Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Muna fatan kun ji dadin labarai da rahotannin da muka kwashe tsawon wannan rana muka kamo muku.

  Sai ku tara gobe domin samun karin labarai da rahotanni.

  Kafin nan, za ku iya dubawa kasa don karanta abubuwan da muka wallafa. Sannan za ku iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta.

  Mu kwana lafiya.

 2. Abincin da Buhari ya tura Kano bai lalace ba - Gwamnatin Ganduje

  Gwamnatin jihar Kano da ke Najeriya ta musanta zargin da wasu suke yi cewa ta bar kayan abincin tallafin da gwamnatin tarayya ta aika jihar ruwan sama ya dake su.

  Sanarwar da Kwamishinan watsa labaran jihar, Muhammad Garba, ya aike wa manema labarai ranar Talata ta ce ba gaskiya ba ne zargin da wasu ke yi cewa an bar kayan abincin ya lalace sakamakon dukan ruwan saman.

  "Gwamnatin Kano tana mai yin watsi da rahotannin da wasu masu bakar aniya suke yadawa cewa an bar hatsin da gwamnatin tarayya ta turo Kano mako biyu da suka wuce a matsayin tallafi a filin KASCO inda ruwan sama ya lalata shi," in ji sanarwar.

  Kwamishinan ya kara da cewa tun kafin a kawo tallafin ruwan sama ya dade da sauka a Kano kuma gwamnati ta dauki matakin rufe kayan abincin da tamfol mai hana ruwa shiga domin kada ya lalace.

  A cewarsa, kwamitin da aka dora wa alhakin tattara tallafin cutar korona ya soma shirin rarraba kayan abinci ga talakawa.

  Ganduje da Sadiya
 3. Ɗan sanda 'ya kashe baƙar-fata a Amurka'

  Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka, FBI, ta ce za ta gudanar da bincike kan mutuwar wani bakar-fata a jihar Minnesota bayan wani bidiyo ya nuna yadda dan sanda ya danne wuyansa.

  A cikin bidiyon an ji mutumin, wanda yake da kimanin shekara 40, yana ihu sannan yana ta gaya wa dan sanda da ya danne shi da gwiwar kafarsa cewa "ba na iya numfashi."

  Rundunar 'yan sandan Minneapolis ta ce tana bincike kan laifin.

  Wannan lamari ya tuna wa mutane abin da ya faru da wani bakar-fata mai suna Eric Garner, wanda ya mutu lokacin da aka tsare shi a shekarar 2014.

  An shake wuyan Garner da wani karfe inda ya rika cewa "Ba zan iya yin numfashi ba" kusan sau goma sha biyu.

  Wannan kalami nasa ya zama wani furuci da masu fafutuka suka rika yi a wajen zanga-zangar kyamar cin zarafin da 'yan sanda suke yi wa bakaken-fata a Amurka.

  Rundunar 'yan sandan Minnesota ta amince cewa mutumin ya mutu ne sakamakon danne shi da dan sandan ya yi.

  Dan sandan ya danne wuyan mutumin da gwiwar kafarsa
 4. 'Yan wasan Man Utd Marcus Rashford da Paul Pogba sun shirya komawa tamaula

  'Yan wasan Manchester United biyu Marcus Rashford da Paul Pogba za su kasance cikin wadanda za a zaba domin buga tamaula idan aka komo Gasar Premier, a cewar kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer.

  Rashford da Pogba sun yi doguwar jinya lokacin da aka dakatar da gasar saboda annobar korona a watan Maris.

  Dukkan 'yan wasan sun koma atisaye na rukunin wasu 'yan wasa marasa yawa inda suka hadu da sauran 'yan wasan United a makon jiya.

  Solskjaer ya ce: "Sun ['yan wasan biyu] warke sosai."

  Karanta cikakken labarin a nan:

  Paul Pogba da Marcus Rashford
 5. Amurka ta zargi Rasha da aika jiragen yaki Libya

  Rundunar sojin Amurka ta zargi Rasha da aika jiragen yaki Libya domin goyon bayan 'yan bindigar Rasha da ke abota da Janar Khalifa Haftar.

  Shugaban rundunar sojin Amurka da ke Afirka, Janar Stephen Townsend, ya ce tun da fari sai da jiragen yakin na Rasha suka yi zango a Syria domin sake wa jiragen fenti don su batar da kama kafin ya isa Libya.

  Bai fadi lokacin da jiragen suka isa kasar ba.

  Wannan zargi yana zuwa ne kwana daya bayan gwamnatin Libya wadda Majalisar Dinkin Duniya take mara wa baya ta ce an kwashe daruruwan 'yan yakin sa-kai na kasar Rasha daga fagen yaki da ke kudancin Tripoli.

