Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

 1. Rufewa

  A nan muka kawo karshen labarai da bayanai kai-tsaye da muke kawo maku a wannan a shafi.

  Sai kuma Litinin idan Allah Ya kai mu.

  Za ku iya duba kasa don karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sauran sassan duniya wanda muka wallafa, mun gode.

 2. An jinkirta zabe a Habasha saboda fargabar damuna

  Hukumar zaben Habasha ta dage babban zaben kasar da aka dade ana jiran gudanar da shi da kusan mako biyu.

  A yanzu za a gudanar da babban zaben ne ranar 29 ga watan Agusta.

  A baya, an sanya ranar 16 ga Agusta sai dai an yi ta sukar batun saboda ana yanayin damuna ne a kasar inda mutane da dama suke zaune a kauyuka.

  Da take sanar da sauyi a jadawalin zaben, Shugabar hukumar, Birtukan Mideksa - wata tsohuwar mai shari'a wadda ta taba zama firsunan siyasa - ta ce a karshen watan Agusta ruwan sama na raguwa.

  Za a fara rijistar masu zabe a watan Afrilu, kuma jam'iyyun siyasa za su iya fara yakin neman zabe a karshen Mayu na 2020.

  Ethiopia
  Image caption: Birtukan Mideksa, Shugabar hukumar zabe, ta ce ana samun raguwar ruwan sama a karshen watan Agusta
 3. An kashe mutum 20 a Mali

  An kashe mutum 20 a yankin Mopti da ke tsakiyar Mali a wani sabon rikici da ya barke tsakanin wasu kabilu biyu da ba sa ga maciji da juna.

  Harin wanda aka kai a cikin dare, ana zargin 'yan banga da ga al'ummar Dogon ne suka kai shi, wato kauyen da aka kashe mutum 160 a watan Yunin bara.

  Harin dai ya janyo saukar manyan jami'an gwamnatin Mali a lokacin.

  Mahukunta daga kauyen sun ce kauyen wanda Fulani ne a cikinsa, an kona shi inda mutum 20 suka mutu, yayin da har yanzu kuma ba a ga wasu 20 ba.

  Sojojin Mali
  Image caption: Sojojin Mali
 4. An lakada wa ango duka ranar aurensa

  An kori wani ango daga wajen bikinsa bayan matarsa ta farko ta je wajen domin sanar da amaryar cewa yana da mata biyu.

  Asif Rafiq Siddiqi, wanda ke a tsakanin 34 zuwa 37, ya sha duka da mari daga wajen mahalarta bikin amaryar da zai kara aura.

  An yaga masa kaya inda ya ranta ana kare ya samu wasu suka ce-ce-shi. An dai halatta auren mata a Paistan.

  To sai dai kuma, duk da an halatta wa mutum ya auri mata hudu, to dole ne ya shaida wa sauran matansa kafin auren.

  To sai dai ga dukkan alamu, Mr Siddiqi bai bi wannan tsari ba, shi ya sa a lokacin da amaryar ta sa ta samu labari, ita da 'yan uwanta ba su yi wata-wata ba suka lakada masa duka.

  Wannan lamari dai ya faru ne a birnin Karachi.

  An lakadawa ango duka
  Image caption: An lakadawa ango duka
 5. 'An gano gangar mai biliyan daya a arewa maso gabashin Najeriya'

  Karamin ministan albarkatun mai a Najeriya, Chief Timipre Sylva ya ce an gano gangar danyen mai kimanin biliyan daya a arewa maos gabashin kasar.

  Sylva ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a karshen taron duniya da aka gudanar kan man fetur a Abuja, babban birnin kasar.

  ''Bayanan da muke samu sun ce an gano gangar danyen mai kimanin biliyan daya a arewa maso gabashin kasar.'' in ji Sylva.

  Daily Trust ta rawaito Sylva na cewa akwai bukatar a kara kaimi wajen hako mai a kasar saboda za a iya gano karin man a wasu wuraren.

