Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Sai wani jikon

  Mun zo karshen rahotannin kai-tsaye na abubuwan da suka faru ranar Juma'a a Najeriya da makwabta da ma sassan duniya.

  Sai kuma ranar Litinin idan Allah ya kai mu.

  Kafin nan, za ku iya ci gaba da karanta labarai da kallon bidiyo da hotuna a babban shafinmu, kazalika da tattaunawa a Facebook da Twitter da Instagram dinmu.

  Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

  Wata yarinya 'yar gudun hijira
  Image caption: Wani mutum yake taimaka wa wata karamar yarinya 'yar gudun hijira a gabar ruwa bayan wani jirgin ruwan sojoji ya ceto su daga nutsewa a gabar ruwan Turkiyya zuwa kasar Girka
 2. Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya sun yi ganawar musamman a Gombe

  Gwamnonin arewa maso gabashin Najeriya
  Image caption: Gwamnonin sun amince su rika zama sau hudu a shekara don tattaunawa

  Gwamnonin jihohi shida na arewa maso gabas a Najeriya sun yi wata ganawa ta musammnan a ranar Alhamis a jihar Gombe, inda suka tattauna matsalolin tsaro da kuma na zamantakewa da suke fuskanta a yankin nasu.

  Jaridar intanet ta Premium Times ta ruwaito cewa gwamnonin sun bukaci kwamishinonin shari'asu da su tattauna da jami'an tsaro domin kyautata tsaro a yankin ta hanyar doka.

  Jaridar ta ce gwamnonin Adamawa da Borno da Bauchi da Gombe da Taraba da Yobe sun taru ne a garin Gombe, inda suka kara wa juna sani game da yadda za su kawo karshen matsalolin.

  View more on twitter

  Ganawar ta kwana daya wadda kuma aka fara da rana, ta zarce har zuwa dare kuma daga baya aka fitar da sanarwar bayan taro.

  Gwamna mai masaukin baki, Inuwa Yahaya, ne ya karanta sanarwar, wadda ta kunshi abu 14 sannan ya ce za a rika yin irin wannan zaman sau hudu a shekara.

  Daga cikin abubuwan da suka amimnce da su akwai:

  • Gamsuwa da kafa hukumar habbaka yankin arewa maso gabas ta Northeast Development Commission da gwamnatin tarayya ta yi
  • Gode wa Shugaba Buhari sakamakon kafa hukumar
  • Bayar da dukkanin hadin kai da taimako don cimma muradan hukumar
  • Bai wa kwamishinonin shari'ar jihohin umarnin hada kai da jami'an tsaro domin dakile matsalolin tsaro a yankin
  • Kungiyar gwamnonin ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa ayyukan hako man fetur da ake yi a wasu jihohin yankin
  • Kafa kwamitin gudanarwa na abubuwan da aka cimma yayin taron
  • An amince gwamnonin za su rika yin irin wannan ganawar sau hudu a duk shekara
 3. 'Yan sanda aka hara a harin bam na Tunisia

  Mota
  Image caption: 'Yan sanda biyar ne suka jikkata

  Harin da aka kai kusa ofishin jakadancin Amurka a Tunis babban birnin Tunusiya, mutum biyu ne suka kai shi yayin da suka kusaci wani wurin duba ababen hawa.

  A wani bayani da ya fitar, ministan cikin gida na Tunusiya ya ce maharan sun hari wasu jami'an tsaro ne da ke sintiri a yankin.

  'Yan sanda biyar ne suka jikkata, sai kuma wani farar hula da ya ji karamin rauni, a cewar hukumomi.

  Wani harin makamancinsa da aka kai a tsakiyar Tunis a watan Yuni da kuma na shekara guda kafinsa, jami'an tsaron aka hara.

  Yankin da ofishin jakadancin Amurkar yake cike yake da tsaro a unguwar Lac 2, inda wasu ofisoshin jakadanci na kasashe suke.

