A nan za mu dakatar da kawo ma ku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Da fatan za ku kasance da mu a gobe inda za mu ci gaba da kawo maku labarai da rohotanni da suka shafi cutar coronavirus a duniya.
Sai da safe.
Yadda Buhari ya sanya wa dokar hana fita hannu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar hana fita a jihohin Legas da Abuja da Ogun hannu bayan kammala jawabinsa ga 'yan kasar a ranar Litinin, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan kafofin sadarwa na intanet Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter.
Labarai da dumi-dumiBuhari ya tsawaita dokar hana fita
Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya tsawaita dokar hana fita na tsawon mako biyu a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.
Covid 19 ta fi murar aladu a 2009 hatsari sau 10
Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar coronavirus ta fi annobar cutar murar aladu da aka taba samu a 2009 hatsari sau 10.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce sabbin alkalumman cutar a duniya yana tabbatar da girman cutar da yadda ta ke da yadda za a yi maganinta
"Mun san cewa Covid 19 na yaduwa da sauri, kuma mun san tana da hatsari - sau 10 fiye da cutar murar aladu a 2009," kamar yadda Tedros ya fada a lokacin da yake jawabi a Geneva ranar Litinin.
Murar aladu a 2009 da ta ake kira H1N1 an kiyasta cewa ta kashe mutum kusan 200,000 a duniya.
An yi wa Sule Lamido gwajin coronavirus
Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce an yi masa gwajin covid-19, cutar sarkewar numfashi da coronavirus ke haddasawa.
A sakon da ya wallafa a shaifinsa na Facebook ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce daraktan kiwon lafiya na ma'aikatar lafiyar jihar Kano, Dr Imam Wada Bello ne ya aika masa da sakon da ke neman ya mika kansa a yi masa gwaji saboda ya halarci jana'iza ranar Alhamis wacce shi ma mutumin nan da aka gano yana dauke da cutar a Kano ya halarta.
"Muna so ka ba mu dama mu gwada ka domin ganin ko akwai yiwuwar kana cikin hatsarin kamuwa da cutar", in ji sakon.
Gwamnan ya ce da misalin karfe daya da rabi na ranar Litinin shi da direbansa da jami'in tsaron da ke ba shi kariya aka yi musu gwajin coronavirus.
Coronavirus: Emmanuel Macron zai yi wa 'yan Faransa jawabi
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai yi wa 'yan kasar jawabi kan coronavirus ta gidan talbijin ranar Litinin da misalin karfe takwas na dare a agogon kasar.
Wannan shi ne karo na uku da shugaban zai yi jawabi ga 'yan kasar ta talbijin tun da aka samu barkewar cutar.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da coronavirus ke raguwa a Faransa.
Ranar Lahadi, mutanen da ke mutuwa sanadin cutar sun ragu a rana ta hudu a jere, yayin da adadin mutanen da ke bukatar kulawar gaggawa ma ya ragu.
A yayin da wa'adin dokar hana fita da aka sanya a kasar yake dab da cika, Mr Macron zai yi jawabin kan matakin da za a dauka na gaba.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Labarai da dumi-dumiCOVID-19: Wadanda suka mutu a Birtaniya sun kai 11,329
Adadin mutanen da suka mutu a Birtaniya bayan an kwantar da su asibiti sannan aka tabbatar suna dauke da coronavirus ya kai 11,329.
Ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a ta ce an samu wannan adadi ne bayan mutum 717 sun mutu lokacin bikin Easter ranar Lahadi.
'Yan Boko Haram sun kashe mutum bakwai a Borno
Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa wasu da ake jin
mayakan Boko Haram ne sun kashe matafiya akalla bakwai a cikin wani hari da
suka kai kan motocin da suke tafiya a ciki.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru
kusa da garin Auno mai tazarar kilomita 20 daga babban birnin jihar Maiduguri
ranar Lahadi da yamma.
Wannan dai na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da ‘yan Boko
Haram din suka kashe matafiya akalla 30 tare da kona motoci 18 a garin na Auno
inda matafiyan suka yada zango.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Covid-19: An kama mutunen da suka je daurin aure masallaci
Rundunar 'yan sandan Accra, babban birnin kasar Ghana, ta kama mutum 29 a wani masallaci da ke yankin Nyamekye Darkuman saboda karya dokar hana taruwa a cikin jama'a.
