Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Da fatan an sha ruwa lafiya, Allah Ya karbi ibadunmu. A nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai-tsaye sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

  Da fatan za ku kasance da mu tare da bibiyarmu aFacebookdaTwitterdaInstagram

 2. Labarai da dumi-dumiKwamishina ya rasu a Sokoto

  Gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da rasuwar kwamishinan filaye da gidaje Surajo Gatawa.

  Ya rasu ne a ranar Lahadi inda aka yi jana'izarsa bayan Sallar Magariba a Sokoto, kamar yadda mai taimakawa Gwamnan jihar kan harakokin watsa labarai Muhammad Bello ya tabbatar wa BBC.

  Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce ya rasu ne bayan gejeruwar rashin lafiya.

  Amma ba a bayyana dalilin rasuwarsa ba a sanarwar.

  Marigayin wanda Allah Ya karbi ransa yana da shekara 63 a duniya, ya taɓa wakiltar Isa da Sabon Birni a majalisar Tarayya tsakanin 1999-2007, sannan ya taɓa riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni bayan ya yi kansila.

  Ya rasu ya bar mata uku da ƴaƴa.

  Cikin kwana biyu jihar Sokoto ta yi rashin manyan mutane, da suka hada da tsohon karamin ministan Lafiya da ƙanin mahaifin gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal.

 3. Cutar korona ta kashe mutum 2,239 a Afrka

  Hukumar daƙile cuta masu yaɗuwa ta Tarayyar Afirka CDC ta ce mutum 61,181 suka kamu da cutar korona a ƙasashe 53 mambobin ƙungiyar.

  Bayanan da aka wallafa a shafin Twitter na Afirka CDC sun bayyana cewa cutar ta kashe mutum 2,234 a ƙasashen Afirka, yayin da kuma mutum 20,932 suka warke daga cikin waɗanda suka kamu da cutar a ƙasashe mambobin ƙungiyar Tarayyar Afirka 53.

  Cutar ta fi yaɗuwa a arewacin Afirka, sai kuma yankin yammacin Afirka inda mutum 17,973 suka kamu

  View more on twitter
 4. 'Yan bindiga ya kashe mutum 20 jihar Tillaberi

  Tillaberi

  Gwamnan Tillaberi a Jamhuriyar Nijar ya ce 'yan bindiga a kan babura sun kai hara-hare inda suka halaka mutum 20.

  Tidjani Ibrahim Katiella ya ce 'yan bindigar sun kaddamar da hare-haren ne a kauyuka uku tare da sace shanu da dama da kuma fasa shaguna.

  Tun daga watan Disambar bara, an kashe sojoji akalla 170 a Tillaberi - jihar da ke makwabtaka da kasar Mali.

  A kwanakin baya ne gwamnatin kasar ta sabunta dokar ta baci a jihar wacce ke karkashin wannan dokar tun a shekara ta 2017.

  A makon da ya gabata ne sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Antinio Guterres ya gargadin cewa kungiyoyin masu jihadi a yankin Sahel na amfani da annobar korona domin kaddamar da hare-haren.

 5. Mutum 12 sun warke daga cutar korona a Borno

  Borno

  Gwamnatin jihar Borno ta ce an sallami mutum 12 daga asibitin koyarwa ta Jami'ar Maiduguri bayan sun warke daga cutar korona.

  Maitaimakin gwamnan jihar Umar Kadafur wanda ke jagorantar yaƙi da cutar korona ne ya sanar da haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

  Sanarwar ta ce tun a jiya aka sallama mutum biyu. Kuma yanzu majinyatan korona 22 ne ke jiran sakamakon gwaji ya fito domin sanin ko sun warke daga cutar.

 6. An gano masu korona da suka tsere a Kaduna

  Gwamnatin Kaduna a arewacin Najeriya ta ce jami'an tsaro sun yi nasara gano mutum biyu masu ɗauke da cutar korona da suka tsere bayan sanar da su sakamakon gwajin da aka yi masu.

