Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Fauziyya Kabir Tukur

time_stated_uk

 1. Kammalawa

  Duka-duka a nan muka kawo karshen kawo muku bayanai na abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da ma sauran sassan duniya. Sai kuma idan Allah ya kai mu ranar Litinin.

  Kafin nan ku ci gaba da kasancewa da shafinmu na BBC Hausa.com da sauran shafukanmu na kafafaen sada zumunta domin samun labarai. Mun gode

 2. MTN ya ba abokan cinikinsa hakuri kan rashin sabis

  Kamfanin sadarwar wayar salula na MTN, ya nemi afuwa ga miliyoyin abokan cinikinsa da ke tsakiya da kuma Yammacin Afirka, bayan da aka samu matsalar sabis sakamakon lalacewar wata wayarsu da ke karkashin ruwa.

  Kamfanin ya ce yana yin dukkan mai yuwuwa domin shawo kan matsalar, wacce ta fara a ranar Alhamis.

  Hanyoyin sadarwa na waya da kuma Internet a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun rika katsewa, amma masu amfani da layin a kasashen Ghana, Najeriya da Ivory Coast suma sun koka game da matsalar sabis din.

  MTN
 3. 'Akwai yiwuwar hana Rev Father Mbaka yin wa'azi'

  Ejike Mbaka tare da shugaba Muhammad Buhari

  Babban limamin cocin Katolika da ke Legas, Adewale Martins, ya ce akwia yiwuwar hana Rev Fr Ejike Mbaka na cocin Adoration Ministry daga yin wa'azi, idan har ya ci gaba da irin yadda yake gudanar da wa'azin nasa da ya kauce wa tanade-tanaden akidar katolika.

  Adewale Martins wanda fafaroma ya nada a matsayin babban limamin cocin ta katolika a 2012, ya shaida wa sashen BBC Igbo cewa dole ne Father Mbaka ya daina 'wuce gona da iri'.

  Martins dai na mayar da martani ne kan hasashen da Mbaka ya yi cewa Sanata Hope Uzodinma zai zama gwamnan jihar Imo.

  A ranar jajiberin sabuwar shekara ne dai Mbaka ya yi hasashen cewa Hope Uzodinma zai zama gwamnan jihar Imo a shekarar 2020.

 4. Labarai da dumi-dumiKotu ta rushe zaben Sanata Ifeanyi Uba

  Sanata Ifeanyi Uba

  Wata babbar kotu a birnin Abuja da ke zama a yankin Bwari ta rushe zaben Sanata Ifeanyi Ubah na jam'iyyar Young Progessives Party da ke wakiltar jihar Anambra a majalisar dattawan Najeriya.

  Gidan talbijin na Channels TV da ya rawaito labarin ya ce Sanata Ubah na da damar daukaka kara nan gaba.

 5. Gini ya rushe a Legas

  Wani gini mai hawa biyu ya rushe a titin Ago Palace Way da ke Legas da misalin karfe shida na safiyar yau.

  Jami'an hukumar LASEMA mai kula da muhalli a Legas sun ciro mutum daya da ya makale a cikin ginin da ransa.

  Mutumin ya makale ne a cikin baraguzan ginin.

  Rushewar ginin ya ritsa da shi ne a lokacin da yake bacci, kamar yadda wasu mazauna unguwar suka shaida wa wakilin BBC.

  Sauran mutanen da ke zaune a cikin ginin sun tsere, inda wasu suka samu kananan raunuka.

  Gini ya rushe a Legas
  Image caption: Ginin bayan da ya rushe a Ago Palace Way
  Gini ya rushe a Legas
  Gini ya rushe a Legas
  Gini ya rushe a Legas
  Gini ya rushe a Legas
 6. Harin masu tada kayar baya ya halaka mutane a Mali

  Rahotanni daga Mali na cewa kimanin mutane 15 ne suka mutu ranar Alhamis sakamakon wani hari da ‘yan tada kayar baya suka kai kan wani kauyen Fulani da ke tsakiyar kasar.

  Kawo yanzu, kafafen yada labaran kasar basu yi rahoto game da ta’annatin ba.

  Mutanen da suka fito daga kabilar Dogon na zargin Fulani da shigo da shanunsu cikin gonakinsu tare da lalata musu amfanin gona.

  Lamarin dai ya dade yana janyo rikici tsakanin bangarorin biyu amma an sha yin sulhu a tsakaninsu musamman game da rikicinsu kan albarkatun kasa.

  Sai dai rikicin masu da’awar kishin Musulunci da ya fara a arewacin Mali a 2012 tare da yaduwa zuwa yankunan tsakiyar kasar a 2015 ya janyo rashin dai-daito da karuwar makamai da kuma rashin ikon da gwamnati take da shi a yankin.

  Mali Attack
 7. Farin dango sun far wa Sudan ta Kudu

  Ministan noma da abinci a Sudan ta Kudu ta sanar da annobar farin dango a kasar, wacce ya ce barazana ce ga kayan abinci a kasar.

