Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Fauziyya Kabir Tukur da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Ban kwana

  Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.

  Ku duba kasa domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta a yau Alhamis zuwa yanzu da muke rufewa.

  Za ku iya ci gaba da karanta sauran labarai a sauran shafukanmu.

  Muna kara gode maku da kasancewa tare da mu.

 2. Kyanda ta kashe sama da mutane 50,000 a Afirka

  Akalla mutane 140,000 ne ciwon kyanda ya kashe a kamarin da cutar ta kara yi a duniya.

  Afrika ce ta fi yawan mamatan da mutane 52.600 kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ambata.

  Ana dai iya kauce wa wannan cuta ta hanyar allurar riga-kafi. Sai dai an sami rashin cigaban allurar a cikin shekara goma a duk fadin duniya.

 3. Mawakiya Cardi B na kan hanyar zuwa Najeriya

  Cardi B
  Image caption: Cardi B ta lashe kyautuka da dama ciki har da Grammy

  Shahararriyar mawakiya 'yar Amurka Cardi B tana kan hanyarta ta zuwa nahiyar Afirka a karon farko, inda za ta yi wasa a wurin bikin Livespot X Festival da zai gudana a jihar Legas.

  Belcalis Almanzar, wadda aka fi sani da Cradi B ta wallafa a Instagram: "1:03am drop my KK in NY on my way to Afrriiiiicaaaaaaaaaa baybeeeee!!!!!!."

  View more on instagram

  A watan da ya gaba ne ta bayar da sanarwar cewa za ta zo Najeriya domin yin wasa a Legas.

  Za ta yi casun ne a wurin bikin na kwana biyu tare da taurarin mawakan Afirka daga Ghana da Najeriya, irin su Tiwa Savage da Shata Wale da R2bees da sauransu.

  Bikin zai gudana a ranakun Asabar da Lahadi.

 4. A saki Sowore, a ba shi dubu ₦100 – Kotu ta umarci DSS

  Omoyele Sowore
  Image caption: Daga cikin laifukan da ake zarginsa har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta

  Mai Shari'a Ijeoma Ojukwu ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta bai wa hukumar tsaro ta DSS umarnin a ranar Alhamis, inda ta ce a sake shi cikin sa'a 24 tare da biyansa naira ₦100,000.

  Mai shari'ar ta ce umarnin ya biyo bayan kin bin umarnin kotu ne da DSS din ta yi na sakin Omoyele Sowore, wanda aka bayar tun 6 ga watan Satumba.

  Misis Ojukwu ta ce ba zai yiwu hukumar DSS ta mayar da kanta kamar kotu ba, sannan kuma ta bayar da umarnin sakin abokin shari'ar Sowore wato Olawale Bakare.

  Kazalika ta dage sauraron karar har zuwa 6 ga watan Disamba.

  DSS tana tsare da Sowore bisa zarginsa da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon kiran juyin juya hali da ya yi - ya yi masa lakabi da Revolution Now.

  Omoyele Sowore shi ne mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake wallafawa a intanet.

  Daga cikin laifukan da ake zarginsa da su har da tsokanar Shugaba Buhari a shafukan sada zumunta.

 5. Majalisar Dattawa ta amince da dokar kasafin kudi ta 2020

  Sanatoci a Najeriya

  Majalisar Dattijai a Najeriya ta sa hannu kan dokar kasafin kudi ta 2020, wanda ya kai naira tiriliyan 10.59.

  Majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya ce yaba wa abokan aikinsa kan kokarin da suka yi wajen tabbatar da cewa sun gyara tsarin kaddamar da kasafin kudi ta yadda zai kasance duk karshen shekara.

  A baya dai majalisar kan dauki sama da wata hudu kafin kammala muhawara tare da amincewa da kasafin kudin.

  Ahmed Lawan ya ce da ma dai wannan na daya daga cikin abubuwan da suka ci alwashin yi a majalisa ta tara.

  Ya kuma yi wa bangaren zartaswa fatan alheri da fatan gudanar da aiki da kasafin kudin yadda ya kamata.

 6. Sudan da Amurka za su tura jakadu kasashen juna

  Amurka da Sudan za su tura jakadu kasashen juna a karon farko cikin shekaru sama da ashirin.

  Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo da Firayim Ministan Sudan, Abdallah Hamdok suka sanar da haka lokacin da Mista Hamdock ya kai ziyara Washington.

  Rabon da kasashen su aika da jakadu kasashen juna tun shekaru 23 da suka gabata.

