Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir, Buhari Muhammad Fagge, Awwal Ahmad Janyau da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Rahotanni a wannan shafi sun zo karshe

  Mun kawo karshen rahotannin kai-tsaye a wannan shafi. Ku yi kasa domin karanta abubuwan da suka faru a yau Laraba.

  Umar Mikail ke cewa a yi sahur lafiya - ga masu azumi.

 2. 'Yan majalisa su sa ido kan bashin da Buhari zai karbo – PDP

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Ibrahim Isa daga Abuja

  Babbar jam`iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci Majalisar Dattawan kasar ta sa-ido sosai wajen ganin gwamnatin shugaba Buhari ta yi amfani da naira biliyan 850 da za ta ranta ta hanyar da ta dace.

  Jam`iyyar ta ce ba ta gamsu da yadda gwamnatin APC mai mulkin Najeriya ta sarrafa wasu kudaden da ta karbi rancensu a baya ba.

  A ranar Talata ne Majalisar Dattawan Najeriyar ta amince wa shugaban kasar karbar rancen don cike gibin kasafin kudin wannan shekarar.

  Mr Kola Olagbondian, shi ne kakakin jam`iyyar PDP na kasa, kuma ya fada wa wakilin BBC Ibrahim Isa cewa sun shawarci 'yan Najeriya su dora laifin duk abin da ya biyo baya kan 'yan majalisar tarayya.

 3. Rikicin addini ya barke a sansanin 'yan gudun hijirar Najeriya na Kamaru

  Sansanin 'yan gudun hijira

  Wani rikici na addini ya barke tsakanin Musulmai da Kiristoci ‘yan gudun hijirar Najeriya mazauna sansanin Minawao da ke cikin Kamaru a ranar Laraba.

  Hakan ya kai ga an rusa gidaje da kona wasu na bangarorin biyu masu adawa da juna, musamman mazauna shiyya ta biyu da ta uku na sansanin.

  Har wa yau, sun ji wa juna rauni da makamai. Sai dai jami’an tsaro sun shiga tsakani, abin da ya kawo lafawar rikicin.

  Wakilin BBC a Kamaru, Mahamman Babalala ya ce alamu sun nuna cewa dukkan bangarorin ‘yan asalin Jihar Borno ne da suka fito daga kananan hukumomin Goza da Bama.

  Rikicin ya fara ne tsakanin yara biyu kanana (dan Kirista da dan Musulmi), inda suka kaure da dambe. Bayan mahaifin Musulmin ya raba su, sai mahaifin daya yaron ya ce ba a yi wa yaronsa adalci ba.

  Iyayen biyu sun ci gaba da husuma tsakaninsu, kuma bayan labari ya shiga unguwanni sai rikicin ya zama na bambancin addini.

 4. Najeriya ta tattauna da jakadan China kan halin da 'yan Najeriya ke ciki

  Geoffrey Onyeama

  Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya gana da jakadan China a Najeriya ranar Laraba, kamar yadda ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  Jakada H.E Zhou Pingjian ya ziyarci Onyeama ne domin tattaunawa game da zargin da ake yi cewa ana nuna wa 'yan Najeriya wariya a China sakamakon annobar cutar korona.

  A karshen makon nan ne dai hukumomi a Najeriya suka ce sun bayyana wa China rashin jin dadinsu game da halin da 'an Afirka ke ciki a kasar.

  Tun a farkon watan Afrilu ne aka fara samun rahotannin da ke cewa hukumomin China na fitar da 'yan Afirka daga gidaje da dakunan otel-otel dinsu tare da killace su, duk da cewa ba sa dauke da cutar korona.

  Sai dai China ta sha miusanta wannan zargi.

  View more on twitter
 5. Mun damu da halin da Mubarak Bala ke ciki – Amnesty International

  Amnety International

  Kungiyar kare hakki ta Amnesty International ta ce tana bibiyar halin da Mubarak Bala wanda aka ce shi ne shugaban wadanda babu ruwansu da addini a Najeriya yake ciki, bayan kamashi da jami'an 'yan sanda suka yi.

  Amnesty ta ce ta damu matuka kan karuwar barazanar da ake yi wa rayuwarsa a kafafen sada zumunta a Najeriya.

  A ranar Talata aka kama Mubarak Bala a jihar Kaduna, wanda ake sa ran za a mayar da shi Kano jiharsa ta haihuwa, kuma daga nan ne dimbin Musulamai suka rubuta wa hukumomi korafi da zarginsa da yin batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

  Ba a sani ba dai ko za a saurari karar tasa a Kano, inda ake gudanar da Shari'a a wasu kotunan jihar.