  Albarkatun mai
 6. Masu zanga-zanga sun lalata dukiyoyi a gidan zababben gwamnan Bayelsa

  Wasu fusatattun magoya baya da ake zargin mambobin jam'iyyar APC ne sun kai hari gidan zababben gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri sakamakon hukuncin kotun koli da ya kwace nasarar dan takarar jam'iyyar APC, Chief David Lyon ranar Juma'a.

  Masu zanga-zangar tun da farko sun rufe titunan Yenagoa babban birnin jihar domin gudanar da zanga-zanga kan hukuncin kotun.

  Daily Trust ta ruwaito cewa zanga-zangar ta juye zuwa rikici inda aka lalata dukiyoyin wasu jagororin PDP.

  Sun lalata motocin da aka ajiye a harabar gidan zababben gwamnan da kofofi da kuma winduna na gidan lamarin da ya sa mutanen da suke gidan a lokacin neman tsira.

 7. An wanke 'yan jaridar da ake zargi da yunkurin juyin mulki a Turkiyya

  Kotu a Turkiyya ta wanke wasu 'yan jarida biyu daga zargin ta'addanci bayan yunkurin juyin mulkin da bai kai ga gaci ba.

  Sun hada da wata fitacciyar marubuciya da ake kira Asli Erdogan da yanzu haka ke neman mafaka a Jamus.

  Ana zargin suna da alaka da jaridar Ozgud Gundem wadda yawancin masu karanta ta Kurdawa ne.

  Hukumomi a kasar sun rufe kamfanin jaridar a watan Satumban 2016, bayan ta da yada farfagandar da ta kai ga yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

 8. Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton Amnesty International

  Rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton kungiyar Amnesty International da ya zargi sojojin kasar da kona kauyuka a Borno.

  Rundunar ta yi martanin ne a shafinta na Twitter inda ta ce daman Amnesty International ta saba batawa sojin Najeriya suna.

  Ta ce zarge-zargen da kungiyar ta yi yaudara ce kawai da kuma rashin sanin abubuwan da suke faruwa game da yakin da ake da masu tada-kayar baya a arewa maso gabashin kasar.

  View more on twitter
 9. Kotu ta tsare mutanen da suka yi fashi a wani banki a Abuja

  Wata babbar kotu ta ba da umarnin tsare mutum biyar da ake zargi da hannu a kai hari kan wani bankin kasuwanci a Abuja babban birnin Najeriya.

  Mai shari'a Ajoke Adepoju ne ya ba da umarnin tsare mutanen a kurkukun Kuje sakamakon gurfanar da su a gaban kotu yau Juma'a.

  Gidan talbijin na Channels ya ruwaito an gurfanar da mutanen a rundunar 'yan sanda ta Abuja makwanni bakwai bayan sun aikata laifin da ake zarginsu.

  Ana zarginsu da aikata laifuka biyar da suka shafi hada baki wajen yin fashi tare da rike mallakar makamai ba bisa ka'ida ba.

  Lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhumen da ake yi musu, dukkan mutanen biyar sun musanta zargin.

  Lauya mai gabatar da kara James Idachaba ya roki kotu ta bai wa bangarorin biyu mako guda domin fara sauraron shari'ar.

  Ya kuma sanar da kotu cewa 'yan sanda a shirye suke su gabatar da shaidu bakwai domin bada bahasi a karar.

  Abuja
 10. An kai shugabar jami'a kara kan tilasta wa dalibai cire kayansu don duba hailarsu

  An shigar da korafi gaban 'yan sanda a India kan wata shugabar jami'a a yammacin Indiya bayan da aka tilasta wa dalibai mata cire suturunsu don tabbatar da cewa ba su fara haila ba.

  Ana kuma binciken wani mai kula da masaukin baki da malamai guda biyu a Sahjanand Girls Institute da ke jihar Gujarat bayan da aka garzaya da dalibai 68 zuwa dakin wanka kuma aka ba da umarnin kwabe musu kaya.

