Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Ahmad Janyau da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Mustapha Musa Kaita

  Multi-Media Broadcast Journalist

  Masu bibiyarmu a wannan shafin a daidai wannan lokacin muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

  Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labarai da rahotannin.

  Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin:

  • Aisha Buhari ta nemi ƴan sanda su saki ma’aikatanta
  • Brazil yanzu ita ce kasa ta biyu da cutar korona ta fi yin kisa
  • 'Ƴan majalisa masu korona a Ghana sun ƙi ƙauracewa majalisa'
  • IS ta yi ikirarin kashe mayaƙan sa-kai 90 a Borno
  • ‘An yi wa garin Monguno ƙawanya’
  • An fara yi wa Jemagu gwajin cutar korona a Thailand
  • Gwamnati ta buɗe gidajen kallon ƙwallo a Kano
  • Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Landa

  Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da kuma wasu muhimmai.

 2. Akwai yiwuwar sake saka dokar kulle a Iran

  ..

  Shugaban ƙasar Hassan Rouhani ya bayyana cewa akwai yiwuwar sake saka dokar kulle a ƙasar idan har mutane ba su bin dokokin da aka gindaya.

  Ana samu tashin gwauron zabi a yawan masu kamuwa da cutar a kullum tun bayan da ƙasar ta sassauta dokar kullenta a tsakiyar watan Afrilu.

  An samu sama da mutum 2,400 da suka kamu da cutar a ranar Asabar, hakan ya sa jumullar waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar ya kai 184,955.

  Yawan waɗanda suka mutu a ƙasar a halin yanzu ya kai 8,730.

  Shugaba Rouhani ya bayyana cewa a watan da ya gabata an samu haɗin kan jama'a wajen bin ƙa'idoji da kusan kashi 80 cikin 100, inda a halin yanzu ya dawo kashi 20 cikin 100.

 3. Ministan Lafiya na ƙasar Chile ya yi murabus.

  Shugaban ƙasar Chile Sebastian Piñera, ya bayyana cewa ministan lafiya na ƙasar Jaime Mañalich ya yi murabus, a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin ganin cewa ta shawo kan annobar korona.

  'Yan adawa a ƙasar sun yi kira ga gwamnatin ƙasar kan kawo sauyi ga ɓangaren kiwon lafiya na ƙasar, sun kuma ce dama tun tuni ya kamata a ce ministan ya yi murabus.

  Sabon ministan lafiya na ƙasar Enrique Paris ya yi alƙawarin cewa zai saurari ra'ayoyin waɗanda ba su gamsu da yadda gwamnatin ƙasar ke tafiyar da al'amuran korona ba.

  Sama da mutum dubu uku suka mutu sakamakon cutar korona a Chile.

  ..
 4. Najeriya ta dawo da mutum 269 daga Indiya

  .

  Gwamnatin Najeriya ta dawo da mutum 269 da suka maƙale a Indiya sakamakon hana zirga-zirgar jirage da aka yi.

  Waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mutum 103 da suka sauka Legas sai kuma mutum 166 da suka a Abuja babban birnin ƙasar.

  A jiya Juma'a ne ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya yi albishir kan cewa a yau Asabar jirgin Air Peace zai dawo da mutum 260 daga Indiya.

  Ya wallafa haka ne a shafinsa na Twitter bayan an dawo da mutum 102 daga Masar.

  A halin yanzu, waɗanda suka dawo sun shiga killacewa ta dole na kwanaki 14 domin daƙile yiwuwar yaɗuwar cutar korona.

 5. Ministan Lafiya na Ghana ya kamu da korona

  Ma'aikatar lafiya ta Ghana

  Rahotanni daga Ghana sun ce gwaji ya tabbatar da ministan lafiya na ƙasar ya kamu da cutar korona.

  Shafin Ghanaweb ya ce ministan Kwaku Agyeman Manu tun makon da ya gabata aka kwantar da shi a asibitin Jami'ar Ghana a Accra amma yana samun sauki.

  Jaridar ta ce shi ne babban jami'in gwamnati na farko da ya kamu da korona a ƙasar Ghana wanda kuma ke jagorantar yaƙi da cutar a ƙasar.