 4. An bukaci 'yan Ethiopia su tara tiriliyan N1.8 don gina madatsar ruwa

  Daga Kalkidan Yibeltal BBC News, Addis Ababa

  Madatsar ruwa

  Kasar Habasha wato Ethiopia, ta kaddamar da wani shirin tattara kudin gudummawa daga 'yan kasarta domin samar da kudin gina dam din nan na wutar lantarki daga Kogin Nilu, wanda tuni ya jawo tayar da jijiyoyin wuya tsakaninta da makwabta.

  An bukaci mutane su yi amfani da wayoyinsu na hannu su aika kudi domin samar da madatsar ruwan da aikinta zai lakume dala biliyan biyar, kusan naira tiriliyan 1.8.

  A baya-bayan nan gwamnati ta ki sa hannu kan wata yarjejeniya da Masar da Sudan kan gina madatsar ruwan, wadda Amurka ta shiga tsakani a kai.

  Masar da Sudan na fargabar samar da madatsar ruwan zai hana su damarsu ta samun ruwan sha da kuma yin iko da shi.

 5. Coronavirus ta shiga Peru

  Shugaba Martín Vizcarra
  Image caption: Shugaba Martín Vizcarra

  Shugaba Martín Vizcarra, ya tabbatar da bullar cutar numfashi ta coronavirus a kasar da safiyar ranar Juma'a.

  Mr Vizcarra, ya ce wanda ya kamu da cutar mai shekara 25 ya ziyarci Spaniya da Faransa da kuma Jamhuriyar Czech.

  ''Mun tanadi matakan da suka dace ta bangaren lafiya,'' a cewar shugaban kasar.

 6. Coronavirus: An soke taron jakadun Tarayyar Turai a Brussels

  An dage wani taron jakadun Tarayyar Turai da aka tsara yi da safiyar ranar Juma'a a Brussels.

  Ita kuma jakadar Croatia ta killace kanta bayan da ta kusanci wani ma'aikacin majalisar Turai da ya kamu da cutar coronavirus.

  Akasarin jakadun suna wajen taron lokacin da suka samu labarin dage zaman.

  Majalisar Turai na aiki don ganin ta zakulo sauran mutanen da suka yi mu'amala da ma'aikacin.

 7. Mutum 12 sun sake kamuwa da cutar coronavirus a Masar

  Kasar Masar ta sanar da cewa mutum 12 sun kamu da cutar coronavirus a wani jirgin ruwan yawo.

  Ma'aikatar lafiya ta kasar ce ta sanar da hakan inda ta ce mutanen fasinjoji ne da ke cikin jirgin ruwan wanda ke a kogin Nilu.

  Jirgin ruwan dai na kan hanyarsa ta zuwa birnin Aswan daga Luxor.

  Kasar Masar ce dai ta fara samun wadanda suka kamu da cutar ta coronavirus a cikin kasashen Afirka.

  A baya dai kasar ta tabbatar da cewa mutum uku sun kamu da cutar, inda mutum guda daga cikinsu ya samu sauki sosai bayan an yi masa magani.

  Mutum 12 sun sake kamuwa da cutar coronavirus a Masar
  Image caption: Mutum 12 sun sake kamuwa da cutar coronavirus a Masar
 8. Hotuna: An bude cibiyar kebe masu coronavirus a Kenya

  Gwamnatin Kenya ta bude asibitin killace masu coronavirus a Nairobi babban birnin kasar.

  An bude cibiyar a asibitin gundumar Mbagathi a dai-dai lokacin da jama'a ke fargaba kan tanadin da gwamnatin kasar ta yi don tunkarar cutar.

  Kenya
  Kenya
  Kenya
  Image caption: Cibiyar na da gadaje 120 da sashen bayar da kulawa ta musamman zai kula da marassa lafiya 10
 9. Mutanen da suka kamu da Coronavirus a Iran na karuwa

  Iran

  Hukumomin lafiya a Iran sun ce an samu karin mutanen da suka kamu da cutar Coronavirus a kasar.

  Hukumomin sun ce a yanzu an tabbatar da sama da karin mutum 1,200 da suka kamu da cutar.

