Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Nabeela Mukhtar Uba

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibiyarmu, muna godiya da kuka kasance da mu a yau kuma a nan za mu dakata da kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

  Da fatan za ku kasance da mu gobe, Laraba inda za mu ci gaba da kawo maku labarai kai tsaye kan abubuwan da suka shafi Najeriya da makwabtanta da ma sassan duniya.

  Mu wayi gari lafiya.

 2. Rasha ta yi kutse a zaɓen Amurka na 2016 – Majalisar Amurka

  Kwamitin kula da harkokin leƙen asiri na Majalisar dattijai ta Amurka ya ce Rasha ta ta yi kutse a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a shekarar 2016 a madadin Donald Trump.

  A cikin wani rahoto da aka wallafa bayan shekaru uku da rabi da bincike, kwamitin da ya ƙunshi yan jam'iyyun Republicans da Dimokrats ya ce shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen na Donald Trump wato Paul Manafort ya ba wasu jami'an Rasha bayanai a kan yawan Amurkawa da su ka yi rajistar zaɓe.

  Sai dai kwamitin ya kasa cimma matsaya a kan ko kwamitin yaƙin neman zabe na Donald Trump ya aikata laifi wajan haɗa kai da Rasha domin masu zabe su kaɗa kuria ga wani dan takara.

  Amma kwamitin ya tabbatar da abubuwan da mai bincike na musaman wato Robert Mueller ya gano wanda shugaba Trump ya bayyana a matsayin bita da ƙullin siyasa

 3. Ronald Koeman ne sabon kocin Barcelona

  wasanni

  Ronald Koeman zai kasance sabon kocin Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona, in ji Shugaban Ƙungiyar Josep Maria Bartomeu.

  Koeman mai shekara 57 a duniya, wanda a yanzu shi ne yake jan ragamar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Netherlands, zai koma Barcelona cikin makon nan.

  Da ya ke jawabi a daren yau Talata, Bartomeu ya ce "Koeman shi ne zaɓinmu."

  Tsohon ɗan wasan Netherlands kuma ɗan wasan Barca Koeman ya je Barcelona yau Talata domin ƙarasa ƙulla yarjejeniya da ƙungiyar.

  Ana ta raɗe-raɗin cewa fitaccen ɗan wasan ƙungiyar Lionel Messi na iya barin ƙungiyar amma Bartomeu ya ce: "Na yi magana da Koeman kuma Messi shi ne ginshiƙin ƙungiyar.

  "Kwantiraginsa zai ƙare ne a 2021, na yi magana da Leo da mahaifinsa.

  "Shi ne gwarzon ɗan wasa a duniya. Babu shakka a tafiyar Koeman, muna sa ran ganin nasarori daga Messi."

  Amma shugaban ya ƙara da cewa ƙungiyar za ta sayar da 'yan wasanta.

 4. An sake ƙaddamar da gwajin maganin korona a Afirka ta Kudu

  Pumza Fihlani BBC News, Johannesburg

  korona
  Image caption: Afirka ta Kudu ce ke da yawan masu kamuwa da korona a nahiyar Afirka

  Afirka ta Kudu ta ƙaddamar da gwajin maganin annobar korona a karo na biyu.

  Za a yi gwajin maganin wanda kamfanin Amurka Novavax ya yi a jami'ar Witwaters.

  Farfesa Shabir Madhi na Jami'ar ya ce gwajin zai ƙunshi mutum 2,900 kuma zai taimaka wajen gano ko magungunan da aka yi gwajinsu a wasu wuraren zai yi aiki a Afirka.

  Ana gudanar da gwaje-gwaje a sassan duniya kuma ƙwararru na cewa akwai yiwuwar a samu magani nan da wata 12 zuwa 18 idan har komai ya tafi dai-dai.

  Gwajin maganin na Novavax shi ne na biyu a Afirka ta Kudu.

  A Nahiyar Afirka, Afirka ta Kudu ce ke da yawan masu kamuwa da korona.

  Yayin da bazuwar cutar ya ɗan ragu a 'yan makwannin nan, har ta kai ga an sassauta dokar kulle, masana harkar lafiya sun ce akwai fargabar a sake samun ƙaruwar masu fama da wannan cuta kamar yadda aka gani a wasu sassan duniyar.

  Gwamnatin ta yi kira ga jama'a su ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin hana hakan faruwa.

 5. Ecowas ta yi tur da boren sojoji a Mali

  Mali
  Image caption: Sojoji na rangadi bayan an jiyo ƙarar harbe-harbe a wani sansanin sojoji kusa da Kati a Bamako, babban birnin Mali.

  Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas ta yi tur da abin da ta kira tawayen sojoji a Mali inda ta buƙaci sojoji su koma sansaninsu.

  Wannan na zuwa ne bayan wasu harbe-harbe da aka yi cikin wani sansanin sojoji da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.

  Ecowas ta nanata rashin goyon bayanta ga duk wani yunƙurin sauyin mulki ba bisa tsarin doka ba a yayin da soji suka kama shugaban kasar.

  Tashin hankalin ya yi dai-dai da kiraye-kirayen zanga-zanga da 'yan hamayya ke yi ta neman Shugaba Ibrahim Boubkar Keita ta yi murabus.

  Jama'ar ƙasar dai na nuna fushinsu kan aka samu taɓarɓarewar tsaro da matsalar cin hanci da kuma rashin alkinta arzikin ƙasar.

 6. Buhari ya sake ganawa da Jonathan kan rikicin Mali

  Mali

  Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaba Goodluck Jonathan ɗazu a fadarsa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

  A watan da ya gabata ne Dr Jonathan ya jagoranci wata tawaga daga ƙungiyar ECOWAS domin ganawa da Shugaba Buhari kan rikicin siyasar da ke faruwa a Mali.

  Mai bai wa shugaba Buhari shawara kan kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad ne ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.

 7. 'Yan hamayya a Mali na neman sulhu

  Chi Chi Izundu West Africa Correspondent

  Mali

  Ɓangaren hamayya a ƙasar Mali na neman a yi tattaunawar sulhu domin warware rikicin da ya kunno kai bayan harbe-harben da aka jiyo a wani sansanin sojoji da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.

  "Babu wani zabi sai tattaunawa ....[Muna] neman maslaha kuma muna fatan za a warware lamarin ta hanyar shari'a kuma cikin tsari," in ji mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin June 5 Movement, Issa Kaou Djim.

  Ana tunanin a sansanin soji na Kati ne sojoji suka taɓa yin tawaye a shekarar 2012, lamarin da ya haifar da juyin mulki.

  Ofishin jakadancin Faransa da Norway da Sweden sun shawarci mutane da su yi zamansu a gida.

  Tun watan Yuni, dubban mutane suke gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya ajiye muƙaminsa.

  Sun zarge shi da jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani mawuyacin hali da matsalar cin hanci da kuma ƙin yin wani abu kan ta'addanci.

 8. Najeriya ta gayyaci jakadan Ghana don nuna ɓacin ranta

  Geoffrey Onyeama

  Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa sun gayyaci jakadan ƙasar Ghana domin shaida masa ɓacin ransu game da rufe shagunan 'yan kasuwar Najeriya da ake yi a Ghanar.

  Wannan ne yanƙuri na farko da ƙasashen biyu suka yi domin samar da mafita ta hanyar dipilomasiyya bayan Mista Onyeama ya ce za a ɗauki matakin gaggawa game da lamarin ranar Litinin.

  Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ya shaida wa BBC cewa suna sa ran kawo ƙarshen matsalar cikin gaggawa.

  Kizito Obiora ya ƙara da cewa shagunan 'yan Najeriya fiye da 100 aka rufe a birnin Accra.

  "Masu shagunan waɗanda mafi yawansu 'yan Najeriya ne, ba su da wani zaɓi illa su bar ƙasar tun da an rufe musu harkokin kasuwancinsu," in ji shi.

 9. Kotu ta samu ɗan Hezbollah da laifin kisan Rafik Hariri

  'Yan mintunan da suka wuce, wata kotu a Netherlands ta samu wani ɗan ƙungiyar Hezbollah da laifi a kisan tsohon firaministan Lebanon Rafik Hariri.

  Salim Jamil Ayyash na cikin mutum hudu da ake zargin suna da hannu a kisan marigayin shekara 15 da suka gabata.

  Sai dai alkalin kotun ta ce babu shaidar da ta nuna cewa shugabanin kungiyar ko gwamnatin Syria sun taka rawa a kisan Raik Hariri.

  Mai Sharia Janet Nosworthy ta ce shekaru sama da 15 kenan da aukuwar lamarin amma kawo yanzu wadanda lamarin ya shafa na cikin damuwa.

 10. 'Ƙasashen duniya na ta'azzara annobar korona saboda ɓangaranci'

  WHO

  Ƙasashen duniya na ƙara ta'azzara annobar korona ta hanyar saka muradansu a gaba domin samun allurar rigakafinta, kamar yadda shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya yi gargaɗi.

  Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana a wurin wani taro ta intanet: "Yin aiki tare tsakanin ƙasashen duniya ƙudiri ne da kowacce ƙasa za ta so ta cimma - babu wanda ya tsira har sai kowa ya tsira."

