Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nasidi Adamu Yahaya, Buhari Muhammad Fagge da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

 1. Rufewa

  A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da suka shafi Najeriya da sauran sassan duniya da muke farawa tun safe.

  Kuna iya komawa kasan shafin don karanta wadanda aka wallafa a baya. Sai kuma gobe da safe idan Allah Ya kai mu za mu zo muku da wasu sabbain labaran.

  A madadin wadanda suka yi ta wannan aiki tun safe kamar Nasidi Adamu Yahaya da Buhari Muhammad Fagge, Halima Umar Saleh ke fatan Allah ya ba mu alkahirinSa.

 2. Za mu iya magance fashi da makami da ta'addanci - Fadar shugaban Najeriya

  Buhari

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zanga-zangar da ake yi don nuna adawa da kashe-kashen da ke faruwa a arewacin Najeriya na iya ɓata ayyukan da sojoji ke yi a yankin.

  A wata sanarwa da fadar gwamnatin kasar ta fitar a ranar Talata mai dauke da sa hannun mai taimaka wa Shugaba Buhari kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban ya yi kira ga al'ummar jihar Katsina da kar su fitar da rai kan sojoji wadanda ake da yakini a kansu shekaru da dama da suka wuce na yadda suke shawo kan rikice-rikice.

  Sanarwar ta kuma bai wa 'yan kasar tabbacin cewa dakarun sojinta za su iya magance matsalar fashi da makami da ta'addanci, inda ta ce a kara hakuri ana daukar matakan da suka dace na kare rayukan 'yan kasar.

  Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Talatar da safe wasu kungiyoyi da dama suka fatsama kan tituna a birnin Katsina da ke arewacin Najeriyar inda suka yi kira a dauki mataki game da kashe-kashen da ke faruwa a yankin.

  Shugaba Buhari ya kuma bai wa al'ummar jihar Katsina hakuri da neman su bayar da goyon baya ga ayyukan soji da ke faruwa a jihar.

  Ku karanta cikakken labarin a nan.false

 3. An bukaci yin bincike kan kisan gillar da aka yi wa sojojin Libiya

  Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta bukaci da a gudanar da bincike a kan wasu kashe-kashe na gilla da azabtarwa da aka yi wa sojojin gwamnatin Libya wadda duniya ta amince da ita, a Tripoli.

  A sanarwarta ta baya-bayan nan ga manema labarai Human Rights Watch ta ce ta ga shaidu na hoton bidiyo da aka sanya a shafukan intanet, na wadannan laifuka da ake zargin mayakan bijirarren Janar din nan Khalifa Haftar sun aikata, a lokacin da suke fafutukar kwace babban birnin Libyar.

  Tuni dai dakarun Janar din suka ja baya, bayan shafe sama da shekara daya suna yaki.

 4. Labarai da dumi-dumiKotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban APC

  Adams Oshiomhole

  Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Najeriya ta tabbatar dakatar da Adams Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar APC, saboda rashin kwararan hujjoji.

  Kotun ta tabbatar da wannan hukuncin ne a ranar Talata, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

  A watan Maris ne wata babbar kotu a Abuja, babban birnin kasar ta bayar da umarni dakatar da Oshiomhole a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

 5. Coronavirus: Iyaye sun daɗe ba su ga jaririn da suka ba da hayar haihuwarsa ba

  Har yanzu a Ukraine ana ci gaba da kokarin sada jarirai da iyayensu, wadanda matan da aka bai wa hayar haihuwarsu ke haifa.

  A watan da ya gabata jami'ai sun ce wajen yara 100 ne iyayensu ba su samu ganin su ba a Kyiv, bayan da matakan kullen cutar korona suka hana iyayen na ainihi yin bulaguro a fadin duniya.

  Amma a yanzu wasu kasashen sun dage takunkuman don haka iyaye na samun damar ganin 'ya'yansu.

  Latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:

  Video content

  Video caption: Coronavirus: Iyaye sun daɗe ba su ga jaririn da suka ba da hayar haihuwarsa ba
 6. Coronavirus: Lagos ta ɗage lokacin bude masallatai da coci-coci

  Lagos mosque

  Gwamnatin jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriyata ta ce ta dage lokacin da za a bude majami'u da masallatai har zuwa wani lokaci a nan gaba.

  Gwamnan jihar Babajide Olusola Sanwo-Olu ya ce an yanke hukuncin hakan ne sakamakon yadda ake samun karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar korona a jihar.

  A baya dai gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar bude masallatai da majami’u a ranakun 19 da 21 na wanann wata.

 7. Shugaban Mali zai fara tattaunawar kafa gwamnatin hadin gwuiwa

  Ibrahim Boubakar Keita

  Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keita ya bayyan cewa zai fara tattaunawar kafa gwamnati hadin gwuiwa.

  Mr Keita na fuskantar matsin lamba ta fuskar siyasa, saboda tabarbarewar tsawo a Mali da kuma matsin tattalin arziki.

  Ko a farkon watan nan dubban mutane sun fantsama kan tituna a karkashin wata jam'iyyar hadaka, inda suke kira ga shugaban ya yi murabus.

  Masu hasashe sun ce kawo yanzu ba a iya gano ko batun kafa gwamnatin hadin gwuiwar zai dakatar da boren da wani mai fada a ji Mahmoud Dicko ya shirya ba.

 8. Indiya ta ce an kashe mata sojoji 20 a fadanta da China a kan iyaka

  Rahotanni daga Indiya na cewa kawo yanzu an kashe sojojin kasar 20, a wani kazamin fada tsakaninsu da na China a ci gaba da rikicin kan iyaka.

  Ita ma kafar yada labaran China ta ce sun samu asarar rayuka duk da ba ta yi wani karin bayani ba.

  Wakilin BBC ya ce ''China na ikirarin cewa sojojin Indiya sun ketaro musu kan iyaka ba bisa ka'ida ba, to amma akwai rahotannin da ke cewa tuni an fara zama kan teburin sulhu tsakanin manyan jami'an bangaroran biyu.''

  Wannan shi ne rikici mai muni da ya faru tsakanin kasashen biyu a cikin shekaru da dama.

 9. Trump ya sanya hannu kan dokar yi wa hukumar 'yan sandan Amurka sauye-sauye

  Trump

  Shugaba Trump na Amurka ya rattaba hannu kan dokar yi wa hukumar 'yan sandan kasar wasu sauye-sauye.

  Gyaran fuskar zai hada da samar da kudaden kara bayar da horo ga 'yan sanda, da kuma samar da hanyoyin sa ido kan irin cin zarafin da suke yi ga al'umma.

  Daga yanzu kuma jami'in tsaro ba zai sake cakumo wuyan wanda ake zargi ba idan har ba rayuwarsa ce a cikin hadari ba.

  Amurka ta fuskanci karin matsin lamba kan yin garambawul ga hukumar 'yan sandanta tun bayan kisan bakar fatar nan George Floyd da wani dan sanda farar fata ya yi.

 10. Wani jagoran addinin kirista dan Amurka ya amsa laifin lalata da kananan yara mata

  Gregory Dow

  Wani jagoran addinin kirista dan kasar Amurka ya amsa laifin lalata da kananan yara mata, a wani gidan marayu da ya bude shi da mai dakinsa a Kenya.

  A shari'ar da aka masa a wata kotu da ke Amurka, Gregory Dow ya amsa laifuka hudu na lalata da 'yan matan a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2014 a gundumar Bomet da ke Yammacin Kenya.

  Dama Mr Dow wanda ya fito daga jahar Philadelphia ya gudu Kenya a shekarar 2017 don kaucewa kamu, bayan da ya ji labarin cewa 'yan sanda na da masaniya a kan abin da ya aikata.

