Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

 1. Rufewa

  A nan muke muku sallama a labarun da muke kawowa kai tsaye na wannan mako.

  Ranar Litinin idan Allah Ya kai mu, za mu ci gaba da kawo muku karin labaran abubuwan da ke faruwa kai tsaye a Najeriya da sauran kasashe.

  Yi kasa domin karanta labaran abubuwan da suka faru a sassan duniya a wannan makon.

 2. Coronavirus da kashe mutum na farko a Birtaniya

  Yawan wadanda suka kamu da cutar a Birtaniya ya karu zuwa 19 a ranar Juma'a Fabrairu 28.

  Mutum na farko ya rasu ta dalilin kamuwa da cutar coronavirus a Birtaniya.

  Mutuwar mutumin na zuwa ne yayin da yawan 'yan Birtaniya da suka kamu da cutar ya kai 19, bayan an samu karin mutun uku da ke dauke da ita a ranar Juma'a.

  Firai minista Boris Johnson zai jagoranci taron kwamitin gaggawa na gwamnati a game da karuwa masu kamuwa da coronavirus a kasar.

  Ma'aikatar lafiya ta Japan ta ce mutumin na daga cikin 'yan kasar da suka hau jirgin ruwan Diamond Princess da ke gabar kasar.

  Daruruwan mutanen da ke cikin jirgin sun kamu da cutar mai shafar nunmfashi, bayan an killace jirgin a gabar Yokohama na kasar Japan.

  Jirgin ruwan da ya makale a gabar Yokohama, Japan
  Image caption: Jirgin ruwan da mutumin ya hau
 3. 'Yan adawa a Kamaru sun rasa kujerun majalisa

  Daga Killian Ngala BBC News, Yaoundé

  Jam'iyyar hamayya a Kamaru ta rasa tasirin da take da shi a majalisar dokokin kasar saboda sakamakon zaben 'yan majalisa na ranar 8 ga watan nan.

  Sakamakon zaben da majalisar kundin tsarin mulkin kasar ta sanar ya nuna jam'iyyar Cameroon People’s Democratic Movement (CPDM) mai mulki ce ke da rinjaye bayan ta lashe kujera 139 cikin 167.

  Jam'iyyar hamayya ta Social Democratic Front (SDF) kuma ta rasa kujera 10 ina yanzu take da kujera 5 kadai.

  Jam'iyyun hamayya a yanzu suna da kujera 28 ne jumulla.

  Wani masanin shari'a Ashu Ninety ya fada wa BBC cewa a yanzu haka babu wata jam'iyyar adawa da za ta iya kafa kungiyar 'yan majalisa kuma hakan na nufin bangaren hamayya ya rasa damarsa ta rike mahimman mukamai a majalisar kuma ba zai iya neman a yi garambawul ba.

  Kamaru
 4. Yadda mai gadi ya zama minista

  Daga Issa Ahmed BBC News Somali

  Ba kasafai aka fiya samun mai gadi ya zamo minista ba amma hakan ta faru a kan wani dan Somalia Suleiman Yusuf Koore.

  Ya fara a matsayin mai gadi a gidan rediyon Hargeisa wadda ke harabar ma'aikatar yada labaran kasar.

  A matsayinsa na ministan yada labarai a yanzu, Koore shi ne mafi girman mukami a wajen.

  ''A can baya, ba a bari na na shiga ofishin da nake ciki yanzu saboda ni mai gadi ne,'' kamar yadda ya fada wa BBC Somalia.

  A lokacin yana zaune da iyalinsa a wajen Hargeisa kuma yana karbar $12 duk wata.

  Ministoci a yankin Somalia suna karbar $2,000 kowane wata da kuma alawus din $705.

  Koore ya shafe shekara 25 ana damawa da shi a siyasa sannan ya rike mukamai a matsayinsa na minista - amma a Disamba ya fara rike mukamin ministan yada labarai - ma'aikatar da yake kallo a matsayin gida.

  ''Ya yi ma'ana sosai cewa na zama minista a ma'aikatar da na yi aiki ina matashi saboda ta na da muhimmanci a rayuwata,'' kamar yadda ya fada wa BBC.