  Wannan na zuwa a yayin da wasu rahotanni suka ce wasu daga cikin ƴan majalisar Ghana gwaji ya tabbatar da suna ɗauke da cutar korona inda kuma suka ƙi killace kansu a gidajensu.

  Zuwa yanzu sama da mutum 11,000 aka tabbatar da sun kamu da korona a Ghana yayin da cutar ta kashe mutum 48.

 6. Labarai da dumi-dumiAn yi girgizar ƙasa a Japan

  An yi girgizar ƙasa mai girman kusan maki bakwai a kudu maso yammacin Japan.

  Girgizar ƙasar ta yi zurfi sosai kuma babu wani gargaɗi da gwamnati ta yi kan cewa ko akwai guguwar tsunami.

  Girgizar ƙasar ta faɗa ne a tsibiran Okinawa da kuma Kyushu.

  Sai dai har yanzu babu wani rahoto dangane da waɗanda suka samu rauni ko kuma suka mutu

 7. Jama'a da dama sun fito zanga-zanga a birnin Paris

  ..

  Dubban mutane ne suka fito zanga-zanga a Paris babban birnin Faransa domin nuna goyon bayansu ga zanga-zangar da ake yi a wasu ƙasashe na duniya kan muhimmancin rayuwar baƙar fata, wato Black Lives Matter.

  Sun fito zanga-zangar ne domin tunawa da wani ɓakar fata da 'yan sanda suka kashe a ƙasar a 2016.

  Adama Traore mai shekaru 24 ya mutu ne bayan da 'yan sandan ƙasar suka kwantar da shi ƙasa.

  Masu zanga-zangar su nuna jin daɗinsu da mazauna wani gida suka keta wani babban rubutu na masu tsatsauran ra'ayi da ke saman wani rufi.

  'Yan sanda sun kama mutum 12 da ake zargin sun maƙala rubutun. 'Yan sandan sun harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar

 8. Kasashen Turai sun ƙulla yarjejeniya kan riga-kafin korona

  Kasashen Itliya da Jamus da Netherlands sun ƙulla yarjejeniya da kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca domin samar da maganin riga-kafi ga al'umarsu.

  Yarjejeniyar ta shafi samar da magani kimanin miliyan 400, wanda aka samar a jami'anr Oxford ta Birtaniya.

  A lokacin da yake sanar da matakin, ministan lafiya na Italiya Roberto Speranza ya ƙara da cewa kafin ƙarshen shekara suke fatan karbar kason farko na riga-kafin

 9. Dubban mutane sun fito zanga-zanga a Landan

  ..

  Dubban jama'a masu zanga-zanga ne suka taru a tsakiyar Landan, duk da gargaɗin da 'yan sanda suka yi na hana zanga-zanga.

  Rahotanni sun bayyana cewa an jefi 'yan sanda da kwalabe a wani wuri da ake kira Parliament Square, inda wasu rukunin jama'a ke cewa suna kare gumakan garin ne daga masu zanga-zanga kan nuna wariyar launin fata.

  'Yan sanda a Landan din sun haramta wa ƙungiyoyi daban-daban zanga-zanga, biyo bayan rikice-rikicen da aka samu a makon da ya gabata.

  Daga cikin zanga-zangar, akwai masu iƙirarin muhimmancin baƙar fata, wato Black Lives Matter, inda aka yi irin wannan zanga-zanga a wurare daban-daban ciki kuwa har da tsakiyar Landan.

 10. Ina ya kamata a saka takunkumi?

  Takunkumi

  Sabuwar dokar saka takunkumi za ta fara aiki a ranar Litinin a Ingila inda aka tilastawa mutane yin amfani da takunkumi a motocin sufuri.

  Haka ma ma'aikatan sibiti da masu jinya da ziyara dole su saka takunkumi.

  Wannan na daga cikin sabbin shawarwarin hukumar Lafiya ta duniya inda ta ce a dinga saka takunkumi a taron jama'a inda ba za a iya bayar da tazara ba.

  Kamfanin Uber zai bukaci direbobinsa da fasinja saka takunkumi daga ranar Litinin. Haka ma a Wales da Scotland an shawarci mutane su dinga saka takunkumi a wuraren da yin nesa da nesa zai yi wahala.