  Sanarwar da aka wallafa a shafin gwamnatin Kaduna na Twitter ta ce kwamishinan lafiya na jihar Dr Amina Mohammad Baloni ta tabbatar da cewa yanzu haka suna cibiyar killace masu cutar korona.

  Gwamnatin ta ce tun da aka lalabe mutanen biyu aka rasa ta waya, jami'an tsaro suka bi sawunsu.

  Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi wa mutanen biyu gwajin cutar yayin da suke killace a gidajensu amma da sakamako ya fito cewa suna ɗauke da cutar sai aka neme su aka rasa kuma suka daina daga wayar hukumomi.

 7. Ƙarin mutum 21 sun warke daga cutar korona a Legas

  Gwamnatin jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta ce ƙarin mutum 21 sun warke daga cutar korona

  Gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu ya faɗi a Twitter cewa maza 17 da mata 4 ne suka warke, dukkaninsu ƴan Najeriya an sallame su.

  Yanzu jimillar mutum 469 suka warke daga cutar korona a Legas, a cewar gwamnan

  View more on twitter
 8. Masu cutar korona a Kamaru sun kusa 2,600

  Ministan lafiyar Jamhuriyar Kamaru, Malachie Manaouda ya ce izuwa yau Lahadi, kasar na da mutum 2579 masu dauke da cutar Covid-19.

  A ranar 6 ga watan Maris ne aka samu mutum na farko mai dauke da cutar a Kamaru.

  Daga cikin wannan adadin, mutum 1465 sun warke a yayin da mutum 114 suka rasu.

  A halin yanzu kuma 'yan kasar ta Kamaru su 139 wadanda suka makale a Dubai tun lokacin da kasar ta rufe kan iyakokinta, su samu damar isa gida.

  View more on twitter
 9. Coronavirus: Ƙarin mutum bakwai sun warke a Abuja

  Wasu mutum bakwai da ke jinyar cutar korona a Abuja, babban birnin Najeriya sun warke, kamar yadda ministan birnin Mallam Mohammed Musa Bello ya bayyana.

  Ministan ya ce ya zuwa karfe 10:00 na safiyar Lahadi, mutum 92 aka sallama a Abuja in aka hada da ƙarin bakwai din, bayan gwaji ya nuna ba sa dauke da cutar.

  "Mutanen Abuja, an samu wani labari me daɗi, ina shaida muku cewa an sallami ƙarin mutum bakawai daga cibiyoyin lafiya," in ji ministan, a wani sakon Twitter.

  Hukumar NCDC mai yaki da yaduwar cutuka a Najeriya ta ce mutum 343 aka tabbatar sun kamu da korona a Abuja ya zuwa daren Asabar, inda takwas suka mutu.

  View more on twitter
 10. Cutar korona ta sake ɓulla a Wuhan

  Korona

  Wuhan, garin da aka fara samun ɓarkewar cutar korona a China, ya bayar da rahoton sake ɓullar cutar a karon farko sama da wata ɗaya.

  Wanda ya kamu da cutar a Wuhan yana cikin mutane 14 da hukumar lafiya ta China ta ce sun kamu da cutar bayan sanar da babu sauran mai ɗauke da cutar makwannin da suka gabata.

  Mutumin ɗan shekara 89 ne da haihuwa, an bayyana cewa yana cikin mawuyacin hali bayan gwaji ya tabbatar da yana ɗauke da cutar, kamar yadda kafofin yaɗa labaran China suka ruwaito.

  Mutun 82,901 suka kamu da korona a China, yayin da cutar ta kashe mutum 4,633. Tsauraran matakai da aka ɗauka na hana kulle sun taimaka wajen rage yaɗuwar cutar.

 11. Coronavirus: An samu karin cibiyoyin gwaji a Najeriya

  Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya - NCDC ta bayyana cewa an samu karin cibiyoyin gwajin cutar korona har uku a cikin kasar.

  A yanzu kenan akwai cibiyoyi 23 da ake gwajin covid-19 a fadin kasar.