  Rasha ta sha musanta zargin.

  Rasha ta sha musanta zargin
 6. Za a gwada riga-kafin cutar korona a Kenya

  Wata cibiyar da ke gudanar da bincike a Kenya ta sanar cewa za ta soma gwajin wani sabon riga-kafin cutar korona wanda aka samar a Jami'ar Oxford da ke Ingila a kasar.

  Cibiyar mai suna Kemri-Wellcome trust ta ce za ta nemi ma'aikatan lafiya kimanin 400 domin su amince wajen a yi gwajin riga-kafin riga-kafin a kansu.

  Cibiyar tana so a yi gwajin ne a garin Kilifi da ke kusa da tasoshin jiragen ruwa na kasar don a samar da abin da ta kira “Riga-kafi Daya wanda zai yi wa kowa magani”.

  Riga-kafin mai suna ChAdOx1 nCoV-19, wanda tuni aka gwada shi kan mutum fiye da dubu daya a Birtaniya, yanzu za a gwada shi a Kenya tare da taimakon cibiyar bincike ta kasar, Kenya Medical Research Institute.

  Dole ne ma'aikatan lafiyar sama da 400 su kasance 'yan sama da shekara 18 a duniya kuma wadanda suke aiki a garin na Kilifi.

  Ana ta ce-ce-ku-ce kan gwada riga-kafin cutar korona a kan 'yan Afirka, sai dai masu bincike sun ce za a nemi amincewar hukumomi kafin a gwada riga-kafin.

  Dole ma'aikatan lafiyar su kasance mazauna garin na Kilifi
  Image caption: Dole ma'aikatan lafiyar su kasance mazauna garin na Kilifi
 7. El-Rufai: 'Zan ɗaure iyayen da suka kai 'ya'yansu almajiranci'

  Nasir E-Rufai

  Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa daga yanzu za a riƙa hukunta iyayen da suka kai 'ya'yansu makarantar allo a jihar.

  Gwamnan ya bayyana cewa duk malamin da ya karɓi yara a matsayin almajirai a makarantar allo za a ɗaure shi ko kuma a ci tararsa naira dubu 100 ko 200.

  El-Rufai ya bayyana haka ne ranar Litinin yayin wata ziyara da ya kai wata cibiya da aka killace tare da kula da almajirai kusan 200 da aka mayar da su Kaduna daga Jihar Nassarawa a Kurmin Mashi da ke birnin Kaduna.

  El-Rufai ya koka kan cewa duk almajiran da aka ɗebo daga wasu jihohi 'yan Kaduna ne, yana mai cewa jihar na da alhakin ba su duk wani taimako da suke buƙata domin ci gabansu.

  "Saboda haka za mu ci gaba da karɓar almajirai 'yan Kaduna domin kula da su sannan mu saka su a makarantu na zamani kusa da inda iyayensu ke zaune," in ji El-Rufai.

 8. Ana bikin cika shekara 30 da kafa jam'iyyar SDF a Kamaru

  A yau Talata jam’iyyar adawa ta SDF wadda Ni John Fru Ndi yake jagoranta take cika shekara 30 da kafuwa.

  Wannan ya dace da ranar kafuwar mulkin demokuraɗiyya a Kamaru, abin da ya buɗe kofar kafuwar tarin wasu jam’iyyun siyasa.

  Kodayake hakan ya faru a cikin wani mawuyacin hali bayan an yi ta ɗauki ba daɗi daga ɓangaren gwamnati, wadda ta bai wa jami’an tsaronta umarnin murƙushe duk wani yunkurin bore domin yi wa jam’iyyar RDPC ɗaya tilo kishiya, wadda har yanzu ke tafiyar da mulki a Kamaru.

 9. Buhari na jimamin rasuwar Shugaban Limaman jihar Ogun

  Muhammadu Buhari

  Shugaba Muhammdu Buhari na Najeriya ya jajanta wa iyalan Alhaji Liadi Orunsolu, Shugaban Limaman Jihar Ogun, wanda ya rasu ranar Talata, 26 ga watan Mayu, yana da shekara 98.

  Wata sanarwa da Femi Adesina, mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ta ambato shugaban yana cewa marigayin ya yi rayuwa "mai cike da tsoron Allah kuma mai tsawo" sannan ya yi addu'ar Allah ya ji ƙansa.

  Kazalika Buhari ya buƙaci jama'a da su yi koyi da kyawawan ayyukansa.

 10. Korona ta kashe mutum na farko a Jihar Anambra

  Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano

  Gwamnatin Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutum na farko a jihar sakamakon annobar korona.