 11. Gwamnati ta buɗe gidajen kallon ƙwallo a Kano

  Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar da umurnin buɗe wuraren kallon ƙwallo da fina-finai a jihar duk da fargabar yaɗuwar cutar korona.

  Wannan na zuwa a yayin da aka ci gaba da wasannin ƙwallon ƙafa a turai inda mafi yawanci matasa ke kallo a gidajen da ake nuna wasannin a talabijin.

  Sanarwar da Abba Anwar mai taimaka wa gwamnan kan harakokin watsa labarai ya fitar a ranar Asabar ta ce, gwamnan ya amince a buɗe wuraren kallon ne bayan wata ziyara da ƙungiyar masu gidajen kallon ƙwallon kafa suka kai masa a ofishinsa.

  Sannan a cewar sanarwar, gwamnan ya bayar da takunkumi 40,000 a raba wa gidajen nuna kwallon ƙafa domin kiyaye shawarwarin da hukumomin lafiya suka bayar na rage yaɗuwar cutar.

  Gwamnan Kano
 12. An fara yi wa Jemagu gwajin cutar korona a Thailand

  Masana a Thailand sun fara yi wa Jemagu gwajin cutar korona saboda suna tunanin barazana ne ga lafiyar al'umma.

  Samfurin a kalla jemagu 300 za a ƙarba daga wani kogo da ke yankin Chanthaburi a kudu maso gabashin Thailand.

  Ana tunanin cutar korona ta samo asali ne daga jemage a China kafin ta yaɗu ga mutane, ko da yake ba a tabbatar da gaskiyar hakan ba.

  Jemage
 13. Nijar na nazarin buɗe iyakokinta

  Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

  Hukumomin Nijar na nazarin buɗe kan iyakokin kasar na ƙasa da na sama nan bada jimawa ba kamar yadda kafofin yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

  Jaridar aNiamey ta ce batun buɗe iyakokin na daga cikin abin da taron majalisar ministoci ya tattauna musamman kwamitocin da ke yaƙi da annobar korona a ƙasar wanda Firaminista Briji Rafini ya jagoranta.

  A cewar jaridar, gwamnati ta ce tana shirin buɗe iyakokinta tare da la'akari da amincewar kwamitin ƙwararru.

  Amma buɗe iyakokin ya dogara ne da matakan da sauran ƙasashen Afirka suka ɗauka.

  Alkalumman hukumomin lafiya a Nijar sun ce mutum 169 ne ake kula da su yanzu haka, yayin da mutum 38 aka tabbatar da suna ɗauke da cutar daga cikin jimillar 974 da suka kamu a ƙasar.

 14. Labarai da dumi-dumi‘An yi wa garin Monguno ƙawanya’

  Rahotanni daga Borno jihar Borno sun ce an yi wa garin Monguno ƙawanya inda ake tunanin sojoji ne ke musayar wuta da mayakan Boko Haram.

  Wasu mazauna Maiduguri sun shaida wa BBC cewa da misalin 12:30 na ranar Asabar ƴan uwansu da ke Monguno suke ta kira suna sanar da su halin da suke ciki. Kuma BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar mazauna garin na Monguno amma layukan waya ba su zuwa.

 15. IS ta yi ikirarin kashe mayaƙan sa-kai 90 a Borno

  Mayakan Boko Haram

  Ƙungiyar IS da ke iƙirarin jihadi ta yi iƙirarin kashe mayaƙan sa-kai 90 a jihar Borno yankin arewa maso gabashi.

  A sanarwar da ta wallafa ranar Juma'a, IS ta ce mayaƙanta ne suka kai wa gangamin mayaƙan sa-kai hari a garin Gubio inda suka yi musayar wuta da ya kai ga kashe kusan 90 da raunana wasu.

  Ta kuma yi ƙirarin cewa mayaƙanta sun yi ƙoƙarin kashe mayaƙanta bayan sun nemi su juya wa sojojin Najeriya baya.

  Tun da farko rahotanni sun ce mutum 81 aka kashe a harin da aka kai ƙauyen Foduma kolamaiya da ke ƙaramar hukumar gubio a ranar Talatar da ta gabata.

