Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

Bayyana ra'ayinka

 1. Rufewa

  Mustapha Musa Kaita

  Multi-Media Broadcast Journalist

  Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokacin muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye a wannan shafin.

  Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labarai da rahotannin.

  Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

  • Iraƙi ta amince Amurka ta janye sojojinta daga ƙasar
  • Najeriya ta samu adadi mafi yawa na masu korona a rana guda
  • Koriya ta Arewa ta ce babu amfanin alaƙa tsakaninta da Trump
  • Mutum 216,446 sun kamu da korona a Afirka
  • Majalisar Wakilai ta karrama Abba Kyari
  • Rashin shugabanci na gari ne matsalar 'yan Najeriya – Atiku
  • Rayukan al'ummar Yemen na cikin haɗari – MDD
  • Kotu a Burundi ta bayar da umarnin rantsar da sabon shugaban ƙasa
  • Jawabin Buhari cin mutuncin dimokradiyya ne – PDP
 2. Covid-19: An dawo da mutum 102 Najeriya daga Masar

  ..

  Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa an dawo da mutum 102 Najeriya daga Masar a yau Juma'a.

  Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  Ya bayyana cewa ana dakon isowar wasu mutum 260 daga ƙsar Indiya a safiyar gobe Asabar.

  A cewarsa, jirgin Egypt Air ne ya dawo da mutum 102 yau daga Masar, sa'annan ana sa ran jirgin Air Peace zai dawo da na Indiya.

  View more on twitter
 3. 'Yan sanda sun kama mutum 35 a Hong Kong

  ..

  'Yan sanda a Hong Kong sun kama mutane 35 a lokacin zanga-zangar cika shekara guda da fara taho mu gama tsakanin masu rajin tabbatar da dimokradiyya da masu fafutuka da gwamnati.

  An dai fara boren ne kan adawa da wani kudurin doka da 'yan majalisa suka gabatar na tasa ƙeyar 'yan yankin Hong Kong zuwa China don fuskantar hukunci a lokacin da suka aikata laifi.

  Daga bisani, an janye hakan a watan Satumba, amma duk da wannan ana ci gaba da zanga-zangar ko da yake daga bisani ɓarkewar annobar korona ta janyo dakatarwa.

 4. Asibitoci a Brazil sun shiga mawuyacin hali – WHO

  ///

  Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargaɗin cewa sashen kula da marasa lafiya na gaggawa na asibitocin Brazil na cikin mummunan yanayi.

  Hakan ya faru ne sakamakon a halin yanzu, masu ɗauke da korona sun mamaye kashi 90 cikin 100 wuraren.

  Daraktan shirin gaggawa na WHO Michael Ryan ya ce wannan abin damuwa ne musamman a yankuna masu cunkoson jama'a.

  Mista Ryan ya ƙara da cewa baki ɗaya fannin lafiya na ƙasar Brazil ya faɗa halin ni 'ya su sakamakon ƙaruwar masu ɗauke da cutar Covid-19.

  Brazil ce ta biyu a yawan masu kamuwa da cutar korona a Duniya. A halin yanzu mutum sama da mutum dubu 800 suka kamu da cutar.

 5. Filin ƙwallo ya cika maƙil da 'yan kallo a Vietnam

  ..

  Vietnam ce ƙasa ta farko da ta bayar da izini ga 'yan kallo su halarci filin wasan ƙwallo ƙafa tun bayan ɓullar cutar korona.

  Mutane sun cika filin wasa maƙil yayin da ake wasa tsakanin Ha Tinh da kuma Ha Noi, ko da aka ga jama'a sun yi yawa sai aka dakatar da wasan.

  Duk da cikar da aka yi, babu wanda ya ji rauni - sai dai an ci gaba da wasan inda wasu 'yan kallon suka tsaya a tsaye ta gefen layin da ake tsere a filin ƙwallo.

  A halin yanzu, mutum 333 ne kacal aka tabbatar da sun kamu da cutar ta korona a ƙasar, babu kuma wanda cutar ta kashe.

 6. Shafin Twitter ya rufe shafuka 180 a ƙasashe 3

  Kamfanin Twitter ya ce ya rufe wasu shafuka kimanin 180 mallakin gwamnati kuma mafi yawa daga China sai kuma sauran daga Turkiyya da Rasha.

  Kamfanin ya ce ana amfani da shafukan wajen kai wa masu suka hari da yaɗa labarai marasa tushe.

  Twitter ya kuma ce ya bankaɗo wasu shafukan da dama da ake amfani da su ta irin wannan fuska.

  A cewar kamfanin, sakonnin da ake wallafawa a shafukan sun fi mayar da hankali kan labaran da suka dace da jam'iyyar kwamunisanci da kuma yadda take tafiyar da batun annobar korona.

