Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Sojoji sun kashe 'yan bindiga 89 a Zamfara

  Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe 'yan bindiga tamanin da tara da ke kai hare-hare a kan farar hula a jihar Zamfara.

  Kakakin Rundunar, Manjo Janar John Enenchie, ya ce sun samu taimakon daga jihar Neja wajen kai wa 'yan bindigar farmaki.

  A cewarsa kuma sun yi nasarar kwato makamai da daruruwan shanu da aka sace.

  An kuma ceto mutum biyar da aka yi garkuwa da su.

  Sama da shekaru biyar kenan da jihar Zamfara da wasu jihohi makwabta ke fuskantar hare-hare babu kakautawa na 'yan fashi da ke sake kassara arewacin kasar data sha fama da rikicin Boko Haram.

  Shanu
  Image caption: Shanu fiye da 300 aka gano a cikin daji
 2. Rufewa

  A nan za mu dakatar da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye musamman kan abubuwan da ke faruwa game da cutar korona daga sassan duniya.

  Sai ku kasance da mu Idan Allah Ya kai mu gobe, inda za mu ci gaba da kawo ma ku labarai da rahotanni kai-tsaye.

 3. 'Yan sanda sun kama wadanda suka yi fasa kaurin wiwi a cikin akwatin gawa

  ‘Yan sanda a Afrika Ta Kudu sun cafke wasu mutane biyu da kokarin fasa kaurin kilo 80 na tabar wiwi a cikin akwatin saka gawa.

  Hukumar ‘yan sanda da ke yankin Kwazulu Natal ta bayyana cewa mutanen sun yi badda kama ne da sunan masu sana'ar shirya binne gawa.

  Bayan gudanar da bincike ne aka gano kilo 80 na tabar wiwin a cikin jakunkuna 30 a cikin akwatin gawa.

  A yanzu dai an cafke mutanen kuma ana shirin gurfanar da su a gaban kotu sati mai zuwa.

  Dan sandan Afrika ta Kudu
  Image caption: Dan sandan Afrika ta Kudu
 4. Coronavirus: Fiye da 7,000 sun warke a Afirka

  Tarayyar Afirka ta ce adadin mutum 27,862 suka kamu da cutar korona a kasashe mambobinta 52.

  Alkalumman da bangaren kungiyar da ke kula da cututtuka masu yaduwa ya wallafa a Twitter sun bayyana cewa cutar korona kawo yanzu ta kashe mutum 1,304 yayin da kuma mutum 7,633 suka warke.

  Cutar ta fi yaduwa a yankin arewacin Afirka, kamar yadda alkalumman suka nuna

  View more on twitter
 5. Coronavirus: Cikin wata daya fiye da mutum 1,000 suka kamu a Najeriya

  Cutar korona na kara yaduwa a Najeriya inda ake samun karuwar masu dauke da cutar, kuma take kara yaduwa a sassan kasar.

  Cikin wata daya an samu mutum fiye da 1,000 da suka kamu da cutar a Najeriya.

  Alkaluman cutar da hukumar NCDC ke fitarwa sun sauya daga 42 da aka bayyana sun kamu a ranar 24 ga Maris zuwa 1,095 a ranar 24 ga Afrilu.

  A rana daya 24 ga Afirlu, mutum 114 aka tabbatar da sun kamu da cutar, haka ma a ranar 21 ga Afrilu mutum 117 suka kamu, adadi mafi girma da aka samu a Najeriya.

  Sannan yawan wadanda suka mutu cikin wata daya sun haura 30 tsakanin 24 ga Maris zuwa 24 ga Afrilu.

  Sai dai yayin da cutar ke kara yaduwa, ana kuma kara samun wadanda ke warkewa daga cutar.

  Zuwa yanzu cutar ta yadu a jihohi 26 na Najeriya hadi da Abuja. Kuma yanzu alkalumman hukumar NCDC sun nuna yawan wadanda suka kamu da cutar sun kai 1,095 yayin da 208 suka warke, 32 kuma suka mutu.

