Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibiyarmu nan muka kawo karshen shirin na kawo muku bayanai kai tsaye kan annobar korona. Mun gode.

 2. Cutar korona ta kama shugabannin da ke yaki da ita a Kano

  Ma'aikatar Lafiyar jihar ta Kano ta bakin kwamishinanta, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa ta sanar da kamuwar shugabanni uku na kwamitin da ke yaki da cutar korona a Kano.

  Mutanen da cutar ta harba sun hada da shugaban kwamatin wanda bayan gwaji sakamako ya nuna yana dauke da cutar.

  View more on twitter
 3. Coronavirus: 'Dole gwamnatocin Arewa su tallafa wa 'yan cirani a Legas'

  Okada

  Masana harkar lafiya a Najeriya sun yi kira ga gwamnatocin Arewacin kasar da su tallafa wa 'yan uwansu masu cirani a Kudancin kasar musamman jihar Legas da birnin Abuja.

  Tun dai bayan da cutar korona ta yadu a jihar ta Legas da birnin na Abuja, gwamnatin Tarayyar kasar ta sa dokar hana zirga-zirga al'amarin da ya sa 'yan arewacin kasar masu ciranin suka rinka kwara garuruwansu.

  Dr Nasiru Sani Gwarzo ya shaida wa BBC cewa yadda 'yan cirani ke kwarara zuwa garuruwansu musamman jihar Kano, ya taka karawa wajen yaduwar cutar a jihar Kano.

  A cikin mako guda masu cutar a jihar Kano sun kai 21 inda kuma mutum daya ya mutu.

  Dr Gwarzo ya ce dole ne gwamnatocin arewacin kasar su tashi tsaye wajen ganin sun hana 'yan ciranin komawa yankin ta hanyar tallafa musu da dan abin da suke bukata domin ciyar da kansu.

 4. Yadda matata ta haihu ana tsaka da dokar hana fita a Kano

  Yakubu Abdu
  Image caption: Yakubu Abdu dan-gwangwan ne a Jihar Kano

  Tun a daren ranar Alhamis ne mutanen Kano suka shiga cikin dokar hana fita ta tsawon mako guda domin yaki da cutar korona sai kuma ga matar Yakubu Abdu ta haihu.

  Wasu bidiyo da hotuna da suka bulla a shafukan sada zumunta sun nuna yadda jami'an tsaro a Kano suke tabbatar da dokar hana fitar, inda suka rika saka wadanda suka yi kunnen kashi tsallen kwado.

  Yakubu Abdu dan-gwangwan ne da ke yawo a fadin birnin domin zakulo karafa a cikin bola ko kuma shara.

  "Matata ta haihu a jiya (Alhamis) kuma an garkame ni a cikin gida yau maimakon na fita neman abin da za ta ci ita da jaririn - ba tare da tsammanin tallafi daga wajen wani ba. Ina ganin wannan shi ne karshen tashin hankali," in ji Yakubu Abdu.

  Tururuwar da 'yar kasuwa kan yi daga kasashen Nijar da Chadi zuwa Kano na taimaka wa tattalin arzikin jihar sosai, musamman a manyan kasuwar tufafi ta Kantin Kwari da kuma Kasuwar Dawanau ta hatsi.

  Yakubu Abdu
  Image caption: Gwamnatin Kano ta ce dokar hana fitar ta mako guda ce
 5. Ana shirin yin gagarumin bikin Ista a Habasha

  Ethiopia

  Kiristoci cocin gargajiyar Orthodox na shirye-shiyen gudanar da bikin Ista a kasar Habasha wato Ethiopia yayin da ake tsaka da dokar haramta tarukan addini domin hana yaduwar cutar korona.

  Da yawa daga cocin Orthodox sun kulle kofofinsu a birnin Addis Ababa - abin da ba a saba gani ba a "Mako Mai Tsarki".

  Kasar tana cikin dokar-ta-baci, wadda ta haramta taro na sama da mutum hudu.

  Ethiopia

  Wannan biki ya sa da wuya a iya tabbatar da dokar musamman a kasuwanni, yayin da ake shirin yin bikin a ranar Lahadi.

  Kasuwanni sun cika makil a Addis Ababa, akasarin masu shaguna ba sa saka takunkumin rufe fuska sannan babu damar bayar da tazara.

  Hukumomi sun mayar da daya daga cikin manyan kasuwannin zuwa wani babban fili da zummar karfafa wa mutane gwiwa da su bai wa juna tazara, sai dai hakan ba ta samuwa.

 6. Coronavirus: An sallami mutum uku a Kaduna

  Ma'aikatar Lafiya ta jihar Kaduna ta sanar da sallamar mutum uku bayan warkewa daga cutar korona.