  ..
 7. Ƙasashe na fargabar ɓarkewar cutar korona karo na biyu

  Ana ta samun fargaba a faɗin duniya sakamakon tsoron da ake yi na sake ɓullar cutar korona karo na biyu.

  An kulle kasuwannin dillalan kayan abinci shida a Beijing babban birnin ƙasar China, an kuma sake jinkirta komawar ɗalibai makaranta bayan an sake samun sabbin mutanen da suka kamu da cutar ta korona.

  A wannan makon ne aka buɗe Indiya daga dokar kulle, sai dai ana samun ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar a kullum.

  A Korea ta Kudu, ƙasar za ta ci gaba da ɗaukar matakan kariya da kuma kula da muhalli har sai yawan jama'ar da ke kamuwa da cutar sun ragu.

  Akwai fargaba ƙwarai a ƙasar Rasha sakamakon a halin yanzu ita ce ƙasa ta uku a yawan waɗanda suka kamu da cutar ta korona - ana ganin cewa an yi saurin sassauta dokar kulle a ƙasar.

 8. Labarai da dumi-dumiAPC ta haramta wa Obaseki sake tsayawa takara

  .

  Kwamitin da ke tantance 'yan takara na jam'iyyar APC a jihar Edo ya haramta wa gwamnan jihar Godwin Obaseki shiga zaɓen fitar da gwani wanda za a gudanar kafin tsayar da ɗantakarar gwamna.

  Shugaban kwamitin, Jonathan Ayuba ne ya bayyana hakan yayin da ya ke bayar da rahoton ayyukan kwamitin ga shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole.

  Ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takarar ne sakamakon matsalar da ake ganin akwai tattare da takardun makaranta na gwamnan.

  Sai dai a wani ɓangaren kuma, kafofin yaɗa labarai na Najeriyar sun ruwaito cewa Mista Obasekin ya ce ba zai ɗaukaka ƙara ba.

  An dai kwana biyu zaman doya da manja tsakanin Obaseki da Shugaban Jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, wanda hakan ya kawo rabuwar kai musamman a jam'iyyar APC reshen jihar Edo.

  Gwamna Obaseki ne dai ya gaji Adams Oshiomhole bayan ya sauka daga gwamnan jihar a 2016.

 9. Jawabin Buhari cin mutuncin dimokradiyya ne – PDP

  ..

  Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana jawabin da Shugaba Buhari ya yi na Ranar Dimokraɗiyya a matsayin "cin mutuncin dimokraɗiyya".

  PDP ta ce Buhari ba shi da abin da zai nuna da yake tabbatar da cewa shi mai bin ƙa'idojin dimokraɗiyya ne, saboda haka ya gasgata iƙirarin da jam'iyyar ke yi na cewa "ba zai iya mulkar Najeriya ba".

  A martanin da take mayar wa kan bayanin da shugaban ya yi na ranar 12 ga Yuni a matsayin Ranar Dimokraɗiyya, ta ƙara da cewa Buhari ya gaza kare rayukan 'yan Najeriya.

  "Yan Najeriya sun yi mamaki, yayin da 'yan bindiga ke kashe mu a Zamfara da Katsina da Kaduna da Borno hatta a jajiberin bayanin nasa, shi kuma yana iƙirarin cewa gwamnati ta samar da tsaro," in ji sanarwar da PDP ta fitar.

  Jam'iyyar ta yi kira ga 'yan Najeriya da "su farga, kada su bari farfagandar jam'iyya mai mulki ta APC ta rufe musu ido".

  View more on twitter
 10. Kotu a Burundi ta bayar da umarnin rantsar da sabon shugaban ƙasa

  ..

  Kotu a Burundi ta bayar da umarnin gaggauta rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Evariste Ndayishimiye.

  An sa ran cewa Shugaba Pierre Nkrunziza zai sauka daga kan karagar mulkin da ya shafe shekaru 15 yana kai, sai dai kuma Allah ya yi masa cikawa a ranar Litinin.

  Kamar yadda ƙundin tsarin mulkin ƙasar ya nuna, kakakin majalisar ƙasar ne ya kamata ya ja ragar shugabancin ƙasar na riƙon ƙwarya, sai dai hakan bai faru ba.

  A maimakon haka, sai ministocin ƙasar suka kai batun kotu.

  Mista Ndayishimiye wanda jami'iyyarsa ɗaya da tsohon shugaban ƙasar, ya lashe zaɓen ƙasar ne a watan Mayu inda aka sa ran cewa zai karɓi mulki a watan Agusta, sai dai lamarin ya sauya a halin yanzu.

 11. Labarai da dumi-dumiƘarin mutum 202 sun mutu a Ingila sakamakon korona

  Ƙarin mutum 202 sun mutu a Ingila sakamakon kamuwa da cutar korona, kamar yadda alƙaluman gwamnati na kullum suka nuna.

