Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge, Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Rufewa

  A nan za mu dakata da kawo ƙarshen labarai da rahotannin da muke kawo maku kai tsaye musamman kan batutuwan da suka shafi Najeriya da sauran sassan duniya.

  Da fatan za ku kasance da mu gobe inda za mu ci gaba da kawo labarai da rahotanni kai tsaye.

  Sai da safe.

 2. Gwamnati Najeriya na son a fadada yi wa mutane gwajin korona a jihohi

  Boss Mustapha

  Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda mutane suka yi watsi da ka'idojin da aka shata na sassauta dokar kulle domin takaita yaduwar cutar korona.

  Shugaban kwamitin shugaban kasa da ke yaki da cutar korona kuma sakataren gwamnati Boss Mustapha ya bukaci gwamnatocin jihohi su fadada aikin gwajin cutar tsakanin al'umma tare da tabbatar da ganin an bi ka'idojin nisantar juna musamman a wuraren da mutane ke taruwa.

  Gwamnatin kuma ta ce har yanzu ba a kai lokacin da za a bude makarantu ba da wuraren kallon wasanni da sauran wurare na taron jama'a, duk da gwamnatin ta buɗe wuraren ibada.

 3. An kashe sojojin 24 a harin Mali

  Sojojin Mali

  Rundunar sojin Mali ta ce sojojinta 24 aka kashe a wani harin kwantan ɓauna da ƴan bindiga suka kai wa ayarinsu a yankin da ke fama da matsalar tsaro.

  Kakakin rundunar sojin ya ce an gano sojoji 8 daga cikinsu bayan harin da aka kai ranar Asabar a kusa da garin Diabaly a yankin Segou da ke nisan kilomita 100 da kan iyaka da Mauritania.

  Wannan ne adadi mafi girma da aka kashe sojoji tun watan Nuwamban bara inda aka kashe sama da sojojin Mali 50 a harin da ƴan bindiga suka kai.

  Tuni shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita ya yi tayin tattaunawa da ƴan bindiga masu ikirarin jihadi.

 4. Sojoji sun gano matatar da ake kwashe man Najeriya a Delta

  Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce wani jirgin ruwan sojan sama mai suna Delta ya gano wata sabuwar matata ta ɓoye da aka gina a cikin Warri ta kudu a jihar Delta.

  Sanarwar da kakakin rundunar tsaron ta Najeriya John Enenche ya fitar ta ce matatar da na ɗauke da ɗanyen mai da yawansa ya kai ganga 943.3 da aka kwace a ranar 10 ga watan Yuni

  Sai dai ya ce babu wanda aka kama yayin da mutanen da ke cikin matatar suka gudu bayan sun tsinkayi jami'an tsaron da suka kawo samamen.

  Sanarwar ta ce akwai kuma wata matata da aka gano a Uwakeno cikin yankin na karamar hukumar Warri ta kudu wanda sanarwar ta ce tana ɗauke da gas kusan lita 10,000 da aka tace da kuma ɗanyen mai ganga 440.90.

  View more on twitter
 5. Elrufa'i ya janye jami'an tsaro a kan iyakokin Kaduna

  Gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin janye dukkanin shingayen da aka datse kofofin shiga jihar tare da ba jami'an tsaro umurnin su janye.

  Sanarwar da aka wallafa a shafin Twitter na gwamnatin jihar ta ce za a toshe hanyoyin ne kawai lokacin da dokar hana fitar dare ta fara aiki daga karshe 8 na dare zuwa 5 na safe.

  Sannan gwamnati ba za ta sake tura jami'ai ba a kan iyakokin jihar.

  View more on twitter
 6. Turkiyya da Rasha za su ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya a Libya

  BBC

  Turkiyya ta ce za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da Rasha domin kokarin kawo karshen rikicin Libya, duk da dage dattaunawar zaman lafiyar da aka yi a karshen lokaci a ranar Lahadi.

  Kasashen biyu na goyon bayan bangarorin biyu da ke hamayya da juna a rikicin.