  Sanarwar wadda aka wallafa a shafin Twitter, ta ce an yi wa mutanen gwaji guda biyu inda gwajin ya nuna ba sa dauke da cutar.

  Yanzu adadin mutanen da suka warke daga cutar kuma aka sallame su ya zama hudu.

  View more on twitter
 7. Babu ranar kammala gasar Premier ta bana

  Premier League

  Kungiyoyin gasar Premier ta Ingila sun ce za su kammala wasa 92 da suka rage musu a kakar wasa ta bana kodayake ba su tattauna kan ranar da za a ci gaba da gasar ba a taron da suka gudanar ranar Juma'a.

  An yi tsammanin kungiyoyin za su tattauna kan wa'adin ranar 30 ga watan Yuni da aka sanya domin ci gaba da tamaula amma sai kawai suka yi muhawara kan "yiwuwar sauya tsarin" gasar.

  Hukumar Gasar Premier ta ce "babban burinmu shi ne" mu kammala wasannin amma a halin yanzu "dukkan ranakun ba a da tabbas" a kansu.

  Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Premier saboda annobar coronavirus.

  Karanta cikakken rahoton a nan

 8. An yi gobara a ofishin INEC na Abuja

  INEC

  Wata gobara da ta tashi a ofishin Hukumar Zabe ta Najeriya INEC da ke Abuja ta kone sashen kula da ayyukan jam'iyyu da kuma sashen yada labarai na hukumar.

  A wata sanarwa da kwamishinan sadarwa na hukumar ya fitar, Festus Okoye ya ce da karfe 11:30 na ranar Juma'a ne gobarar ta kama, inda nan take masu kashe gobara da ke harabar hukumar suka fara aikin kashe ta.

  INEC

  Daga baya jami'an hukumar kashe gobara ta kasa suka karaso, in ji INEC.

  "Ban da kujeru da tebura, babu wasu abubuwa masu muhimmanci da aka yi asara," a cewar sanarwar.

  Ta ci gaba da cewa: "Rahoton zaben fitar da gwani na jam'iyyu da kuma tarukansu na nan lafiya kalau. Su ma bayanan kudin da aka kashe a kamfe ba su tabu ba. Saboda haka gobarar ba za ta shafi ayyukan hukumar ba ko kadan."

  Sai dai hukumomi ba su bayyana dalilan da suka haifar da tashin wutar ba.

  Hukumar INEC ce ke da alhakin shirya dukkanin zabuka a Najeriya, tun daga shugaban kasa da 'yan majalisar tarayya zuwa gwamna da 'yan majalisar jihohi, zuwa shugaban karamar hukuma da kansiloli.

 9. Labarai da dumi-dumiWasu mutum 847 sun mutu a Birtaniya

  Mutum 847 ne suka mutu a rana guda a Birtaniya, wanda ya kawo jumullarsu zuwa 14,576.

  Ma'aikatar Lafiyar kasar ce ta wallafa bayanin a shafinta na Twitter.

  View more on twitter
 10. An kama mutanen da ke yunkurin harba wa 'yan sanda cutar korona a Tunisia

  'Yan sanda a Tunisia
  Image caption: Dokar hana fita a kasar Tunisia za ta kare ne a ranar 19 ga Afrilu

  Ma'aikatar harkokin cikin gida a kasar Tunisia ta ce ta kama mutum biyu, ciki har da wanda ake zargin mamba ne a kungiyar jihadi, bisa zarginsu da yunkurin shafa wa jami'an tsaro cutar korona.

  Ma'aikatar ta ce dan kungiyar jihadin, wanda aka sallama daga gidan yari kwanan nan, ya yi kokarin tunzura masiu dauke da cutar da su tofa wa jami'an tsaro yawu.

  Shi kuwa dayan ya ce an fada masa cewa ya yi ta tofa yawu a ko'ina idan ya je ofishin 'yan sanda na unguwarsu, yayin da ake sa ido a kansa ko yana dauke da cutar ta korona.

 11. Da yuwuwar korona ta kashe mutum 300,000 a Afirka – MDD

  Masu feshin korona

  Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce da yuwuwar cutar korona ta halaka mutum akalla dubu 300,000 a Afirka, sannan ta jawo mutum miliyan 30 su shiga halin talauci.

  Hukumar kula da tattalin arziki ta MDD a Afirka ta yi kiran samar da dala biliyan daya a matsayin kudaden jiran ko-ta-kwana domin taimaka wa nahiyar.

  Duk da cewa har yanzu adadin mutanen da suka kamu da cutar a Afirka bai zarta 20,000 ba, Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce nan da watanni masu zuwa adadin zai iya kaiwa miliyan 10.

