Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Rahotannin sun zo ƙarshe a wannan shafi

  Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarshen rahotannin kai-tsaye.

  Mu haɗu da ku gobe idan Allah ya kai mu da rai da lafiya.

 2. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe 'yan Boko Haram da yawa, sun ceto wata mace

  Nigerian Army

  Dakarun rundunar Operation Lafiya Dole ta sojojin Najeriya ta kashe 'yan ƙungiyar Boko Haram da dama a Kwatara da ke kusa da Mandara na Jihar Borno, a cewar wata sanarwa da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar a daren Talata.

  Sanarawar ta ce dakarun Bataliya ta 192 ne suka kai samame ranar Litinin, inda suka yi nasarar kashe mayaƙan da ba ta faɗi adadinsu ba sannan wasu suka tsere da raunuka.

  Ta ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram biyu sun rasa rayukansu a wani harin da aka kai musu a Darel Jamel da ke kan Titin Miyanti tare da ceto wata mace guda ɗaya a hannunsu.

  Yayin harin, sojojin sun kwato babur biyu da buhu cike da takalman roba 121 da kuma kuɗi naira 29,500.

  Har wa yau, wani mayaƙin ƙungiyar mai suna Mustapha Kori ya miƙa wuya ga sojoiji a garin Gamboru ranar Litinin, a cewar rundunar sojan Najeriya.

  Shugaban rundunar sojan ƙasa ta ƙsar Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya gana da Shugaba Buhari ranar Litinin, inda ya yi masa bayani game da ayyukan rundunar a yankin arewa maso yamma.

  Fiye da wata biyu kenan da Buratai ya koma yankin da zama domin jagorantar yaƙi da ƙungiyoyi masu ikirarin jihadi a jihohin da abin ya fi ƙamari - Borno da Yobe da Adamawa.

 3. Shugabannin Afirka na jimamin rasuwar shugaban Burundi

  Buhari

  Shugaba Mhammadu Buhari na Najeriya ya miƙa ta'aziyyarsa ga gwamnati da kuma al'ummar ƙasar Burundi bisa rasuwar Shugaban Ƙasa Pierre Nkurunziza a ranar Litinin.

  Buhari ya siffanta marigayin da "ɗan kishin ƙasa wanda ya jagoranci ƙasarsa a lokaci maras daɗi" da fasaharsa da hangen nesa.

  "A irin wannan yanayi na alhini, gwamnati da 'yan Najeriya da kuma ni kaina muna miƙa ta'aziyyarmu ga gwamnati da mutanen Burundi," in ji Buhari a wata sanarwa da hadiminsa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar a daren Talata.

  "Muna addu'o'in Allah ya bai wa iayalansa haƙurin jure rashinsa."

  Fadar gwamnatin Burundi ta ce Shugaba Pierre Nkurunziza ya rasu ne ranar Litinin sakamakon bugun zuciya bayan ya shafe shekara 15 a kan mulki.

  Shi ma Shugaban Nijar Issoufou Mahamadou ya miƙa tasa ta'aziyyar ga iyalan Nkurunziza da al'ummar Burundi a shafinsa na Twitter.

 4. An buɗe zirga-zirga tsakanin Wuhan zuwa Beijing a China

  Wuhan zuwa Beijing

  Zirga-zairga jiragen sama daga birnin Wuhan zuwa Beijing, babban birnin China, ta ci gaba bayan ƙasar ta sassauta dokar ta-ɓaci kan harkar lafiya a ƙasar.

  A cewar jaridar China Daily, tafiye-tafiye tsakanin biranen biyu sun ci gaba kuma yanzu ba a buƙatar matafiyan su killace kansu na tsawon kwana 14.

  A birnin Wuhan cutar korona ta fara ɓulla kuma kafin annobar korona, filin jirgin sama na Wuhan ya kasance wata mahaɗa tsakanin gabashi da yammacin China.