 11. Wuraren shan barasa a Zambia za su ci gaba da kasancewa a rufe

  AFP

  Shugaban Zambia ya ce ba zai ba da umarnin sake bude wuraren shan barasa ba da gidajen rawa duk da matsin lambar da yake fuskanta.

  Yanzu Zambia ta tabbatar da mutum 1,382 da suka kamu da Covid-19, cikin mutum 45,248 da aka yi wa gwaji. Kuma mutum 1,142 ne suka warke, cutar kuma ta kashe 11.

  Mista Lungu ya ba da umarnin rufe wuraren shan barasa ne da gidajen rawa watanni biyu baya, sakamakon karuwar masu dauke da cutar da ake samu.

  Ya kuma karbi shawarwari daga masana game da sake bude wuraren yana cewa har sai jami'an lafiya sun aminta da a yi hakan kafin a ba da umarnin.

 12. Magufuli ya yi alkawarin gudanar da zabe na gaskiya da adalci

  Shugaban Tanzaniya John Magufuli ya yi alkawarin ba da damar gudanar da zaben gaskiya da adalci a babban zaben kasar mai zuwa a watan Oktoba, wanda ya ke neman kasar tsayawa takara a karo na biyu

  Ya nemi 'yan siyasa da su kaucewa cin mutunci da kuma tayar da fitina yayin yakin neman zaɓe, lokacin da ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar kamar yadda kundin tsarin mulki ya bukata.

  Magoya bayan Magufuli na masa lakabi da "Bulldozer" suna ziga shi a matsayin shugaban da ya taimaka wajen kawo karshen matsalar cin hanci a cikin gwamnatin kasar.

  Masu sukar sa, suma na zargin sa da tauye 'yancin fadin albarkacin baki tun da ya karbi mulki a 2015.

  Karkashin shugabancinsa, kungiyoyin kare hakkin dan adam da 'yan jarida sun ta fuskantar barazana, wasu saboda suna yi masa shaguɓe.

  AFP
  Image caption: Shugaba John Magufuli zai kara tsayawa takara a karo na biyu
 13. Daidai take da kowa - Guardiola kan mutuwar mahaifiyarsa saboda korona

  getty

  Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi magana kan mutuwar mahaifiyarsa wadda ta kamu cutar korona.

  Dolors Sala Carrio ta mutu tana da shekara 82 a watan Afrilu 'yan makonni bayan Guardiola ya bayar da gudunmawar kudi fam miliyan daya dan a yaki cutar korona.

  "Yadda na dauka daidai take da kowa. Babu wani banbanci," In ji babban kocin wanda ya fito daga yankin Catalonia da ke Spaniya.

  "Duka wadanda muka rasa na da muhimmanci ga iyanlsu. shi yasa suke rayuwa da iyalansu tare, don su zama masu karfin hali."

 14. Coronavirus: An samu koma baya wajen karbar bashin banki a gabashin Afrika

  AFP

  Manyan bankunan Gabashin Afrika sun rage kudin ruwan da suke amsa domin karfafa gwiwar masu karbar bashi, sai dai dabarar ta tashi a kawai.

  Kamfanoni sun ja baya da karbar aro daga bankuna, saboda matsalar tattalin arziki da ake fuskanta a yankin, wadda dokar kulle ta janyo a wani mataki na shawo kan annobar korona.

  Bangaren bankuna a Gabashin Afrika na fuskantar koma baya wajen karbar bashi daga abokan huldarsa tun daga fara fuskantar matsalar lafiya a duniya.

  Matakan da aka dauka kamar na rufe iyakoki, da hana motocin safa-safa aiki ga kuma dokar dare, sun shafi harkokin kasuwanci tare da takaita yadda ake kashe kudi.

  Kenya da Uganda sun rage kiyasin kasafin kudinsu zuwa kashi 7 cikin 100.

  Ka zalika tsakanin watan Maris da Afrilu, darajar aron kudi daga bankin Uganda ta fadi da sama da kashi biyu cikin uku zuwa $132,000.