  Minista Onyioti Adigo Nyikuach ya ce gwamnati ta kafa wani kwamiti don tattara kudi da kayan aiki domin dakatar da yaduwar farin.

  An samu karuwar yaduwar fari sosai a 'yan makwannin nan a yankin da ma kewaye.

  Farin dango
 8. Magungunan bogi na kashe dubban mutane a Afrika

  Fake Drugs

  Shugabannin lafiya daga kasashen Afrika bakwai za su yi taro yau Juma'a a Lome, babban birnin Togo don sa hannu kan wata yarjejeniya da za ta mayar da sayarwa da amfani da magungunan bogi su zama manyan laifuka.

  Dubban mutane a Afrika na mutuwa duk shekarar saboda magungunan bogi.

  Wakilai daga Jamhuriyar Congo da Gambia da Ghana da Nijar da Senegal da Togo da Uganda suna fatan cewa dokokin za su kawo karshen matsalar.

 9. Buhari zai tafi Landan

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi birnin Landan a ranar Juma'a domin halartar taron zuba jari na Birtaniya da Afirka.

  Taron wanda za a yi ranar 20 ga watan Janairun nan, ya zama tafiyar Buhari ta farko zuwa wani wuri a shekarar 2020.

  Ana fatan taron zai samar da sabbin damarmakin kasuwanci da zuba jari da samar da ayyuka, wanda zai amfani nahiyar Afirka da Birtaniya.

  Muhammadu Buhari
 10. An dauke wuta a sassan Najeriya da dama

  Wutar Lantarki

  Babban layin da ke samar wutar lantarki a Najeriya ya lalace sau biyu cikin sa'ao'i biyu ranar Alhamis a wasu sassan Najeriya, wanda kuma ya kara lalata rashin wutar lantarkin da kasar ke fama da shi.

  Layin, wanda kamfanin da ke rarraba wutar lantarki na gwamnati ke kula da shi, ya sha lalacewa a shekarun baya.

  Kamfanin ya sanar da cewa layin ya samu matsala ne da misalin karfe 12.30 na rana ranar Alhamis.

  Kalmomin 'NEPA' da 'national grid' sun yi ta tashe a shafukan sada zumunta a lokacin da mutane suka rika bayyana bacin ransu kan rashin wutar.

 11. Za a rage farashin man fetur a Najeriya

  Gwamnatin Najeriya ta ce za ta rage farashin man fetur ta hanyar samar da iskar gas wacce ake iya aiki da ita a madadin sauran makamashi, a matsayin wata hanyar samun makamashi ga ababen hawa a fadin kasar.

  A wani taron manema labarai, karamin ministan mai, Timipre Sylva ya ce gwamnatin Najeriyar na aiki wajen ganin ta sa hannu kan kudirin doka na man fetur, PIB, kafin watan Mayun bana.

  Sai dai bai bayyana hanyoyin da za a bi ba wajen cimma hakan.

  Timipre Sylva
 12. Barka da safiya

  Yola

  Da fatan Juma'atu babbar rana ta riske ku lafiya.

  Ku kasance da mu don sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya baki daya.

 13. Karshe

  To maus bibiyar mu a nan muka kawo karshen kawo muku labarai kai tsaye na yau. Da fatan za ku kasance tare da mu a gobe Juma'a domin ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a Afirka da ma Najeriya da Nijer da sauran sassan duniya.

 14. WAEC ta ayyana makarantu 165 a Kwara da masu 'magudin jarrabawa'

  Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya yi barazanar kakaba wa shugabannin makarantun jihar takunkumi musamman wadanda aka kama da hannu a magudin jarrabawa.

  Ya ce irin wannan magudin na jarrabawa a 2019 ne ya sa hukumar jarrabawar ta WAEC ta sanya makarantu 165 na jihar a jerin makarantu masu magudin jarrabawa sannan kuma ta ci su tarar kudi N250,000.

  AN dai gudanar da jarrabawar WAEC a jihar tsakanin 8 ga watan Afrilu da 31 ga watan Mayu.

 15. 'Yan bindiga sun kashe mutum biyu a Zamfara

  Zamfara

  'Yan bindiga sun kashe wasu ma'aikatan lafiya guda biyu da ke aiki a garin Makosa na karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

  Jaridar Punch ta rawaito cewa ma'aikatan lafiyar na aikin duba yadda ma'aikata ke tafiyar da diga allurar shan inna ta Polio a ranar Talata a yankin lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude musu wuta, bayan far wa kauyen da misalin karfe 2:30 na rana.

  Da ma dai al'umomin kauyuka a yankunan jihar Zamfara na kokawa kan yadda mahara ke ci gaba da kai musu hare-hare, duk da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin jihar ke ikirarin cewa ta cimma da maharan a watannin baya.

 16. Kotu za ta ci gaba da shari'ar Ayo Fayoshe

  Babbar kotun jihar Legas ta ware ranar 17 ga watan Fabrairu domin yanke hukuncin amince wa ko akasin haka dangane da bayyanar shugaba mai kula da hada-hadar bankin Zenith da ke birnin Ado-Ekiti, Mr Johnson Abidakun a gaban kuliya domin bayar da shaida kan shari'ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar EKiti, Ayo Fayoshe.

