Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  Ku kasance da mu zuwa gobe a shafinmu bbchausa.com inda za mu ci gaba da kawo rahotanni da labarai da dumi duminsu.

  Sai gobe.

 2. Sojoji sun fatattaki ƴan fashi kan iyakar Katsina da Kaduna

  Rundunar sojin Najeriya ta ce jami'anta sun fatattaki ƴan fashi a kan iyakar Katsina da Kaduna a ranar Lahadi.

  Rundunar tsaron ta ce rundunar Operation Accord da ke yaƙi da ƴan fashin tare da hana su walwala tsakanin jihohi ne ta fafattake su inda ta kashe biyu sauran kuma suka gudu da rauni a jikinsu.

  Sanarwar ta ce an kai harin ne a Tabani da Tashan Bawa da ke kan iyaka tsakanin ƙaramar hukumar Sabuwa a Katsina da kuma Kuyello cikin yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna.

  Sannan sojojin sun samu makamai da suka hada da bindiga AK47 da wayoyin salula biyu.

  View more on twitter
 3. 'Boko Haram ta kashe sojojin Najeriya 6 a Borno'

  Rahotanni daga jihar Borno a yankin arewa maso gabashi sun ce an kashe sojojin Najeriya guda shida a musayar wuta da mayaƙan Boko Haram.

  Kamfanin Dillacin Labaran Faransa AFP, ya ce wata majiyar soji ta ce mayaƙan ISWAP ne suka abka wa sansanin sojojin a Auno da ke kusa da garin Maiduguri inda suka kashe sojoji shida a harin da mayakan suka kai a ranar Asabar da yamma.

  Majiyar ta ce an shafe tsawon sa'a biyu ana musayar wuta tsakanin mayaƙan da kuma sojoji, wanda ya tilastawa sojojin ficewa daga sansanin. Kuma Mayaƙan sun kwashi makamai da bindigogi tare da kone gine-gine.

  Kuma ta ce akwai sojoji 45 da ba a gani ba, waɗanda ake tunanin sun tsere lokacin da aka kawo harin ba su dawo ba.

  Sojojin Najeriya da ke fada da Boko Haram
 4. Malamin Coci ya kaddamar da maganinsa na korona a Kamaru

  Maganin Samuel Kleda na Korona

  Aarchbishop na Douala a Jamhuriyyar Kamaru ya kaddamar da maganinsa da ya yi ikirarin cewa yana maganin cutar korona.

  Shafin ActuCameroun ya ce Monsignor Samuel Kleda babban malamin mabiya addinin Kirista ne a Kamaru ya raɗa wa magungunansa da ya ce suna maganin korona sunan Elixir Covid da kuma Adsak Covid.

  Ya kuma yi ikirarin warkar da kusan mutum 3,000 masu dauke da cutar korona da magungunansa da ya yi amfani da wani ganyen itacen da ake kira "Mafura" a Kamaru.

  A cewar Jaridar an gudanar da bikin kaddamar da maganin ne a ranar Asabar a birnin Douala.

  Sannan yana bayar da maganin ne kyauta a mujami'un ɗarikarsa a biranen Yaounde da Garoua da Bertoua da Buea da Bafoussam da Bamenda.

  Bishop Kleda ya ce yana sauraren hukumomin lafiya a Kamaru ya ji abin da za su ce bayan sun dauki samfurin maganinsa domin tabbatar da ingancinsa.

  Hukumar Lafiya ta duniya dai ta yi gargadi kan amfani da maganin da ba ta tabbatar da ingancinsa ba, yayin da har yanzu ake binciken maganin da zai warkar da cutar korona.

 5. Hissene Habre zai koma gidan yari bayan wata biyu a gida

  Nan da lokaci kaɗan za a mayar da tsohon shugaban Chadi Hissene Habre gidan yari a Senegal bayan shafe tsawon wata biyu ana tsare da shi a gidansa don gudun kada ya kamu da cutar korona.

  Habre mai shekara 70, an daure shi ne a 2016 kan laifukan cin zarafi da ya aikata lokacin da yana kan karagar mulki. Kusan mutum 40,000 aka kiyasta cewa an kashe karkashin mulkinsa a wauraren 1980.

  Daga cikin wadanda ya kulle zamaninsa sun dadi da suka ji labarin cewa zai koma gidan yari. Daya daga cikinsu ya ce Habre bai damu da ko fursuna ya mutu ba a gidan yari

  Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre
 6. Joe Biden ya fara samun goyon bayan manyan ƴan Republican

  Tsohon sakataren harakokin wajen Amurka Colin Powell, ya ce ɗan takarar jam'iyyar Democrats da ke hamayya Joe Biden zai zaba a zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.

  Shi ne mutum na farko daga cikin manyan jiga-jigan jam'iyyar Republican da ya ce zai marawa babban mai hamayya da Trump baya.

  A yayin zantawarsa da CNN, Mista Powell ya ce Trump ya kaucewa kundin tsarin mulki.

  Ya ce ba zai taba goyon bayan shi ba.