  Mahukuntan kwalejin sun ce daga baya matan sun nemi afuwa saboda keta ka'idojin saukar baki, wadanda suka dade a India.

  Mahukuntan makarantar na gani cewa galibi mata na rashin tsafta a lokacin da suke haila.

 11. An wanke dan majalisar Zimbabwe na bangaren hamayya daga zargin cin amanar kasa

  Wata kotu a Zimbabwe ta wanke dan majalisa na bangaren hamayya daga zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Emmerson Mnangagwa.

  Job Sikhala ya fuskanci hukuncin zama a gidan yari na tsawon shekara 20 bayan da aka kame shi bisa yi wa gwamnati zagon kasa bayan fada wa magoya bayansa a wani gangami da aka gudanar bara cewa jam'iyyarsa ta MDC za ta hambarar da shugaban kasa kafin zabe mai zuwa.

  An gudanar da bukukuwa a ciki da wajen babbar kotun da ke tsakiyar birnin Masvingo bayan da aka wanke shi.

  Wani dan jarida a Zimbabwe ya wallafa wani hoton bidiyo a shafinsa na Twitter inda ya nuna magoya bayan MDC suka fantsama kan tituna.

  View more on twitter

  Alkalin da ya saurari shari'ar Job Sikhala a Masvingo ya ga baiken zargin cewa Job ya na son kifar da gwamnati.

  An kuma wanke shi daga wannan zargi.

  Alkalin ya ce ya kamata a bar 'yan siyasa su zama 'yan siyasa inda ya ce babu aibu a cikin abin da Job ya fada.

  A watannin baya-bayan nan mutane da dama sun fuskanci tuhumar yi wa gwamnati zagon kasa sai dai masu sukar gwamnati na cewa alama ce hukumomi na cin zarafin bangaren hamayya.

 12. Majalisar dokokin Ekiti ta amince da kudirin Amotekun a matsayin doka

  Majalisar dokokin Ekiti a yau Juma'a ta amince da kudirin samar da hukumar tsaro ta jihar a matsayin doka.

  Shugaban majalisar, Funminiyi Afuye ya ce ''kasancewar kudirin ya samu wuce karatu na biyu, a yanzu ya zama doka.''

  Afuye wanda ya yaba wa 'yan majalisar bisa jagorancinsu da kuma sadaukarwarsu ga kudirin ya ce majalisar ta bi tsari wajen tabbatar da kudirin a matsayin doka.

  Shugaban majalisar ya ce za su mika kudirin ga Gwamnan jihar Dr Kayode Fayemi domin amincewarsa.

  Dokar ta samu wuce karatu na daya da na biyu a majalisar ranar Alhamis, inda aka mika shi ga kwamitin tsaro na majalisar domin duba shi kafin majalisar ta dage zamanta zuwa ranar Juma'a.

  'Yan majalisar wadanda suka tafka muhawara kan kudirin sun bayyana cancantarsa saboda matsalolin tsaron da ake fuskanta a jihar da yankin kudu maso yammacin Najeriya.

  An kuma gudanar da zaman sauraron ra'ayin jama'a kan kudirin a jiya Alhamis.

  A baya-bayan nan ma, majalisar dokokin Ogun ta amince da kafa hukumar tsaro ta Amotekun.

  Ekiti
 13. An karkatar da akalar jiragen sama saboda hazo

  An karkatar da akalar jiragen saman da ke kan hanyar zuwa Najeriya domin sauka a wasu filayen jiragen sama saboda yanayin hazo da kuma iska da ke kadawa.

  A baya-bayan nan ana fuskantar yanayin hazo a Legas da wasu jihohin Najeriya.

  Hukumomin kula da filayen jiragen sama sun ce iskar na da karfi sannan tun kwana uku da suka gabata ake juya akalar jiragen da za su sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammad zuwa ko dai babban birnin tarayya Abuja ko kuma Accra, babban birnin Ghana.

  Ana fuskantar yanayin hunturu da ke kadawa daga yankin Sahara tsakanin Nuwamba zuwa Maris.