  Bankunan kasashen gabashin Afrika suna da dinbin garin kudi a kasa, kuma hada-hadar da suke yi ta bayar da bashi wadda ke kawo musu riba sosai ta tsaya cik.

 15. Instagram zai wuce Twitter wajen samun labarai

  Getty

  Wani bincike ya gano cewa shafin sada zumunta na Instagram da aka fi amfani da shi wajen wallafa hotuna yana dab da wuce shafin Twtter a matsayin wani waje na samun labarai.

  Binciken na kamfanin dillancin labarai na bangaren Reuters Institute Digital News na 2020 ya gano cewa amfani da Instagram domin yada labarai ya ninka sau biyu tun daga 2018.

  Yadda matasa ke yayinsa ya nuna samun daukakarsa. Wanda hakan ke cewa kusan kashi daya cikin hudu na 'yan shekara 18 zuwa 24 na amfani da Instagaram a matsayin wajen samun labaran da suka shafi korona.

  Sai dai kafafen sada zumunta na cikin wuraren da ake samun labarai marasa tushe.

  Kaso 26 ne cikin 100 kawai suka ce sun amince da kafafen sada zumunta wajen samun labaran da suka shafi Covid-19.

  Irin wannan kason sun ce sun amince da mahajojin hira da abokai wajen samun labarai kamar su Facebook Messenger da WhasApp.

  Amma gwamnati ta ce kafafen yada labarai sun samu amincewar mutane da kimanin kaso 59 cikin 100 idan aka kwatanta da na sada zumunta.

  Amma Instagram yanzu na samun kusan kashi uku na wadanda suka amsa bayanai lokacin wannan binciken, kuma da kashi biyu cikin uku na 'yan kasa da shekara 25.

  Kuma kashi 11 cikin 100 cikinsu na amfani da shi ne wajen samun labarai, wanda yanzu ya zarce Tiwita da digo daya.

  BBC
 16. An fara gudanar da bincike kan kamfanin Apple

  Apple Logo

  Tarayyar Turai ta fara gudanar da bincike har kashi biyu kan zargin kamfanin fasaha na Apple da bijirewa wasu dokokinta.

  An shigar da kara kan Apple da bijirewa wasu ka'idojin kasuwanci a Tarayyar Turai, da suka hada da salon yadda kamfanin ke sayar da kaya a shagonsa na intanet wato Apple Store.

  Ana kuma zargin Apple da kin biyan kaso 300 da kamfanonin fasaha ke biya ga manhajojinsu, da kuma boye kayan da ke da araha ga masu shiga Apple Store din.

  Masu shigar da koken sun kuma koka kan yadda kamfanin ya hana abokan hamayya amfani da manhajar biyan kudinta na Apple Pay.

  To amma Apple ya nuna takaicin yadda Tarayyar Turai ta aminta da abin da ta kira koke marar tushe da abokan hamayya suka shigar.

 17. Koriya Ta Arewa ta tayar da bam a ofishin hadin gwiwarta da Koriya Ta Kudu

  Koriya

  A wani martani bayan tayar da wasu abubuwa masu kama da bama-bamai a kan iyakarta, Koriya Ta Kudu ta gargadi makwabciyarta ta Arewa, da ta kwana da shirin cewa za ta mayar da martani idan ta ci gaba da tsokanar ta.

  A wani taron gaggawa da ta kira, majalisar tsaron kasar ta ce take-taken Koriya Ta Arewa ya nuna cewa ba ta bukatar zaman lafiya a yankin Korean Peninsula.

  Wakiliyar BBC ta ce a da hankali da Koriya Ta Arewa ke yi a yankin Korean Peninsula ba mamaki wata dabara ce take son yi ta ganin ta jawo Koriya Ta Kudu da Amurka kan teburin sulhu.

  Tun da farko Koriya Ta Kudun ta ce tana aiki da Amurka wurin lura da irin karfin soji da makwabciyar take kokarin nunawa da kuma barazanar da take musu.