  Amurka ta rufe ofishin jakadancinta da ke Khartoum a 1996, a cewarta saboda ta'addanci.

  Amurka ta sake bude ofishin a 2002 ba tare da jagorancin wani jakada ba, sai mai kula da ofishin kawai.

 7. 'Yan ci rani 57 sun mutu a gabar tekun Mauritaniya

  A kalla mutum 57 suka mutu a yayin da jirgin ruwansu ya kife a gabar tekun Mauritania, a cewar hukumar kula da da 'yan ci rani ta Majalisar Dinkin Duniya.

  A makon da ya gabata ne jirgin ruwan ya bar Gambiya dauke da 'yan ci rani 150, a cewar Kungiyar da ke kula da Kaura ta kasa da kasa.

  Wadanda suka tsira sun shaida wa MDD cewa mai ne ya kare wa jirgin a yayin da yake tunkarar Gabar tekun Mauritaniya.

  A baya wannan hanyar ce 'yan ci rani daga yankin Afirka Ta Yamma ke bi a kokarinsu na tafiya Turai, amma yanzu sun fi bin hanyar Libiya.

  Gabar Teku
 8. An kama jarka 23 ta man fetur boye a cikin makara

  Jarkokin man fetur
  Image caption: Gwamnatin Najeriya na yaki da fasa kwaurin kayayyaki ba man fetur kadai ba

  Kwamiti mai yaki da fasa kwaurin man fetur a Najeriya na hukumar Customs ya kama wasu jarkoki makare da man fetur boye a cikin makara a kan iyakar Ikorodu ta jihar Legas.

  Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa jarka 23 aka boye a cikin makara guda biyu, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada ya bayyana.

  Abdullahi Maiwada ya kara da cewa an dauko makarar ne a mota kirar Mazda 626 mai lambar LSD 617 CW.

  "A yunkurinmu na ci gaba da yaki da fasa kwauri, kwamitin hadin gwiwa mai yaki da fasa kwaurin man fetur na shiyyar Ogun I sun kama jarka 13 mai cin lita 25 da kuma jarka shida mai cin lita 10 ta man fetur boye a cikin makara guda biyu," in ji shi.

 9. Majalisar jihar Kano ta amince da dokar kirkiro sabbin masarutu

  Umar Abdullahi ganduje

  Majalisar dokokin jihar Kano ta sa hannu kan dokar nan mai cike da ce-ce-ku-ce ta kirkiro sabbin masarautu a jihar, wadda ta bukaci a kirkiro karin masarautu hudu a jihar.

  An sa hannu kan dokar ne a yau Alhamis bayan da majalisar zartarwar jihar ta aikawa majalisar dokokin da ita ranar Litinin.

 10. Kotu ta ce a mayar da El-Zakzaky da matarsa gidan yari

  Wata kotu da ke zama a Kaduna ta yanke hukuncin mayar da jagoran kungiyar IMN a Najeriya Sheikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa gidan yari daga hannun hukumar tsaro ta farin kaya.

  Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Alhamis da safe, inda ta ce za a mayar da su gidan yarin ne don lauyoyinsu da likitocinsu su samu damar ganinsu cikin sauki.

  Tun watan Disambar shekarar 2015 gwamnatin Najeriya ke tsare da malamin biyo bayan rikicin da ya faru tsakanin mabiyansa da jam'ian tsaro a Zariya.

  Alkalin Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga ci gaba da sauraron shari'ar har zuwa 9 ga watan Fabrairun 2020.

  A watan Maris ne Mai Shari'a Gideon Kudafa ya daga sauraren karar har sai baba ta gani sakamakon sanya shi cikin mambobin kotun sauraron kararrakin zabe.

  zakzaky
 11. An yanke wa Sanata Orji Kalu hukuncin dauri shekara 12

  Orji Uzo Kalu

  Wata babbar kotu a Legas ta yanke wa sanata mai ci kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzo Kalu hukuncin zama a gida kaso tsawon shekara 12 bisa zargin almundahanar Naira biliyan 7.65.

  Mai shari'a Mohammed Idris ya bayyana cewa an kama sanatan da laifin da ake zarginsa da shi, kuma an kwashe tsawon shekara 12 ana shari'ar.

  An yi sharia'r Mista Kalu tare da kamfaninsa Slok Nigeria Limited ne da kuma Darektan harkokin kudi na gidan gwamnatin jihar Abia a lokacin da Mista Kalu ke gwamna, Udeh Udeogu.