  "Ya kamata mu guji nuna ɓangaranci wurin samar da rigakafin," in ji shi.

  Ya ƙara da cewa ya tura da wasiƙa ga dukkanin mambobin ƙungiyar WHO yana roƙon su haɗa kai domin samar da rigakafin.

 11. Wace ce korona kuma! 'Yan Wuhan na shaƙatawarsu kafaɗa da kafaɗa

  Wuhan

  Dubban mutane sun taru kafaɗa da kafaɗa ba tare da takunkumin fuska ba, suna ta wasa da balam-balam din zama a cikin ruwa tare da yin shewa a wani bikin kaɗe-kaɗe.

  Ba wai shi ne hoto mafi shahara a 2020 ba, amma abu ne da ya ja hankali a karshe mako a birnin Wuhan, inda Covid-19 ta samo asali a bara.

  Wuhan

  Hotunan da aka wallafa ana bikin rakashewa a wurin shakatawar Maya Beach da ke Wuhan - alamomi da ke nuna wannan yankin ya fita daga kangin da duniya ta shiga na yaki da cutar korona - yanzu ya zama tarihi.

  Karanta cikakken labarin a nan:

 12. An yi harbe-harbe a kusa da sansanin soji a Mali

  Mali Army

  Wani mai magana da yawun rundunar sojin Mali ya tabbatar da cewa an yi harbe-harbe a cikin wani sansanin sojin da ke babban birnin kasar Bamako.

  Ofishin jakadancin Norway ya ce ya samu bayanai cewa dakaru suna kan hanyarsu ta zuwa babban birnin kuma ofishin jakadancin Faransa ya bayar da shawrar cewa mutane su zauna a gida.

  Hakan na zuwa ne a yayin da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta yake fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga mulki inda ake yin zanga-zangar adawa da shi.

  Ana ci gaba da samun fushi daga 'yan kasar kan munin da lamarin tsaro ke yi inda rikice-rikicen 'yan ta'adda da na kabilanci ke ta karuwa.

  Mutane suna kuma yin korafi kan karuwar cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki.

 13. Labaran Rana Cikin Minti Ɗaya

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari labarai cikin minti ɗaya
 14. Obama ya zaɓi waƙar Wizkid ta ‘smile’ a jerin wakokinsa na 2020

  Wizkid

  Tsohon shugaban ƙasar Amurka Barrack Obama ya zaɓi waƙar Wizkid mai suna ‘smile’ a jerin wakokin da ya fi saurara na shekarar 2020.

  Smile wadda matashi ɗan Najeriya Wizkid ya rera, na ɗaya daga cikin waƙoƙi 53 a jerin waƙoƙin na Obama.

  Sauran mawaƙan da ke cikin jerin su ne Beyonce da Rihanna da Nas da J. Cole da Nina Simone da Frank Ocean.

  Obama ya ce za a saka wasu wakokin a taron ƙasa na jam'iyyar Democrat na wannan makon da aka fara a daren Litinin.

  Tsohon shugaban ƙasar Amerika ya ƙaddamar da jerin waƙoƙin tun yana kan kujerar mulki a 2015.

  Za ku iya saurarar waƙar Smile idan kuka latsa hoton da ke ƙasa:

  View more on youtube
 15. An kuɓutar da 'yan Nijar 11 da Boko Haram ta shiga da su Najeriya

  Sojojin Nijar

  Dakarun ƙasar Nijar sun kuɓutar da wasu 'yan ƙasar guda 11 da ƙungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su kuma ta shiga da su Najeriya, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP.

  Yahaya Godi, sakataren gwamnatin Jihar Diffa mai iyaka da Najeriya ya shaida wa AFP cewa daga cikinsu akwai mata uku da yara huɗu kuma an kuɓutar da su ne a ɓangaren Najeriya na Tafkin Chadi.

  "Dakarunmu ne suka kubutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a kusa da Tafkin Chadi na ɓangaren Najeriya a kusa da wani sansanin Boko Haram," in ji Yahaya Godi.

  An sace mutanen ne ranar 11 da 12 na watan Agusta a ƙauyuka biyu na yankin Gueskerou, wata unguwa da ke ɓangren Nijar a yankin Tafkin Chadi.

  Tafkin Chadi ya ratsa ta ƙasashen Najeriya da Nijar da Chadi kuma ya zama wata matattarar 'yan Boko Haram da sauran masu iƙirarin jihadi.

 16. Dokokin da Najeriya ta saka wa fasinjojin jiragen ƙasa da ƙasa

  Jirgin sama

  Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa daga ranar 29 ga watan Agusta.