  Akwai babban kalubale ta fuskar yaki da cutar a Afirka, kasancewar a kasashe da dama jama'a ba sa samun ruwa mai gudana, yayin da kusan kashi 60 cikin 100 na mutanen nahiyar ke rayuwa a wurare masu cunkoson jama'a.

 12. Mutum 14 sun mutu a gobarar sansanin 'yan gudun hijirar Jihar Borno

  'Yan gudun hijira a Jihar Borno

  Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ce akalla mutum 14 ne suka mutu sannan wasu 15 suka jikkata a wata gobara da ta tashi a sansanin 'yan gudun hijirar da Boko Haram ta raba da muhallansu a Jihar Borno.

  MDD ta ce gobarar, ita ce mafi muni a baya-bayan nan kuma ta faru ne a ranar Alhamis a garin Ngala da ke kan iyaka da kasar Kamaru.

  Ofishin da ke tattara kayan agaji na MDD ya ce an samu gobara sau 12 cikin watan da ya gabata a sansanonin 'yan gudun hijira daban-daban a Jihar Borno.

  Ta kara da cewa matsuguni 300 ne suka kone, inda suka bar dubban mutane a filin Allah. Kungiyoyin agaji suna nema musu tallafi.

  Ba a san dalilin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

  Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana lamarin a matsayin "abin tashin hankali matuka" sannan kuma ya yi umarni da a gudanar da bincike.

  Fiye da mutum miliyan biyu ne suka rasa muhallansu a yakin Boko Haram da aka shafe shekara 10 ana yi.

 13. Wasu kungiyoyin Musulunci sun raba kayan yaki da korona a Abuja

  Alhikma Wal Hasana

  Wasu kungiyoyi masu alaka da addinin Musulunci na Alhikma Wal Hasana da kuma Kungiyar Fityanu a Najeriya sun raba kayan kare kai daga cutar korona a Abuja, babban birnin kasar.

  Alhikma Wal Hasana

  Daga cikin irn abubuwan da kungiyoin suka raba wa al'umma sun hada da: takunkumin rufe fuska 4,800 da man wanke hannu na sanitizer 500 da kuma sabulun wanke hannu 1,000.

  Kungiyoyin suka ce sun so su raba wa talakawa 10,000 na kayayyakin, "amma duba da halin da kasa ke ciki samun gudunmuwa ta yi karanci da kuma tsadar kayan aiki da ake fama da ita," in ji su.

  Alhikma Wal Hasana

  Wuraren da aka yi rabo sun hada da sansanonin 'yan gudun hijira na Karmajiji da Durimi, sai Kubwa da Zuba da Tafa da Sabon Wuse.

 14. Wasu malamai sun sha alwashin yin sallar Juma'a a masallatan Pakistan

  Masallata a masallacin Jamia Thanvi da ke Karachi

  Wasu malamai sun sha alwashi gudanar da Sallar Juma'a a masallatai daban-daban a fadin kasar Pakistan, duk da matakan da aka dauka na hana taruwar jama'a domin dakile cutar korona..

  A farkon mako, wasu kungiyoyin addinin musulunci sun ce dkar hana fita daga gida bata hau kan masu zuwa masallatai ba.

  Sun ce sun bai wa tsofaffi umarnin yin sallolinsu a gida, suna masu cewa masallatai za su bi tsarin nesa-nesa da juna wajen sallah.

  Ranar Talata, wani malamin addinin Musuluncin kasar Taqi Usmani ya ce, "a halin da ake ciki, za a rika gudanar da salloli biyar ta hanyar daukar matakan kariya."

  Mutum kusan 7,000 aka tabbatar suna dauke da cutar korona a Pakistan, yayin da akalla mutum 120 suka mutu.

 15. Cutar Korona: A takaice...

  Kayan tallafin cutar korona
  • Hukumomi a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, ta kaddamar da rabon kayan abinci a yau Juma'a da zummar rage radadin da halin mutane suka shiga sakamakon tilasta musu zaman gida a yakin da ake yi da cutar korona.
  • Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afirka (Africa CDC) ta ce za ta kaddamar da shirin raba kayan gwajin cutar korona miliyan daya domin cike "wagegen gibin" da aka samu na rashin gwajin cutar a baya. Shugaban hukumar John Nkengasong ya ce akwai karancin gudanar da gwajin cutar a Afirka.
  • Sabbin alkaluma daga Jami’ar Johns hopkins mai bibiyar yaduwar cutar korona sun nuna cewa mutum miliyan 2,169,022 ne suka harbu da cutar a fadin duniya. Daga cikin wannan adadi, dubu 146,071 sun mutu, sannan dubu 552,264 sun warke.
  • Firai Ministan Sudan Abdalla Hamdok ya sauke gwamnan babban birnin kasar, Khartoum, bayan ya amincewa da dokar hana yin sallar jam'i, wadda gwamnati ta saka domin dakile yaduwar cutar korona. Janar Ahmed Abdul Hammad Mohammed ya ce ba zai aiwatar da matakin da aka dauka na haramta yin sallah a masallatai da kuma ibada a coci-coci ba wadda za ta soma aiki ranar Asabar.
  • Mazauna birnin Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya, sun wayi garin Juma’a cikin dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya. Gwamna Abdullahi Umar Gamnduje ya ce dokar ta tsawon mako guda ce domin dakile yaduwar cutar korona, wadda zuwa yanzu ta kama mutum 21 a jihar kuma daya yam mutu.
 16. Afirka za ta zama cibiyar coronavirus - Hukumar Lafiya ta Duniya