  Mai magana da yawun gwamnati ya bukaci gwamnati a Pyongyang da ta martaba yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2018.

 18. Akwai alamun nasara kan samun maganin cutar korona a Burtaniya

  Wani gwaji da aka gudanar a Burtaniya ya nuna alamun nasara kan samun waraka ga masu cutar Korona.

  Bincike ya gano cewa maganin dexamethasone yana taimakawa wurin yakar cutar musamman ga wadanda ta yiwa mugun kamu.

  An gano cewa maganin na tasiri sosai ga wadanda ma ke amfani da na'urar taimaka wa numfashi wato ventilator.

  Masu bincike a Jami'ar Oxford sun ce wannan babbar nasara ce, kuma dama Dexamethasone na daga cikin magungunan da ake sa ran su taimaka wurin samar da riga-kafin cutar ta korona.

  Wakiliyar BBC ta sashen lafiya ta ce wannan gagarumar nasara ce aka samu ta hanyar Dexamethasone, idan aka yi la'akari da yadda cutar ke mummunar illa ga wasu da yada da kisa nan take.

 19. Naira Marley: Jirgin da ya kawo mawakin Abuja ya bai wa gwamnati hakuri

  Wani kamfanin jirgi a NAjeriya ya bai wa ministan zirga-zirgar jiragen sama hakuri kan kai fitaccen mawakin nan Naira Marley Abuja da ya yi daga Legas a ranar Asabar, don gudanar da wata kalankuwa.

  Ministan ya dakatar da Kamfanin na Executive Jet kan abin da ya kira yin zirga-zirgar da ba ta zama ta wajibi ba wanda hakan kin bin umarnin gwamnati ne da ta sanya na dakile yaduwar cutar korona a kasar.

  A wata wasikar neman afuwa da ya tura wa ministan zirga-zirgar jiragen saman, shugaban kamfanin Sam Iwuajoku, ya ce an tanadi jirgin ne don bulaguron wani alkali a ranar Lahadi, wanda daga baya ya sauya shirin tafiyar tasa.

  A cikin wasikar Mr Iwuajoku ya ce ya bayar da umarnin tafiyar jirgin ne a ranar Asabar bayan da ya ga sunayen fasinjojin kuma ya ga akwai wani minista a cikin jerin.

  ''Na ga sunan wani Fashiola Babatunde, na zaci Ministan Ayyuka ne da jama'arsa, don haka sai muka yanke shawarar tafiyar jirgin saboda bai wa ministan dama, ban san cewa taron mashiririta ba ne,'' a cewar Mr Iwuajoku said.

  Fitaccen mawakin kasar Azzez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, na daga cikin wadanda jirgin ya dauka har.

  Wata kafar yada labarai ta wallafa wasikar ban hakurin da kamfanin ya aike wa ministan a shafinta na Twitter:

  View more on twitter
 20. MDD ta cire sunan Saudiyya daga jerin sassan da ayyukansu ke cutar da ƙananan yara

  Yemen War

  Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun soki Majalisar Dinkin Duniya MDD kan cire Rundunar sojin hadaka da Saudiyya ke jagoranta da ta yi daga jerin wasu sassa da ayyukansu ke cutar da ƙananan yara.

  A wani rahoto tun farko da MDD ta fitar, ya gano yadd dakarun taron dangin suka hallaka ko jikkata ƙananan yara fiye da 200 a bara a yakin da take da mayakan Houthi a Yemen.

  Babban Sakataren Majalisar, Antonio Guterres ya ce an samu matuƙar raguwar mutanen da ke mutuwa ko jikkata saboda hare-hare ta sama.

  Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun soki Mista Guterres da banzatar da hujjojin da suke nuna keta hakkoki da aka yi.

  Yaƙin da aka shafe shekara biyar ana wanda ya daidata Yemen, ya yi sanadin mutuwar nutun 100,000, ya kuma jawo mutane sun shiga halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi mafi muni da aka taba samu a duniya.