  Yayin annobar kuwa, Wuhan ya kasance cikin tsauraran dokokin kulle na tsawon kwana 76. Ayyukan agajin gaggawa ne kaɗai akae bari su shiga ko fita daga birnin.

 5. Za a binne George Floyd

  George Floyd

  Yanzu haka ana gudanar da jana'izar baƙar fatar nan - George Floyd - a Houston, Texas, wanda mutuwarsa a hannun 'yan sanda ta jawo zanga-zanga a faɗin duniya.

  Za a ɗauki gawarsa ne daga wata coci da aka ajiye domin mutane su samu ganinta ranar Litinin, sannan a binne shi kusa da mahaifiyarsa.

  Mista Floyd ya mutu a Minneapolis da ke Amurka a watan da ya gabata bayan wani ɗan sanda farar fata ya maƙure masa wuya da gwiwarsa na tsawon minti tara.

  "Duk sanda aka yi wa George Floyd adalci lokacin ne za mu samu adalci a tsakanin ƙabilun Amurka," in ji ɗan takarar jam'iyyar Democrat Joe Biden a wurin jana'izar.

 6. Matasa da dama sun jikkata a wurin jarrabawar neman aiki a Malawi

  Tasawira

  Hukumomin lafiya a garin Mzuzu na ƙsar Malawi sun ce mutum 158 sun ji rauni bayan wani turmutsutsi da aka yi sakamakon taruwar mutane akasarinsu matasa a wurin jarrabawar ɗaukar aikin gwamnati.

  Ma'aikatar lafiya ta sanar da cewa za ta ɗauki ɗaruruwan ma'aikatan lafiya domnin su shiga karkara a matsayin masu wayar da kai game da kiwon lafiya.

  An nemi masu neman aikin da su halarci tattaunawar neman aikin a wurare daban-daban na ƙasar.

 7. Kakakin majalisar Burundi zai zama shugaban rikon kwarya

  Ana sa ran kakakin majalisar Burundi Pascal Nyabenda zai karbi shugabancin kasar na rikon kwarya, sakamakon mutuwar shugaban kasar Pierre Nkurunziza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

  A wani sakon Twitter wanda masu adawa da shugabancin Mista Nkurinziza suka wallafa, sun saka wata makala da ke nuna yadda ake cike gurbin da shugaban kasa ya bari.

  View more on twitter
 8. Labarai da dumi-dumiEl-Rufai ya sassauta dokar hana fita a Kaduna

  Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya sassauta dokar hana tafiye-tafiye a jihar amma babu zirga-zirga daga ƙarfe 8:00 na dare zuwa 5:00 na asuba.

  A jawabin da gwamnan ya yi ta kafafen yaɗa labarai ranar Talata, sassaucin zai fara aiki daga Laraba 10 ga watan Yuni.

  Gwamna El-Rufai ya ce wuraren sana'a za su iya buɗewa idan sun samar da na'urar auna zafin jikin mutum da man wanke hannu na sanitizer da kuma yin nesa-nesa da juna.

  Ya ƙara da cewa sa'o'in aiki za su riƙa farawa daga 9:00 na safe zuwa 3:00 na rana.

  View more on twitter
 9. An tumɓuke gunkin wani sarki a Belgium da aka kashe miliyoyin 'yan Afirka a ƙarƙashin mulkinsa

  An tumɓuke gunkin wani sarki a ƙasar Belgium, wanda a ƙarƙashin mulkinsa aka kashe miliyoyin mutane a ƙasar DR Congo, bayan zanga-zangar Allah-wadai da wariyar launin fata a birnin Antwerp.

  Tun a jiya Litinin masu zanga-zangar suka ɓata fuskar gunkin Sarki Leopold II.

  Da ma dai masu rajin kare haƙƙi sun sha kiraye-kirayen a cire gunkin sarkin.

  Wani ɗan jarida da ke zaune a Belgium ya wallafa bidiyon lokacin da mahukunta suke tsige gunkin daga gurbinsa.

