Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Direbobin dakon mai sun janye yajin aiki a Najeriya

  Direbobin da ke dakon man mai daga jihar Legas sun janye yajin aikin da suka shiga bayan tattaunawa da gwamnatin jihar.

  Ƙungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG ta janye yajin aikin ne da yammaci Litinin ranar da ta ce za ta tsunduma cikin yajin aiki saboda matsalolin rashin kyan hanya, bata gari da takurar jami'an tsaro a kan hanya.

  Wakilin BBC a Legas ya ce ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawar da shugabannin ƙungiyar suka yi da ɓangaren gwamnati.

  Gwamnati kuma ta yi alƙawarin diba buƙatunsu tare da magance su.

 2. Yadda aka bude makarantu a Kano

  Daliban da ke ajin karshe a makarantun sakandare a jihar Kano a Najeriya suka koma makarantu don rubuta jarabawar kammala sakandare.

  Ga bidiyon yadda aka buɗe makarantun a Kano da kuma matakan da aka ɗauka.

  Video content

  Video caption: Yadda aka bude makarantu a Kano
 3. Boko Haram za ta ci gaba da yin ɓarna – Idriss Deby

  Shugaban Chadi

  Shugaban Chadi Idriss Deby ya ce za a ɗauki lokaci kafin kawo ƙarshen ayyukan Boko Haram a yankin tafkin Chadi.

  Shugaban ya shaida wa wata kafar yaɗa labaran Faransa cewa ya yi nasarar kakkaɓe Boko Haram a Chadi a lokacin da ya shiga gaba domin yaki da ƙungiyar amma kuma ya ce za a ci gaba da fama da ayyukan ƙungiyar a yankin.

  Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai kama shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ba, sai ya ce ba ya tafi yaƙi ba ne da burin kama wani ɗan Boko Haram illa ya kakkabe ƙungiyar baki ɗaya.

  “Boko Haram har yanzu tana da sauran kwanaki kuma za ta ƙara yin ta’adi,” inji shugaba Deby.

  Shugaban wanda aka bayyana a matsayin Mashal ya kuma ce akwai ɓaraka daga rundunar hadin guiwa da aka kafa wanda ya sa har yanzu aka kasa magance rikicin Boko Haram.

 4. An yi ɓarin wuta a gidan yarin Mogadishu

  Gidan Yarin Somalia

  Hukumomi a Somalia sun ce mutum 10 sun mutu yayin harbe-harben bindiga da fursunoni suka yi a cikin babban gidan yarin ƙasar da ke birnin Mogadishu.

  Ma’aikatar watsa labaran kasar ta ce an kashe fursunoni shida mambobin ƙungiyar Al Shabab da kuma wasu jami’an kula da gidan yarin guda huɗu.

  Rahotanni sunce wani daga cikin ƴan gidan yarin ne ya kwaci ƙaramar bindiga daga jami’in gidan yarin daga nan kuma sauran fursunoni suka abka wurin da ake ajiye makamai.

  An dai tura kwararrun jami’an ƴan sanda da suka yi ƙoƙarin kwantar da rikicin wanda ake ganin wani yunƙuri ne ƙoƙarin ɓallewa daga gidan yarin.

 5. Jifan shugaban kasa ya janyo wa wasu ɗaurin shekaru 30

  Wata kotu a Burundi ta ɗaure wasu shekaru 30 da suka ƙunshi maza biyu da mace ɗaya saboda sun jefi ayarin shugaban kasa.

  Kotun ta kama su da laifin yunƙurin halaka shugaba Evariste Ndayishimiye.

  An zarge su da jifan ayarin shugaban da duwatsu lokacin da ya ziyarci lardin Kayanza da ke arewacin kasar a Larabar da ta gabata.

  Mai gabatar da ƙara ya nemi a yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru bakwai saboda jifa da duwatsu, yayin da kuma kotu ta ce ta kama su da laifin yunkurin halaka shugaban tare da yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru 30.

  A wannan watan ya kamata a rantsar da shugaba Evariste Ndayishimiye bayan ya lashe zaben da aka gudanar watan Mayuamma aka rantsar shi a watan Yuni saboda mutuwar shugaba Pierre Nkurunziza da ya gada.

  Shugaban Burindi
 6. Najeriya za ta ware mako ɗaya don ƙarfafa saka takunkumi

  Gwamnatin Najeriya ta ce saboda har yanzu ba a samu rigakafin cutar korona ba dole ta dogara da matakai na kariya kamar amfani da takunkumi.

  Ministan lafiyar ƙasar yayin da yake bayani kan halin da ake ciki game da matakan da gwamnati ke ɗauka game da cutar korona ya ce za su ƙarkafa amfani da takunkumi tsakanin ranar bakwai zuwa 14 ga watan Agusta da za a yi bikin mako ɗaya kan amfani da takunkumin a duniya.