Kakakin rundunar Efia Tenge, wanda ya bayyana haka ranar Litinin, ya ce mutanen sun je masallacin ne domin daura auren wani mutum inda aka taru sosai.
An bayar da belinsu bayan da aka dauki bayanansu.
Ana sa ran za su gurfana a gaban kotu a makon da muke ciki.
Coronavirus ta kara kashe mutum 6 a Saudiyya
An kara samun mutum shida da cutar coronavirus ta kashe a Saudiyya inda yawan wadanda suka mutu a kasar yanzu suka kai mutum 65, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.
An kuma kara samun mutum 472 da suka kamu da cutar inda yanzu jimillar wadanda ke dauke da cutar suka kai 4,934.
An kuma kara samun mutum 44 da suka warke inda yawansu wadanda suka warke yanzu suka kai mutum 805.
Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasar a yau Litinin.
Sanarwar da mai ba shugaban shawara kan harakokin yada labarai Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7 na yamma wanda za a watsa a kafofin watsa labarai na kasar.
Ana dai tunanin batun annobar coronavirus ne da kuma matakan da gwamnati ke dauka za su mamaye jawabin shugaban, inda ake sa ran watakila ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jihohin Legas da Abuja da kuma Ogun.
Gwaji ya tabbatar da Boris Johnson ya warke daga coronavirus
Gwamnatin Birtaniya ta ce sai da gwaji ya tabbatar da Firai ministan kasar Boris Johnson ya warke daga cutar coronavirus sannan aka sallame daga asibiti a ranar Lahadi.
Kakakin gwamnatin kasar ya ce Firaministan yanzu yana ida murmurewa a gidansa da ke Chequers.
Ya ce nan ya fi dacewa da shi maimakon gidan da aka fi sani mai lamba 10.
Firaministan ya yi magana da Dominic Raab, wanda ya kasance mataimakinsa. "Firaministan yanzu ya mayar da hankali ga kula da lafiyarsa ba tare da mayar da hankali ga aikin gwamnati ba," a cewar kakakin gwamnatin kasar.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
China ta tsaurara tsaro kan iyakokinta da Rasha
China
ta tsaurara tsaro a iyakokinta da Rasha da ke arewa maso gabashi bayan karuwar
yawan masu kamuwa da coronavirus a Rasha.
Kusan rabin
mutum dubu daya da ke dauke da cutar ‘yan China ne da suka tsallako kan iyaka a
yankin gabashi mai nisa na Rasha.
Yanzu China
tana killace duk wanda ya shigo daga Rasha ta kan iyaka na tsawon mako hudu.
A rana
daya an samu adadi mafi girma da suka kamu da coronavirus a Rasha inda mutum
sama da 2500 suka kamu – kusan rabinsu a Moscow.
Ana samun karuwar masu mutuwa sanadin COVID-19 a Belgium
Alkaluma daga Belgium sun nuna cewa adadin mutanen da ke mutuwa a kullum sakamakon coronavirus ya karu zuwa 303 ranar Litinin, inda jimulla ake da mutum 3,903 da suka mutu sanadinta.
Wadanda suka mutu sun hada da mutanen da ke gidan gajiyayu da aka zarga da kasancewa dauke da cutar, amma ba a yi musu gwaji ba.
Ko da yake za a iya ganin kamar wadanda suka mutu ba su da yawa idan aka kwatanta da sauran kasashen Turai, amma yawan jama'ar Belgium bai wuce miliyan 11.5. Jamus na da yawan jama'a miliyan 83, kuma mutum kusan 3,000 ne suka mutu sakamakon coronavirus. - don haka a alkalumance mutanen da suka mutu a Belgium ya kusa na Spain da Italiya.
Belgium ta tabbatar mutum 30,000 suka kamu da cutar.
COVID-19: Mutum sama da 2500 sun warke a Afirka
Hukumar yaki da cututtuka ta Afirka, Africa CDC, ta ce mutum 2570 ne suka warke daga coronavirus a kasashe 52 mambobin kungiyar Tarayyar Afirka ya zuwa ranar Litinin, 13 ga watan Afrilun 2020.
Sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce 14,528 ne suka kamu da cutar yayin da mutum 788 suka mutu a kasashen.