  Somaliland
  Image caption: Suleiman Yusuf Koore ya zama ministan yada labaran yankin Somalia a Disamba
 5. 'Coronavirus: Najeriya ta na da isassun kayan aikin gano cutar'

  Gwamnatin Najeriya ta yi kira ga 'yan kasar su kwantar da hankalinsu yayin da aka samu bullar cutar coronavirus a kasar.

  A cewar ministan yada labaran kasar Lai Muhammad, gwamnati a shirye take ta gano tare da kula da bullar cutar.

  Ya kuma ce a irin wannan lokaci ne ake samun masu yada labaran karya inda ya ce shafin Facebook yana aiki da gwamnati wajen cire wasu bayanan karya kan coronavirus.

  View more on twitter
 6. An dakatar da ma'aikacin Kenya Airways saboda nadar hoton bidiyon jirgi

  An dakatar da wani ma'aikacin kamfanin Kenya Airways saboda nadar hoton bidiyo yayin da jirgi ke sauka daga China a tashar jirgin sama ta Kenyatta da ke Nairbo babban birnin kasar.

  An yada hoton bidiyon a sassan kasar sannan ya haifar da ce-ce-ku-ce kan gazawar gwamnati ta dakatar da jiragen da suka taho daga China sauka a kasar yayin da ake fama da bazuwar coronavirus.

  Yayin da akasarin 'yan kasar ke kiran ma'aikacin da ''dan bankada'', kamfanin jirgin saman ya kare matakin dakatar da Gire Ali bisa dalilai na tsare-tsaren kamfanin.

  Ali ya wallafa hoton bidiyon ranar Alhamis da ya nuna jirgin kamfanin China Southern Airlines mai dauke da fasinjoji 239.

  Shi ne jirgi na farko daga China da ya sauka a kasar bayan an kakaba takunkumin mako biyu saboda barkewar cutar.

  Duk da ma'aikatar lafiya ta Kenya ya ce dukkanin fasinjojin da ke jirgin sun samu izinin tafiya, da yawa daga cikin 'yan Kenya na son gwamnati ta dakatar da jirage daga China sauka a kasar saboda bullar cutar.

  A ranar Juma'a, kotu a kasar ta bada umarnin hana jirage daga China sauka a kasar na tsawon kwana 10 bayan da wata kungiya ta shigar da kara.

  Kenya
 7. Amurka ta yi gargadi kan yiwuwar sake kai hari a Kenya

  Kenya

  Ofishin jakadancin Amurka a Kenya ya yi gargadin harin ta'addanci a wani babban otel da ke Nairobi babban birnin kasar duk da cewa ba a iya gano inda wajen yake ba.

  Cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis, ofishin ya ce ''kungiyoyin ta'adda'' na iya ''kitsa hari'' kan wajen da ''baki da kuma 'yan kasuwa suke yawan zuwa''.

  Gargadin ya sanya fargabar sake afkuwar harin da aka kai a Janairun 2019 lokacin da Al Shabab ta kai hari otel din DusitD2 tare da kashe mutum 21.

  Amurka ta bukaci 'yan kasarta su kara taka tsan-tsan a lokacin da suke ziyara ko zama a otel-otel din da ke Nairobi''.

  Shugaban 'yan sandan Kenya ya ce sun tura jami'ansu zuwa birnin tare da karfafa tsaro a iyakokin kasar sai dai ya bukaci mutane su kara sa ido.

  Ya kuma wallafa wata sanarwa a shafin Twitter jim kadan bayan ofishin jakadancin Amurkan ya yi gargadin.

  View more on twitter
 8. Rikicin kabilanci ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 12 a Habasha

  Hukumomi a Habasha sun ce mutum 12 sun mutu wasu 7,000 kuma sun daidaita sakamakon rikicin kabilanci a yammacin jihar Gambella.

  Sama da gidaje 400 aka kone sannan aka kwashe dabbobin gida kimanin 300.