  Sabbin cibiyoyin su ne a :

  • Asibitin koyarwa na jami'ar Fatakwal
  • Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Ribas da kuma
  • Asibitin koyarwa na jami'ar Benin da ke jihar Edo
  View more on twitter
 12. Tsohon ministan lafiya Dr. Haliru Alhassan ya rasu

  Allah ya yi wa tsohon ministan lafiya na Najeriya Dr. Haliru Alhassan rasuwa ranar Lahadi.

  Wani jika ga marigayin ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar bayan wata gajeriyar jinya.

  Haliru Alhassan, shi ne karamin ministan lafiya a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan a shekarar 2014.

 13. An tura masu karya dokar kulle cibiyar killace masu korona a Rivers

  Gwamnan jihar RIvers a Najeriya, Nyesun Wike ya umarci a kai masu karya dokar hana zirga-zirga cibiyar killace masu cutar korona a jihar.

  Gwamna Wike ya saka dokar hana fita a kananan hukumomin Port Harcourt da Obio/Akpor domin dakile yaduwar cutar korona.

  Bidiyon ya nuna gwamnan yana zagaye a ttituna da kansa, inda ya rika bai wa jami'an tsaro umarnin fitar da mutanen daga motocinsu tare da kai su cibiyoyin killace masu cutar korona.

  View more on twitter
 14. Spaniya ta tabbatar da mutuwar mutum 143 - adadi mafi karanci

  Spaniya ta tabbatar da karin mutum 143 da suka mutu sakamakon cutar korona cikin sa'a 24 da suka gabata, mafi karancin adadi kenan cikin wata biyu.

  Wannan adadi ne mafi karanci tun daga ranar 18 ga watan Maris, kwana biyu bayan saka dokar kulle. Yanzu jumillar adadin ya kama 26,621.

  Firaminista Pedro Sanchez ya fada ranar Asabar cewa kashi 51% na al'ummar kasar za su fara kashi na farko na sassaucin dokar kulle mai mataki hudu a ranar Litiinin.

 15. Wadanda suka kamu da cutar korona sun zarta 200,000 a Rasha

  Rasha ta tabbatar da wasu mutum 11,012 da suka kamu da cutar korona cikin sa'a 24 da suka gabata, jumillar wadanda suka kamu a kasar ya zama 209,688.

  Wasu mutum 88 sun rasa rayukansu sakamakon cutuka masu alaka da cutar ta korona ranar Lahadi, wanda baki dayan adadinsu ya kama 1,915, a cewar hukumomi.

  Masu kamuwa da cutar sun rika zarta 10,000 a kullum tun daga makon da ya gabata. Hukumomi sun ce hakan na faruwa ne saboda yawan gwajin da ake yi.

  Yanzu Rasha ce ta biyar a yawan wadanda suka kamu a fadin duniya bayan Amurka da Italiya da Birtaniya da Spaniya.

 16. Mutum biyu sun tsere a Kaduna bayan sun kamu da korona

  Jami'an tsaro na bin sawun wasu mutum biyu da suka kamu da cutar korona a Jihar Kaduna bayan an neme su an rasa tare da kashe wayoyinsu.

  Gwamnatin jihar ta bayyana cewa an yi wa mutanen biyu gwajin cutar yayin da suke killace a gidajensu amma da sakamako ya fito cewa suna dauke da cutar sai aka neme su aka rasa kuma suka daina daga wayar hukumomi.

  Kwamishinar Lafiya ta Jihar Amina Mohammed-Baloni ta ce "abu ne mai hadari" mutanen da suka kamu da cutar su rika kashe wayoyinsu sannan ta ce wajibi ne su rika kai kansu ga hukuma.

  Sanarwar da gwamnati ta fitar ranar Lahadi ta ce tuni aka mika wa jami'an tsaro bayanan mutanen sannan ta shawarci mazauna jihar da su kai rahoto ga hukumomi da zarar sun samu labarin inda mutanen suke.

  View more on twitter
 17. Dan wasan Brighton ya kamu da cutar korona

  Brighton Albion

  Dan wasan kungiyar Brighton na uku ya kamu da cutar korona.

  Dan wasan wanda ba a bayyana sunansa ba, an yi masa gwaji ranar Asabar kuma yanzu za a killace shi na tsawon kwana 14.

