Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Mu kwana lafiya

  Masu bibiyarmu, karshen rahotannin kenan.

  Mu hadu da ku gobe Juma'a idan Allah ya kai mu.

  Umar Mikail ne ke cewa mu zama lafiya.

 2. Labarai da dumi-dumiKarin mutum 14 sun harbu da Covid-19 a Najeriya

  Wasu mutum 14 sun harbu da cutar Covid-19 a Najeriya da suka hada da 13 a Jihar Legas da kuma mutum daya a Jihar Delta.

  Hukumar NCDC ce mai yaki da cutuka a Najeriya ta bayyana hakan.

  Ta ce ya zuwa yanzu - karfe 9:30 agogon Najeriya - mutum 288 ne suka kamu da Covid-19 a fadin kasar.

  An sallami 51 daga cikinsu sannan bakwai sun mutu.

  View more on twitter
 3. Kwana 100 kenan da gano cutar coronavirus

  Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus

  A ranar 31 ga watan Disamba - kwana 100 daidai kenan - gwamnatin China ta bayar da rahoton gano wata cutar "murar mashako" da ba a san kalarta ba ga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO.

  Wannan cuta ce ta zamo annobar da ake kira Covid-19 a yau.

  Cutar da aka fara samun bullarta a birnin Wuhan, tuni ta karade sassan duniya, inda mutum fiye da miliyan daya da rabi suka harbu sannan kusan 90, 000 suka mutu.

  Shugaban WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya tuna da wadannan kwana 100 na alhini a wurin taron manema labarai ranar Alhamis.

  • 31 ga Disamba: China ta bayar da rahoton gano cutar "murar mashako da ba a san irinta ba" a birnin Wuhan
  • 11 ga Janairu: China ta bayar da rahoton mutuwar mutum na farko daga Covid-19
  • 13 ga Janairu: Mutum na farko a wajen kasar China ya kamu da cutar a kasar Thailand
  • 30 ga Janairu: Hukumar Lafiya ta WHO ta ayyana dokar ta-baci kan cutar
  • 7 ga Fabarairu: Cutar ta kashe Li Wenliang, wani Dakta a China da ya yi kokarin ankarar da China kan cutar
  • 11 ga Maris: WHO ta ayyana cutar a matsayin annoba ta duniya
  • 27 ga Maris: Firai Ministan Britaniya Boris Johnson ya kamu da cutar - shugaba na farko kenan da aka sani ya harbu da ita
 4. Gwamnan Bauchi Bala Kaura ya warke daga coronavirus

  Bala Muhammad

  Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya warke daga coronavirus bayan da sakamakon gwajinsa a karo na biyu ya fito, bayan shafe fiye da mako biyu yana jinya.

  Gwamna Bala Muhammad Kaura da kansa ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis da maraice.

  Karanta cikakken labarin a nan

  View more on twitter
 5. An kashe fursuna 36 a Iran a zanga-zangar coronavirus

  Iran

  A Iran, fursuna kusan 36 ne aka kashe bayan jami'an tsaro sun yi amfani da harsasai da hayaki mai sa hawaye wurin tarwatsa zanga-zangar da fursunonin suka yi.

  Sun tayar da kurar ne bayan sun yi fargabar cewa suna cikin hadarin kamuwa da coronavirus a gidan yarin, a cewar Amnesty International.

  Kungiyar ta ambato wasu majiyoyi da ke cewa an yi amfani da karfin da ya wuce kima a gidajen yarin Sepidar da Sheiban da ke birnin Ahvaz a ranar 30 da kuma 31 ga watan Maris.

  Hukumomi ba su ce komai ba a lokacin.

 6. Coronavirus: 'Yan kabilar Igbo sun bai wa gwamnatin Kano tallafin kayan miliyan 5

  Shugaban Kwamitin tattara tallafin Coronavirus da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa wato Farfesa Muhammad Yahuza Bello tare da 'yan kwamitinsa sun karbi kayan tallafi daga kungiyar masu sayar da magunguna na kabilar Igbo domin a tallafawa mabukata.