  In dai aka zarge shi da laifin batanci ga addini a kotun Shari'ar Musulunci da yiyuwar a yanke wa Mista Bala hukuncin kisa.

  Amma Amnesty ta shawarci hukumomi da su kare 'yancinsa na dan Adam tare da tabbatar da an bi kundin tsarin mulkin Najeriya.

  Mubarak Bala ya fice daga Musulunci a 2014, kuma ya ci gaba da kokarin yada munufarsa ta rashin bin kowanne addini a yankin da Musulmai suka fi yawa.

  Kungiyoyin marasa addini ta duniya sun yi kira da a gagguta sakin Mubarak Bala.

 6. Shugaban kasar Guinea ya ce mantaleta na maganin cutar korona

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama domin kallon bayanin Abdulbaki Jari

  Shugaban Kasar Guinea, Alpha Conde ya shawarci mutane da su rika shafa mantaleta a hanci kuma su rika shan ruwan zafi domin hakan zai masu maganin cutar korona.

  Sai dai a bayanin da Abdulbaki Jari ya saba yi kullum kan annobar cikin dakika 60, masana harkar lafiya sun ce babu hujja da ke tabbatar da gaskiyar hakan.

 7. Za mu dauki ma'aikata 1,000 a kowacce karamar hukumar Najeriya – Gwamnati

  Festus Keyamo

  Karamin Ministan Kwadago a Najeriya, Festus Keyamo ya rantsar da wani kwamiti da zai aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na daukar mutum 1,000 aiki a kowacce karamar hukuma 774 a kasar.

  A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, fadar gwamnatin Najeriya ta ce an rantsar da kwamitin ne bayan Shugaba Buhari ya amince da fara gudanar da shirin na tsawon wata uku.

  Ta ce an kirkire shi ne da zummar rage wa 'yan kasa radadin da annobar korona ta jefa su ciki.

  Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin babban darakta a ma'aikatar samar da aikin yi Dr. Nasiru Ladan, sai kuma wakilai daga ma'aikatun kudi da lafiya da aikin gona da sufuri da ruwan sha da ma'aikatar ayyuka da gidaje.

  Idan shirin ya tabbata, gwamnatin Najeriya za ta bai wa mutum dubu 774,000 aikin yi na tsawon wata uku.

  View more on twitter
 8. Ana tsara yadda za a ci gaba da gasar La Liga

  La Liga

  Mahukuntan gasar La Liga na tsara hanyar da kungiyoyi za su koma yin atisaye cikin gaggawa da zarar gwamnatin Spaniya ta amince.

  A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasanni a Spaniya don gudun yada cutar korona.

  Mahukuntan gasar La Liga sun tsara hanyoyi da dama kan yadda 'yan kwallo ya kamata su fara atisaye, inda suka karkata kan matakan kare lafiya da zarar gwamnati ta amince.

  Cikakken labarin yana nan

 9. Tunusiya za ta sassauta dokar hana zirga-zirga

  Wani butun-butumi na yawon sintiri yayin dokar hana fita a babban birnin kasa
  Image caption: Wani butun-butumi na yawon sintiri yayin dokar hana fita a babban birnin kasar

  Ministan Lafiya na Tunusiya Abdelatif el-Makki ya ce kasarsa ta shawo kan bullar cutar korona a karon farko.

  Mutane 40 ne suka mutu dalilin cutar a kasar da ke arewacin Afirika, kuma wadanda suke dauke da cutar ba su kai 1,000 ba.

  Yanzu kuma tana shirin sassuta dokokin hana zirga-zirga da ta sa a matakan yaki da cutar korona.

  Cikin sassucin, za a kyale masu abinci da masu gine-gine su bude wajen kasuwancinsu a mako mai zuwa, kuma rabin ma'aikatan gwamnati za su koma bakin aikinsu.

 10. Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 11

  Sojojin Najeriya

  Rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole da ke arewa maso gabashin kasar ta ta ce ta halaka mayakan Boko Haram kusan 11 a cikin mako guda da ya gabata.

  Rundunar ta ce ta yi artabu da 'yan kungiyar ne a ranaku daban-daban, abin da ya kai ga rasa ran sojanta daya sannan daya ya ji rauni.

  An kai hare-haren ne a Jihar Borno, a cewar rundunar. Ta kara da cewa wasu mayakan kungiyar biyu sun mika wuya tare da kwato makamai da babura da aka yi wa fentin kakin sojoji.