  Rikicin ya samo asali ne bayan kisan wani jami'in gwamnati a yankin da kabilar Nuer suka fi yawa.

  Akasarin rikice-rikicen da ake yi a Gambella na faruwa ne kan takaddamar albarkatun kasa.

  A baya-bayannan an samu tashin hankali a sassan kasar inda aka kashe daruruwan mutane sannan sama da mutum miliyan uku suka rasa muhallansu.

  Ethiopia
 9. Coronavirus: Kotu a Kenya ta dakatar da jirage daga China

  Alkali a Kenya ya dakatar da zirga-zirgar jirage tsakanin Kenya da China tare da ba da umarnin gwamnati ta samar da wani tsari na hana bazuwar coronavirus.

  Tun 11 ga watan nan aka dakatar da jiragen kamfanin jirgin sama na China Southern Airlines da ke ta shi daga Guangzhou su bi ta Changsha zuwa Nairobi, amma aka dage dakatarwar ranar Laraba lokacin da fasinjoji 239 suka isa Kenya.

  Wata kungiya kuma ta shigar da kara inda ta bukaci kotu ta dakatar da zirga-zirgar jiragen.

  Kotun ta kuma amsa rokon kungiyar inda ta dakatar da zirga-zirgar jiragen.

  Mai shari'a James Makau ya ce dakatarwar ta kwana 10 ce sannan ya ba da umarnin a dauki matakan kariya da sa ido da kuma magance cutar coronavirus.

  Za a gabatar da tsare-tsaren a gaban kotu domin ta yi nazari a kai.

 10. Coronavirus: Abubuwan da muka sani game da bullar cutar a Najeriya

  • An tabbatar da bullar a Najeriya ranar 27 ga watan Fabrairu a karon farko a kasar da kuma yankin kudu da Sahara da ke Afirka tun bayan barkewar cutar a China a watan Janairu.
  • Mara lafiyar yana samun sauki kuma ana lura da shi a wani asibitin gwamnati da ke Legas
  • An duba mutumin dan Italiya a tashar jirgin sama amma ba a gano yana dauke da cutar ba saboda ana daukar kwanaki kafin gano kwayar cutar.
  • Hukumomin lafiya sun fara bibiyar mutanen da suka shiga jirgi tare da wanda ya kamu da cutar.
  • Ministan lafiya ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin dakile bazuwar cutar. A yanzu haka, akwai wuraren gwaji hudu inda ake gwada mara lafiya.
  • Kimanin likitoci 60 aka tura tashar jirgin saman Murtala Muhammed domin taimaka wa wajen tantance matafiya.
  • Ya zuwa yanzu, Najeriya ta ce ba ta duba yiwuwar hana saukar jirage daga kasashen da suka samu bullar coronavirus sannan ba ta shirin kebe bakin da za su shigo kasar.
 11. Wasu matukan jirgin ruwan Afirka Ta Kudu biyu sun kamu da corona

  Wasu matukan jirgin ruwan Afirka Ta Kudu biyu da ke tuka jirgin Diamond Princess, sun kamu da cutar coronavirus, a cewar Ma'aikatar Lafiya Ta Duniya.

  Ma'aikatar ta ruwaito jami'an kasar Japan na cewa marasa lafiyar biyu ba su nuna alamar kamuwa da cutar karara ba, amma ana ba su magani a Japan.

  Jirgin ruwa yana dauke da a kalla mutum 3,700, amma an killace shi a gabar tekun Yokahama.

  Akwai gomman 'yan Afirka Ta Kudu a cikin jirgin har yanzu, amma ba za a bar su su fita daga jirgin ba har sai sun kammala mako biyu suna kebance ana sa ido a kansu.

 12. Hotunan taro kan yadda za a shawo kan corona a Najeriya

  NCDC
  NCDC
 13. Hisbah ta kama almajirai 21 a Kano

  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da kama almajirai su 21 a yammacin jiya Alhamis.

  Babban Daraktan hukumar, Dr. Aliyu Musa ya ce kamen almajiran da suka yi na zuwa ne bayan umarnin da gwamnan Kano Abdulllahi Umar Ganduje ya bayar na kama yaran da ke bara tare da iyayyensu ko masu kula da su.