  View more on twitter
 7. Yara 97,000 sun kamu da korona cikin mako biyu

  Shugaba Trump

  Wani binciken wata asibitin yara a Amurka ya ce aƙalla yara 97,000 suka kamu da cutar korona tsakanin mako biyu a watan Yuli.

  Binciken ya nuna ƙaruwar yaduwar cutar ga yara kanana da kashi 40 a sassan Amurka yayin da wasu jihohin kasar suka fara buɗe makarantu.

  Yadda malamai da ɗalibai suka kamu da rashin lafiya ya tilasta aka sake rufe wata makaranta a Georgia. Kuma yaro ɗan shekara bakwai shi ne mafi ƙanƙantar shekaru da cutar ta kashe a Amurka.

  Rahoton na zuwa a yayin da shugaba Trump ke ci gaba da nanata cewababu yadda za a yi ace yara sun kamu da cutar duk da hujjojin da ke nuna cewa ba gaskiya ba ne.

 8. Gwamnatin Lebanon ta yi murabus

  Gwamnatin Lebanon ta yi murabus sakamakon fushin jama’a kan fashewar da aka samu ranar Talata da ta ɗaiɗaita wasu sassa na birnin Bierut tare da kashe sama da mutum 200.

  Firaministan kasar ne Hassan Diab ya sanar da matakin a jawabin da ya gabatar wa ƴan kasar ta kafar talabijin ranar Litinin.

  Yawancin ƴan kasar dai na zargin shugabannin Lebanon da gazawa da kuma yin ko oho da matsalar rasha.

  Tsawon kwanaki biyu aka ɗauka mutane na zanga-zanga kan fashewar.

  Shugaban kasar ya ce wasu tarin makamai ne da aka ajiye ba bisa ka’ida ba a tsawon shekaru ne suka haifar da fashewar.

 9. Dakarun Faransa sun shiga farautar ƴan bindiga a Nijar

  Sojojin Faransa tare da haɗin guiwar na Nijar sun shiga farautar ƴan bindigar da suka kashe Faransawa ma'aikatan agaji guda shida da suka kashe tare da mai masu jagora da kuma direba.

  Kungiyar agaji ta Acted a Faransa ta yi allawadai da kisan wanda ta bayyana a matsayin rashin imani.

  Ƴan ta'adda sun daɗe suna kai hare-hare a Nijar da makwabtanta Mali da Najeriya da kuma Burkina Faso

  An ga mota ƙirar 4x4 da aka kone a kusa da inda aka kai harin.
 10. Rasha ta ci tarar Google kan bayanan da aka haramta

  Kafafofin yaɗa labarai sun ce wata kotu a Moscow ta ci tarar kamfanin Google sama da dala dubu ashirin saboda kasa toshe bayanan da aka haramta a Rasha.

  Karo na uku kenan da ake cin tarar kamfanin na Amurka a cikin shekaru uku kan aikata laifin.

  A tsarin dokar Rasha, wajibi ne duk wani shafin bincike ya kasance ya bi tsarin gwamnati da zai bayar da shawara kan shafukan da aka haramta a Rasha.

 11. Yadda ɗalibai suka koma karatu a Kano

  Daliban da ke ajin karshe a makarantun sakandare a jihar Kano a Najeriya da ma wasu jihohi a kasar suka koma makarantu don rubuta jarabawar kammala sakandare.

  Gwamnatin jahar ta ce ta gudanar da feshi tare da samar da dukkan kayan kare kai daga kamuwa da cutar korona a tsakanin daliban a makarantu sama da 500 da ke jahar kuma tana sa ran dalibai sama da 25,000 ne za su zauna jarabarwar WAEC da za a fara a mako mai zuwa.

  Dalibai sun koma karatu a Kano
  Dalibai sun koma karatu a Kano
  Dalibai sun koma karatu a Kano
  Dalibai sun koma karatu a Kano
 12. Abin da gwamnonin arewa maso gabas suka tattauna da Buhari

  Gwamnonin arewa maso gabas

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin shiyar arewa maso gabas da kuma manyan hafsoshin soji a fadarsa a yau Litinin.

  Daga cikin gwamnonin da suka yi ganawar da Shugaba Buhari sun haɗa da Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum, da gwamnan Adamawa Alhaji Amadu Umar Fintiri da gwamnan Bauchi, Alhaji Bala Mohammed da gwamnan Gombe Alhaji Inuwa Yahaya.

  An kuma yi taron ne tare da Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da mai ba shugaban kasa shawara kan sha'anin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma sakataren gwamnati Boss Mustapha.