  Kazalika ta ce ta karbi wasu sabbin 'yan gudun hijira 19 a sansaninta daga kauyen Jebe.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutum 20,000 sannan ya tilasta wa mutum kusan miliyan daya tserewa daga mahallansu.

  View more on twitter
 11. Coronavirus: Mutum 49 sun warke a Legas

  Gwamnatin Legas ta ce karin mutum 49 sun warke daga cutar korona.

  Sanarwar da ma'aikatar lafiya ta jihar ta fitar a Twitter ta ce wadanda suka warke sun kunshi mata 28 da maza 21 da suka hada da 'yan kasashen waje.

  Ta kuma ce tuni aka sallami wani dan kasar Girka a cibiyar killace masu korona da ke Yaba.

  A cewar sanarwar yanzu adadin mutum 187 suka warke a jihar.

  View more on twitter
 12. Gwamnatin Tanzania ta fadi yawan masu korona

  AFP

  Firaiministan Tanzaniya Kassim Majaliwa ya ce akwai mutum 480 da ke dauke da korona a kasar, wannan na zuwa ne bayan wata kakkausar suka da gwamnatin ta sha a kafafen sada zumunta saboda gaza fitar da bayanai kan cutar a kullum.

  Rabon da gwamnatin ta bayyana halin da ake ciki game da cutar tun a makon jiya inda ta ce akwai masu dauke da cutar 306 a fadin kasar.

  Karancin ba da bayanai kan masu dauke da cutar ya janyo jita-jitan cewa gwamnatin na boye ainihin adadin masu dauke da cutar a kasar.

  Shugaban kasar John Magufuli ya shawarci mutanen kasar da su mayer da hankali wajen yin ibada a matsayin hanyar dakile yaduwar cutar.

  Ya ce wannan annoba shaidan ne ya kawo ta don haka yawan addu'a zai kawo karshenta.

 13. Labarai da dumi-dumiCutar korona ta kashe fiye da mutum 26,000 a Birtaniya

  Cutar korona ta kashe mutum 26,097 a birtaniya daga 2 ga Maris zuwa 28 ga Afrilu.

  A karon farko, alkalumman sun hada da wadanda suka mutu tsakanin al'umma da kuma asibitoci.

  Mace-macen da aka kidaya, su ne mutanen da gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.

  Sakataren harakokin wajen Birtaniya ya ce an samu karin wadanda suka mutu 765 idan aka kwatanta da yawan wadanda suka mutu a ranar Talata.

 14. Yawan wadanda korona ta kashe a Indiya sun zarta 1,000

  Yawan wadanda suka mutu a Indiya sun zarta mutum 1,000, kamar yadda alkalumman jami’ar Johns Hopkins suna nuna.

  A ranar Laraba an samu adadi mafi yawa inda mutum73 suka mutu.

  Sama da mutum 31,000 aka tabbatar da suna dauke cutar a kasar.

  Ana ganin dai adadin ya yi kadan idan aka kwatanta da wasu kasashe, amma masana sun ce akwai karancin gwaji a kasar.

 15. An bukaci 'yan majalisar Uganda su dawo da kudaden korona

  'Yan majalisa a Uganda

  'Yan majalisa a Uganda da suka raba wa kansu biliyan 10 na kudin kasar kwatankwacin fam miliyan biyu domin wayar da kai kan cutar korona an bukaci su dawo da kudaden.

  An bayyana cewa kowanne dan majalisa ya samu dala dubu biyar, wasunsu kuma sun ki karbar kudin.

  Shugaban Ugandan Yoweri Museveni ya soki 'yan majalisar tare da yin allawadai da raba wa kansu kudade da suka yi

  Wata babbar kotu a Kampala yanzu ta bukaci 'yan majalisar su dawo da kudaden.

  Zuwa yanzu mutum 79 da suka kamu da cutar korona a Uganda.

 16. Firaministan Guinea-Bissau ya kamu da korona

  Nuno Gomes Nabiam, Firaministan Guinea-Bissau, da wasu ministocinsa uku, gwaji ya tabbatar da suna dauke da cutar korona.

  An killace su a wani hotel da Bissau babban birnin kasar bayan tabbatar da sakamakon gwajin a ranar Talata, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta kasar ta sanar.

  Yanzu sama da mutum 70 suka kamu da cutar a kasar da ke yammacin Afirka, yayin da mutum guda ya mutu.

  Ministan lafiya na kasar Antonio Deuna ya yi gargadin cewa adadin na iya karuwa.