  Trump ya mayar da martani a Twitter inda ya kira Mista Powell a matsayin mai cin amana, wanda ya ce ya jefa Amurka cikin mummunan yaki a Gabas Ta tsakiya.

  View more on twitter
 7. An buɗe coci-coci a Abuja ranar Lahadi

  Coci-coci daban-daban sun buɗe a yau Lahadi a Abuja baban birnin Najeriya bayan shafe sama da watanni biyu a rufe.

  An rufe coci-coci a ƙasar ne a yunƙurin daƙile cutar korona a ƙasar.

  Wasu daga cikin masu shiga cocin na wanke hannuwansu da sabulu kafin su shiga.

  Kuma akasari jama'ar da suka halarci cocin na bayar da tazara a tsakaninsu.

  ..
  ..
  ..
  ...
  Image caption: Usher dey check worshipper temperature before she enta church
 8. Limamai na fargaba kan buɗe masallatai a Birtaniya

  Shugaban limamai a Birtaniya ya shawarci masallatai kada su buɗe duk da shirin gwamnati na buɗe wuraren ibada a kasar.

  Ana sa ran gwamnati za ta ba masallatai da coci coci a Ingila damar budewa domin gudanar da ibada na dan lokaci, ba tare da dawo da harakokin ibada kamar yadda aka saba ba.

  Da yake cewa masallatai wurin taruwar jama'a ne domin sallar jam'i, shugabannin musulmi sun yi gargadi kan bude masallatan.

  Imam Qari Asim, shugaban kula da masallatai da limamai ya ce bude masallatan zai ."haifar da kalubale mai girma."

  Ya ce musulmi na iya gudanar da sallolinsu a gida, amma masallatai an yi su ne domin sallar jam'i.

  kungiyar Limamai a Birtaniya
 9. Yawan masu korona a Saudiyya ya haura 100,000

  Yawan masu cutar korona a Saudiyya ya haura 100,000 a yau Lahadi bayan ma'aikatar lafiya ta ƙasar ta bayyana cewa an samu sabbin mutum 3,045 da suka kamu da cutar a ranar Lahadi.

  A yau dai, jumullar waɗanda suka kamu da cutar a Saudiyya sun kai 101,941.

  A yau Lahadi ne karo na farko da yawan masu kamuwa da cutar a kullum a ƙasar suka haura 3,000.

  Hukumomi a ƙasar sun bayyana cewa yawan waɗanda suka mutu sakamakon cutar a ƙasar shi ne 712.

  View more on twitter
 10. Zanga-zangar ƙyamar wariyar launin fata ta bazu a Turai

  Ana ci gaba da zanga-zanga a Turai karkashin tutar fafutika da ake kira Black Lives Matter, kan nuna adawa da kisan George Floyd da ƴan sanda suka yi a Minneapolis watan da ya gabata.

  Masu zanga-zangar kyamar wariyar launin fata

  A Madrid, dubban mutane ne suka fito zanga-zangar suna ɗaga kwalayen da ke ɗauke da bayanan adawa da nuna wariya. Sun sanya takunkumi amma tare da yin watsi da bayar da tazara.

  Masu zanga-zangar kyamar wariyar launin fata
  Masu zanga-zangar kyamar wariyar launin fata

  Ana sa ran ci gaba da zanga-zangar a Landan da Copenhagen da kuma Brussels

  A biranen Amurka kuma an ci gaba da gudanar da zanga-zangar a biranen Portland da Seattle, yayin da aka samu arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma 'yan sanda bayan gudanar da zanga-zangar cikin lumana a mafi yawancin biranen Amurka.

  Masu zanga-zangar kyamar wariyar launin fata
  Masu zanga-zangar kyamar wariyar launin fata
 11. China ta musanta zargin da Amurka ke yi kan korona

  China ta musanta zargin cewa ta boye bayanai kan cutar korona, tana mai cewa ta sanar da Amurka tun farkon cutar a watan Janairu kafin ta zama annoba a duniya.

  China ta mayar da martanin ne a wata sanarwa da ta fitar tana kare kanta kan zargin Amurka.

  China ta fuskanci suka daga gwamnatin Trump inda ya shugaban ya zargi China da boye bayanai kan cutar korona.

  Amma a martanin da ta mayar, China ta ce ba abin da ta boye. Sai dai babu inda ta fadi likitocin Wuhan da aka yi wa gargadi su yi gum da bakinsu kan fargabar da suka nuna game da cutar tun a farkon bullarta.

 12. Sojojin Najeriya sun ce sun ƙwato makamai a Katsina da Zamfara

  A yunkurin kawo zaman lafiya a jihohin Katsina da Zamfara, rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe wasu ɓarayi uku tare da kama huɗu inda kuma suka ƙwato wasu makamai a hannunsu a ƙauyukan Katsina da Zamfara.

  A wata sanarwa da hedikwatar tsaron ƙasar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa sojojin sun samu nasarar kwato babur ƙirar Bajaj a Mararrabar Maigora a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina da ke iyaka da Zamfara.