  Hakan ya sa adadin waɗanda suka mutu ya kai 41,481 jumilla.

 12. 'Yan sanda na so a sake haramta sayar da barasa a Afrika ta Kudu

  ...

  Ministan 'yan sanda a Afrika ta Kudu Bheki Cele ya danganta ƙaruwar laifuka da ake samu da ɗage dokar hana siyar da barasa da aka yi.

  Tun a ranar 1 ga watan Yuni ne aka cire wata doka a ƙasar da ta hana siyar da barasa.

  Mista Cele ya bayyana cewa yana fata kwamitin da ke yaƙi da cutar korona za su yi abin da ya dace.

  An gano cewa barasa na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo rikice-rikice da aikata laifuka a Afrika ta Kudu.

  A halin yanzu, ana sayar da barasa ne kawai daga ranar Litinin zuwa Alhamis daga 9:00 na safe zuwa 5:00 na yamma.

  Minsitan 'yan sandan a kwanakin baya ya bayyana cewa an samu raguwar aikata laifuka sakamakon barasa da aka hana sayar wa baki ɗaya a lokacin dokar kulle a ƙasar.

 13. Rayukan al'ummar Yemen na cikin haɗari – MDD

  ..

  Hukumomi da ke ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi kakkausan gargaɗi kan cewa rayukan al'ummar Yemen na cikin haɗari sakamakon duka da ya yi musu yawa na yaƙi, da annobar korona da kuma rashin kuɗi.

  A taron da aka yi a Geneva, mai magana da yawun MDD ya ce nan da makwanni masu zuwa za su rufe kashi uku bisa huɗu na ayyukansu a ƙasar idan ba a samu kuɗin gudanarwa ba.

  Wani daga cikin jami'in hukumar ya bayyana cewa rabin kuɗin da aka yi wa ƙasar alƙwari a farkon watan Yuni sun samu.

  Akwai damuwa musamman kan tsaftataccen ruwan sha da muhalli mai inganci a ƙasar.

  Asusun kula da ƙananan yara na MDD wato UNICEF ya yi gargaɗin cewa zai kulle wasu ayyukansa da kusan 'yan ƙasar Yemen miliyan hudu ke cin abinci a ƙarƙashi

 14. Uwar Gidan shugaban Ukraine ta kamu da korona

  Uwar Gidan shugaban Ukraine

  Uwar Gidan Shugaban Ƙasar Ukraine mai shekara 40 ta kamu da cutar korona.

  Ofishin shugaban ya bayyana a shafin Facebook cewa Olena Zelenski ba ta nuna alamun cutar ba tukunna amma tana killace daga sauran mutanen gida.

  Sai dai gwaji ya nuna cewa Shugaba Zelensky mai shekara 42 da yaransu guda biyu ba sa ɗauke da cutar.

  a makon da ya gabata ne Zelensky ya ce an ci tararsa bisa karya dokar kulle. Hakan ya faru bayan an gan shi a hoto yana shan shayi a wani kanti ranar 3 ga watan Yuni duk da cewa haramcin buɗe kantunan sayar da abinci yana nan daram a lokacin.

 15. Daga cikin bayanin Shugaba Buhari na Ranar Dimkuraɗiyya

  • 'Yan bindiga sun yi amfani da dokar kulle a Katsina da Borno, inda suka kashe mutane da dama
  • Annobar korona na kawo wa dimokuraɗiyyar Najeriya barazana
  • Gwamnatin Tarayya za ta samar wa mutum 774,000 aikin yi - 1,000 a kowacce ƙaramar hukuma a Najeriya
  • 'Yan jarida ne madubin al'umma kuma "na gode musu kan tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya"
  • Buhari ya ce tuni Najeriya ta fara shuka miliyoyin bishiyoyi a faɗin ƙasar. Ya ce wannan ya biyo bayan alƙawarin da ya yi a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma bishiya miliyan 25 gwamnati za ta jagoranci shukawa

  Karanta ƙrin bayani game da ranar a nan:

 16. Rashin shugabanci na gari ne matsalar 'yan Najeriya – Atiku

  Atiku Abubakar

  Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP mai adawa a zaɓen 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce "rashin shugabanci na gari" ne babban dalilin halin da 'yan Najeriya ke ciki.

  Atiku yana taya 'yan Najeriya murnar bikin Ranar Dimokuraɗiyya ne a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a.

  Ya ce duk da cewa ana bikin tunawa ne da gwarazan dimokuraɗiyya a Najeriya, 'yan Najeriya da suka rasa rayukansu sakamakon rashin shugabanci na gari, su ne gwarazan dimokuraɗiyya.