  Ya ce suna kamen almajirai tun baya da aka kafa dokar hana bara a jihar cikin 2014, amma dai a nan gaba za su fadada wannan aiki zuwa kan iyayen wadanda suka kama.

  Ga sauran karin bayani a hirar Dr. Aliyu Musa da BBc Hausa:

  Video content

  Video caption: Hira da Dr. Aliyu Musa babban Darakta a hukumar Hisbah kan kama almajirai
 14. Harin gwamnatin Syria ya kashe sojojin Turkiyya 33

  Dakarun Syria

  A kalla sojojin Turkiyya 33 ne suka nutu a wani hari da gwamnatin Syria ta kai wani yanki da ke karkashin ikon 'yan hamayya a arewa maso yammacin Syria a wani fada da yake kara ta'azzara.

  Turkiyya, wacce take goyon bayan 'yan hamayya, ta ce ta kai hari kan sansanonin gwamnati a matsayin ramuwa.

  Rasha, wadda ita ce babbar kawar Syria, ta ce sojojin Syria sun kai wa dakarun Turkiyya hari a yankin Idlib lokacin da suke gumurzu da mayaka masu ikirarin jihadi.

  Rasha ta musanta cewa ba hannun dakarunta a fadan da aka yi a yankin Balyun.

 15. Commonwealth na son magance rikicin makiyaya da manoma a Najeriya

  Kungiyar kasashe renon Ingila, Commonwealth, ta shirya wani taro don nemo bakin zaren magance rikicin Fulani makiyaya da manoma musamman a Najeriya da sauran tashe-tashen hankali da ake zargin makiyayan da aikatawa a kasar.

  Najeriya na daya daga cikin kasashen Afirka da ake fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma, abin da ke jawo asarar rayuka da dukiya musamman ta amfanin gona.

  Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti-Allah Kautal Hore a Najeriyar, Alhaji Bello Abdullahi Badejo wanda ya halarci taron ya leka ofishinmu na London bayan zaman taron a jiya Alhamis, inda ya yi wa Muhammad Annur Muhamad karin bayani kan abubuwan da suka gabatar a wurin:

  Video content

  Video caption: Hira da Bello Abdullahi Badejo na Miyetti Allah kan Commonwealth
 16. Kotu ta soke tsigewar da aka yi wa mataimakin gwamnan Kogi

  Wata babbar kotu a Kogi da ke tsakiyar Najeriya ta ayyana tsigewar da majalisar dokokin jihar ta yi wa mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba a matsayin 'saba ka'ida'.

  Alkalin kotun mai shari'a John Olorunfemi yayin da yake yanke hukunci ranar Alhamis, ya ce cire Achuba daga kan kujerarsa da majalisar dokokin jihar ta yi ya saba kundin tsarin mulkin kasa, sannan ba a bi ka'ida ba wajen nada Edward Onoja a matsayin mataimakin gwamna.

  Mai shari'a Olorunfemi ya bayyana matakin majalisar a matsayin juyin mulki a tsarin dimokradiyya yana mai cewa matakin ya ci karo da sashe na 188 karamin sashe na 8 - wanda ya hana majalisa daukar mataki idan kwamiti ya gano cewa tsohon mataimakin gwamna ba shi da laifi.

  Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa Achuba a baya ya kalubalanci tsigewar da majalisar dokokin jihar ta yi masa, inda ya nemi kotu ta soke tsigewar da aka yi masa sannan ta mayar da shi kan kujerarsa.

  Kogi
 17. Iran ta soke Sallar Juma'a saboda coronavirus

  Iran ta soke gabatar da Sallar Juma'a a birnin Tehran da kuma wasu manyan biranen yankunan kasar 22 a karon farko cikin gomman shekaru, don takaita yaduwar cutar corona.

  Kasar ta kuma takaita zirga-zirga kan hanyoyin zuwa manyan wuraren ibadar mabiya Shi'a a Qom, wajen da annobar Covid-19 ta fara bulla da kuma Mashhad.