  Rahotanni na cewa an fasa tattaunawa tsakanin ministocin harkokin wajen Rasha da na Turkiyya ne saboda banbancin da ake da shi kan makomar birnin Sirte na Libyan.

  Birnin na karkashin ikon Khalifa Haftar da ke kawance da Rasha.

  Amma dakarun gwamnatin da ke samun goyon bayan Turkiyya na kokarin kara karbe ikon yankin.

 7. Cikin Hotuna: masu siyayya a kantuna na fara sabuwar rayuwa

  Dubban masu mutane ne ke jerin gwano a shagunan siyayya a Ingila, yayin da aka sassauta dokar kasuwanci a ranar Litinin.

  Ana ta daukar matakan tabbatar da kariya tsakanin mutanen ta hanyar takaita mutanen da za su rika shiga shagunan, tsarin bin layi, da sanya takunkumi da kuma wanke hannu a ko wacce mashiga.

  PA Media
  Image caption: Yayin da sanya takunkumi ke kara zama ruwan dare a matakan kariya wasu shagunan na kara tsaurara tsaro
  Getty Images
  Image caption: Ma'aikata na sanya abin kariya a wajen aiki a York
  Alamy Live News
  Image caption: Sai farinciki ake kara nunawa a Brighton
 8. Yawan wadanda cutar korona ta kashe a Saudiyya ya haura dubu daya

  gazette

  Hukumomi a Saudiyya sun ce yawan marasa lafiyan da suka mutu sakamakon cutar korona a kasar ya haura mutum 1,000.

  Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce cikin sa'a 24 mutum tara sun rasa rayukansu. wanda ya kai adadin wadanda suka mutum dalilin cutar ya kai 1,011.

  An kuma samu sabbin masu dauke da cutar 4,500 wanda ya kai yawansu zuwa sama da 132,000.

  Saudiyya na fuskantar ƙaruwar adadin masu dauke da cutar, yayin da hukumomi ke kokarin sassauta dokar kullen da aka ƙaƙaba saboda korna.

 9. Botswana na bincike dalilin mutuwar giwaye sama da 150

  ANBARASAN ETHIRAJAN

  Jami'an da ke lura da gandun daji a Botsuwana sun fara gudanar da bincike kan mutuwar wasu giwaye sama da 150 a yankin Okavango cikin watanni biyu.

  An samu kasusuwan halittun ne a wuri daya a tare, abin da ke nuna ba farautar su aka yi ba mutuwa su ka yi.

  Rahotanni na cewa, an aike da samfurin kashushuwan zuwa kasar Afrika ta Kudu da ke makwabtaka domin gudanar da wani gwajin, jami'ai a Botsuwana na sauraren sakamakon domin gano musabbabin mutuwar ta su.

  Botsuwana ce ke da kashi uku na adadin giwayen da ke nahiyar Afrika, wanda adadinsu ke raguwa a yan shekarun nan saboda yawan farautarsu da ake.

 10. Rasha ta yanke wa sojan Amurka hukuncin shekara 16 a gidan yari

  Paul Whelan

  Rasha ta yanke wa wani tsohon sojan Amurka Paul Whelan hukuncin shekara 16 a gidan yari bisa kama shi da laifin leƙen asiri.

  An kama shi a wani ɗakin otel wata 18 da suka gabata tare da ma'adanar bayanan kamfuta ta USB, wanda jami'an tsaro suka ce tana ɗauke da bayanan sirrin ƙasar.

  Kotun Birnin Moscow ta same shi da laifin samun bayanan sirri.

  Paul Whelan wanda ke da katikan shaidar zama ɗan ƙasashen Birtaniya da Canada da Ireland, ya yi watsi da shari'ar a matsayin "ta boge" kafin yanke hukuncin.

 11. Ma'aikatan Fadar Shugaban Kenya guda huɗu sun kamu da korona

  Uhuru Kenyatta

  Ma'aikatan Fadar Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya huɗu sun kamu da cutar korona, a cewar wata sanarwa da fadar fitar.

  An kai dukkaninsu zuwa wani asibiti da ke kusa da fadar domin ba su kulawa.

