Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Post update

  To a nan mu ma muka kawo karshen wannan shirin na kai tsaye. Ku ci gaba da kasance wa da BBC Hausa.

 2. Girman kasafin 2020

  Shugaba Muhammadu Buhari ya ce an samu karin kaso 9.75 cikin 100 a kan kasafin kudin shekarar 2019 na kusan naira tiriliyan 9.

  Hakan na nufin kasafin kudin Najeriya zai kama fiye da naira tiriliyan 10.

  Buhari
  Image caption: Lokacin da shugaba Buhari yake mika kasafin kudin 2019
 3. Buhari ya yi kira ga majalisa

  Shugaba Buhari ya bukaci majalisar dokoki da ta guji yin tsaiko wajen amince wa da kasafin kudi, al'amarin da ya janyo tsaiko a kasafin kudin shekarun da suka gabata.

 4. Buhari ya mika daftarin kasafi

  Shugaba Buhari ya kammala jawabi inda ya mika kundin daftarin kasafin kudin na 2020 ga majalisar dokokin Najeriya

  @Presidency
 5. Kasafi ga ma'aikatu

  Aiki da gidaje – Biliyan N262

  Sufuri – Biliyan N123

  Hukumar ilmin matakin farko ta UBEC – Biliyan N112

  Tsaro – Biliyan N100

  Aikin gona – Biliyan N83

  Albarkatun ruwa – Biliyan N82

  Ilimi – Biliyan N48

  Lafiya – Biliyan N46

  Hukumar Raya Arewa maso gabas – Biliyan N38

  Birnin tarayya – Biliyan N28

  Neja Delta – Biliyan N24

 6. Kasafin ma'aikatu

  Shugaba Buhari ya ce an kara wa hukumar Kare hakkin dan adam kudi da fiye da kaso 50 cikin 100, a daftarin kasasfin kudin na 2020.

 7. Kun san kasafin majalisar dokokin Najeriya?

  Shugaba Buhari ya ware wa majalisar dokokin Najeriya naira biliyan 125, inda aka ware naira biliyan 110 ga ma'aikatar shari'a a daftarin kasafin na 2020.

 8. Yadda aka gina daftarin kasafin kudi

  Shugaba Buhari ya ce an gina kasafin kudin ne a kan dala 57 na farashin gangar danyen mai.

 9. Abin da ya sa nake son kara haraji a Najeriya—Buhari

  Shugaba Buhari ya ce daftarin kasafin kudin zai kara harajin kaya daga kaso 5 cikin 100 zuwa 7.5 cikin 100.

  Ya ce za a yi amfani da harajin ne wurin inganta fannin kiwon lafiya da ilimi da gine-ginen hanyoyi.

  BBC
 10. Buhari ya fara jawabi

  Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin gabatar da daftarin kasafin kudin 2020, inda da farko ya fara yaba wa majalisar dokokin kasar bisa kokarinsu na aiki tare da bangaren zartarwa.

  BBC
 11. Kasafin kudin 2020 zai inganta rayuwar 'yan Najeriya - Lawan

  BBC

  Shugaban Majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ce yana kyautata zaton kasafin na 2020 zai inganta rayuwar 'yan kasar sannan ya bunkasa tattalin arzikinsu.

  Ya bukaci majalisa da bangaren zartarwa da su yi aiki tare wajen ganin an aiwatar da kasafin cikin nasara.

 12. An fara bayanai a Majalisa

  Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan yana jawabin maraba ga shugaban kasa da 'yan tawagarsa.

  Ahmed Lawan
 13. 'Sai Baba!'

  Wasu 'yan majalisa sun kaure da kiran 'Sai Baba' lokacin da Shugaba Buhari ya isa zauren majalisar wakilan kasar.

  Buhari
  Image caption: Buhari ya shiga Majalisa
 14. Abin da ya faru a baya

  A baya dai an kai ruwa rana tsakanin tsoffin majalisun da suka gabata da bangaren shugaban kasar inda aka yi zarge-zargen yin cushe a kasafin kudin 2016.

  A 2018 kuma an samu hatsaniya a zauren majalisar dokokin inda wasu 'yan adawa suka yi wa Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin shekarar.

  Shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar, Hon Abdulmumini Jibril, wanda ya zargi shugabannin majalisar da yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na 2016 ya janyo cece-ku-ce.

  Wannan al'amarin dai ya janyo kwamitin da`ar majalisar wakilan yin bincike dangane da zargin da Hon Abdulmumini Jibril ya yi na cushen.

  Majalisar wakilan ta zargi dan majalisar da bata wa shugabanninta suna da kuma saba wa ka`idojinta, al'amarin da ya janyo har aka dakatar da shi na watanni kafin kotu ta nemi a janye dakatarwar.

  Buhari
  Image caption: An yi wa shugaba Buhari ihu a 2017 lokacin gabatar da kasafin ga majalisa
 15. Majalisa ta yaba da kasafin bana

  Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da shugaban kasar zai gabatar da daftarin kasafin kudi a kan lokaci.

  Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sanya bangaren dokoki a cikin sha'anin kasafin kudin tun ma kafin shugaban ya je zauren majalisar.

  A cewarsa, shugaban ya amince a sanya kudin yi wa mazabu aiki (constituency projects) a kasafin kudin 2020, yana mai cewa ba za a samu matsala wurin amincewa da kasafin kudin a wannan karon ba.

  Buhari
  Image caption: Buhari a majalisar zartarwa lokacin sanya hannu kan daftarin kasafi ranar Litinin
 16. Kasafin kudin Najeriya

  Ranar Talatar nan ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na 2020 ga 'yan majalisar dokoki.

  Shugaban zai gabatar da kasafin kudin ne a zauren majalisar wakilai, inda 'yan majalisar dattawa za su hadu tare da na wakilai domin sauraren jawabin shugaban.

  Zai gabatar da kasafin kudin ne da misalin karfe biyu a agogon Najeriya.

  Buhari
  Image caption: Shugaba Buhari ya sa hannu a kan daftarin kasafin kudin na bana