  Hakan ya kara adadin mutanen da suke da cutar zuwa kusan 5,000 - mutum 124 ne suka mutu saboda cutar a kasar.

  Hukumomin sun soke gudanar da sallar Juma'a a sassan kasar tare da bijiro da matakan kariya domin hana bazuwar cutar a tsakanin biranen kasar.

  A wasu kasashen ma, an soke gudanar da sallar Juma'a saboda cutar ta numfashi.

 10. Gwamnatin jihar Nasarawa ta hana bara

  A

  Gwamnatin jihar Nasarawa a Najeriya ta bi sahun wasu jihohin kasar wajen hana kananan yara yawon bara da sunan karatun allo.

  Tuni dai gwamnatocin jihohin Kano da Neja suka dauki irin wannan matakin.

  Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta barar ne karakshin wata doka ta kare hakkokin yara.

  Sakamakon wannan matakin, gwamnatin jihar za ta mayar da yara fiye da dubu talatin jihohinsu na asali.

 11. Buhari ya gana da jakadan Iran mai barin gado

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin jakadan Iran a kasar mai barin gado, Morteza Rahimi Zarchi.

  Ya karbi bakuncin nasa ne a wata ziyarar bankwana da ya kai masa fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

  Bashir Ahmad mai taimaka wa shugaban kan kafafen sada zumunta ne ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a.

  View more on twitter
 12. 'Mutum biyar sun jikkata' a harin bam a Tunisia

  Kimanin mutum biyar ne suka ji rauni bayan wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a Tunis babban birnin Tunisia.

  Ya ta da bam din ne a kusa da ofishin jakadancin Saudiyya kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.

  AFP ya ce maharin ya je wajen a kan babur ne.

  Harin bam a Tunisia
  Image caption: Kamfanin dillancin labarai na AFP ya wallafa hoton wajen da aka kai harin
 13. An samu raguwar mutane a Masallacin Harami saboda Coronavirus

  Ana ci gaba da samun hotunan Harami tun bayan da hukumomi a Saudiyya suka hana baki shiga kasar saboda fargabar yaduwar cutar Coronavirus.

  Hoton farko da aka dauka ta sama ya nuna yadda masu sauke farali ke gudanar da ibada a kusa da Ka'aba yayin da hoto na biyu kuma an dauke shi ne ranar Alhamis.

  Saudiyya dai ta sanar da bullar cutar ta numfashi, inda ta ce ya zuwa yanzu akwai mutum biyar da suka kamu da cutar.

  Harami
  Masallacin Harami
 14. An samu fashewar wani abu kusa da ofishin jakadancin Amurka a Tunisia

  An samu tashin wani abin fashewa kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke Tunis babban birnin kasar Tunisia.

  A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, harin na kunar bakin wake ne.

  Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta ce fashewa ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

  View more on twitter
 15. An shigar da korafi don sakin mutanen da aka samu da laifin kisan Laurent Kabila

  Congo
  Image caption: Ana iya ganin hoton Laurent Kabila a kan titunan kasar shekaru bayan mutuwarsa

  Iyalan dubban mutanen da aka kulle saboda kisan Laurent Kabila, tsohon shugaban Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo sun shigar da korafi kan hukumomi domin a saki mutanen.

  Suna fatan sabuwar gwamnatin kasar za ta amince da bukatunsu.

  Wani dogari ne ya harbe Mr Kabila a shekarar 2001.

  Kotun soji a kasar ta samu kusan mutum 100 da laifin kisan ba tare da samun damar daukaka kara ba.

  An yanke wa mutum 24 hukuncin kisa, sauran kuma aka kulle su.

  Tuni mutum 10 suka mutu a kurkuku.

  Wata kotun kare hakkin bil adama ta na ganin hukuncin da aka yanke wa mutanen bai dace ba.

