Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Awwal Janyau da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Mustapha Musa Kaita

  Multi-Media Broadcast Journalist

  Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

  Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko Instagram domin duba wasu labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kai.

 2. Gwamnatin Najeriya ta ce makarantu su fara shirye-shiryen buɗewa

  ..

  Gwamnatin Najeriya ta buƙaci gwamnatocin jihohi da shugabannin makarantu masu zaman kansu da su zama cikin shiri domin buɗe makarantu a ƙasar.

  Babban mai kula da tsare-tsare na kwamitin da shugaban ƙasar ya kafa don yaƙi da annobar korona Dakta Sani Aliyu, ya bayyana hakan yayin da kwamitin ke bayar da bayanai kan yanayin cutar a ƙasar.

  Ya bayyana cewa makarantun firamare da sakandare da jami'o'i su zama cikin shiri domin akwai yiwuwar buɗe su nan ba da jimawa ba.

  Kwamitin shugaban ƙasar ya ce gwamnatocin jihohi su fara tantacewa da tabbatar da duka makarantu a ko wane mataki sun bi ƙa'idojin da aka gindaya na yaƙi da cutar korona da kuma tabbatar da cewa sun samar da wani tsari a ƙasa, da za su iya sa ido ga shirye-shiryen buɗe makarantun.

 3. Ma'aikatan lafiya na zanga-zanga a Afrika Ta Kudu

  Ma'aikatan lafiya a Afrika Ta Kudu sun bijire wa dokar haɗa taruka bayan da suka yi zanga-zangar ƙin biyansu albashi da kuma rashin kayan aikin yaƙar annobar Korona.

  Ma'aikata a Pretoria sun shaida wa BBC cewa ana maimaita kayan da bai kamata a yi amfani da su fiye da sau ɗaya ba saboda karancinsu.

  Sun kuma ce za su gudanar da zanga-zangar gama gari nan da mako guda matuƙar ba su samu abin da suke so ba.

  A ranar Talata ne ma'aikatan lafiyar suka gudanar da addu'o'i ga yan uwansu da suka mutu a sanadiyyar annobar Korona.

 4. MINTI ƊAYA DA BBC - LABARAN YAMMA 03/09/2020

  Video content

  Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
 5. 'Yan bindiga sun kashe 'yan banga 18 da 'yan sanda uku a jihar Neja

  Video content

  Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren tattaunawar Ishaq Khalid da Kanar Kabiru Muhammad Maikundi mai ritaya

  Hukumomi a jihar Neja, sun tabbatar da mutuwar akalla mutum ashirin da biyu a wasu hare-hare biyu da 'yan bindiga suka kai a garin Dukku da ke ƙaramar hukumar Rijau da kuma a garin Kagara.

  Waɗanda aka kashe sun haɗa da 'yan banga 18, da 'yan-sanda uku da kuma farar hula guda. Lamuran sun faru ne daga yammacin Talata zuwa maraicen jiya Laraba.

  Haka kuma rahotanni daga ƙaramar hukumar Shiroro a jihar ta Neja na cewa 'yan bindiga sun sace mutane kimanin ashirin.

  Kanar Kabiru Muhammad Maikundi mai ritaya, shi ne Daraktan Kula da Lamuran Tsaro a jihar, ya kuma tabbatar wa BBC kashe mutanen a Dukku da Kagara, amma ya ce batun sace mutane a karamar hukumar Shiroro ba gaskiya ba ne.

 6. Za a fara biyan tarar dala 10 kan ƙin saka takunkumi a Rwanda

  ..

  Hukumomi a Kigali babban birnin Rwanda sun bayyana cewa duk wanda aka kama bai saka takunkumi ba ko kuma bai saka shi da kyau ba zai biya tarar dala 10.

  Hukumomin sun bayyana cewa irin wannan tarar za a ci ga wanda ya keta dokar da aka saka ta bayar da tazarar mita biyu a bainar jama'a a ƙasar, ko kuma keta dokar kullen da aka saka da dare.

  Waɗanda aka kama kuma sun haɗa wani taro ba bisa ƙa'ida ba ko kuma shagali tarar da za su biya za ta iya kai ta dala 200, waɗanda kuma suka halarci taron ko shagalin kuma dala 25 kowanen su.

  Irin waɗannan matakan da gwamnatin ta ɗauka na daƙile yaduwar korona a ƙasar ya jawo mata caccaka musamman a shafin Twitter.

  Mutum 4,200 ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a ƙasar, inda kuma aka tabbatar da mutuwar mutum 17.

 7. Labarai da dumi-dumiGwamnatin Najeriya ta sake sassauta dokar kulle

  Gwamnatin Najeriya ta sake sassauta dokar kullen da ta saka kan annobar korona inda dokar za ta fara aiki daga 12:00 na dare zuwa 4:00 na asuba.