  Babban hafsan sojan kasa Janar Tukur Yusuf Buratai ya halarci taron da kuma Janar Abayomi Olonisakin, da ministan kula da sha'anin ƴan sanda Alhaji Muhammad Dingyadi.

  Bayan ganawar Gwamnan Borno Farfesa Zulum ya shaidawa manema labarai cewa sun tattauna ne da shugaban kan muhimman ƙalubalen da yankin yake fama da su musamman matsalar tsaro da taɓarɓarewar abubuwan more rayuwa da kuma batun haƙo man fetir a yankin.

  An yi ganawar ne bayan zargin zagon ƙasa da gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya yi wa rundunar sojin Najeriya saboda harin da ƴan Boko Haram suka kai wa tawagarsa kusan mako biyu da suka gabata. Ko da yake hukumomin sojin Najeriya sun ce suna bincike bayan yin allawadai da al'amarin.

  Gwamnonin arewa maso gabas
  Gwamnonin arewa maso gabas
  Gwamnonin arewa maso gabas
 13. Afghanistan za ta saki ɗaruruwan ƴan Taliban

  Jami'ai daga gwamnatin Afghanistan sun ce shugaban ƙasar Ashraf Ghani ya amince da dokar sakin ƴan Taliban 400 da ake tsare da su.

  Ana ganin sakinsu mataki ne da zai buɗe kofar soma tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarorin biyu a birnin Doha.

  Tuni gwamnatin ta saki kusan fursunonin Taliban 500 amma tana ɗari-ɗari da sakin sauran waɗanda ake zargi da aikata miyagun laifuka.

  A ranar Lahadi ne taron majalaisar ƙoli ta Jirga ta amince da sakinsu.

  Taron Jirga
 14. Nijar na farautar ƴan bindigar da suka kashe Faransawa

  Shugaban Nijar

  Hadin guiwar dakarun Nijar da na kawance na ci gaba da farautar ƴan bindigar da suka yi wa Faransawan shida da wasu ƴan Nijar biyu kisan gilla.

  Duk da ba wani ƙarin bayani da ya fito daga hukumomin ƙasar amma shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou a shafinsa na Twitter ya yi alawadai da faruwar wannan lamari.

  Ga rahoton da wakiliyar BBC a Nijar Tchima Illa Issoufou ta aiko.

  Video content

  Video caption: Rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai.
 15. Waɗanda suka kamu da korona za su kai miliyan 20 a duniya

  Cutar korona

  Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kasashe za su iya sake bude harkokin yau da kullum matukar za su kiyaye sharuɗɗan kaucewa bazuwar cutar korona.

  Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce ana sa ran cikin makon nan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar za su kai miliyan 20, waɗanda cutar ta kashe kuma za su kai kwatar miliyan.

  Shi ma babban jami'in hukumar Michael Ryan ya ce cutar babu ruwanta da lokaci, idan ba a dauki mataki ba za ta sake dawowa da karfi. Dr Maria van Kekhove da ke jagorantar yadda WHO ke tafiyar da cutar ta ce dole kowa ya bada gudunmawarsa wajen daƙile ta.

  Ta ce idan an ce a zauna a gida to a zauna, amma idan ta kama dole a fita lallai a bi ƙa'idar da aka shimfida.

  sannan idan an umurci a sanya takunkumi a wuraren taron jama'a da kantuna don sayayya to ku a wannan doka.

  Amurka da Brazil da India ne kasashen da cutar ta fi yin ƙamari inda suke da rabin waɗanda suka kamu a duniya.

 16. Hukumar NDLEA ta kama mutum 205 masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Abuja

  NDLEA

  Hukumar Hana Sha da fataucin Miyagun ƙwayoyi ta NDLEA reshen birnin Abuja ta ce ta kama mutum 205 masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi daga watan Janairu zuwa Yulin 2020.

  180 daga cikinsu maza ne sai kuma mata 25.

  Shugaban hukumar na Abuja, Lawan Hamisu ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na NAN ranar Litinin cewa sun ƙwace ƙwaoyi da suka kai nauyin 3,546.632 a wannan tsakanin.

  Ƙwayoyin da aka ƙwace sun haɗa da ganyen wiwi da hodar ibilis da ƙwayar Tramadol da Exol da Rophynol da Diazepam.

  Ayyukan hukumar sun ragu a watan Afrilu sakamakon dokar kulle da ake ciki a Abuja, a cewar Lawan Hamisu.

  "Wannan dalilin ne ya sa adadin waɗand aka kama suka ragu amma duk da haka abin ba mai daɗin ji ba ne."