  Ta kara da cewa Afirka ba ta da isassun na'urorin da ke tamaika wa masu dauke da cutar korona wajen yin numfashi.

  Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa nahiyar Afirka ka iya zama cibiyar cutar korona nan gaba.

  An samu karuwa sosai ta mutanen da ke kamuwa da cutar a nahiyar a makon jiya.

  Mutum kusan 1,000 ne suka mutu sannan kimanin mutum 18,000 suka harbu da cutar ta korona a Afirka ya zuwa yanzu, ko da yake wannan adadi yana baya sosai idan aka kwatanta da na Turai da Amurka.

  Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce cutar na bazuwa daga manyan birane zuwa wasu yankunan a nahiyar.

  Ta kara da cewa Afirka ba ta da isassun na'urorin da ke taimaka wa masu dauke da cutar korona yin numfashi.

 17. An kori minista daga aiki saboda coronavirus

  Mr Mandetta
  Image caption: Mr Mandetta ya yi mutumin da zai gaje shi fatan alheri

  Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya sauke Ministan Lafiyar kasar saboda yadda yake tafiyar da batun cutar korona.

  Ministan, Luiz Henrique Mandetta, ya wallafa sakon Twitter inda ya ce Mr Bolsonaro ya mika masa takardar sallama daga aiki.

  Shugaba Bolsonaro ya fito fili ya soki Mr Mandetta saboda ya bai wa mutane umarni su dauki matakin yin nesa-nesa da juna wajen mu'amala, su kuma zauna a gidajensu.

  Shugaban na Brazil bai amince da wadannan matakai ba, inda ya rika cewa cutar korona ba komai ba ce face "wata 'yar karamar mura."

  A sakon da Mr Mandetta ya wallafa a Twitter ya ce: "Ina mika godiya ta ga dukkan mutanen da suka yi aiki tare da ni a Ma'aikatar Lafiya, kuma ina yi wa mutumin da zai gaje ni fatan alheri."

 18. Ma'aikatan otal biyar sun kamu da coronavirus

  Ma'aiakcin lafiya

  Ministan Lafiyar Kenya Mutahi Kagwe ya tabbatar da karin mutum 12 da suka kamu da cutar korona a kasar, ciki har da ma'aikatan otal-otal su biyar.

  Mr Kagwe ya shaida wa manema labarai cewa an yi wa mutun fiye da 450 gwaji ranar Juma'a da safe inda ya ce: "Mun samu mutum 12 da ke dauke da cutar ko da yake bamu gama gwaji a yau ba".

  An killace matafiyan da suka isa kasar daga kasashen waje a wasu otal-otal da ke Nairobi.

  An tabbatar wasu daga cikinsu suna dauke da cutar korona, ko da yake ba a taba tunanin cewa ma'aikatan otal-otal din suna dauke da cutar ba sai da aka yi musu gwaji.

  Ya zuwa Juma'a, an tabbatar mutum 246 na dauke da cutar a Kenya.

  Mr Mutahi ya ce gwamnati tana kara kaimi wajen yin gwaji domin gano matsayin mutanen da suka yi mu'amala da wadanda ke dauke da cutar ta korona.

 19. Coronavirus: An kaddamar da rabon kayan abinci a Abuja

  Hukumar Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, ta kaddamar da rabon kayan abinci da zummar rage radadin da mutane suka fada a ciki sakamakon tilasta musu zaman gida.

  Gwamnati ta yi wa mutane kulle ne a matakin dakile yaduwar cutar korona.

  A sakon da Hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Juma'a, ta ce minista a ma'aikatar Babban Birnin Tarayya, Ramatu Aliyu, ta kaddamar da shirin raba kayana abincin a karamar hukumar Abaji da ke wajen birnin.

  Ya zuwa yanzu, an tabbatar mutum 67 sun kamu da cutar korona a Abuja.

  View more on twitter