  Wani matukin jirgin sama ya shaida wa BBC cewa filin jirgin saman Murtala Muhammad ba shi da na'urar da zai taimaka wa jiragen sauka.

  Hakan na nufin jiragen ba za su iya sauka ba idan ana hazo.

  Dubban fasinjoji ne suka yi cirko-cirko a filin jirgin saman Legas sannan wasu suna wasu filayen jiragen saman domin isa Legas.

  Babban jami`in sadarwa na hukumar kula da jiragen sama na Ghana Mr Eric Mireku Amaning ya fada wa manema labarai cewa, kusan jirage shida ne suka sauya akala zuwa Ghana mafi yawan su wadanda zasu sauka a Najeriya.

  Ya cigaba da cewa jiragen sun hada da British Airways da Delta Airlines da Emirates Airlines da Air France da Qatar Airways da kuma RwandAir, yayin da wasu daga cikin jiragen har yanzu suke zaman jiran yanayi ya inganta kafin su tashi zuwa Najeriya.

  Legas
  Image caption: Wadannan fasinjoji sun tsinci kansu a Accra a maimakon Legas
  Legas
  Image caption: Fasinjoji a Accra na dakon bayanai kan lokacin da za su samu tafiya Legas
 14. 'Sojojin Najeriya sun kone wasu kauyuka'

  Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa sojojin Najeriya sun kona wasu kauyuka na jihar Borno tare da tursasa wa mazauna kauyukan barin muhallansu a wani martani na harin da aka kai baya-bayan nan.

  Kungiyar ta ce ta samo wannan bayanin ne daga tattaunawar da ta yi da mazauna kauyukan da aka kona.

  Kauyukan ne: Bukarti da Ngariri da kuma Matiri.

  Kungiyar ta ce sojojin sun kuma kama tsare wasu maza shida ba tare da laifin komai ba daga kauyukan da ta konan.

  Kungiyar ta Amnesty ta tattara dukkan bayananta a kan rikicin da ke faruwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na tsawon shekara 10.

  Amnesty ta ce, an hana mazan da aka tsaren magana da kowa kusan wata guda tare da azabtar da su har sai da aka sake su a ranar 30 ga watan Janairun 2020.

  Daraktan kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho, ya ce " Ya kamata a bincike sosai a kan abin da ya faru a game da kona kauyukan da kuma tursasawa mazauna yankunan barin gidajensu ba tare da laifin komai ba."

  Daraktan ya ce "Mun jima muna nanata irin cin zarafin da sojojin Najeriya ke yi wa fararen hula, amma ba a dauki matakin komai ba, don haka yakamata a bincika a yi wa wadanda aka zalinta adalci."

  Sojin Najeriya
 15. PDP ce ta lashe zaben Bayelsa - INEC

  Hukumar zaben Najeriya, INEC, ta tabbatar da cewa jam'iyyar PDP ce ta lashe zaben gwamnan jihar Bayelsa da ke kudu maso kudancin kasar.

  Shuugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya tabbatar da hakan a taron manema labaran da hukumar ta gudanar ranar Juma'a a Abuja, babban birnin kasar.

  A ranar Alhamis ne kotun kolin kasar ta sauke David Lyon, na jam'iyyar APC, mutumin da a baya INEC ta bayyana a matsayin wanda ya lashe zabe, saboda mataimakinsa Biobarakuma Degi-Eremienyo ya mika wa INEC takardun bogi lokacin da ya tsaya takara a zaben ranar 16 ga watan Nuwambar da ya gabata.

  Da yake jawabi, Farfesa Yakubu, ya ce Mr Douye Diri na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben, kasancewar mutumin da ya zo na biyu da yawan kuri'u a zaben na watan Nuwamba.

  Shugaban na INEC ya kara da cewa Mr Diri ya samu kuri'a 143,172 sannan ya samu kashi 25 cikin dari a kananan hukumomi takwas da aka gudanar da zaben.