  Ma'aikatar Lafiya Ta Iran ta yi gargadi cewa yawan wadanda suka kamu da cutar zai karu nan da kwanaki masu zuwa.

  A ranar Alhamis, an ruwaito cewa an samu masu dauke da cutar 245 da kuma wadanda suka mutu 26.

  A yanzu haka Iran ce ta biyu a yawan wadanda suka mutu daga cutar bayan China.

  Mataimakiyar shugaban kasar Iran a bangaren sha'anin mata Masoumeh Ebtekar, wacce ita ce macen da take da mafi girman mukami a gwamnatin kasar, ta zamo babbar jami'a da ta kamu da cutar a baya-bayan nan, bayan an tabbatar da hakan ranar Alhamis.

  Wata kafar yada labarai ta intanet ta kasar ta ruwaito cewa Ms Ebtekar ta halarci wani taro ne da Shugaba Hassan Rouhani da kuma wasu ministoci, jim kadan kafin a tabbatar da kamuwar ta.

  Iran's health ministry reported 106 new confirmed cases of Covid-19 on Thursday
  Image caption: Ma'aikatar Lafiya Ta Iran ta ruwaito cewa an samu mutum 106 da ke dauke da cutar Covid-19 a ranar Alhamis
 18. An sake gano gidan sayar da jarirai a Najeriya

  'Yan sanda a Najeriya sun ce sun kai samame kan wani gida da ake sayar da jarirai a jihar Ribas da ke kudu maso kudancin kasar.

  Sun ce sun ceto mata masu ciki hudu tare da jarirai fiye da ashirin masu tsakanin shekara daya zuwa hudu.

  'Yan sandan sun kara da cewa sun kama mutum uku wadanda suke zargi da gudanar da gidan, inda ake tsare matasan mata masu ciki har sai sun haihu.

  Daga nan za a sayar da jariran ga masu so.

  An kubutar da jarirai da iyayensu da dama a irin wadannan gidaje, galibi a kudancin Najeriya.

  An kubutar da jarirai da iyayensu da dama a irin wadannan gidaje, galibi a kudancin Najeriya
  Image caption: An kubutar da jarirai da iyayensu da dama a irin wadannan gidaje, galibi a kudancin Najeriya
 19. An halasta sayar da tabar wiwi a Malawi

  Malawi ta kasance kasar Kudancin Afirka ta baya bayan nan da ta halasta nomawa da sayarwa da kuma fitar da tabar wiwi kasashen waje.

  Masu shan wiwi a kasar suna bayyana ta da sunan "Zinaren Malawi", inda ta kasance daya daga cikin magunguna mafi warkarwa.

  Sai dai hukumomi basu halasta shan ta ba.

  Sun ce za a yi amfani da ita ne don yin magani da sarrafa tufafi da kuma takardu.

  Sayar da wiwi ka iya maye gurbin taba sigari, wadda 'yan kasar Malawi suka shahara wurin tallan ta.

  Sauran kasashen kudancin Afirka da suka halasta noman wiwi sun hada da Zambia, Lesotho da kuma Zimbabwe.

  Amma Afirka ta kudu ta ki halasta noman wiwi.

  Amma Afirka ta kudu ta ki halasta noman wiwi.
  Image caption: Amma Afirka ta kudu ta ki halasta noman wiwi.
 20. Coronavirus: Batun da aka fi tattaunawa a kai a Najeriya

  Tun bayan da coronavirus ta bulla a jihar Lagos da ke Najeriya, 'yan kasar suka mayar da hankali wurin tattauna batun. Galibin 'yan kasar na son sanin yada ake kauce wa kamuwa da cutar, ko kuma yadda za a dakile ta.

  A shafukan sada zumunta musamman a Twitter, 'yan Najeriya sun yi ta tsokaci a kan cutar.

  Abubuwan da suka fi tattaunawa a kai su ne: #coronavirusnigeria #CoronaVirusUpdate, #CoronaVirusOutbreak, Corbid-19, China da kuma Ebola.

  'Yan Najeriya na cike da fargaba