  Mamacin mai shekara 66 na cikin sabbin mutum 9 da aka tabbatar sun kamu da cutar.

  Gwamnan jihar, Willie Obiano ne ya sanar da hakan a wani jawabi da ya yi ranar Litinin, inda ya bayyana cewa marigayin bai kai rahoton halin da yake ciki ba ga ma'aikatan lafiya da wuri.

  "Mutanen Anambra, ya kamata a sani cewa mutuwar da muka samu guda ɗaya zuwa yanzu, ɗan shekara 66 ne da bai kai kansa ga ma'aikatan lafiya da wuri ba," in ji Obiano.

  "An kai rahotonsa a makare kuma kafin sakamakon gwajinsa ya nuna yana ɗauke da cutar - sa'a 24 - ya rasu. Akwai yiwuwar a iya shawo kan lamarin da an samu rahoto da wuri."

  Gwamna Willie Obiano ya ce mutum tara aka tabbatar sun kamu da korona a Anambra ya zuwa Litinin.

  View more on twitter
 11. Tsohon soja ya tara dala 19,000 domin yaƙi da korona a Ghana

  Private Joseph Hammond

  Wani tsohon soja ɗan ƙasar Ghana da ya fafata a Yaƙin Duniya na Biyu mai suna Private Joseph Hammond ya tara kusan dala 19,000 (kwatankwacin naira miliyan bakwai) domin tallafa wa yaƙi da annobar korona a ƙasar.

  Private Hammond ya shiga rundunar Royal West African Frontier Force tun yana ɗan shekara 16.

  A matsayinsa na ɗan shekara 95 a yanzu, yana yin tattaki na tsawon mil biyu a kowacce rana na mako ɗaya domin tara kuɗin.

  Tsohon sojan ya ce ya samu ƙwarin gwiwa ne daga Kaftin Sir Tom Moore, wani tsohon sojan Yaƙin Duniyar da ya tara wa Hukumar Inshorar Lafiya ta Birtaniya dala miliyan 35 domin yaƙi da korona.

 12. Ana ci gaba da gwajin riga-kafin korona a kan 'yan Adam

  Riga-kafi

  An fara yin gwajin riga-kafin cutar korona a kan 'yan Adam a karon farko a Yammacin Duniya a yau Talata.

  An fara gwajin riga-kafin wadda aka yi wa laƙabi da NVX-CoV2373 ne a birnin Melbourne na Australia.

  Wani kamfanin Amurka mai suna Novavax ne ya samar da shi kuma za a gwada shi a kan mutum 130, yayin da ake sa ran samun sakamakonsa nan da watan Yuli.

  Akwai riga-kafi sama da 100 da ake yin gwaji a faɗin duniya yanzu haka, kuma kusan dozin sun fara gwaji a kan mutane.

 13. An tara kusan naira tiriliyan huɗu don samar da riga-kafin korona a duniya

  Riga-kafin korona

  Wata gidauniya mai rajin tallafa wa samar da riga-kafin cutar korona ta tara dala biliyan $10.4 - kusan naira tiriliyan huɗu - domin aikin samar da maganin, a cewar shugabar Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU).

  Ursula von der Leyen ta ce tara kuɗin ya nuja yadda duniya ta haɗu wuri guda domin kawo ƙarshen annobar.

  Kiran wanda EU ta ƙaddamar a farkon wannan watan, an yi shi ne domin samar da riga-kafi mai sauƙin kuɗi wadda kuma za ta ishi duniya baki ɗaya.

  View more on twitter
 14. Ranar Lahadi za a buɗe Masallacin Annabi na Madina

  Masallacin Annabi S.A.W.

  Hukumomi a Saudiyya sun bayyana cewa za a buɗe Masallacin Madina na Annabi S.W.A. ranar 8 ga watan Shawwal, wanda ya yi daidai da Lahadi, 31 ga watan Mayu.

  Wannan ya biyo bayan matakin da ƙasar ta ɗauka na sassauta dokar kulle da kuma ɗage dokar hana fita ta awa 24 da ta saka domin hana bukukuwan Idi.

  Sai dai za a sassauta dokar ne a wajen birnin Makkah kaɗai, abin da ke nufin ba za a buɗe Masallacin Ka'aba ba a yanzu, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

  Karanta yadda Saudiyyar za ta cire dokar hana fitar a nan

  View more on facebook
 15. INEC ta fitar da tsarin gudanar da zaɓe yayin annobar korona

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari bayanin kakakin INEC

  Hukumar zaben Najeriya ta fitar da wasu sabbin ka'idojin yadda za a gudanar da zabuka a jihohin Edo da Ondo a cikin yanayin annobar cutar korona.