  Mr Douye Diri ya samu kashi 25 cikin dari na kuri'un da aka kada
 16. Za a kori wasu 'yan China daga Kenya

  Ministan ciki gida na Kenya ya bayar da umarnin korar 'yan kasar China hudu, wadanda aka kai kotu bayan bidiyonsu ya karade shafukan sada zumunta suna yi wa wani dan kasar bulala.

  Minista Fred Matiang ya sanya hannu kan takardar fitar da 'yan kasar ta China sa'o'i kadan bayan kotu ta bai wa 'yan sanda damar tsare 'yan kasar ta China hudu tsawon kwana 15.

  Har yanzu ba a tuhume su a gaban kuliya ba.

  An tsare su ne ranar tara ga watan Fabrairu bayan jami'an tsaro sun kai samame a kantin sayar da abinci na Chez Wou Restaurant da ke yankin Kileleshwa a ajen birnin Nairobi.

  An gano cewa daya daga cikinsu ne kawai yake da izinin yin aiki a kasar.

  View more on twitter
 17. Lauyoyi sun bukaci a kama Oshiomhole

  Wata kungiyar lauyoyi a Najeriya, Revolutionary Lawyers’ Forum, ta nemi jami'an tsaron kasar su kama shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar, Adams Oshiomhole, sannan su tuhume shi a laifin cin amanar kasar.

  Jaridar TheCable ta ambato shugaban kungiyar Tope Akinyode yana cewa sun yi kiran ne saboda kalaman da Oshiomhole ya yi cewa ba za a rantsar da kowa kan kujerar gwamnan jihar Bayelsa ba, jim kadan bayan kotun koli ta soke zaben gwamnan jihar na jam'iyyar APC.

  Alkalan kotun sun bukaci a rantsar da dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben.

  Mr Tope ya ce kalaman da Oshiomhole ya yi tamkar wani yunkuri ne na kifar da gwamnatin jihar ta Bayelsa.

  Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce:“Muna kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kamawa da kuma hukunta Oshiomhole a kotu bisa aikata laifin cin amanar kasa."

  Adams Oshiomhole
  Image caption: Adams Oshiomhole
 18. Laifukan yaki: ‘Za a iya yi wa al-Bashir shari’a a Sudan

  Wata kungiya da ke rajin kare hakkin dana dam ta ce za a iya yi wa tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir shari’a kan zargin akata laifukan yaki da na take hakkin dana dam a kasar maimakon a kotun hukunta masu akata manyan laifukan yaki ta ICC da ke Hague.

  Ranar Laraba ne shugaban mulkin sojan kasar Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya shaida wa kungiyar kare hakkin dana dam ta Human Rights Watch (HRW) cewa zai bai wa ICC hadin kai a yayin da take son gurfanar da Mr Bashir da sauran mutanen da ake zargi da take hakkin dana dam a gaban kuliya.

  Sai dai shugabar Human Rights Watch ta shaida wa BBC Newsday shugabannin kasar sun ce mai yiwuwa gwamnatin Sudan ta yi masa shari’a a cikin kasar, ko kuma kotun ICC ta je kasar domin gudanar da shari’ar.

  Ana zargin al-Bashir da akata laifukan yaki a yankin Darfur.

  Omar al-Bashir
  Image caption: Omar al-Bashir
 19. EFCC tana tattaki kan yaki da cin hanci

  Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’anati tana tattaki a duk fadin kasar ranar Juma’a domin wayar da kan jama’a game da illar cin hanci da rashawa.

  Hotunan da hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter sun nuna yadda ake yin tattakin a jihohi daban-daban na kasar.

  EFCC ta ce ta ware ranar 14 ga watan Fabrairu, wato Ranar Masoya ta Duniya domin gudanar da tattakin ne domin ta janyo hankalin ‘yan kasar bisa illar wannan mugunyar dabi’a.

  View more on twitter
  View more on twitter
  View more on twitter
 20. Kakan yi fada da masoyiyarka?

  Ranar Masoya ta Duniya