  Coronavirus
  Image caption: Yadda cutar ke ci gaba da yaduwa
 6. Likitoci a Pakistan suna yajin cin abinci

  Wasu likitoci da ma'aikatan jinya a yankin Punjab da ke Pakistan sun shiga yajin cin abinci, bayan sun koka kan rashin kayan aikin duba masu cutar Korona.

  Mai magana da yawun ma'aikatan lafiyar ya bayyana cewa sun duba irin hadarin da suke fuskanta kuma idan ba a kare su ba to ko daukacin al'umma na cikin hadari.

  Likitoci hamsin ne aka kama a garin Quetta, bayan sun bukaci karin kayan aiki a farkon wannan watan.

  Yajin cin abincin na zuwa a daidai lokacin da gwamnatin Pakistan ke rokon ma'aikatan lafiya 'yan kasar da ke zama kasashen waje da da su ba da ta su gudummawa ko da ta kafar intanet ne.

 7. An samar da wurin gwajin cutar korona a Sokoto da Zaria

  Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar da karin wuraren gwajin cutar korona guda biyu a Najeriya.

  A sanarwar da ta wallafa a Twitter, hukumar ta ce za a iya gwajin cutar a asibitin koyarwa na Jami'ar Usman Danfodio a Sokoto da kuma asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

  Hukumar ta ce yanzu tana da cibiyoyin gwajin cutar korona 15.

  View more on twitter
 8. Labarai da dumi-dumiCutar korona ta kashe sama da mutum 200,000 a duniya

  Yawan wadanda cutar korona ta kashe a duniya sun zarta mutum 200,000, kamar yadda alkalumman jami'ar Johns Hopkins da ke bin diddigin cutar suka nuna.

  Wannan na zuwa a yayin aka samu karin wadanda cutar korona ta kashe a Faransa.

  Yanzu mutum 22,614 cutar ta kashe a fadin Faransa.

  Tun da farko, Birtaniya a ranar Asabar ta zama kasa ta biyar da adadin wadanda suka mutu a asibiti sakamakon cutar korona suka kai 20,000, bayan Amurka da Italiya da Spain da kuma Faransa.

 9. 'Akwai yiyuwar kara tsawaita dokar hana fita a Najeriya'

  Hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya NCDC ta nuna cewa lokaci bai yi ba yanzu da za a sassauta dokar hana fita a kasar.

  Yayin da kwamitin shugaban kasa kan cutar korona ke bayani kan matakan da ake dauka a ranar juma'a, shugaban hukumar NCDC Dr Chikwe Ihekweazu, ya ce duk da cewa hana ifta ya yi mummunan illa ga tattalin arziki amma akwai bukatar a kara hakuri da jure wa kara jure domin tabbatar da ingantacciyar lafiyar al'umma.

  "Za mu wuce wannan lokacin mu koma ga rayuwarmu da muka saba, amma har yanzu ba mu kai ga wannan lokacin ba, don haka nake neman juriya da hakuri da goyon baya."

  A ranar Litinin wa'adin dokar hana fita ta tsawon mako biyu da shugaba Buhari ya tsawaita a jihohin Legas da Ogun da kuma babban birnin Tarayya Abuja domin dakile yaduwar cutar korona za ta kawo karshe.

  A kallum kuma cutar korona kara yawa take inda ake samun karuwar masu dauke da cutar, da kuma yadda take kara yaduwa a sassan Najeiya.

  Dr Chikwe Ihekweazu
 10. Wata matar da aka ce ta mutu ta dawo a Ecuador

  Wata mata mai shekara 74 da aka ce cutar korona ta kashe ta a Ecuador a watan da ya gabata, an same ta da ranta.

  Wani dan uwan Alba Maruri ya gane jikinta amma daga nesa, kuma an binne gawarta.

  Bayan makwanni uku Maruri ta tashi, tana neman ta yi magana da ‘yar uwarta. Danginta sun farin ciki amma sun ce za su kai asibitin da al’amarin ya faru kotu kan rudanin da aka haifar da kuma kudaden da suka kashe na binne gawar.