  Babban mai kula da tsare-tsare na kwamitin da shugaban ƙasa ya kafa don yaƙi da annobar korona Dakta Sani Aliyu ne ya bayyana hakan yayin da kwamitin ke bayar da bayanai kan yanayin cutar a ƙasar.

  Tun a watan Maris ɗin wannan shekarar ne gwamnatin Najeriyar ta saka wannan dokar kullen a jihohin Legas da Ogun da Abuja babban birnin ƙasar, sai dai lokaci bayan lokaci an ta sassauta dokar.

  A watan Yunin bana ne gwamnatin tarayyar ta sassauta dokar daga 10:00 na dare zuwa 4:00 na asuba.

 8. Gwamnan Ogun ya ziyarci Shugaba Buhari

  ...

  Gwamnan jihar Ogun a Najeriya Prince Dapo Abiodun, ya ziyarci Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari, a fadarsa da ke Abuja.

  Shugaban ya karbi wani kundin hotuna da gwamnan ya yi masa tsarabarsa da ke ɗauke da hotunan aikin da gwamnan ya yi a makonni 52 da ya yi a matsayinsa na gwamnan jihar.

  ...
 9. Ranar Asabar jiragen ƙasa da ƙasa za su ci gaba da zirga-zirga a Najeriya

  ..

  Ministan sufurin jiragen sama a Najeriya Hadi Sirika ya bayyana cewa a ranar 5 ga watan Satumba za a ci gaba da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da wasu ƙasashen.

  Ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin shugaban ƙasa kan yaƙi da cutar korona ke bayar da bayanai kan cutar a ƙasar.

  Ministan ya ce filayen jiragen Abuja da Legas ne kaɗai za a buɗe domin jigilar.

  Ya ce duk wanda ya shiga Najeriya daga wata ƙasa dole ne a killace shi na mako guda a wani wuri da gwamnati ta tanada, kuma mutum ne zai ɗauki nauyin kansa a wurin killacewar.

  Haka zalika ga masu fita ƙasar da shiga, dole ne sai sun yi gwajin cutar ta korona, in ji ministan.

 10. Buhari ya tsawaita aikin kwamitin shugaban ƙasa na yaƙi da korona zuwa Disambar bana

  ..

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita aikin kwamitin da ke yai da cutar korona zuwa Disambar wannan shekara.

  Sakataren gwamnatin tarayya wanda shi ne shugaban kwamitin, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Alhamis.

  A baya dai, 17 ga watan Satumba ya kamata a ce kwamitin ya ƙarƙare aikinsa, sai dai saboda buƙatar ci gaba da yaƙi da cutar a ƙasar, kwamitin zai ci gaba da aiki har zuwa ƙarshen shekara.

 11. An yi kashe-kashe tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ISWAP a jihar Borno

  ..

  Rahotanni daga arewa maso gabashin Najeriya na cewa an samu ƙarin tashe-tashen hankali tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan ƙungiyar ISWAP wadda ta balle daga ƙungiyar Boko Haram.

  Ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya ta ISWAP ta ce mayaƙanta sun kashe sojojin Najeriya aƙalla 20 a hare-hare biyu da suka kai kan sojojin a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

  Ga cikakken labarin a nan:

 12. Abin da kuke bukatar sani da ya faru a duniya kan cutar korona

  Yawan masu kamuwa da cutar korona na karuwa a wani lamari mai ta da hankali a wasu sassan duniya a cewar jami'ai, a yayin da ake ci gaba da samun rarrauwar kawuna tsakanin kasashn duniya kan sahihiyar hanya mafi inganci da za a bi a samar da riga-kafin Covid-19.

  Ga dai wasu bayanai na baya-bayan nan:

  • A Amurka, wani shiri da ake yi na samar da riga-kafi ga kungiyoyi da dama na jawo damuwa. Cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta kasar CDC ta shaida wa jami'an lafiya a dukkan jihohin kasar 50 cewa shirya fara bayar da riga-kafi nan da ranar 1 ga watan Nuwamba.
  • Indiya ta kara samun yawan wadanda suka kamu da cutar a rana daya, inda a yau aka samu mutum 83,883 da suka kamu. Yawan masu cutar a yanzu ya kai miliyan 3.85, inda ta zama kasa ta uku da masu cutar suka fi yaa a duniya
  • Yawan masu kamuwa da cutar korona a Turai na sake karuwa kamar irin yadda aka gani a watan Maris lokacin da kwayar cutar ta shiga nahiyar, a cewar shugaban hukumar lafiya ta Tarayyar Turai
  • Amma yawan wadanda suke mutuwa sakamakon cutar a Brazil yana raguwa
  • Wani jarumin fina-finan Amurka kuma tsohon dan wasan kokawa Dwayne Johnson 'The Rock' ya kamu da cutar korona shi da iyalansa duk da irin matakan kariyar da yake dauka
  • A Italiya kuwa, an shiga rana ta biyu ta Bikin Baje kolin Fina-Finai na Venice - biki irinsa na farko da aka yi tun bayan barkewar annobar cutar korona.
 13. Wanda ya yi wa Annabi SAW batanci a Kano ya daukaka kara

  Bangaren shari’a na jihar Kano ya ce matashin nan da wata Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa saboda batanci ga Annabi Muhammadu SAW ya daukaka kara a yau.

