ba dan Najeriya ba ne, kotun ta yi watsi da ikirarin da cewa abu ne da ya shafi harkoki kafin zabe, ita tana sauraron abin da ya biyo bayan zabe ne.

  APC dai na cewa ne Atiku dan kasar Kamaru ne, wanda hakan ya haramta takararsa ta shugabancin Najeriya.

  Tun farko INEC ce ta fara cewa lamarin na kafin zabe ne, inda ita ma kotun ta tabbatar da haka a yau.

  Kotun ta umarci Buhari da jam'iyyar APC da su sake shirya sabon korafin da za su gabatar wa kotu a kan hakan domin tun a baya ya kamata su yi hakan.

  Atiku Abubakar
  Image caption: Atiku Abubakar
 12. Buhari 'yan Najeriya suka zaba, in ji APC

  Jam'iyyar APC ta yi imanin cewa 'yan Najeriya ne suka zuba wa Shugaba Muhammadu Buhari kuri'u, shi yasa ma har suka shiga Next Level, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

  View more on twitter
 13. Me mutane ke cewa a shafukan sada zumunta?

  Tuni dai mutane a shafukan sada zumuntar Najeriya musamman Twitter suke ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan hukunci da za a yanke.

  Magoya bayan ATiku Abubakar tuni sukaa kaddamar da wani maudu'i mai taken #AtikuIsComing.