 16. Faransa ta amince a mayar da dan uwan tsohon Shugaban Burkina Faso gida

  François Compaoré na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifi a Burkina Faso
  Image caption: François Compaoré na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifi a Burkina Faso

  Faransa ta ba da izinin mayar da François Compaoré dan uwan tsohon Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré gida wanda ake nema ruwa a jallo kan kisan wani dan jarida a shekarar 1998.

  Ana zargin François Compaoré da hannu a kisan Nobert Zongo wanda ke binciken mutuwar direban Mr Compaoré da wasu mutum uku da aka kone.

  Kisan Mr Zongo dai ya janyo zanga-zanga a Burkina Faso.

  Lauyoyin Mr Compaoré sun soki matakin Faransa saboda yana iya fuskantar hukuncin kisa idan aka same shi da laifi a kasarsa, hukuncin da babu shi a Faransa..

 17. Coronavirus: An haramta gudanar da taruka a Kenya

  Kenya

  Ministan lafiya na Kenya Mutahi Kagwe ya sanar da haramta duk wasu taruka da suka hada da baki daga wasu kasashen na wani dan lokaci saboda fargabar yaduwar Coronavirus.

  Mr Kagwe ya bayyana haka ne a bikin kaddamar da asibitin kula da kuma kebe masu dauke da cutar a Nairobi babban birnin kasar.

  Ya ce sun bar wani jirgin Italiya sauka a kasar domin ya kwashe 'yan Italiya zuwa kasar.

  Kenya ta haramta saukar jirage daga Iran da Koriya ta Kudu kari kan haramcin da aka yi kan saukar jirage daga arewacin Italiya a kokarin hana bazuwar cutar daga kasashen da suke fama da ita.

 18. Coronavirus: An soke gasar Oscars ta Bollywood

  An soke gudanar da gasar Oscars ta Bollywood saboda barkewar cutar coronavirus.

  An tsara gudanar da bikin ba da kyaututtukan na International Indian Film Academy Awards tsawon kwana uku daga 27 ga watan nan.

  Amma masu tsara taron sun yanke shawarar dage bikin saboda cutar da ke ci gaba da yaduwa a kasashe da dama.

  Ya zuwa yanzu akwai kimanin mutum 31 da suka kamu da cutar a India.

  India
 19. Gwamnatin jihar Neja ta hana bara

  Video content

  Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken rahoton Zahraddeen Lawan

  Gwamnatin jihar Neja za ta fara hukunta iyayen yaran da aka kama suna bara a wani mataki na hana bara a jihar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  Muhammad Sani Idris, kwamishinan watsa labarai na jihar ya ce jihohi da dama a arewacin kasar sun hana bara, lamarin da ya sa mutane ke baro wadannan jihohi suna kwarara jihar Nejar.

  A baya ma gwamnatoci a jihar sun taba hana bara, sai dai matakin bai yi tasiri ba, sai dai a yanzu gwamnatin jihar ta ce daukar matakin ya zama tilas.

  Gwamnatin ta tabbatar da kafa wani kwamiti da zai tsara yadda za a tabbatar da aiki da manufar hana bara a jihar duk da yake ba ta hana kai yara makarantun allo ba.

 20. Coronavirus: An sake kebe mutum uku a Najeriya

  Kwamishinan Lafiya a jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da killace wasu mutum uku da ake zargi sun kamu da Coronavirus.

  An kebe su ne a wani asibiti da ke Yaba a matsayin rigakafi ga yaduwar cutar, kamar Farfesa Abayomi ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  Nan gaba ake sa ran za a saki sakamakon gwajin da aka yi wa mutanen.

  Najeriya ta tabbatar da bullar cutar a karon farko a kasar ranar 27 ga watan Fabrairu – kasa ta farko a yankin kudu da hamada da ta samu bullar cutar.

  Farfesa Akin Abayomi ya ce daya daga cikin mutanen uku dan Najeriya ne da ya dawo kasar ranar Litinin bayan shafe mako daya a Faransa.

  Daga baya kuma ya nuna alamun ciwon kai da matsalar numfashi.

  Sauran mutanen kuma matafiya ne daga Ingila da kuma China.

  View more on twitter