Ya zuwa yanzu dai, Afirka na cikin nahiyoyin da ba a samu mutuwa sosai kan coornavirus ba, abin da masana kiwon lafiya suka alakanta da rashin isassun na'urorin gano masu dauke da cutar.
Sun jaddada kira ga mutane su dauki matakan kare kansu daga kamuwa da cutar, wadanda suka hada da yawaita wanke hannaye da yin nesa-nesa da juna da amfani da kyalle wajen yin atishawa da makamantansu.
An sanar da karin mutum 158 da suka kamu da COVID-19 a Ghana inda jimilla aka tabbatar da mutum 566 ya zuwa maraicen Lahadi.
Ma'aikatar lafiyar kasar Ghana ta ce an samu karn masu dauke da cutar ne saboda matakan da ta dauka na gano masu fama da ita kwana 13 da suka wuce.
Ya zuwa yanzu, an samu bullar cutar a yankuna 10 na kasar.
Yankin Greater Accra yana da mutum 452, yayin da na Ashanti yake da mutum 49, sai kuma yankin Gabashin kasar da ke da mutum 32 masu fama da coronavirus.
Mutum hudu sun warke daga cutar ta COVID-19 a Ghana yayin da mutum takwas suka mutu.
Yadda ake wanke hannu
Wanke hannu shi ne babbar hanyar kare kai daga kamuwa daga cutar coronavirus. Ku kalli bidiyon nan na dakika 56 domin ganin yadda ya kamata ku rika wanke hannayenku.
Video content
Video caption: Yadda ake wanke hannuYadda ake wanke hannu
Ana jimamin shekara 13 da kisan Sheikh Jafar
A ranar Litinin ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Sheikh Jafar Mahmud Adam ya cika shekara 13 da rasuwa.
Wadansu 'yan bindiga ne suka harbe malamin yayin da yake Sallar Asuba a ranar 13 ga watan Afrilun shekarar 2007 a Kano - wato a jajiberin zaben gwamnoni wanda aka yi a shekarar.
Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya.
Duk da cewa har yanzu jama'a na ci gaba da bayyana mutuwarsa a matsayin wani babban rashi, amma kuma har yanzu babu wani da aka kama laifin kisan malamin.
Sheikh Jafar MahmudCopyright: Sheikh Jafar Mahmud
Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya.Image caption: Marigayin yana daya daga cikin manyan malaman addini a bangaren mabiya Sunnah da ke da dimbin magoya baya.
Rahoto kai-tsaye
Daga Nasidi Adamu Yahaya da Awwal Ahmad Janyau
time_stated_uk
Rufewa
A nan za mu dakatar da kawo ma ku labarai da rahotanni kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Da fatan za ku kasance da mu a gobe inda za mu ci gaba da kawo maku labarai da rohotanni da suka shafi cutar coronavirus a duniya.
Sai da safe.
Yadda Buhari ya sanya wa dokar hana fita hannu
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa dokar hana fita a jihohin Legas da Abuja da Ogun hannu bayan kammala jawabinsa ga 'yan kasar a ranar Litinin, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan kafofin sadarwa na intanet Bashir Ahmad ya wallafa a Twitter.
Dokar hana fita za ta ci gaba da aiki a Birtaniya
Dominic Raab ya ce babu wani sauyi da gwamnatin Birtaniya ke tunani ga dokar hana fita ta coronavirus da aka kafa.
Sakataren harakokin wajen kasar ya ce an samu nasara a tsarin, amma "har yanzu ba a samu saukin cutar ba."
Wannan na zuwa a yayin da gwamnati ta ce tana tunanin sauya shawarwarinta kan amfani da abin rufe fuska.
Coronavirus: An kara samun mutum biyu a Kano
Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta wallafa a Twitter cewa an saman karin mutum biyu da suka kamu da cutar korona a jihar.
Sanarwar ta ce yanzu jimillar mutum 3 ke dauke da cutar a jihar.
Labarai da dumi-dumiBuhari ya tsawaita dokar hana fita
Shugaban Najeriya Muhammadu buhari ya tsawaita dokar hana fita na tsawon mako biyu a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.
Covid 19 ta fi murar aladu a 2009 hatsari sau 10
Hukumar lafiya ta duniya ta ce cutar coronavirus ta fi annobar cutar murar aladu da aka taba samu a 2009 hatsari sau 10.
Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce sabbin alkalumman cutar a duniya yana tabbatar da girman cutar da yadda ta ke da yadda za a yi maganinta
"Mun san cewa Covid 19 na yaduwa da sauri, kuma mun san tana da hatsari - sau 10 fiye da cutar murar aladu a 2009," kamar yadda Tedros ya fada a lokacin da yake jawabi a Geneva ranar Litinin.
Murar aladu a 2009 da ta ake kira H1N1 an kiyasta cewa ta kashe mutum kusan 200,000 a duniya.
An yi wa Sule Lamido gwajin coronavirus
Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce an yi masa gwajin covid-19, cutar sarkewar numfashi da coronavirus ke haddasawa.
A sakon da ya wallafa a shaifinsa na Facebook ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce daraktan kiwon lafiya na ma'aikatar lafiyar jihar Kano, Dr Imam Wada Bello ne ya aika masa da sakon da ke neman ya mika kansa a yi masa gwaji saboda ya halarci jana'iza ranar Alhamis wacce shi ma mutumin nan da aka gano yana dauke da cutar a Kano ya halarta.
"Muna so ka ba mu dama mu gwada ka domin ganin ko akwai yiwuwar kana cikin hatsarin kamuwa da cutar", in ji sakon.
Gwamnan ya ce da misalin karfe daya da rabi na ranar Litinin shi da direbansa da jami'in tsaron da ke ba shi kariya aka yi musu gwajin coronavirus.
Ya ce suna jiran sakamakon gwajin.
Coronavirus: Emmanuel Macron zai yi wa 'yan Faransa jawabi
Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai yi wa 'yan kasar jawabi kan coronavirus ta gidan talbijin ranar Litinin da misalin karfe takwas na dare a agogon kasar.
Wannan shi ne karo na uku da shugaban zai yi jawabi ga 'yan kasar ta talbijin tun da aka samu barkewar cutar.
Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da coronavirus ke raguwa a Faransa.
Ranar Lahadi, mutanen da ke mutuwa sanadin cutar sun ragu a rana ta hudu a jere, yayin da adadin mutanen da ke bukatar kulawar gaggawa ma ya ragu.
A yayin da wa'adin dokar hana fita da aka sanya a kasar yake dab da cika, Mr Macron zai yi jawabin kan matakin da za a dauka na gaba.
Labarai da dumi-dumiCOVID-19: Wadanda suka mutu a Birtaniya sun kai 11,329
Adadin mutanen da suka mutu a Birtaniya bayan an kwantar da su asibiti sannan aka tabbatar suna dauke da coronavirus ya kai 11,329.
Ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a ta ce an samu wannan adadi ne bayan mutum 717 sun mutu lokacin bikin Easter ranar Lahadi.
'Yan Boko Haram sun kashe mutum bakwai a Borno
Rahotanni daga jihar Bornon Najeriya na cewa wasu da ake jin mayakan Boko Haram ne sun kashe matafiya akalla bakwai a cikin wani hari da suka kai kan motocin da suke tafiya a ciki.
Majiyoyi sun ce lamarin ya faru kusa da garin Auno mai tazarar kilomita 20 daga babban birnin jihar Maiduguri ranar Lahadi da yamma.
Wannan dai na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan da ‘yan Boko Haram din suka kashe matafiya akalla 30 tare da kona motoci 18 a garin na Auno inda matafiyan suka yada zango.
Covid-19: An kama mutunen da suka je daurin aure masallaci
Rundunar 'yan sandan Accra, babban birnin kasar Ghana, ta kama mutum 29 a wani masallaci da ke yankin Nyamekye Darkuman saboda karya dokar hana taruwa a cikin jama'a.
Kakakin rundunar Efia Tenge, wanda ya bayyana haka ranar Litinin, ya ce mutanen sun je masallacin ne domin daura auren wani mutum inda aka taru sosai.
An bayar da belinsu bayan da aka dauki bayanansu.
Ana sa ran za su gurfana a gaban kotu a makon da muke ciki.
Coronavirus ta kara kashe mutum 6 a Saudiyya
An kara samun mutum shida da cutar coronavirus ta kashe a Saudiyya inda yawan wadanda suka mutu a kasar yanzu suka kai mutum 65, kamar yadda kafofin yada labaran kasar suka ruwaito.