  Shugaban da iyalinsa "suna cikin ƙoshin lafiya," in ji sanarwar.

  Baki ɗayan ma'aikatan, ciki har da shugaban da iyalinsa, ana yi musu gwaji a-kai-a-kai.

  Domin a tabbata an daƙile yaɗuwar cutar, yanzu "za a tsaurara yanayin zirga-zirga" ga ma'aikatan fadar da ke zaune a wajenta.

  Ya zuwa yanzu Kenya na da mutum fiye da 3,000 da suka harbu da cutar korona sannan sama da 80 sun mutu sakamakon cutar - wadda ake yi wa laƙabi da Covid-19.

  View more on facebook
 12. Kotu a Malawi ta hana yi wa alƙalin alƙalan kasar ritaya

  Getty

  Kotu a Malawi ta ba da umarnin gwamnati ta dakatar da bai wa alkalin alkalan kasar Andrew Nyirenda hutun ritaya.

  A tsarin dokar kasar, alkalin alkalan kasar na ritaya ne kawai in ya kai shekara 65, amma Andrew Nyirenda zai cika shekara 65 ne a karshen shekara mai zuwa.

  Gwamnati ta ce ta ga Andrew Nyirenda ya ki yin hutu na ranaku da yawa - sama da lokacin da ya dauka yana aiki - ya kuma kamata ya sauka yanzu.

  Sai dai kotu ta dakatar da hakan.

  Kotuna da bangaren shugabancin kasar ba sa ga muciji tun lokacin da alkalai suka soke zaben shugaba Peter Mutharika a bara, tare da ba da umarnin sake sabon zaben shugaban kasar - wanda za a yi yanzu a ranar 23 ga watan Yuin da muke ciki.

  Mista Mutharika na fuskantar kalubale daga abokin karawarsa Lazarus Chakwera wanda ya ke shugabantar gamayyar jam'iyyun 'yan adawa tara a kasar.

 13. Shugaban Janjaweed ya musanta aikata zargin laifukan yaki a gaban kotun manyan laifuka ta duniya

  ICC
  Image caption: Shugaban 'yan ta da ƙayar bayan Sudan Ali Kushayb ya bayyana gaban kotun ne ta hoton bidiyo

  Shugaban 'yan ta da ƙayar bayan Sudan da suka yi yaƙi a yankin yammacin Dafur shekara 20 baya, ya musanta aikata laifukan yaki.

  Ali Kushayb ya yi magana ne a karon farko da bayan gurfanarsa gaban kotun manyan laifuka ta duniya.

  Shi ne shugaban tawagar Jamjaweed - dan tada kayar bayan gwamnati mai hadari, wanda suka aikata cin zarafi iri-iri ga fararen hula a kasar.

  An ba da umarnin kama shi ne shekara 13 baya, tare da jerin zarge-zarge 50 da ake tuhumarsa da su, ciki harda laifukan yaƙi kan fararen hula, da suka hadarda kisan kai da fyade da kuma azabtarwa.

  An zagaye shi ne a makon jiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, in da yake buya tun watan Fabrairu, lokacin da Sudan ta sanar cewa za ta mika duk wadanda ake zargi gaban kotun manyan laifuka ta duniya.

  Shi ma tsahon shugaban kasar Omar al-Bashir kotun na nemansa ruwa a jallo.

  An kashe kusan mutum 300,000 yayin rikicin na Dafur kuma kusan mutum miliyan 2.5 sun tsere daga muhallansu.

 14. An ki ba da belin masu fafutukar da ake zargin an ci zarafinsu a Zimbabwe

  Getty
  Image caption: Joana Mamombe 'Yar majalisar jami'iyyar adawa a Zimbabwe daya daga cikin matan da suka ce an ci zarafinsu

  'Yar majalisar jami'iyyar adawa a Zimbabwe da kuma wasu masu fafutuka da suka ce an sace su tare da azabtar da su a watan da ya gabata, an ƙi ba da belin su bayan an tuhumesu da yi wa 'yan sanda karya.