  EFCC ta gabatar da Abidakun domin maye gurbin matukin motar daukar kudi mai sulke ta bankin na Zenith da ke Ado-Ekiti, Adewale Aladegbola wanda ya bayar da shaida tun da farko.

  Hukumar EFCC dai ta gurfanar da shi ne a ranar Litinin kan tuhume-tuhume 11 ciki har da laifukan cin hanci da rashawa da halarta kudin haram da sauransu.

  Ana kuma zargin shi da karbar dala miliyan biyar daga hannun tsohon ministan tsaron kasar Musiliu Obanikoro, wanda ta ce ya yi amfani da su wajen yakin neman zaben gwamnan jihar a shekarar 2014.

  Sai dai tsohon gwamnan ya musanta duka wadannan tuhume-tuhumen.

  Fayoshe
 17. Masu garkuwa sun saki dagacin Karshi a Kano

  'Yan sanda

  A ranar Alhamis din nan masu garkuwa suka saki dagacin garin Karshi da ke karamar hukumar Rogo ta jihar Kano, bayan kwashe kwanaki uku a hannunsu.

  A ranar Litinin ne dai aka sace hakimin a kauyensa da ke yankin kudancin Kano.

  Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da sace dagacin na Karshi a karamar hukumar Rogo.

  Garin nasa na iyaka da jihar Kaduna.

  Rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta ce ta tura wata runduna ta musamman domin neman dagacin da kuma kubutar da shi.

  Ana kara samun yawaitar sace mutane domin kudin fansa a wasu jihohin Najeriya, tun bayan da abin ya yi kamari a shekarar 2019.

 18. Macen da ta fi kowa kudi a Afrika na son ta yi shugabancin kasarta

  ‘Yar gidan hamshakin mai kudi kuma tsohon Shugaban Angola, Isabel dos Santos ta ce ta na duba yiyuwar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben kasar da za ayi a 2022.

  Hakan na zuwa ne duk da kwace kadarorinta da kuma zargin karkatar da sama da biliyoyin daloli mallakin gwamnati – zargin da ta musanta.

  Cikin wata hira da gidan talabijin din RTP a ranar Laraba, an tambaye ta kan ko tana da sha’awar zama shugaban kasa, sai ta ce "abu ne mai yiwuwa…..zan yi bakin kokarina don kare kasata. "

  Lokacin da mahaifinta Jose Eduardo dos Santos yake shugaban kasa, an nada shi a matsayin shugaban kamfanin mai Sonangol.

  Wata kotun Angola ta umarci a kwace kadarori da rufe asusunta na banki da na mai gidanta Sindika Dokolo da kuma makusancinsu Mario Leite da Silva a Disamba.

  Lamarin ya zo ne bayan zarge-zargen karkatar da sama da dala biliyan 1 daga Sonangol da wani kamfanin hada-hadar lu’u-lu’u Sodiam ga kamfanonin da suke da jari a cikinsu.

  A hirar, ta musanta zarge-zargen da ke cewa cin zarafi ne kan iyalinsa da kuma kokarin rusa mata burinta na siyasa.

  "Ba zamu iya amfani da cin hanci ko kuma batun yaki da cin hanci, domin a yi nazari kan ‘yan siyasar kasar...batu ne na gumurzu don mulki," a cewarta.

  Isabel dos Santos
 19. An bude sabon ofishin ma'aikatar harkokin mata a Najeriya

  Ofishin harkokin mata

  Shugaba Muhammadu Buhari ya bude sabon ofishin Ma'aikatar Harkokin Mata a Abuja, babban birnin Najeriya.

  Mai taimaka wa Shugaban kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya wallafa haka a shafinsa na Twitter.

  View more on twitter

  Bikin bude ofishin ya samu halartar manyan jami'an gwamnati kamar sakataren gwamnati Boss Mustapha, Ministan Sadarwar Najeriya Ali Isa Pantami da Ministar Jin-Kai da bayar da Tallafa Sadiya Umar Farouk.

 20. Syria

  An kashe mutum 18 a wani hari a Idlib duk da yarjejejniyar tsagaita wuta

  Harin Syria

  A kalla fararen hula 18 ne suka mutu a wani jerin hare-haren sama da aka kai wata kasuwa da wata unguwa da ke da yawan masana'antu a birnin Idlib da 'yan tawaye ke rike da shi a Syria.

  Wata kungiya mai sa ido ta ce jiragen gwamnatocin Rasha da Syria ne suka kai hare-haren.

  An kai hare-haren saman ne duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da Rasha da Turkiyya su ka yi a farkon watan nan.

  Idlib ne babban birnin lardin arewa maso yamma kuma nan ne 'yan tawaye suka fi karfi.

  Har yanzu gwamnatin Syria da na Rasha ba su ce komai ba kan hare-haren.