An kuma kara samun mutum 472 da suka kamu da cutar inda yanzu jimillar wadanda ke dauke da cutar suka kai 4,934.
An kuma kara samun mutum 44 da suka warke inda yawansu wadanda suka warke yanzu suka kai mutum 805.
Buhari zai yi wa 'yan Najeriya jawabi
Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga 'yan kasar a yau Litinin.
Sanarwar da mai ba shugaban shawara kan harakokin yada labarai Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7 na yamma wanda za a watsa a kafofin watsa labarai na kasar.
Ana dai tunanin batun annobar coronavirus ne da kuma matakan da gwamnati ke dauka za su mamaye jawabin shugaban, inda ake sa ran watakila ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jihohin Legas da Abuja da kuma Ogun.
Gwaji ya tabbatar da Boris Johnson ya warke daga coronavirus
Gwamnatin Birtaniya ta ce sai da gwaji ya tabbatar da Firai ministan kasar Boris Johnson ya warke daga cutar coronavirus sannan aka sallame daga asibiti a ranar Lahadi.
Kakakin gwamnatin kasar ya ce Firaministan yanzu yana ida murmurewa a gidansa da ke Chequers.
Ya ce nan ya fi dacewa da shi maimakon gidan da aka fi sani mai lamba 10.
Firaministan ya yi magana da Dominic Raab, wanda ya kasance mataimakinsa. "Firaministan yanzu ya mayar da hankali ga kula da lafiyarsa ba tare da mayar da hankali ga aikin gwamnati ba," a cewar kakakin gwamnatin kasar.
China ta tsaurara tsaro kan iyakokinta da Rasha
China ta tsaurara tsaro a iyakokinta da Rasha da ke arewa maso gabashi bayan karuwar yawan masu kamuwa da coronavirus a Rasha.
Kusan rabin mutum dubu daya da ke dauke da cutar ‘yan China ne da suka tsallako kan iyaka a yankin gabashi mai nisa na Rasha.
Yanzu China tana killace duk wanda ya shigo daga Rasha ta kan iyaka na tsawon mako hudu.
A rana daya an samu adadi mafi girma da suka kamu da coronavirus a Rasha inda mutum sama da 2500 suka kamu – kusan rabinsu a Moscow.
Ana samun karuwar masu mutuwa sanadin COVID-19 a Belgium
Alkaluma daga Belgium sun nuna cewa adadin mutanen da ke mutuwa a kullum sakamakon coronavirus ya karu zuwa 303 ranar Litinin, inda jimulla ake da mutum 3,903 da suka mutu sanadinta.
Wadanda suka mutu sun hada da mutanen da ke gidan gajiyayu da aka zarga da kasancewa dauke da cutar, amma ba a yi musu gwaji ba.
Ko da yake za a iya ganin kamar wadanda suka mutu ba su da yawa idan aka kwatanta da sauran kasashen Turai, amma yawan jama'ar Belgium bai wuce miliyan 11.5. Jamus na da yawan jama'a miliyan 83, kuma mutum kusan 3,000 ne suka mutu sakamakon coronavirus. - don haka a alkalumance mutanen da suka mutu a Belgium ya kusa na Spain da Italiya.
Belgium ta tabbatar mutum 30,000 suka kamu da cutar.
COVID-19: Mutum sama da 2500 sun warke a Afirka
Hukumar yaki da cututtuka ta Afirka, Africa CDC, ta ce mutum 2570 ne suka warke daga coronavirus a kasashe 52 mambobin kungiyar Tarayyar Afirka ya zuwa ranar Litinin, 13 ga watan Afrilun 2020.
Sanarwar da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce 14,528 ne suka kamu da cutar yayin da mutum 788 suka mutu a kasashen.
Ya zuwa yanzu dai, Afirka na cikin nahiyoyin da ba a samu mutuwa sosai kan coornavirus ba, abin da masana kiwon lafiya suka alakanta da rashin isassun na'urorin gano masu dauke da cutar.
Sun jaddada kira ga mutane su dauki matakan kare kansu daga kamuwa da cutar, wadanda suka hada da yawaita wanke hannaye da yin nesa-nesa da juna da amfani da kyalle wajen yin atishawa da makamantansu.
Masu dauke da COVID-19 sun kai 566 a Ghana