  "A bayyane take cewa matsalar shugabanci ce kan gaba a cikin al'amuran da suka fi ƙuntata wa 'yan Najeriya a wannan jamhuriyar," in ji shi.

  Ya ƙara da cewa duk shugabannin da suka gabata sun yi bakin ƙoƙarinsu wurin ci gaban ƙasar amma har yanzu ƙoƙarin nasu bai kai ba, "domin babu abin da 'yan Najeriya za su kalla su yi farin ciki".

  View more on twitter
 17. Majalisar Wakilai ta karrama Abba Kyari

  Abba Kyari

  Majalisar Wakilan Najeriya ta karrama Abba Kyari, Shugaban Rundunar Sirri ta 'yan sandan Najeriya (IRT) ranar Alhamis.

  Majalisar ta ce ta karrama ofisan ne saboda jajircewarsa wurin daƙilewa tare da kama manyan masu aikata laifuka a Najeriya.

  Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ne ya miƙa masa kyautar a zaman majalisar na ranar Alhamis bisa gayyatar Honarabul Alhassan Ado Doguwa, Jagoran Majalisa.

  Abba Kyari

  Daga cikin nasarorin da Abba Kyari ya samu akwai kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane Chukwudi Onwuamadike (wanda aka fi sani da Evans) da Bala Hamisu (Wadume).

  Sauran sun haɗa da waɗanda ake zargi da kisan tsohon babban hafsan sojin Najeriya Alex Badeh da kuma waɗanda ake zargi da yin garkuwa da sirikin dogarin Shugaba Buhari.

  View more on twitter
 18. Cutar korona ta hana Werner komawa Chelsea, Barca tana son dauko ‘yan wasan Tottenham da Chelsea

  Timo Werner

  An dakatar da shirin komawar dan wasan Jamus Timo Werner Chelsea daga RP Leipzig a kan £52m saboda dokokin killacewa da aka sanya sakamakon cutar Covid-19, abin da ya hana dan wasan mai shekara 24 yin gwaje-gwajen kiwon lafiyarsa. (The Athletic -subscription required)

  Rahotanni na cewa Barcelona tana son dauko 'yan wasan baya daga Tottenham da Chelsea wadanda za ta karbo a shirin musayar da za ta bayar da Philippe Coutinho mai shekara 27. (Sport via Mail)

  Inter Milan tana shirin sayen dan wasan Arsenal Hector Bellerin a kan £27m a bazar duk da cewa shekara uku suka ragewa dan wasan na Spaniya mai shekara 25 kafin kwangilarsa ta kare. (Express)

  Ku karanta sauran jita-jita a kasuwar saye da musayar 'yan wasan Turai a nan

 19. Mutum 216,446 sun kamu da korona a Afirka

  CDC Africa

  Hukumar CDC Africa - mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Afirka - ta ce mutum 216,446 sun kamu da cutar korona a ƙasashen Afirka 54 ya zuwa safiyar Juma'a.

  Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa yanzu yankin Kudancin Afirka ya zarta na arewaci, inda ake da mutum 61,772 da suka kamu da cutar, yayin da 1,239 suka mutu da kuma 33,156 da suka warke.

  Afirka ta Kudu ce kan gaba a yawan masu cutar a yankin da mutum 58,568.

  A yankin arewaci kuwa, 61,615 ne suka kamu, 2,454 sun mutu sannan 26,718 sun warke. Masar ce kan gaba a yankin da mutum 39,726.

  Najeriya ce ta fi saura yawan waɗanda suka harbu da cutar a Yammacin Afirka, inda take da mutum 14,554. Jumillar waɗanda suka kamu a yankin sun kai 46,433.

  Mutum fiye da miliyan bakwai ne suka kamu da cutar a duniya baki ɗaya, kuma fiye da 500,000 daga cikinsu sun mutu.

  View more on twitter
 20. Wuraren killace masu korona a Nepal 'na yaɗa cutar'

  Nepal

  Kamata ya yi a ce cibiyoyin killace masu cutar korona su kare yaɗuwarta, sai dai a ƙasar Nepal sun zama wata cibiyoyin cutar, a cewar Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta ƙasar.

  Kusan mutum 170,000 ne ke killace a cibiyoyi daban-daban a ƙasar.

  A wani rahoto, hukumar ta soki gwamnati kan yadda ta gaza tsaftace wuraren kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tsara.

  WHO ta ce ya kamata a samar da kayan tsaftace hannu da na tsaftace banɗaki a wani ɗaki mai falle ɗaya, in kuma ya zama wajibi sai mutane sun haɗu a ɗaki ɗaya to a bayar da tazarar aƙalla mita ɗaya tsakanin gadaje.

  Nepal na da mutum 4,614 da suka harbu da cutar korona da kuma 14 da suka mutu.