  Nuno Gomes Nabiam ya zama Firaministan a watan Fabrairu
 17. Gwamnatin Legas ta koka kan yawan gawarwakin da ke ajiye

  Gwamnatin jihar Legas ta koka kan yawan gawarwaki da ke jibge a dakukan ajiye gawarwaki a jihar.

  Tun kafa dokar hana fita aka dakatar da jana’iza a jihar har zuwa lokacin kawo karshen kullen, yayin da kuma ake samun karuwar wadanda ke mutuwa saboda cutar korona.

  Gwamnan jihar ya yi kira ga ‘yan uwan mamatan wadanda suka san suna da gawarwaki a ajiye a dakunan ajiye gawa su je su binne gawarsu.

  Gwamnan ya ba iyalan mamatan wa'adin mako biyu idan ba haka ba gwamnati za ta kwashe gawarwakin ta yi jana'izarsu.

  Ku saurari rahoton wakilin BBC Umar Shehu Elleman

  Video content

  Video caption: Gwamnatin Legas ta koka kan yawan gawawwaki da ke ajiye
 18. Burtaniya ta ce ta mayar da mutum sama da milyan daya gida

  Ministan harkokin wajen Burtaniya Nigel Adams ya ce, kasar ta mayar da mutum miliyan 1.3 gida tun bayan barkewar cutar korona.

  Mista Adam ya ce yan kasar 200,000 ne suka dawo gida daga Spaniya tare da wasu 50,000 daga Australia a watan da ya wuce.

  Ya kuma bayyana cewa Burtaniya na shirin dawo da dubban matafiya gida daga mako mai zuwa ta kamfanin jirgin sama na charter, wadanda suka hadarda matafiya daga Bangladesh da Nijeriya da kuma New Zealand.

 19. Mutane sama da biliyan daya da rabi ka iya fadawa halin ni 'yasu a duniya

  AFP

  Kungiyar kwadago ta duniya ta yi gargadin cewa akalla mutum biliya a duniya na fuskantar barazanar dukushewar rayuwa saboda annobar Korona.

  Wannan na nufin abin zai shafi adadin sama da mutum biliyan 1,500 kenan.

  ILO ta ce wadanda ba su da tsayayyen aiki sun fi kowa shiga hadari - ma'aikatan da ke aiki a kamfanoni masu zaman kansu musamman a bangren abinci da dillacin kayayyaki suma na fuskantar wannan barazana.

  Tuni mutum biliyan biyu wadanda ba su da kwakkwaran aiki suka ga sauyi a albashinsu wanda yayi kasa a duniya da kusan kaso 60 cikin 100, tun watan farko da wannan annoba ta shafi yankinsu.

  Wasu miliyoyin ma'aikata, na zaune babu kudi, babu abinci babu tsaro kuma babu wani kwakkwaran fata a rayuwa. Miliyoyin kasuwanci a duniya na neman durkushewa, In ji shugaban kungiyar Guy Ryder.

  "Ba su ajiye komai ba kuma ba su da wata hanyar samun kudi. Wannan ce matsalar da ma'aikatan duniya ke fuskanta. Idan ba mu taimaka musu ba yanzu, za mu iya rasa su," ya kara da cewa.

  Cutar korona ta shafi mutum sama da miliyan uku a duniya kuma tuni ta kashe kusan mutum 220,000.

 20. Dakarun sojan Mozambique sun kashe dinbin masu ikirarin jihadi

  Dakarun sun ta fama da masu ikirarin jihadin tsawon shekara uku
  Image caption: Dakarun sun ta fama da masu ikirarin jihadin tsawon shekara uku

  Jami'an tsaron Mozambique sun kashe kimanin masu ikirarin jihadi 130 cikin mako uku, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayyana.

  Ministan cikin gida Amad Miquidade ya ce yanzu lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar na karkashin ikon gwamnati.

  Ya ce dakarun kasar za su ci gaba da gudanar da sumame domin tabbatar da an fatattaki duka masu ikirarin, da kuma tarwatsa dukkan sansanoninsu.

  Mayakan da ake kira al-Shabab sun ta kashe mutane da kuma kona kauyuka a arewacin Mozambique sama da shekara uku baya.

  Akalla mutum 900 ne aka kashe kuma an ta samun karuwar hare-hare a baya-bayan nan.

  A makon jiya ne, a karon farko hukumomi a kasar suka ce mayakan da ake fafatawa da su wani bangare ne na kuniyar IS.