  View more on twitter
 10. Sanata Orji Kalu ya koma bakin aiki a majalisa

  Sanata Orji Uzor Kalu

  Sanata Orji Uzor Kalu na jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ya koma bakin aiki a yau Talata bayan an sake shi daga Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

  Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito Kalu, wanda ke wakiltar mazaɓar Abia ta Arewa, yana cin alwashin samar wa da al'ummarsa abubuwan alkairi lokacin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan isarsa harabar majalisar.

  Ɗan majalisar wanda tsohon gwamnan Jihar Abia ne, ya ce abin da ke gabansa yanzu shi ne cike gurbin abin da bai samu ya yi ba a wata shida da ya shafe ba ya majalisar.

  An yanke wa Orji Kalu hukuncin shekara 12 a gidan yari sakamakon samunsa da laifin almundahanar kuɗi da suka kai naira biliyan 7.65 da wata Babbar Kotun Tarayya ta yi ranar 5 ga watan Disamban 2019.

  Sai dai wata tawagar alƙalai a Kotun Ƙoli ta yi watsi da hukuncin bisa dalilin cewa Mai Shari'a Mohammed Idris, wanda ya yanke hukuncin, ba shi da hurumin yin hakan kuma ta yi umarni da a sake shi.

  Ranar Laraba da ta gabata ne aka saki sanatan daga gidan yari.

 11. Adam Lallana ya tsawaita zamansa a Liverpool

  Adam Lallana

  Adam Lallana ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Liverpool zuwa karshen kakar bana.

  Dan kwallon tawagar Ingila mai shekara 32 zai bar Liverpool a karshen watan Yuni a lokacin da kwantiraginsa ya cika.

  Ranar 17 ga watan Yuni za a ci gaba da gasar Premier ta 2019-20, bayan kwana 100 da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

 12. Firaministan Habasha ya ci alwashin kammala madatsar ruwa daga Kogin Nilu

  Abiy Ahmed

  Firanministan Habasha Abiy Ahmed ya ce babu gudu babu ja da baya kan shirin gina sabuwar madatsar ruwa da yake yi daga Kogin Nilu, duk da nuna rashin amincewa daga ƙasashen Masar da Sudan.

  Mista Abiy ya ce tuni shirin Grand Renaissance Dam ya lakume dala biliyan shida saboda tsaikon da tattaunawa da wadannan kasashe ta haifar.

  Amma shugaban ya ce ya yanke shawarar ci gaba da aikin dam din a daminar bana.

  A yau Talata ne ya kamata kasashen su ci gaba da tattaunawa kan batun.

  Damuwar da ƙsashen Masar da Sudan ke nunawa ita ce; akwai yiwuwar za su iya fuskantar karancin ruwa matsawar Habasha ta gina sabon dam daga kogin na Nilu.

  A watan Maris ne Habasha ta fice daga shirin shiga tsakani da Amurka ke yi bayan zargin nuna mata bambanci.

 13. Labarai da dumi-dumiShugaban Burundi, Pierre Nkurunziza ya rasu

  Allah ya yi wa shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza, rasuwa ranar Litinin.

  Fadar gwamnatin ƙasar ce ta sanar da rasuwar shugaban a shafinta na Twitter a yau Talata, inda ta ce ya rasu ne sakamakon bugun zuciya.

  An kai Nkurunziza mai shekara 55 asibiitn Karusi a daren Asabar bayan ya sha halartar wani filin wasa a kusa da gidansa.

  Ku karanta karin bayani a nan.

 14. Mutum fiye da 3,000 sun kamu da korona a Saudiyya cikin kwana ɗaya

  Saudiyya

  Saudiyya ta sanar da samun mutum 3,288 da suka harbu da cutar korona cikin sa'a 24 da suka gabata.