  An kwantar da Joana Mamombe da Cecilia Chimbiri da kuma Netsai Marova a sibiti 'yan kwanaki bayan an kama su sakamakon shiga cikin wata zan-zanga da ta gudana.

  Sun ce wasu mutane da ba su sani ba sun dauke su daga ofishin 'yan sanda suka lakaɗa musu duka kuma suka nemi lalata da daya daga cikinsu.

  Gwamnati ta zargesu da yada labaran karya da za su iya ta da hankali.

  Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun bayyana wannan turka-turka a matsayin misalain kama-karyar siyasa a Zimbabwe.

 15. Coronavirus: An kulle kasuwanni da makarantu a China

  Getty
  Image caption: A wata kasuwa aka kara samun masu dauke da cutar

  An kara sanya dokar kulle a garuruwa 10 masu makwabtaka da Beijing babban birnin China, a wani yunkuri na dakile annobar korona da ta shafi babbar kasuwar abinci a brinin.

  An samu Karin mutum 36 da ke dauke da cutar a yau Litinin. Wani jami’in gunduma ya ce an samu sabbin masu dauke da cutar ne a kasuwa ta biyu mafi girma da ke yankin Haidian.

  Ya ce za a rufe kasuwar da makarantun da ke kusa da yankin, kuma sake bude makarantun firaimare da aka shirya a yau Litinin an sake dage shi zuwa nan gaba kamar yadda jaridar Global Times ta wallafa.

  Babu kuma wani bako da za a bari ya shiga garuruwa 10 da aka killace.

  Ma'aikatar Lafiya ta Kasar ta ce a ranar Alhamis an samu mai dauke da cutar guda sannan aka samu mutum shida a ranar juma'a - wanda wadannan ne masu cutar na farko da aka samu cikin kimanin wata biyu.

  Getty
 16. Indiya na neman hanyoyin shawo kan korona

  Getty

  Ministan cikin gidan Indiya Amit Shah, na jagorantar wani taron gaggawa na jam’iyyun siyasa a babban birnin kasar Delhi, wanda za a tattauna hanyoyin da za a shawo kan matsalar annobar korona a kasar.

  Ya zuwa yanzu Indiya ta tabbatar da mutum dubu 40 da suka kamu da cutar a kasar, sai dai jami’ai sun yi gargadin cewa, la’akari da karuwar masu cutar da ake samau a yanzu, adadin zai iya karuwa kafin karshen wata mai kamawa.

  A ranar Asabar ne, Gwamnati ta samar da kekunan dokin da za a rika amfani da su lokacin da bukatar gaggawa ta taso, yayin da jami’an ke kokarin samar da Karin gadaje a asibiti.

  Asibitoci a kasar sun cika makil, yayin da rahotanni ke cewa ana mayar da marasa lafiyar da ke cikin matsanancin yanayi gida daga asibitoci.

 17. An yanke hannun matar da tsohon mijinta ya sara da adda

  Wata mata a garin Makueni da ke gabashin Kenya tana can kwance a asibiti bayan tsohon mjinta ya sare ta da adda, a cewar kafofin watsa labaran kasar, wadanda suka samu labarin daga wurin jami'an lafiya.

  Likitoci sun yanke hannun Purity Muthoki sakamakon munanan sara guda 31 da ya yi mata a wurare daban-daban.

  Tsohon mijinta, Boniface Mutua, ya je gidanta kuma makwabtanta sun ji lokacin da Ms Muthoki take ihu.

  Da suka isa gidan, sun tarar an kulle shi daga ciki kuma bayan sun roki Mr Mutua ya bude kofa sanna ya tsere daga gidan.

  Daga nan ne suka fi shi da gudu inda suka yi ta dukansa har ya mutu.

  Wani babban jami'in 'yan sandan yankin Joseph Ole Naipeyan ya shaida wa kakafen watsa labaran kasar cewa an kai gawar mutumin dakin ajiye gawarwaki kuma an dauki matar zuwa asibiti inda likitoci suka ce tana samun sauki.