  Da ma dai hukumar ta ce ba za ta ɗage zaɓukan gwamna na wasu jihohi da kuma na cike gurbi da ta tsara yi ba a bana saboda cutar ta korona amma za ta ɗauki matakan hana bazuwarta.

  A watannin Satumba da Oktoba INEC za ta gudanar da zaɓukan gwamna a jihohin na Edo da Ondo da kuma zaɓukan cike gurbi na 'yan majalisa da dama.

  Kakakin hukumar Malam Aliyu Bello ya ce sun raba matakan gida uku; kafin da bayan da kuma lokacin zaɓen.

  "Kafin zaɓe ana buƙatar mutane su tabbata sun bai wa juna tazara domin kada su yaɗa cutar. Sannan a lokacin zaɓe INEC ta tanadi abin wanke hannu, masu jefa kuri'a za su saka takunkumi," in ji Malam Aliyu.

  "A lokacin tattara sakamako INEC za ta samar da na'urar auna zafin jikin mutum kuma idan aka samu wanda jikinsa ya nuna alamun cutar za a sada shi da hukumomi."

 16. Za a buɗe masallatai a Saudiyya, ban da na Harami

  Saudiyya

  Saudiya za ta soma sassauta dokar kulle daga ranar 21 ga watan Yuni sannan ta cire dokar hana fita kwata-kwata a fadin kasar, bayan kusan wata biyu a yaƙin da take yi da annobar korona.

  Za a ɗage dokar ne a ko'ina ban da birnin Makkah.

  Za a buɗe dukanin masallatai da ke wajen Makkah daga ranar 31 ga watan Mayu, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

  Karanta cikakken labarin a nan

 17. A tabbata an zubar da makamai a Afirka yayin annobar korona – Buhari

  Muhammadu Buhari

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin Afirka da su tabbata an cimma kudirin da aka saka a gaba na "watsar da makamai" a matsayin maudu'in da aka zaɓa na bikin Ranar Afirka ta 2020.

  Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta AU ce ke shirya bikin Ranar Afirka da ake kira Africa Day duk shekara a ranar 25 ga watan Mayu - wannan karon da haɗin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) aka shirya shi.

  Taken bikin na wannan shekara shi ne: "Zubar da makamai yayin annobar korona" - 'Silencing the Guns in the context of the COVID-19'' a Turance.

  A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban, Garba Shehu ya fitar ranar Litinin, Buhari ya ja kunnen 'yan Afirka cewa "zaman lafiya, tsaro da kuma haɗin kai, su ne ƙashin bayan ci gaba a Afirka".

  View more on twitter
 18. Mutum fiye da 8,000 sun kamu da korona a Najeriya

  Coronavirus a Najeriya

  Sabbin alkaluman da hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta fitar a daren Litinin sun nuna cewa wadanda suka kamu da cutar korona sun haura dubu takwas a Najeriya.

  Alkaluman da ta fitar da misalin 12 saura sun nuna cewa mutum 229 sun sake kamuwa, hakan ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar 8,068.

  Haka kuma hukumar ta ce wadanda suka mutu sun kai 233 a fadin kasar.

  Har yanzu dai Jihar Legas ke kan gaba an samu karin mutum 90 da suka harbu, sai Katsina da ke mataki na biyu da mutum 27.

  Jihar Imo na da mutum 26 sabbin kamu, sai Kano da alkaluma suka nuna an sake samun mutum 23 dauke da cutar.

  Birnin Tarayya Abuja na da mutum 14, Plateau 12, Ogun 9, sai Delta 7.

 19. Kun taɓa ganin yadda Fulani ke shagalin bikinsu kuwa?

  Video content

  Video caption: Latsa hoton da ke sama domin ganin yadda ake kai amarya a bikin Fulani
 20. WHO ta dakatar da gwajin Hydrocholoroquine a matsayin maganin korona

  Hydrocholoroquine

  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta dakatar da gwajin Hydrocholoroquine a matsayin maganin annobar cutar korona.

  WHO ta yanke wannan hukunci ne bayan bincike ya nuna cewa maganin na iya haddasa ciwon zuciya da sanadin rayukan mutane da suka harbu da cutar.

  Ana amfani da Hydrochloroquine wajen maganin Malaria da ciwon gaɓoɓi, sai dai Shugaban Amurka Trump ya ce yana kwankwaɗar maganin a matsayin riga-kafin Korona.

  Shi ma Shugaba Jair Bolsonaro na Barzil ya bayar da umarni a yi amfani da maganin kan marasa lafiya.

  Mista Bolsonaro ya dage kan cewa ba zai sauya matsayarsa ba duk kuwa da wannan sanarwa ta WHO.