  Ba su san tokar gawar da yanzu suka ajiye a gida ba.

  Ecuador na daya daga cikin kasashen Latin Amurka da cutar korona ta yi kamari, inda sama da mutum dubu 22 suka kamu da cutar yayin da kuma kusan 600 suka mutu.

 11. Labarai da dumi-dumiAdadin wadanda suka mutu a Birtaniya ya wuce 20,000

  Sashen kula da jama'a na Birtaniya ya ce wasu mutum 813 sun mutu a asibitocin kasar sakamakon cutar korona.

  Yanzu jumillar adadin ya zama 20,319 - wannan ya sa Birtaniya ta zama kasa ta biyar da take da fiye da mutum 20,000 da suka rasa rayukansu, tare da Italiya da Spaniya da Faransa da Amurka.

 12. Cutar korona ta kara kashe mutum daya a Legas

  Hukumomin lafiya a jihar Legas sun sanar da karin mutum daya da cutar korona ta kashe.

  Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta jihar ta sanar a Twitter ta ce yanzu jimillar mutum 19 cutar ta yi ajalinsu a Legas.

  Sanarwar ta kuma ce daga ranar Juma'a 24 ga Afirlun 2020 an kara samun mutum 80 da suka kamu da cuta, inda yawan wadanda suka kamu suka kai 670.

  View more on twitter
 13. Marayu 23 sun kamu da cutar korona

  Akalla mutum 23 da suka kunshi yara 13 masu bukata ta musamman suka kamu da cutar korona a wani gidan marayu a Belarus.

  Gidan marayun na Vesnova da ke yankin Hlusk, na dauke da sama da yara marayu 170 da kuma matasa masu bukata ta musamman.

  Kungiyar da ke daukar nauyin gidan marayun ta Chernobyl Children International ta shaida wa manema labarai cewa wasu daga cikin yaran, rashin lafiyarsu ta tsananta.

  Masu kula da gidan marayun sun roki gwamnatin Belarus ta kwashe yaran da ke fama da cutar a yi masu tanadin wani wurin da ya dace.

 14. Coronavirus: Fiye da mutum 18,000 sun mutu a Ingila

  Alkalumma daga asibitotin Ingila sun tabbatar da sama da mutum 18,000 cutar korona ta kashe.

  Hukumomin lafiya na Ingila sun kuma sanar da karin mutum 711 da cutar ta kashe, inda yanzu adadin ya kai 18,084.

  A Scotland mutum 1,231 suka mutu, inda aka samu karin mutum 47.

  An kuma kara samum mutum 23 da suka mutu a Wales, inda yanzu adadin mutum 774 hukumomi suka ce cutar ta kashe.

  Asibiton korona a Ingila
 15. Korona ta kama ma’aikatan kamfani kusan 100 a Afirka ta kudu

  Kusan ma’aikata 100 na wani kamfani a Afirka ta kudu da suka bijerewa shawarar bayar da tazara tsakaninsu sun harbu da cutar korona.

  Ma’aikatan wani kamfanin samar da magunguna ne wanda aka rufe a makon nan.

  A ranar Talata ma’aikatar kwadago ta Afirka ta kudu ta ce babu wasu matakai da aka dauka na kariya ga ma’aikata daga kamuwa da cutar, kuma an dakatar da ayyukansu.

  Afirka ta kudu ce ta fi fama da korona a nahiyar Afirka inda sama da mutum 4,000 suka kamu da cutar.

 16. An yi girgizar kasa a yankin Makkah

  An samu girgizan kasa mai karfin maki 2.7 a gabashin Qunfudah da ke cikin yankin Makkah kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.

  An samu girgizan kasar ne ranar Alhamis jajibirin azumin Ramadan. Kuma hukumomin Saudiyya sun ce duk da girgizan kasar ba ta yi karfi ba, amma mutanen yankin sun ji girgizan.

  Hukumomi sun ce ba wannan ne karon farko da aka taba samun girgizan kasa a yankin ba, kuma ba duk girgizan kasa da ake samu ba suke da karfin da tasirinsu zai haifar da wani ta'adi ga al'umma.