 12. Kamaru

  Lauyoyi a Kamaru za su shiga yajin aiki

  Lauyoyi a yankin renon Ingila na yunkurin kaurace wa kotuna da fita tituna su yi zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu kan wasu kudurorin doka biyu da gwamnati ke shirin shigarwa majalisar dokoki.

  Daya daga cikin dokokin za ta bai wa ko wane alkali a Kamaru damar yanke hukunci a kotun soji da kotu ta musamman ta manyan laifuka alhalin kuma yankin renon Ingila na amfani da tsarin dokoki ne na tsarin shari'a mai amfani da dokokin kunne ya girmi kaka, wato "common law" sabanin yankin Faransanci mai amfani da tsarin shari'a mai amfani da rubutattun dokoki, wato "civil law".

  Dokar karshe kuma ta shafi malaman jami’a wadanda za su samu damar yin bitar karatu a dukkanin jami’o’i na sassan kasa da za a iya aika su.

  Wannan sabanin tsakanin amfani da harsunan biyu ne musamman ta bangaren lauyoyi, shi ne masabbabin abinda ya haifar da rikicin da ake ciki a yanzu a yankin rainon Ingila tsawon shekara hudu kenan.

  �o

 13. Gobara ta tashi a kusa da rukunin gidajen Diamond Estate a Legas

  Gobara ta tashi a kusa da rukunin gidajen Diamond Estate da ke kan titin Isheri/Lasu -Igando.

  Rahotanni na cewa gobrara ta tashi ne sakamakon fasa bututun man fetur.

  gobara a legas
  gobara a legas
 14. 'Yan Najeriya na nemar wa matar da ''aka ki ba ta taimako a asibiti'' hakkinta

  'Yan Najeriya ne neman a bi wa wata mata hakkinta wacce ''ta mutu a asibiti bayan da suka ki duba ta'' sakamakon caka mata wuka da aka yi a wuya.'

  Asibitin sun yi watsi da zargin da ake musu na kin kula da ita.

  Rahotanni sun ce wani barawo ne ya caka wa Moradeun Balogun wuka a wuya a kan hanyarta ta koma wa gida.

  An garzaya da ita asibiti inda ta yi ta zubar da jini har ta mutu.

  'Yar uwar marigayiyar Molad, ta ce asibitin sun ki karbarta don duba ta suka ce sai an kawo rahoton 'yan sanda.

  View more on twitter

  Sai dai asibitin da aka kai Ms Balogun sun ce ba su ki karbarta ba.

  Daraktan Asibitin Jolad, Funso Oladipo ya shaida wa Jaridar Premium Times cewa likitoci sun karbi Ms Balogun amma sai suka fahimci cewa tana bukatar dubawar kwararru.

  ''Ba mu karbe ta a asibitin ba. Nan da nan muka mayar da ita Gbagada bayan da muka fahimci cewa ba za mu iya ba ta taimakon da take bukata ba kuma wadanda suka kawo ta sun yi tafiyarsu,'' a cewarsa.

  Sai dai 'yan Najeriya suna ta magana a shafukan sada zumunta cewa an ki a duba ta ne, sannan batun nemar mata hakkinta na ci gaba da tashe.

  Ana ta amfani da maudu'in #JusticeForMoradeun, abokai da iyayen marigayiya Moradeun Balogun sun zargi asibitin da nuna halin ko in kula.

  View more on twitter
  View more on twitter
 15. 'Yan bindiga sun kashe dan canji a Abuja

  Nigeria Police

  Rahotanni daga Abuja babban birnin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun harbe wani mutum a wajen 'yan canjin kudi da ke unguwar Zone 4.

  Wasu ganau sun shaida wa BBC cewa wasu mutum biyu ne suka zo a kafa suka bukaci za su yi canjin kudi, ''ya kawo musu kudin kenan sai ga wata mota ta tsaya, wani ya fito da bindiga ya kwace kudaden ya kuma harbe shi a kirji da kai,'' in ji ganau din.

  Ya kara da cewa ''Da yin hakan sai suka shige mota suka gudu.'' Al'amarin ya faru ne da safiyar Alhamis da misalin karfe 9.

  Wajen da lamarin ya faru waje ne na hada-hadar jama'a kuma a tsakiyar babban birnin yake. Tuni dai aka dauki gawar mamacin zuwa asibiti a cewar abokan aikinsa.

 16. Post update

  Masu bin mu a wannan shafi Assalamu Alaikum!