  Kayayyakin sun hada da:

  1. Indomie katan 100

  2. Man goge hannu da ke yajar kwayoyin cuta (Hand sanitizer) mai mililita 500, guda 120

  3. Katan din sabulu biyar 75

  4. Fakitin safar hannu 70

  5. Buhun shinkafa 100

  6. Katan din Macaroni 50

  Jumullar kudin kayayyakin ya kai kimanin naira miliyan 5.1.

  Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
  Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
  Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
  Gudunmowar kabilar Ibo a Kano
 7. Labarai da dumi-dumiAn fitar da firai ministan Birtaniya daga dakin kulawar gaggawa

  Wani mai magana da yawun firai ministan Birtaniya ya ce: "An fitar da firai minista da yammacin yau daga dakin kulawar gaggawa zuwa wani dakin, inda za a rika kula da shi a ranakun jinyarasa na farko-farko.

  "Yana cike da kwarin gwiwa sosai."

 8. Goyon bayanmu ga WHO cikakke ne – Shugaban Afirka ta Kudu

  Cyril Ramaphosa

  Shugaban Afirka ta Kudu kuma shugaban Kungiyar Hadin Kan Afirka ta AU, Cyril Ramaphosa ya kare Hukumar Lafiya ta Duniya WHO bayan caccakar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata game da matakan yaki da coronavirus.

  A wata sanarwa da aka fitar a daren Laraba, Ramaphosa ya jaddada goyon bayan kungiyar ta AU ga WHO da kuma shugabanta Tedros Adhanom Ghebreyesus sannan ya yi kira ga kasashe da su hada kai wurin yaki da cutar.

  "Yayin da duniya ke fama da coronavirus, akwai bukatar hada kai da haduwar manufa da yin aiki tare domin tabbatar da cewa mun kawo karshen wannan abokiyar gaba," sanarwar ta bayyana.

  Mista Ramaphosa ya kara da cewa AU na goyon bayan WHO, yana mai cewa "ya kamata mu kauce wa zargin juna mai rarraba kawuna".

 9. China ta kare kanta daga zargin boye bayanai kan coronavirus

  Zhao Lijian

  Gwamnatin kasar China ta yi watsi da zargin abin da ta kira "rashin adalici" na cewa ta yi yunkurin yin rufa-rufa kan annobar coronavirus, wadda ta faro daga birnin Wuhan na kasar.

  Zhao Lijian ne mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, ya ce China ba ta yi wata "rufa-rufa ba" ga kasashen duniya game da cutar.

  Ya ce "ta dauke mu lokaci kafin mu san wani abu" game da cutar, wadda a hukumance a gano ta birnin Wuhan na yankin Hubei a shekarar da ta gabata.

  An yi ta zargin China da boye bayanai game da cutar - hadarinta da kuma yaduwarta a farkon al'amari.

  A ranar Laraba ne sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya zargi China da boye bayanai kan cutar a birnin Wuhan.

  A yau Alhamis ne kuma Lijian ya mayar da martani, yana mai nuna cewa cutar ka iya bulla a kowane "birni ko kasa ko yanki na duniya".

  Kazalika ya kare Hukumar Lafiya ta Duniya WHO daga zargin da Donald Trump ya yi na cewa "yar korar China ce".

 10. Shugaban Uganda ya nuna wa 'yan kasa yadda ake motsa jiki a gida

  Shugaban Kasar Uganda, Yoweri Museveni ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Twitter yana motsa jiki a ofishinsa domin karfafa wa 'yan kasar gwiwar motsa jiki a gida saboda coronavirus.

  View more on twitter

  A ranar Juma'a ne dai shugaban ya hana yin atasaye a kan tituna domin rage yaduwar cutar ta coronavirus bayan hotuna da bidiyon mutane sun karade shafukan zumunta suna motsa jiki duk da cewa akwai dokar hana fita a Kampala, babban birnin kasar.

  A shekarar da ta gabata ne shugaban mai shekara 75 ya fada wa 'yan kasa cewa ya mayar da hankali kan lafiyarsa, inda ya ya ce ya rage nauyin kilogiram 30.

  View more on twitter
 11. Buhari ya gana da gwamnan Borno Babagana Zulum

  Muhammdu Buhari da Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ganawar musamman da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum a fadar Aso Villa da ke Abuja.

  Ya zuwa lokacin hada wannan rohoto, BBC ba ta san abin da shugabannin biyu suka tattauna ba.

