Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umar Mikail da Umaymah Sani Abdulmumin

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bibiyar mu ta wannan shafi da haka muke sallama da ku a yau sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri.

 2. Minti daya da BBC na Yamma

  Video content

  Video caption: Minti daya da BBC na yamma 26/08/2020
 3. Manyan masu tunani na duba yadda duniya za ta kasance bayan annobar korona

  Video content

  Video caption: Yadda duniya za ta koma bayan cutar korona

  Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

 4. Tarrayyar Turai ta dakatar da shirinta na horar da sojoji da 'yan sandan Mali

  mali army

  Tarrayyar Turai ta dakatar da shirinta na horar da sojoji da 'yan sandan Mali bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon da ya gabata inda suka kifar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubakar Kaita.

  Wata sanarwa da Tarrayar Turan ta fitar ta ce an tsara shirin ba da horo ne ga gwamnatin da ta kira hallaltaciyya.

  Sojoji sun aiwatar da juyin mulkin ne sakamakon ƙaruwar da ka samu a yawan masu adawa da gwamnati a kan yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar da kuma tashin hankalin da ake fuskanta daga mayaƙa masu ta da ƙayar baya wadanda ke ci gaba da samun karƙuwa a yankin Sahel.

  Sai dai Faransa wadda take ta dubban sojoji a yankin tun daga shekarar 2013 lokacin da ta fatattaki mayaƙa masu ikirarin jihadi daga arewacin Mali ta ce ba za ta janye dakarunta daga kasar ba sakamakon juyin mulkin.

 5. 'An saki' ƴan adawa daga gidan yari a Togo

  An saki ƴan adawa 16 da ake tsare da su a gidan yarin Togo kan laifin ''tawaye'' kamar yadda kamfanin dilancin labaran AFP ya rawaito wani jagoran 'yan adawa na cewa.

  16 daga cikinsu a ranar 21 ga watan Afrilu aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara guda, da kuma dakatar da su na wata takwas.

  Babban jami'i a jam'iyyar MPDD, Fulbert Attisso ya ce tun a ranar Talata aka sako su, kamar yadda AFP ya rawaito.

  ''An killace su yanzu haka a wani otel da ke birnin Lome'', a cewarsa.

  A watan Fabarairu Shugaban Faure Gnassingbé ya sake lashe zabe. Sai dai 'yan adawa sun zargi cewa anyi aringizo.

  A shekarar da ta gabata ya sauya kudin tsarin mulkin kasar domin sake samun damar tazarce da cigaba da zama a mulki har shekara ta 2030 - batun da ya haifar da gagarumin zanga-zanga tsakanin 2017 zuwa 2018.

 6. An tsinto kifayen dolphins a mace a bakin teku

  Dolphins

  An tsinci gawawwakin kifayen dolphins akalla 17 a gabar tekun Mauritius, mako guda da malalar mai a tekun Indiya.

  Sashin kula da kiwon kifi ya ce an gano tarin kifaye a mace, wasu kuma cikin yanayi na galabaita ko ƙoƙarin mutuwa.

  Masu kula da muhalli sun daura laifi kan malalar mai da aka samu a teku - ko kuma nitsewar da wani bangare na jirgin dakon mai ya yi a tekun.

  'Yan sanda sun ce sun tattara bayanai domin bincike da gwaji kan kifayen don gano ainihin dalilin mutuwar su.

  Jirgin ruwan Japan, MV Wakashio ne ya ratsa kusa da wani tsibiri a tekun Indiya a karshen watan Yuli, kuma ya fara tsiyayar da mai.

  Tan 800 na mai ne ya tsiyaye daga jirgin zuwa cikin ruwan, wanda ya haifar da aikin tsabtace ruwan.

 7. Sojojin Burundi da Rwanda sun gana don magance rikici

  Burundi

  A karon farko cikin lokaci mai tsawo dakarun sojin ƙasashen Burundi da Rwanda “sun gana a ranar Laraba don ƙoƙarin magance rikice-rikice, kamar yadda sakataren ƙungiyar ƙasashen yankin ya faɗa.

  Taron na yau da aka yi a kan iyakar ƙasashen tsakanin shugabannin hukumomin leƙen asirin ƙasashen ne, kuma wata hukuma mai ƙasashen yankin gabashin Afrika 12 da ke tabbatar da zaman lafiya ta International Conference of the Great Lakes Region ICGLR ce ta haɗa shi,

  Tun shekarar 2015, Burundi da Rwanda suke fuskantar rikice-rikice na siyasa a tsakaninsu a kan iyakarsu. Kowace gwamnati na zargin ɗayar da mara wa dakarunta baya ta hanyar da ba ta dace ba.