 18. COVID-19: Ƙasashen Turai suna fita daga dokar kulle

  Galibin kasashen Turai na fita daga kangin kullen cutar korona ranar Litinin.

  Watanni uku bayan annobar ta tilasta wa mafiya yawan kasashe sanya dokar kulle, kungiyar tarayyar Turai na shawartar mambobinta da su kyale mutane da kuma harkokin kasuwanci su ci gaba da tafiya kamar yadda suke a baya.

  An janye galibin ‘yan sanda da dakarun da ke aikin tabbatar da kulle a kan iyakoki kasashen Turai.

  Faransa na umartar wadanda suka isa kasar daga Birtaniya da Spaniya da su killace kansu na makonni biyu.

  Ƙasar Sweden na korafin ‘yan kasar na kukan cewa suna shan wahala kafin su tsallaka zuwa makwabtan kasashe Denmark da Finland da Norway.

  Jiragen kasa na ci gaba da zirga-zirga.

  Jiragen kasa na ci gaba da zirga-zirga.
  Image caption: Jiragen kasa na ci gaba da zirga-zirga
 19. An yi wa Sarkin Morocco tiyata a zuciya

  Kamfanin dillacin labaran Morocco MAP ya ruwaito cewa an yi "nasarar" yi wa Sarki Mohammed VI tiyatar ciwon zuciya a wani asibiti da ke Rabat, babban birnin kasar.

  MAP ya ce Sarkin ya yi fama da wani nau'i na ciwon zuciya wanda aka yi amfani da wata na'ura wajen yi masa magani ranar 14 ga watan Yuni.

  "Wannan tiyata ta yi nasara," a cewar MAP, yana mai ambato rahoto daga likitoci biyar na sarkin.

  Rahoton ya kara da cewa tiyatar ta taimaka wajen daidaita bugun zuciyar sarkin, inda ta koma kamar yadda take a bay.

  Wannan shi ne karon farko da aka yi wa sarkin tiyata a zuciya. watan Fabrairun 2018, an yi Sarki Mohammed VI tiyata a wani asibit da ke birnin Paris.

  Mohammed VI ya hau gadon sarautaa shekarar 1999 bayan mahaifinsa Sarki Hassan II ya rasu sakamakon bugun zuciya.

  Sarki Mohammed VI
  Image caption: Wanne ne karo na biyu da aka yi wa Sarki Mohammed VI tiyata a zuciya
 20. Gwamnatin Buhari 'ta gaza kare rayukan 'yan Najeriya'

  Kungiyar kare hakkin Dan adam ta Amnesty International ta ce gwamnatin Najeriya ta gaza kare rayukan 'yan kasar a yayin da matsalar tsaro take ci gaba da yin kamari musamman a arewacin kasar.

  A sanarwar da kakakin Amnesty International, Malam Isa Sanusi, ya aike wa manema labarai ranar Litinin, kungiyar ta ce "Rashin tsaro yana ci gaba da watsuwa a wani bangare na arewacin Najeriya; Katsina, Kaduna, Borno, Benue da wani yanki na jihar Niger, inda 'yan bindiga suke kashe mutane kullum, sannan su sace wasu, lamarin da ya jefa fargaba a zukatan mazauna kauyuka.

  "Gazawar hukumomi wajen daukar matakin da zai kawo karshen wadannan hare-hare ta sa 'yan bindigar na cin karensu babu babbaka a wasu jihohin, kuma wannan lamari yana ci gaba da ta'azzara," in ji Amnesty International.

  Kungiyar ta kara da cewa wadannan hare-hare sun sanya mazauna yankunan sun bar komai a hannun Mahalicci, inda kullum suke kwana su kuma tashi suna fargabar kai musu hare-hare.

  Amnesty International ta nanata kira-kirayen da take yi wa gwamnati da ta mayar da kare rayukan jama'a ya zama babban abin da ta sanya a gaba.

  Rahotanni sun nuna cewa makon da ya gabata kadai 'yan bindiga da mayakan Boko Haram sun kashe mutum kusan 200 a hare-haren da suka kai jihohin Katsina da Borno.

  Buhari