  A baya, wasu 'yan wasan kungiyar biyu sun kamu da cutar.

  'Yan wasan Brighton sun yi ta yin atasaye ba tare da juna ba kuma kulob din ya ce zai kyale su su ci gaba.

  A ranar Litinin kungiyoyin Premier za su gana domin tattauanawa game da shirinsu na ci gaba da gasar da suka kira Project Restart.

 18. Cutar korona ta kashe sama da mutum 2,000 a Afirka

  Kasashen Afirka mambobin kungiyar hadin kan Afirka ta AU guda 53 sun tabbatar samun mutum fiye da 60,000 da suka harbu da annobar cutar korona a kasashensu.

  Bisa alkaluman hukumar CDC Africa - mai yaki da yaduwar cutuka a Afirka - na ranar Lahadi, jumillar mutum 60,657 ne suka kamu a kasashen nahiyar, yayin da 2,223 suka rasa rayukansu, sai kuma 20,792 da suka warke daga annobar cutar.

  Yankin arewacin Afirka ne kan gaba a yawan masu cutar da jumillar mutum 21,536. Kasar Masar wato Egypt ke kan gaba da mutum 8,964 da suka kamu, sai mutum 514 da suka rasu da kuma 2,002 da suka warke.

  Sai kuma kudancin Afirka masu jumilla 10,096. Afirka ta Kudu ke kan gaba da mutum 9,420 da suka kamu, sai kuma 186 da suka mutu da 3,983 da suka warke.

  A yammacin Afirka kuwa, mutum 17,873 cutar ta kama kuma Ghana ce ke kan gaba da mutum 4,263, sai kuma Najeriya da ke biye mata da 4,151.

  View more on twitter
 19. Ma'aikatan lafiya 12 sun kamu da korona a Bauchi

  Kwamishinan Lafiya na Jihar Bauchi Dr Aliyu Maigoro ya ce ma'aikatan lafiya 12 sun harbu da cutar korona a jihar.

  A wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Asabar, kwamishinan ya bayyana cewa shida daga cikinsu suna garin Azare, yayin da sauran shidan suke birnin Bauchi, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

  "Ya zuwa yau [Asabar], muna da ma'aikatan lafiya 12 da suka harbu da Covid-19 a fadin Jihar Bauchi. Shida daga cikinsu na Azare, yayin da sauran suke a nan Bauchi," in ji shi.

  Ya kara da cewa: "Ina tabbatar muku cewa babu wanda ya rasu daga cikin wadannan ma'aiktan lafiya."

  Sannan kwamishinan ya yi magana kan marasa lafiyar da suka tsere daga cibiyar killace masu cutar korona, kuma ya ce suna aiki da makwabtan jihohi domin bin sawunsu.

  "Akwai hadin gwiwa tsakanin jihohi; babu dadewa mun kama wani da ya shigo daga Taraba kuma mun killace shi."

  Ya zuwa daren Asabar, Jihar Bauchi na da wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar korona 161.

 20. Kar ku yarda da labaran karya kan Osinbajo - Laolu

  Mai taiamaka wa Farfesa Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Najeriya, kan harkokin yada labarai ya shawarci 'yan Najeriya da su yi watsi da abin da ya kira "labaran karya" da ake yadawa saboda rashin ganin Osinbajo da Buhari a bainar jama'a.

  Mista Laolu Akande ya wallafa hotonsa tare da Osinbajo a cikin ofis a shafinsa na Instagram, inda ya yi kira ga jama'a da su ci gaba da yin watsi da "masu tayar da zaune tsaye wadanda ke tambayar inda Shugaba Buhari da mataimakinsa suka shiga".

  "Ni da mai gidana kenan a ofis a daren jiya - Juma'a - muna duba abubuwan da suka faru a wannan makon," Akande ya bayyana a karkashin hoton.

  Kazalika, ya bayyana cewa 'yan Najeriya da dama suna ganin shugabannin biyu a talabijin, suna jin su a rediyo sannan suna karanta ayyukansu a jaridu.

  View more on instagram