  Wata biyar kenan da rufe zirga-zirgar jiragen ƙasa da ƙasa a Najeriya sakamakon annobar korona.

  Sai dai ta saka wasu sharuɗɗa, waɗanda sai an cika su kafin fasinjoji su shiga ƙasar daga ƙasshen waje. Ga wasu daga cikinsu:

  • Sai an yi wa fasinjoji gwajin cutar kafin tashi a filin jirgi
  • Za a buɗe shafin intanet da matafiya za su biya kuɗin yin wani gwajin bayan kwana takwas da isarsu Najeriya
  • Fasinjoji za su cike takardun tambayoyi ta intanet sannan su miƙa ta ga hukumomin Najeriya bayan sun isa ƙasar
  • Saka takunkumin fuska
  • Bayar da tazara
  • Wanke hannu
  • Auna zafin jikin matafiya
 17. Amaechi zai sake bayyana a gaban 'yan majalisa kan kuɗin gina layukan dogo

  Rotimi Amaechi

  Ministan Sufuri a Najeriya zai sake bayyana a gaban wani kwamitin Majalisar Wakilai domin yi musu bayani kan bashin kuɗi da Najeriya ta karɓo daga China na gina layin dogo.

  A jiya Litinin ne Rotimi Amaechi ya fara bayyana a gaban kwamitin, inda suka tafka muhawara tare da jefa wa juna kalamai masu zafi game da sharuɗɗan da Najeriya ta yarda da su yayin ƙulla yarjejeniyar da China.

  'Yan majalisar sun zargi ministan wanda ya bayyana tare da jami'an ma'ikatar kuɗi da na hukumar kula da bashi ta ƙasa, da amincewa da sharuɗɗan da China ta kafa tun kafin saka hannu kan yarjejeniyar.

  Amaechi ya buƙaci 'yan majalisar su dakatar da binciken kan kuɗi fiye da naira biliyan 153 da China ta bayar a 2018, yana mai cewa binciken zai sa ƙasar ta jinkirta bayar da wani bashin nan gaba.

  Yanzu haka China na bin Najeriya bashin dala biliyan 3.1 - kwatankwacin fiye da naira tiriliyan ɗaya.

  'Yan Najeriya sun sha bayyana damuwa game da sharuɗɗan yarjejeniyar, waɗanda suka ce ana ƙoƙarin sayar da 'yancin Najeriya ga China.

 18. Italiya ta bai wa Tunusiya dala miliyan 13 don ta hana 'yan cirani shiga ƙasarta

  Tekun Baharrum ko kuma Mediterranean

  Gwamnatin Italiya ta ce ta bai wa ƙasar Tunusiya dala miliyan 13 - kwatankwacin naira biliyan biyar - domin tallafa wa ƙasar wurin ƙarfafa tsaron gaɓar ruwanta.

  Ta bayar da tallafin ne da zummar hana 'yan cirani tsallakawa Tekun Baharrum ko kuma Mediterranean zuwa cikin Italiya.

  Yayin wata ziyara a birnin Tunis, Ministan Harkokin Wajen Italiya, Luigi Di Maio ya ce ƙasarsa ba ta da sauran wuri ga 'yan cirani da ke shiga ta ɓarauniyar hanya a ƙananan jiragen ruwa.

  Tuni Italiya ta yi tayin horar da dakarun kan iyakar Tunusiya na ƙasa da na ruwa domin hana masu neman mafaka tsallakawa ta ɓarauniyar hanya.

  Italiya ta sha fama da ɗarurwan masu shiga ƙasar a kowacce rana ta ɓangaren iyakarta ta kudu, abin da ya ƙara zama mai wuyar gaske sakamakon annobar cutar korona.

 19. Hukumomi a Kamaru sun haramta yi wa ɗalibai karatu lokacin hutu

  Ɗalibai

  Gwamnatin Kamaru ta ta haramta tsara bitar karatu a lokacin hutun makarantu na wannan shekara a wani mataki na yaƙi da yaɗuwar annobar korona.

  Ministar Ilimin Sakandare ce ta bayyana hakan yayin da wasu malaman makarantu suka riƙa bai wa ɗalibai damar yin nazarin abin da suka karanta a baya, ko kuma ba su ɗanɗanon abin da za su karanta nan gaba.

  Sai dai wannan matakin da ministar ta ɗauka ya kawo sauyi a tsarin da aka saba gani musamman ga makarantu masu zaman kansu suke yi domin janyo hankalin iyaye da ɗalibai.

 20. Assalamu Alaikum

  Barkanku da safiyar Talata.

  Ku biyo mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa kai-tsaye a najeriya da sauran sassan duniya.

  Za ku kasance da Umar Mikail ne a yanzu.