  Yanzu jumillar waɗanda suka harbu da cutar a Saudiyya sun kai 108,571, a cewar wata sanarwa daga ma'aikatar lafiya.

  Kazalika ma'aikatar ta ce wasu mutum 37 sun mutu sakamakon annobar, inda yanzu jumillar adadin ya zama 783.

  A kwanan nan, Saudiyya ta fuskanci hauhawar adadin masu kamuwa da cutar a kullum, inda aka rƙa samun mutum fiye da 3,000 a kwana huɗu a jere.

  A gefe guda kuma, mutum 1,815 sun warke kuma yawansu jumilla yanzu ya kai 76,339 a ƙasar zuwa yanzu.

 15. An rufe wata firamare bayan ɗalibi ya kamu da korona a Ingila

  Makaranta a Ingila

  An rufe wata makarantar firamare a yankin The New Forest na Ingila bayan wani ɗalibi ya kamu da cutar korona.

  Makarantar mai suna Pennington Infant School ta ce an sanar da ma'aikata cewa wani yaro ya kamu da cutar a ƙarshen makon da ya gabata.

  Mataimakiyar shugaban makarantar, Amy Wake ta ce an ɗauki matakin rufe makarantar ne "saboda ko-ta-kwana".

  An killace yaron tare da 'yan uwansa sannan an faɗa wa sauran yaran ajinsu da su killace kansu.

 16. Iran ta yanke hukuncin kisa kan 'wanda ya taimaka wa Amurka kashe Soleimani'

  Qassem Soleimani

  Iran ta sanar da yanke hukuncin kisa kan wani mutum da ta ce ya taimaka wa Amurka da Isra'ila da bayanai da suka kai ga kashe babban kwamandanta da jirgi marar matuki a watan Janairu.

  Mai magana da yawun ma'aikatar shari'a Gholamhossein Esmaili ya ce an kama Mahmoud Mousavi da laifin leken asiri kan rundunar sojin kasar, da kuma samar da bayanai kan marigayi Janar Qasem Soleimani.

  Kakakin ma'aikatar ya ce tuni kotun koli ta tabbatar da hukuncin, kuma nan ba da jimawa ba ne za a aiwatar da hukuncin.

  A cewar wakilin BBC ''Kisan Janar Qasem Soleimani ya kara ta'azzara rikicin da dama ke akwai tsakanin Iran da Amurka, kuma ba don barkewar annobar Korona ba da ya dauki hankalin duniya tuni da watakila yaki ya barke tsakanin kasashen biyu.''

 17. 'Yan Democrat sun yafa atamfa don girmama George Floyd

  Shugabar majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi da wasu 'yan majalisar na jam'iyyar Democrat sun sanya atamfa 'yar Ghana da ake kira kente a ranar Litinin don girmama George Floyd, wanda 'yan sanda suka kashe a watan da ya gabata a Minneapolis.

  Sun durkusa tsawon minti takwas da dakika 46 - tsawon lokacin da dan sanda farar fata ya sanya gwaiwarsa a kan wuyan Mista Floyd - sannan daga bisani suka yi wa 'yan jarida jawabi kan wani kudurin doka na kawo sauye-sauye fannin aikin 'yan sanda, a yayin da suka yafa da atamfar kente a kan kafadarsu

  View more on twitter

  Mutuwar Mr Floyd ta jawo zanga-zanga a fadin duniya da kuma yin kira da a kawo sauyi ga aikin 'yan sanda.

  Kente wata atamfa ce ta 'yan Ghana kuma wasu AMurkawa bakaken fata na yawan amfani da ita ko a Amurka.

  Wata kungiyar masu fafutukar kare bakaken fata ce ta bai wa Ms Pelosi kayan, ita kuma ta mika su ga sauran 'yan majalisar, kamar yadda Jaridar Washington Post ta ce.

  Matakin saka atamfar ya jawo bayyana ra'ayoyi mabambanta a shafukan sada zumunta.