 16. 'Ƴan majalisa masu korona a Ghana sun ƙi ƙauracewa majalisa'

  Rahotanni daga Ghana sun ce wasu ƴan majalisa da gwaji ya tabbatar da suna ɗauke da cutar korona sun bijerewa umurnin kwamitin da yake yaƙi da korona a ƙasar da kuma shugabannin majalisa kan su ƙauracewa zauren majalisar.

  Shafin intanet na jaridar Joyonline ya ce shugabannin majalisa sun damu kan yadda wasu ƴan majalisa da ma'aikata da gwaji ya tabbatar da suna da korona suka bijerewa umurnin su ƙauracewa majalisa.

  Sai dai kuma shugabannin majalisar ba su bayyana sunayen ƴan majalisar da gwaji ya tabbatar da suna ɗauke da cutar.

  A cewar jaridar, Kakakin majalisar Prof Mike Aaaron Oquaye ya ce saboda tsoron ƙara yaduwar cutar a zauren majalisar, za a gudanar da wani sabon gwaji kan dukkanin ƴan majalisar da ma'aikata a mako mai zuwa.

 17. Ana fargabar sake barkewar annobar korona a China

  Hukumomi a Beijing sun ce, yankin Fengtai na cikin hatsarin annobar korona yayin da aka saka dokar kulle a yankuna 11.

  Hukumomin sun tabbatar da samun sabbin mutum 45 da suka kamu da cutar a kasuwar xinfadi da ke kudu maso gabashin Beijing - ko da yake babu cikinsu wanda ya nuna alamomin cutar.

  Kasuwar ta kasance ta nama da kayan marmari. Tsoron sake yaduwar cutar ya sa hukumomi a birnin suka hana wasanni da yawon buɗe ido. Sama da ma'aikata 10,000 aka yi wa gwajin korona a kasuwar Xinfadi.

  Kafin yanzu, an shafe sama da kwana 50 ba tare an samu wanda ya kamu da korona ba Beijing.

  A birnin Wuhan ne aka fara samun ɓullar cutar korona wacce yanzu ta zama annoba a duniya

 18. Brazil yanzu ita ce kasa ta biyu da cutar korona ta fi yin kisa

  Brazil

  Brazil yanzu ta sha gaban Birtaniya inda yanzu ita ce kasa ta biyu da cutar korona ta fi yin kisa.

  Sama da mutum 900 suka mutu cikin sa'a 24, inda yanzu yawan wadanda suka mutu suka kai kusan mutum 42,000

  Cutar korona na ci gaba da yaɗuwa a duniya inda sama da mutum miliyan 7 da rabi suka kamu da cutar a duniya yayin da kuma cutar ta kashe mutum 425,000 a duniya, kamar yadda alkalumman Jami'ar John Hopkins suka nuna.

 19. Aisha Buhari ta nemi ƴan sanda su saki ma’aikatanta

  Aisha Buhari

  Mai ɗakin Shugaba Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira ga babban sufeto janar na Najeriya ya saki wasu ma'aikatanta da ake tsare da su.

  Uwar gidan shugaban na Najeriya ta yi kiran ne ga babban sufeto janar na ƴan sandan a wani saƙon da ta wallafa a twitter, inda ta ce tana son a saki jami'an ne don kaucewa jefa rayuwarsu a cikin hatsarin kamuwa da cutar korna a yayin da ake tsare da su.

  Rahotanni sun ce ana tsare ne da babban dogarin uwar gidan shugaban da kuma wasu jami'an tsaron da ke bata kariya.

  Kuma a jerin sakwannin da Aisha Buhari ta wallafa ba ta bayyana dalilin da ya sa ake tsare da su ba, amma wasu rahotanni sun ce an tsare su ne saboda sa'insa da wani mataimaki ga shugaban kasa.

  Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga ofishin sufeto janar na ƴan sanda kan umurnin uwar gidan shugaban na Najeriya.

  View more on twitter
 20. Buɗewa

  Muna maku barka da wannan rana ta Asabar da fatan kun tashi lafiya.

  Ku biyo mu a wannan shafi inda za mu kawo maku labarai da rahotanni musamman a Najeriya da sauran sassan duniya.