  Amma BBC ta san cewa Jihar Borno ba ta cikin jihohin da ke fama da annobar coronavirus - hukumomi ba su bayyana hakan ba.

  Sai dai daga cikin abubuwan da ka iya kai gwamnan fadar shugaban kasa akwai kokarin da gwamnatinsa ke yi na shiryawa cutar ko da a ce - Allah ya kiyaye - ta bulla jihar.

  Sai kuma matsalolin tsaro da suka shafi yaki da kungiyar Boko Haram, wadda hare-haren da take kaiwa a Borno da makwabtan jihohi suka yi sanadiyyar rasa rayukan mutum sama da 20,000, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

  View more on twitter
 12. A ci gaba da yaki da coronavirus a Najeriya...

  Chikwe Ihekweazu

  Shugaban hukumar Nigeria Centre for Disease Control (NCDC) mai yaki da cutuka masu yaduwa a Najeriya, Chikwe Ihekweazu ya gana da shugabannin majalisun tarayyar Najeriya.

  Sun yi ganawar ne domin ba su bayani kan matakan da ake dauka na yaki da coronavirus a kasar.

  Shugaban mamba ne a kwamitin shugaban kasa na musamman kan yaki da coronavirus kuma hukumarsa ce kan gaba a wannan kujiba-kujiba.

  View more on twitter
 13. An hana taron bikin Easter a wasu jihohin Najeriya

  Sufeto Muhammed Adamu

  Babban Sufeton 'yan sanda na Najeriya Muhammed Adamu ya bai wa kwamishinonin 'yan sanda umarni su ci gaba da tabbatar da dokar hana taruka a jihohin da suke cikin dokar yayin bikin Easter.

  A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Twitter, rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce Muhammed Adamu ya taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar.

  Sufeton ya yi kira ga shugabannin addinai da shugabannin al'umma a jihohin Abuja da Legas da Ogun - inda dokar hana fita ke aiki - da su ci gaba da bin dokar sau da kafa sannan su gudanar addu'o'i a gidajensu.

  Kazalika ya roki 'yan Najeriya da su kalli dokar hana fitar a matsayin daya daga cikin koyarwar Easter da suka hada sadaukarwa, jumuri, hakuri, kauna da kuma nasara, sannan ya jaddada aniyarsu ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

  View more on twitter
 14. An saki fursuna 2600 a Najeriya saboda coronavirus

  Fursunoni a Najeriya

  Babu dadewa muka bayyana muku cewa hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Najeiya za ta sallami fursuna 2600 daga gidajen yarin da ke fadin kasar.

  Fursunoni a Najeriya

  Tuni aka saki fursunonin a fadin kasa baki daya.

  BBC ta samu ganin wasu daga cikinsu da aka saki a gidan gyara hali na Kuje da ke Abuja.

  Fursunoni a Najeriya
 15. Karin mutum 765 sun mutu a Ingila

  Hukumar inshorar lafiyar Ingila ta NHS ta bayar da rahoton mutuwar 765 a asibiti sakamakon coronavirus.

  Ta ce 140 daga cikinsu sun rasu ne a jiya Laraba, yayin da 568 suka mutu daga 1 ga watan Afrilu zuwa 7.

  Sauran 57 din sun mutu ne a watan Maris, da suka hada da mutum biyu a ranar 19 da kuma daya ranar 16 ga watan Maris.

 16. Yadda mutanen Wuhan suka ci galabar coronavirus

  Yayin da coronavirus ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya tana kashe mutane, mutanen Wuhan, birnin da cutar ta fara barkewa a fadin duniya sun bayar da shawarwari ga mutanen duniya.

  Wasu daga ciki sun bayyana yadda zama a gida ya zama alheri a gare su da birnin nasu. Sun kuma bayyana yadda suka yi rayuwarsu da yadda suka ci galabar annobar.

  Video content

  Video caption: Coronavirus: Yadda muka yi rayuwarmu lokacin hana fita a Wuhan
 17. Covid 19: Wa ya fi dacewa ya toshe baki da hanci?

  face mask

  Takunkumin kariya da safar hannu da sauran abubuwa na taimaka wa jama'a wajen dakile yaduwar cutar coronavirus - to sai dai ya kamata ayi amfani da su yadda ya dace.