  Zakary Muburi-Muita shi ne sakatare janar na hukumar ICGLR, ya ce taron na yau mafari ne mai kyau na warware rikicin tsakanin maƙwabtan iyu.

 8. An kashe mutum biyu a zanga-zangar adawa da kisan baƙar fata a Amurka

  Jacob Blake (left) was shot several times in the back by police
  Image caption: Yan sanda sun harbi Jacob Blake sau da yawa a bayansa

  Mutum biyu sun hallaka yayin da aka raunata daya a tashin hankalin da ya faru a garin Kenosha da ke jihar Wisconsin ta Amurka.

  Tarzomar ta barke ne bayan da 'yan sanda suka raunata wani baƙar fata mai suna Jacob Blake a harbin da suka yi masa a ranar Lahadin da ta gabata.

  Masu zanga zaga sun yi artabu da yansanda kwantar da tarzoma a dare na uku da sanya dokar hana zirga zirga.

  Hotonan da aka walafa a shafukan sada zumunta sun nuna lokacin da mutane suke guduwa sakamakon harbin bindiga.

  Tun farko mahaifyar Jacob Blake ta yi kira ga masu zanga-zangar a kan su kawo ƙarshen tarzomar.

 9. Cutar korona ta kashe mutum na farko a Zirin Gaza

  coronavirus

  Ma’aikatan lafiya na kokarin daƙile bazuwar cutar korona a Zirin Gaza inda wani mutum mai shekara 61 ya rasu sanadin kamuwa da cutar, kuma shi ne mutum na farko da ya rasa ransa a cikin al'ummar da ke yankin.

  An kuma samu wani da ya rasu a cikin cibiyoyin killace masu cutar korona inda ake buƙatar duk wani da ya shigo cikin yankin ya kilace kansa na tsawon makonni uku.

  Hukumomi a Gaza sun shafe watanni suna ƙoƙarin daƙile bazuwar cutar koronan amma a ranar Litinin ɗin da ta gabata ne aka samu mutum na farko da ya harbu da cutar, abinda ya sa aka sanya dokar kulle ta kwanaki biyu

 10. Post update

  darakta janar na hukumar IAEA ya kai ziyara Tehran
  Image caption: Yarjejeniyar na zuwa ne a yayin da darakta janar na hukumar IAEA ya kai ziyara Tehran

  Iran ta amince ta bai wa masu bincike na Hukumar Kula da Makamashi Ta Duniya ta IAEA damar shiga wasu wurare biyu da ake zargin sansanonin makaman nukiliya ne.

  Wata sanarwa ta haɗaka ta ce Iran na yin hakan ne da zuciya ɗaya don warware matsalar da ke baibaye da batun samar da makaman nukiliya.

  Yarjejeniyar na zuwa ne a yayin da darakta janar na hukumar IAEA ya kai ziyara Tehran.

  Hukumar ta IAEA ta soki Iran kan ƙin amsa tambayoyinta a kan yiwuwar ɓoye bayanai kan shirinta na nukiliya da kuma hana masu sa ido kan sansanonin biyu.

  Ba a bayyana abin da masu sa idon suke zargin abin da ke faruwa a sansanonin ba. Amma ana tunanin a'amuran sun faru ne a shekarun 2000.

 11. Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 100 a Afghanistan

  Ambaliyar Afghanistan

  A ƙalla mutum 100 ne suka mutu sakamakon wata ambaliyar ruwa da aka yi a yankin Parwan a arewacin Afghanistan, a cewar jami'ai.

  Ambaliyar, wacce mamakon ruwan sama ya jawo, ta faru ne a birnin Charikar a ranar Laraba da safe yayin da mutane ke bacci.

  Bayan mace-macen da aka samu, hukumar kare afkuwar bala'i ta Afghanistan ta ce gwamman mutane sun ji rauni kuma kusan gidaje 500 ne suka rushe.

  Ana ci gaba da bayar da bayanai kan ɓarnar da ambaliyar ta jawo a yayin da ma'aikatan agaji suke ta ci gaba da neman mutane a cikin ɓaraguzan gine-gine.

  Jami'ai sun ce yawan waɗanda suka mutun na iya ƙaruwa.