  Hedikwatar tsaron ta ce cikin abubuwan da sojojin suka ƙwato daga wurin ɓarayin sun haɗa da harsasai 496 da bindigogi bakwai da wayoyin sadarwa uku da wasu babura biyu.

  Ko a jiya Asabar sai da sojojin suka bayyana cewa sun kashe 'yan bindiga da ɓarayin shanu 70 a dajin Kachia da ke jihar Kaduna.

  v
  v
  View more on twitter
  v
 13. Real Madrid ta bayar da euro 80m don sayo Havertz, Everton za ta ɗauko Rabiot

  ..

  Real Madridta mika euro 80m domin sayo dan wasanBayer LeverkusenKai Havertz kuma za ta kyale dan wasan na Jamus mai shekara 20 ya ci gaba da zama a kungiyarsa ta yanzu zuwa kakar wasa ta baɗi kafin ya koma Bernabeu.(ESPN via Bild)

  Chelseaza ta yi maraba da kungiyoyin da ke son daukar 'yan wasanta da dama bayan isar dan wasan Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 27, dagaAjaxda kuma dan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 24, dagaRB Leipziga bazarar nan.(Daily Star on Sunday)

  Ku latsa nan don karanta cikakken labarin.

 14. 'Talauci zai sa mutane su fara rayuwa ƙasa da naira 500 a rana'

  ..

  Shugaban Bankin Duniya David Malpass, ya bayyana korona a matsayin naƙasau ga tattalin arziƙin duniya inda ya ce tattalin arziƙin zai iya shafe shekaru 10 kafin ya farfaɗo.

  Ko a watan da ya gabata, sai da shugaban ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar mutum miliyan 60 za su iya faɗawa cikin matsanancin talauci sakamakon annobar korona inda ya ce mutane za su fara rayuwa ƙasa da fam 1.55 a rana.

  A wata hira da BBC a jiya a Asabar, ya bayyana cewa tsananin talauci a yanzu zai iya saka wasu su rinƙa rayuwa a ƙasa da fam ɗaya a duk rana, kimanin ƙasa da naira 500 kenan.

 15. Sanarwa

  Ku kasance tare da mu da karfe biyu na ranar yau Lahadi (02:00pm) 07/06/2020, za mu tattauna kai-tsaye a shafinmu na Facebook tare da Honarabul Gudaji Kazaure. Ku aiko mana da tambayoyinku.

  .
 16. Labarai da dumi-dumiYawan mutanen da korona ta kashe ya haura 400,000

  .

  Jumullar mutanen da cutar korona ta kashe a faɗin duniya sun wuce 400,000 a halin yanzu.

  Kamar yadda ƙididdigar jami'ar Johns Hopkins ta wallafa a shafinta, ta ce sama da mutum miliyan 6.9 ne suka kamu da cutar tun bayan ɓullarta a garin Wuhan da ke China.

  Amurka ce kan gaba a yawan masu ɗauke da cutar da mutum 1,920,061. Sai kuma ƙasar Brazil ce ta biyu da mutum 672,846, sa'annan kuma Rasha da mutum 467,073.

  Amurkar dai ce kan gaba a yawan mace-mace da mutum 109,802.

 17. Jumullar mutum 337 suka kamu da korona a Kaduna

  Gwamnatin Kaduna da ke Najeriya ta ce ya zuwa safiyar Lahadi, 7 ga watan Yunin 2020, mutum 337 ne suka kamu da cutar korona tun lokacin da cutar ta bulla a jihar a watan Maris.

  Gwamnatin ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter.

  Ta kara da cewa mutum 205 sun warke kuma an sallame su, don haka yanzu mutum 122 ne suke ci gaba da fama da cutar, ko da yake cutar ta yi ajalin mutum 10. A cewarta, an yi wa jumullar mutum 2,274 gwajin cutar ta korona a jihar.

  View more on twitter
 18. Wariyar launin fata annoba ce – Anthony Joshua

  .

  Zakaran damben Boksin na duniya ajin masu nauyi, Anthony Joshua ya bayyana wariyar launin fata a matasyin "annoba".

  Ya bayyana hakan ne a wata zanga-zanga da ake gudanarwa ta "Black Lives Matter" wadda ke nufin rayuwar baƙar fata na da muhimmanci.

  Ya bayyana cewa wariyar launin fata cuta ce kuma a halin yanzu sun ayyana ta a matsayin annoba.

  Kalaman na Anthony sun biyo bayan zanga-zanga daban-daban da ake gudanarwa a faɗin duniya kan kisan wani baƙar fata ɗan Amurka wato George Floyd.

  Floyd ya mutu ne bayan 'yan sanda sun kama shi inda ɗaya daga cikinsu ya murƙushe shi a ƙasa na mintuna tara har ya mutu.

 19. Shirin Gane Mani Hanya 06-06-2020

  Video content

  Video caption: Shirin Gane Mani Hanya 06-06-2020

  Tattaunawa da sakataren gudanarwa na hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya wato Nigeria Shippers Council a cikin shirin gane mani hanya. Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren tattaunawar.