  Saudiyya ta ce tana daukar matakai tare da yin kira ga al'ummar kasar cewa lamarin ba wani abin tsoro ba ne ko haifar da fargaba.

  Taswirar yankin Makkah
 17. Labarai da dumi-dumiMutum daya ya kamu da cutar korona a Kaduna

  Gwamnatin Jihar kaduna ta tabbatar da samun karin mutum daya da ya kamu da cutar korona, abin da ya kawo jumillar adadin wadanda suka harbu da ita a jihar zuwa 10.

  A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, gwamnatin ta ce mutumin da ya kamun ya yi mu'amala ne da daya daga cikin wadanda suka kamu a farkon wannan makon.

  Ya zuwa yanzu Kaduna ta sallami mutum shida da suka warke, ciki har da Gwamna Nasir El-Rufai, wanda aka sallama ranar 22 ga watan Afrilu.

  Ta ce hukumar NCDC ta kafa cibiyar yin gwajin cutar a boirnin Kaduna kuma tuni aka gwada mutum 133, yayin da ake kan tantance wasu cibiyoyin biyu a Zaria da Kaduna.

  View more on twitter
 18. Babu hujja ko wanda ya warke daga korona ba zai sake kamuwa ba – WHO

  Coronavirus

  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce "babu wata hujja a yanzu da ke nuna cewa mutanen da suka warke daga cutar korona ba za su sake kamuwa da ita ba".

  An sha bayyana cewa wadanda suka warke daga cutar jikinsu na samun garkuwar da zai iya murkushe cutar.

  A Birtaniya, gwajin garkuwar jikin mutum da kuma sa ido kan wadanda suka warke domin gano girman harbuwa da cutar na daga cikin "rukunai biyar" da gwamnati ta saka a gaba yayin gwaji, a yunkurin kawo karshen cutar.

  Gwajin garkuwar jiki - domin gano ko mutum ya taba kamuwa da cutar a baya - ana ganin yana da tasiri wurin gano dalilan da za su sa a dage dokar hana zirga-zirga da aka saka, da kuma taimaka wa masu binciken samar da rigakafinta.

 19. Kananan shagunan sayar da kayayyaki sun ci gaba da harkoki a Indiya

  Indiya

  Indiya ta sassauta wa kananan shagunan sayar da kayayyaki domin su ci gaba da harkoki wata daya bayan sun kasance a rufe saboda dokar hana fita domin hana yaduwar cutar korona.

  Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce rabin ma'aikata ne kawai za su yi aiki kuma wajibi ne su dabbaka bayar da tazara yayin harkokinsu sannan su saka takunkumin rufe fuska.

  Gwamnati tana kokarin farfado da harkokin tattalin arziki ne.

  Akwai kusan mutum 25,000 da suka kamu da cutar korona a Indiya kuma 780 ne suka mutu sakamakon cutar.

 20. Gwamnatin Legas ta gargadi makarantu masu zaman kansu

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Umar Shehu daga Legas

  Ma’aikatar Ilimi ta jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta gargadi makarantu masu zaman kansu a jihar da su nisanci sake komawa daukar karatun zango na uku, har sai bayan tsawon lokcin da aka dauka na hana yawo ya zo cika.

  Kwamishinar Ilimi ta Jihar Folasade Adefisayo ce ta bayar da umarnin a wata sanarwa da ta bayar, inda ta ce maimakon bude makarantun gara su koma yin amfani da intanet wurin koyar da daliban.

  Wata mai makaranta a jihar ta shaida wa wakilin BBC Umar Shehu Elleman cewa, bincikensu ya nuna cewa kashi 50% na iyayen yaran ba sa amfani da intanet.

  Sai dai gwamnatin jihar ta ce za ta yi amfani da gidajen rediyo domin koyar da daliban kuma a kyauta.

  Tun a watan karshen watan Maris Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a Legas da Abuja da kuma jihar Ogun a wani yunkuri na kauce wa bazuwar cutar korona a jihar.