  Ambaliyar Afghanistan
  Ambaliyar Afghanistan
  Ambaliyar Afghanistan
 12. Isra'ila ta kai wa Hezbollah hari a Lebanon

  Rundunar sojin Israila ta ce jiragen saman yakinta da jiragen sama masu saukar ungulu sun kai hari a sansanonin mayakan kungiyar Hezbollah da ke Lebanon.

  Wakilin BBC ya ce Israilar ta ce ta mayar da martani ne bayan da aka bude wa dakarunta wuta daga wasu yankunan Lebanon.

  Rahotanni sun ce bangaroron biyu ba su samu asarar rayuka ba.

  Sai dai majalisar koli kan tsaro ta Lebanon ta yi Allah-wadai da abin da ta kira harin Israila kuma ta ce za ta gabatar da koke a gaban Majalisar Dinkin Duniya.

 13. Rufe shagunan 'yan Najeriya a Ghana: Mahukuntan Najeriya na ci gaba da neman mafita

  Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya karɓi bayanai daga jakadiyar Najeriya a Ghana game da rufe shagunan 'yan kasuwar Najeriyar da hukumon Ghana suka yi.

  A farkon watan Agusta ne hukumomi a Ghana suka fara rufe shagunan ƙananan 'yan kasuwar ƙasashen waje mazauna ƙasar sakamakon abin da suka kira rashin takardun da suka dace.

  Mafi yawan shagunan da aka rufe na 'yan Najeriya ne kuma a makon da ya gabata Onyeama ya ce Najeriya za ta ɗauki matakin gaggawa, inda suka kira jakadan Ghana don shaida masa ɓacin ransu.

  Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ministan ya ce an kira jakadiyar ne gida Najeriya domin tattauna mafita kan batun.

  "Jakadiyar Najeriya a Ghana Mrs Esther Arewa, wadda aka aka kirawo ta gida ta ba ni bayanai game da rufe shagunan 'yan kasuwar Najeriya a Ghana," in ji shi.

  View more on twitter
 14. Mutanen birnin Yamai na zaune cikin ambaliyar ruwa

  Unguwar Gaweye
  Image caption: Wasu mata kenan tsaye a cikin ruwa a Unguwar Gaweye da ke Yamai, babban birnin Nijar

  Unguwanni da dama a birnin Niamey na Nijar sun wayi gari tsamo-tsamo cikin ruwa ranar Talata bayan wani ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ya haddasa ambaliya daga Kogin Nijar.

  Unguwar Gaweye na ɗaya daga cikin inda ruwan ya fi yi wa ɓarna, inda gidaje rushe tare da malale hanyoyi.

  Unguwar Gaweye
  Image caption: Unguwar Gaweye

  Gidaje da gonakin shinkafa da kasuwanni ne suka lalace yayin da gwamnatin ƙasar ta umaci mazauna yankunan da su fice.

  Unguwar Gaweye
  Image caption: Unguwar Gaweye

  Kusan dukkanin mazauna birnin miliyan ɗaya da rabi na zaune ne a gaɓar ruwan.

  Unguwar Gaweye
 15. Kim Jong Un zai bai wa ƙanwarsa muƙami don ya riƙa hutawa

  Kim Jong Un

  Kafofin yaɗa labaran cikin gida a Koriya ta Arewa sun nuna shugaban ƙasar Kim Jong Un yayin da yake ziyarar aiki bayan wasu rahotanni sun nuna cewa zai wakilta ƙanwarsa don gudanar da wasu ayyuka a madadinsa saboda ya rika hutawa.

  Ya kuma jagoranci wani taron majalisar zartarwarsa da zummar tattauna hanyoyin yaƙi da cutar korona.

  Koriya ta arewa dai ta ce har yanzu babu wanda ya kamu da cutar a cikinta amma masana harkar lafiya a fadin duniya na musanta wannan iƙirari.

  Mahukunta a ƙasar sun rufe iyakoki da haramta shige da fice don gudun shiga da cutar.

 16. Harbin baƙar fatar Amurka: Mutum biyu sun mutu a dare na uku na tashin hankali

  Wisconsin

  Mutum biyu sun mutu ɗaya ya ji rauni a dare na uku na tashin hankali a garin Kenosha na Amurka sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi wa wani bakin fata a Jihar Wisconsin.

  'Yan sanda sun ce an harbe mutum uku amma ba su bayar da bayani a kan ko su wane ne ke da hannu a kisan ba.

  Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ruwaito cewa tashin hankalin ya faro ne a rikici tsakanin masu zanga-zanga da masu gadin gidan mai da ke ɗauke da makamai.

  Tashin hankali ya ɓarke bayan 'yan sanda sun jikkata Jacob Blake ta hanyar harbinsa sau takwas ranar Lahadi.

  Wani bidiyo ya nuna lokacin da ake harbin mutumin mai shekara 29 yayin da yake shiga mota. Lauyoyinsa sun ce sai dai wata “mu’ujiza” zai sa ya iya sake takawa da ƙafarsa.

  Mutane sun yi burus da dokar hana fita a garin domin su yi zanga-zanga, wanda yake ƙarewa da tashin hankali.

 17. Mali na ci gaba da fuskantar wariya saboda juyin mulki

  Ismaël Wagué

  Ƙungiyar ƙasa da ƙasa mai suna International Organisation of La Francophonie (OIF) ta dakatar da Mali daga cikin membobinta, wadda ita ce ƙungiya ta baya-bayan nan da ta irin wannan mataki bayan sojoji sun tsige gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita daga Mulki a makon da ya gabata.

  Matakin da kungiyar da ke wakiltar ƙasashen da ke magana harshen Faransanci ta yi, ya zo kwanaki kaɗan bayan ƙungiyar cigaban tattalin arzikin Afirka ta yamma (Ecowas) ta dakatar da Mali daga cikinta.

  Ƙungiyar ta Ecowas tana tattaunawa da sojoji a kan dawo da mulkin dimokuraɗiyya, sai dai har yanzu ba a da ce ba.

  Sojojin da suka yi juyin mulkin sun ce ba su da sha’awar cigaba da mulki kuma za su yi sabon zaɓe a “lokacin da ya dace”

  Yanzu ba zai yiwu shugabannin kasashen Afirka su dawo da Boubacar Keita kan kujerar mulki ba bayan ya cire sha’awar komawa mulkin.

  OIF ta ce za ta turo nata wakilan zuwa Mali a cikin kwanaki masu zuwa.

 18. Hukumar NDLEA ta kama ƙwayar tramadol guda 11,785,800 a Legas

  NDLEA

  Hukumar Hana Sha da Fatucin Miyagun Ƙwayoyi a Najeriya ta National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) ta kama katan 607 maƙare da ƙwayar tramadol guda 11,785,800 a Jihar Legas.

  Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito kakakin hukumar mai suna Jonah Achema yana cewa shugaban hukumar ne, Muhammad Abdallah ya bayyana haka ranar Laraba.

  NAN ya ce ko a ranar 19 ga Agusta hukumar ta kama katan 255 na ƙwayoyin ciki har da tramadol.

  Sannan a ranar 6 ga watan Agusta sai da hukumar ta kama wata kwantena shaƙe da ƙwayoyi da ake zargin tramadol ce a ciki a garin Apapa na jihar ta Legas.

 19. Usain Bolt ya kamu da cutar korona

  Usain Bolt

  Shahararren dan wasan tsere Usain Bolt ya kamu da cutar korona.

  Bolt wanda ya yi bikin zagoyowar ranar haihuwarsa a kasarsa ta haihuwa Jamaica a makon da ya gabata, ya killace kansa bayan an yi masa gwaji a ranar Asabar.

  "Ya kamu da korona amma Usain ba ya nuna alamun cutar," in ji wakilin Bolt Ricky Simms, kamar yadda ya shaida wa CNN a sakon email.

  Ga cikakken labarin a nan:

 20. Kusan mutum 1.2 ne suka kamu da korona a Afirka

  Afirka

  Ƙasashen Afirka na dab da samun mutum miliyan 1.2 na waɗanda suka kamu da cutar korona, a cewar alƙaluman cibiyar yaƙi da yaɗuwar cutuka a Afirka ta Africa Centres for Disease Control and Prevention (CDC).

  Cibiyar ta bayyana a shafinta na Twitter cewa yanzu adadin ya kai 1,196,710, waɗanda suka mutu 28,014 da kuma 922,833 da suka warke.

  Afirka ta Kudu ce ke da mafi yawan adadin waɗanda suka harbu da cutar (611,450), inda Masar ke biye mata (97,478) sai Morocco (53,252) da Najeriya (52,548) da Ghana (43,622) da Algeria (42,302) da Habasha (42,143) da Kenya (32,803).