 17. Mutum ɗaya ya mutu a Ghana yayin rajistar zaɓe

  Ghana

  Rikici a tsakanin magoya bayan jam’iyyar siyasa a Ghana ya haifar da mutuwar mutum ɗaya, mutum biyu kuma suna cikin mawuyancin hali a lokacin jefa jefa kuri’a na gwaji.

  Wanda ya mutu ya rasu ne bayan harsashin bindiga ya same shi a lokacin hargitsin da ya faru saboda matsaloli dangane da rajistar zaɓen.

  Kazalika harbin bindiga da jami’an tsaro suka yi domin tarwatsa masu hatsaniyar ya kashe mutun ɗaya.

  'Yan sandan Ghana sun kama mutum uku a kan tashin hankalin da ya bata rajistar masu Jefa kuri’a a mazaɓar Dormaa ta Yamma.

 18. Direbobin dakon man fetur sun tsunduma yajin aiki a Najeriya

  tankers Nigeria

  Direbobin da ke dakon man fetur daga jihar Legas sun tsunduma yajin aiki a yau Litinin saboda wasu dalilai da suka ce gwamnati ta gaggara magance mu su.

  A ranar Juma'ar da ta gabata kungiyar kwadago ta ma'aikatan dakon man fetur da iskar gas NUPENG, ta ce za ta dakatar da ayyukanta a Legas da sauran yankuna saboda matsalolin rashin kyan hanya, bata gari da takurar jami'an tsaro a kan hanya.

  Kungiyar ta ce wannan yanayi ya haifar da kunci da jefa damuwa tsakanin direbobin da ke dakon mai zuwa jihohi tsawon watannin yanzu, duk da korafin da suka sha gabatarwa mahukunta.

  Shugaban masu gidajen mai na kasa, Bashir Dan Mallam, ya shaida wa BBC cewa idan direba ya yi lodi sai ya kashe sama da dubu 100 wajen sallamar jami'an tsaro wanda hakan kuma gaskiya na shafar ayyukansu.

 19. An gano yadda ma'aikatan asibiti ke sayar da kayan kariya na cutar korona a Ghana

  coornavirus test

  Wani bincike da sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye ya gudanar ya nuna cewa wasu ma'aikata a asibitocin ƙasar Ghana suna sayar da kayan kariya daga cutar korona don samun makudan kuɗaɗe.

  Fiye da ma'aikatan kiwon lafiya 2,000 ne a ƙasar suka kamu da cutar korona, tun bayan ɓarkewar cutar.

  Ghana ta fuskanci ƙarancin kayan aikin kariya kamar takunkumi fuska.

  Ɗan jarida Anas Aremeyaw Anas ya yi shigar burtu don gano yadda wasu ke saka rayuwar abokan aikinsu cikin haɗari domin samun kuɗi.

  Anas Aremeyaw ya shaida jana'izar wani likita da ya mutu sakamakon cutar korona a kasar Ghana kuma mutane sanye da kayan kariya tun daga sama har ƙasa su ne ke aikin binne gawar, sannan kuma masoya da 'yan uwa ɗauke da furanni sun tsaya daga nesa.

  Dr. Adu wani abokin aikin mamacin ne. Ya ce: "Babban likita ne mai ƙwazo. Mutuwarsa babbar hasara ce sosai ga asibitin da kuma Ghana baki ɗaya."

  Fiye da likitoci 200 ne a Ghana suka kamu da cutar korona. Kullum ma'aikata na cikin kukan rashin isassun kayan kariya.

  Lokacin da cutar korona ta ɓulla a kasar, gwamnati ta umarci asibitoci da su nemi kayan kariya daga cutar ta korona adadin da suke buƙata.

  Ƙasar ta dogara ne wajen samun dubban kayan aiki daga masu bayar da tallafi, ciki har da tsohon shugaban kasar John Mahama.

  Ku karanta cikakken labarin a nan.

 20. Kalaman Dizeani kan 'yan yahoo-yahoo sun jawo mata tsana a Najeriya

  Diezani

  Yan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta na ta ce-ce-ku-ce kan tsohuwar ministar man fetur ta ƙasar Diezani Alison-Madueke.

  Hakan ya biyo bayan wani bidiyo ne da ya ɓulla tana Allah-wadai da 'yan zambar intanet waɗanda ake kira yahoo-yahoo, inda ta ce 'yan Najeriya suna dogara da su.

  Wasu na sukarta cewa ita ma kanta tana fuskantar shari'a game da cin hanci da rashawa amma kuma take da bakin magana.

  Wani mai suna Dr. Dípò Awójídé (@OgbeniDipo) ya ce: "Wadda ke gudun shari'a ce ta samu bakin magana saboda babu wasu tsauraran hukunci kjan satar kuɗin Najeriya.

  View more on twitter