  Wasu mutanen na amfani da takunkumin kariya da aka yi a gida - su ma al'ummar Amurka ana shawartar su da su rinka amfani da takunkumin kariyar a yayin shiga cikin jama'a.

  To sai dai abin tambaya a nan shi ne ko ya kamata hakan? Me ya sa jama'a ke amfani da takunkumin kariya? Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta yi duba ga shaidun baya-bayan nan da suka hada da ko za a sauya tunani kan kwayar cutar.

  Hukumar ta so ta sake yin nazari kan ko akwai wani alfanu a sanya takunkumin kariya ga kowa da kowa. Kwararru sun yanke cewa ya kamata a bar wa ma'aikatan lafiya takunkumin kariya da suke sanyawa a lokacin gudanar da ayyukansu, inda hakan ke nufin na gama-gari ne ba.

  Mutane iri biyu ne kawai ya kamata su sanya takunkumin kariya:

  • Maras lafiya wanda kuma yake dauke da alamun coronavirus

  • Mai kula da wadanda ake zaton suna dauke da coronavirus

  Ba a amince wa dukkan jama'a sanya takunkumin kariya ba saboda wadannan dalilan:

  • Takunkumin ka iya gurbata sakamakon tari da atishawa da wasu mutane suka yi a lokacin sanya ko cire takunkumin.

  • Yawaita wanke hannu da bayar da tazara tsakanin mutane sun fi sanya takunkumin alfanu wajen kare kai daga cuta.

  • Idan mutum ya rufe fuska hakan ka iya janyo zargin ko mai laifi ne Cutar coronavirus dai na yaduwa ne ta hanyar feshi daga atishawa ko tarin mutanen da ke dauke da cutar.

  Irin wannan feshin na shiga jikin dan adam ta hanyar idanu ko hanci ko kuma baki, watakila kai tsaye daga mai cutar ko kuma bayan mutum ya taba wani abu da mai kwayar cutar ya gurbata.

 18. Burundi ta saki dubban mutane daga cibiyar killacewa

  Burundi ta saki mutane 2,261 wadanda aka tsare a cibiyoyin killace marasa lafiya a fadin kasar saboda tabbatar da lafiyarsu.

  Health Minister Thaddée Ndikumana said those released had shown no known symptoms of Covid-19, the respiratory illness caused by coronavirus.

  Ministan lafiya na kasar Thaddée Ndikumana ya ce wadanda aka saki ba su nuna alamun suna dauke da cutar Covid-19 ba.

  Babu babbacin ko an musu gwajin kamuwa da cutar.

  Minisatan ya ce za a ci gaba da tsare mutum 675.

  Zuwa yanzu mutum uku ne aka tabbatar sun kamu da coornavirus a Burundi.

 19. Yakin Yemen: An tsagaita wuta saboda hana yaduwar coronavirus

  yemen

  An tsayar da wuta a yakin Yemen na mako biyu, bayan da gamayyar rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta ta yi kira ga hakan.

  Gamayyar hadakan ta ce tana so ta goyi bayan kokarin Majalisar Dinkin Duniya don kawo mafitar siyasa da kuma taimaka wa wajen hana yaduwar coronavirus, duk da cewa har yanzu ba a samu bullar cutar a Yemen ba.

  Sakataren MDD General António Guterres ya yi maraba da lamarin.

  Amma wani babban jami'i a kungiyar Houthi wacce take yaki da gamayyar, ta kira lamarin da ''tuggu''.

 20. Coronavirus: Ana neman wadanda suka yi mu'amala da likitan da ya mutu a Daura

  Hukumomi a garin Daura na jihar Katsina na ci gaba da kira ga duk wanda ya san ya yi hulda da wani likita da ya rasu a jihar sakamakon cutar Coronavirus da ya fito ya bayyana kansa.

  Mutumin mai suna Dr Aliyu wanda babban likita ne da ke da wani assibiti mai zaman kansa a garin Daura ya kwanta ciwo ne bayan ya dawo daga wani bulaguro a jihar Lagos.

  Wannan yanayi da ake ciki a yanzu ya jefa mutanen Daura a cikin fargaba.

  Ga rahoton Abdou Halilou kan batun:

  Video content

  Video caption: Rahoton Abdou Halilou kan Daura