 18. Koriya Ta Arewa ta katse hanyoyin sadarwa tsakanin ta da Koriya Ta Kudu

  Koriya Ta Arewa ta ce za ta katse duk layukan sadarwa na hukuma da Koriya Ta Kudu ciki har da wani layin kiran gaggawa tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.

  Mahukuntan birnin Pyongyang sun ce wannan ne na farko a jerin matakan da za su ɗauka kan gwamnatin birnin Seoul da suka bayyana da "abokiyar gaba".

  Umarnin ya zo ne daga Kim Yo-Jong 'yar uwar Shugaba Kim Jong Un.

  Matakin ga alama wani martani ne ga wasu takardun nuna adawa da gwamnati, da 'yan Koriya ta Arewa da suka sauya sheƙa bayan sun tsere zuwa kudanci suka riƙa jefawa ƙasar ta sama.

  Mai aikowa BBC rahotanni daga birnin Seoul na cewa sanarwa na iya zama wata dabarar tayar da rikici daga Koriya ta Arewa da fatan amfani da ita a matsayin madogara a tattaunawar da za su iya yi nan gaba.

  Korea
 19. Ambaliyar ruwa ta yi ɓarna a Ghana

  Ambaliya

  Mutum daya ya mutu sakamakon ambaliyar da aka yi a galibin Accra, babban birnin Ghana saboda mamakon ruwan sama ranar Litinin da almuru.

  Ambaliyar ruwan ta rusa gine-gine da dama wadanda suka hada da rumfunan da ke kasuwannin bakin titi.

  Rashin isassun magudanan ruwa da kuma gine-gine a kan hanyoyin ruwa da ake yi a yankuna da dama na birnin na cikin dalilan da suka haddasa ambaliyar ruwan.

  Sojojin Ghana da ma'aikatan Hukumar yaki da Annoba sun kai wa mutane ɗauki.

  Kafafen watsa labaran kasar sun rawaito cewa ruwan ya yi torokon da ya kai mita 4.5 a wasu yankunan birnin.

  Ambaliya

  A shekarar da ta wuce, Bankin Duniya ya bayar da tallafin $200m ga mazauna yankunan da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da tarin shara a yankin Accra. Sai dai ba a dauki wani muhimmin mataki na magance matsalar ambaliyar ruwan ba.

  Mutum kusan 100 sun mutu shekara biyar da suka gabata a birnin lokacin da wani gidan mai ya kama da wuta sakamakon ambaliyar ruwa.

 20. Abin da ya sa ministar Abuja take so a 'dandaƙe masu fyaɗe'

  Minista a ma'aikatar Birnin Tarayyar Najeriya, Ramatu Aliyu, ta ce tana so a rika dandake mutanen da aka samu da laifin fyade ne saboda hakan zai sa masu irin wannan ta'ada su ji tsoron yi wa mata fyade.

  Ministar ta bayyana haka ne sakamakon kokawar da 'yan kasar suke yi a baya bayan nan game da yawaitar matsalar fyade a kasar.

  “Muna so a aiwatar da wata doka da za ta tabbatar da adalci. Daure wadanda aka kama da laifin fyade bai isa ba, don haka tabbas ya kamata a rika dandake su. Idan aka kashe su, ba za su tuna komai ba, amma idan aka dandake su za su ci gaba da rayuwa amma babu kuzari,” a cewar ministar.

  Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya, inda a baya bayan nan aka samun labarin yi wa wasu mata fyade a sassa daban-daban na kasar.

  Daya daga cikinsu ita ce wata yarinya mai shekara 12 wacce ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin kasar cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

  Kazalika, a farkon wannan watan an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami'a bayan sun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.

  Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.

  Ramatu Aliyu ta ce bai kamata a kashe masu fyade ba amma ya zai yi kyau a dandake su
  Image caption: Ramatu Aliyu ta ce bai kamata a kashe masu fyade ba amma ya zai yi kyau a dandake su