  Ku kasance da mu a yau don karanta labaran abubuwan da ke wakana a najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da Chadi sa ma sauran kasashen da ke makwabtaka da su.

 17. Ban kwana

  Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye.

  Ku duba kasa domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta a yau Laraba zuwa yanzu da muke rufewa.

  Za ku iya ci gaba da karanta sauran labarai a sauran shafukanmu.

  Muna kara gode maku da kasancewa tare da mu.

 18. Majalisar Kano ta kasa cimma matsaya kan dokar sabbin masarautu

  Zaman da majalisar dokokin jihar Kano ta yi a yau kan duba dokar kirkiro sabbin masarautu ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.

  Yayin zaman, 'yan majalisar sun yi muhawara kan dokar har na tsawon sa'a uku a kebe ba tare da 'yan jarida ba.

  Sai dai ba su samu yadda suke so ba, yayin da suka yi yunkurin yi wa dokar karatu na biyu a yau din biyo bayan kammala karatu na farko.

  Sai dai sun ci alwashin ci gaba da duba dokar a zamansu na gobe Alhamis.

  A gefe guda kuma, wasu daga cikin 'yan majalisar jam'iyyar adawa ta PDP a jihar sun yi yunkurin sukar dokar a zauren majalisar amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, inda suka rika daga hannu amma aka hana su damar yin magana ba.

  PDP tana da 'yan majalisa 12 ne kacal cikin 40 a majalisar, abin da ke nufin ba za su iya kawo tsaiko ga dokar ba saboda ba su kai biyu bisa uku ba, wanda shi ne yawan 'yan majalisar da doka ta tanada su amince kafin yin wata doka.

  Idan za a iya tunawa dai a ranar 21 ga Satumban 2019 ne Mai Shari'a Usman Na’abba na babbar kotun jihar Kano ya soke dokar farko da majalisar ta yi na kirkiro masarautun Karaye da Gaya da Bichi da Rano, inda ya ce ba a bi ka'ida ba yayin yin ta.

  Daga nan ne kuma 'yan majalisar suka daura aniyar sake yin dokar ta hanyar da ta dace bisa kudirin da gwamnati ta aike masu. A baya dai cikin kwana daya aka kai kudiri kuma aka kaddamar da dokar.

  Masarautar Kano
 19. Buhari ya koma Abuja, ya kaddamar da daftarin tsaro

  Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani daftarin tsaro na kasa baki daya da aka kira shi da National Security Strategy 2019, wanda kuma ofishin mai bai wa shugaban shawara kan harkar tsaro ya samar.

  Bayan haka ne kuma Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa wato Federal Executive Council kamar yadda aka saba duk ranar Laraba.

  Duk wannan ya faru ne jim kadan bayan ya koma birnin tarayya Abuja daga ziyarar aiki da ya kai jihohin Katsina da kuma Kaduna.

  A wurin taron ne kuma Buhari ya jaddada yunkurin gwamnatinsa na inganta harkar tsaro a Najeriya.

  Shugaba Muhammadu Buhari
  Shugaba Muhammadu Buhari
 20. EFCC ta gurfanar da 'Mama Boko Haram' a gaban kotu

  EFCC

  Hukumar yaki da cin hanci a Njaeriya EFCC ta gurfanar daTahiru Saidu Daura da Barista Aisha Alkali Wakil, wadda ake yi wa lakabi da Mama Boko Haram, a gaban kotu bisa zarginsu da laifin zambar kudi naira miliyan 66.

  Hukumar ta ce mai Shari'a Aisha Kumaliya ce ta babbar kotun jihar Borno ce za ta jagoranci shari'ar a yau Laraba, inda ake zarginsu da laifuka har uku.

  Mamallakin kamfanin AMTMAT Global Ventures mai suna Ali Tijjani ne ya yi korafi kan gidauniyar Complete Care and Aids Foundation, wadda Mama Boko haram ke jagoranta, bisa zargin zamba kan biski da ya samar wa gidauniyar.

  Sai dai jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa tuni kotun ta yi zaman kuma har an bayar da belin Aisha Alkali Wakili kan kudi naira milyan 30, amma saboda rashin halartar wadanda ake zargin kotun ta ce za ta dage bayar da belin.

  Barista Aisha Alkali Wakil ta taka rawa yayin tattaunawar sulhu tsakanin kungiyar Boko Haram da gwamnatin Najeriya, abin da ya sa ake yi mata lakabi da Mama Boko Haram.