  Hakan na nufin cewa ya tsallake siradin zartar masa da hukunci matukar ya wuce kwanaki 30 bai daukaka kara ba kan hukuncin da aka yanke masa ba.

  A jiya ne shahararren lauyan nan mai kare hakkin bil adama Femi Falana ya ce kotun ta Kano ta hana takardun shari’ar, wadanda za su ba da damar daukaka kara, to sai dai kotun ta musanta zargin.

  Baba Jibo Ibrahim shi ne kakakin kotunan Kano, kuma abokin aikinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tambaye shi karin bayani kan batun daukaka karar.

  Ku latsa lasifikar da ke kasa don sauraron hirar tasu:

  Video content

  Video caption: Hirar Baba Jibo Ibrahim da Yusuf Yakasai kan daukaka karar Yahaya Sharif
 14. Zimbabwe za ta mayar wa fararen fata gonakinsu

  Gonakin manoma a Zimbabwe

  Zimbabwe na shirin mayar da gonaki kusan 37 ga ƴan ƙasashen waje ƙarƙashin yarjejeniyar ƙasashen duniya, kamar yadda jaridar Herald a ƙasar ta ruwaito.

  An karɓe gonakin ne ƙarƙashin wani shiri mai cike da ce-ce-ku-ce zamanin gwamnatin Robert Mugabe da ta kwace gonakin da turawan mulkin mallaka suka karɓe.

  An ambato ministan noma da ruwa da fiyale Anxious Masuka na cewa gwamnati ba ta da ƙudirin dawo da shirin filayen na tsohuwar gwamnati amma za ta diba bisa tsarin doka.

  Jaridar ta ce manomar da aka ƙwace wa gonakinsu a zamanin Mugabe za a ba su damar karɓar filayensu ko kuma a biya su diyya.

  Amurka ta ce mayar wa manoma filayensu ko biyansu diyya yana cikin sharuɗɗan da ta gindaya wa Zimbabwe kafin ta ɗage wa ƙasar takunkumin kariyar tattalin arziki.

 15. Kwamishinan lafiya na Legas ya warke daga korona

  Kwamishinan lafiya na jihar Legas Farfesa Akin Abayomi ya murmure bayan ya kamu da cutar korona.

  Ma'aikatar lafiya ta jihar Legas ta wallafa bidiyo a shafinta na Twitter da ke nuna nuna kwamishinan a ofishinsa a ranar farko da ya dawo aiki bayan ya murmure.

  View more on twitter
 16. NLC za ta ɗauki mataki kan ƙarin kudin fetir da lantarki - Wabba

  Ƙungiyar ƙwadagon ta NLC ta yi kakkausar suka ga gwamnatin Najeriya game ƙarin farashin mai da kudin lantarki, tana cewa wahalar da karin zai haddasa za ta kare ne a kan talaka.

  Ƙungiyar ta ce ta sha ba gwamnati shawarwari a kan yadda za a inganta rayuwar jama’a amma ta yi biris da su, don haka za ta tattauna da shugabannin rassanta don daukar matakin da ya dace.

  Ku saurari hirar Ibrahim Isa da shugaban ƙungiyar ƙwadagon Kwamred Ayuba Wabba.

  Video content

  Video caption: Hirar Ibrahim Isa da shugaban NLC Ayuba Wabba
 17. Afghanistan da Taliban sun yi musayar fursunoni

  Gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban sun ce sun yi musayar fursunoni matakin da zai buɗe ƙofar fara tattaunawar zaman lafiya tsakaninsu

  A yanzu bangaroran biyu za su fara tattaunawar ne abirnin Doha da ke Qatar.

  A baya an samu tsaiko kan buƙatar Taliban na a saki wasu ƴaƴan ƙungiyar da gwamnati ke yi wa kallon manyan ƴan ta'adda.

  Duk da haka kasashen Turai kamar Faransa da Australia sun nuna rashin amincewa da sakin bakwai daga cikin ƴanTaliban.

  Musayar fursunoni na ɗaya daga cikin ka'idojin da aka gindaya kafin fara tattaunawar zaman lafiyaa watan Fabrairu tsakanin Taliban da gwamnatin Amurka.

 18. Fasinjan jirgin sama 8 sun kamu da korona

  Mahukuntan lafiya na ƙoƙarin gano fasinjan jirgin sama daga Crete zuwa Landon bayan gwaji ya tabbatar da mutum takwas na ɗauke da korona.

  Kamfanin jirgin Wizz ya ce ba zai iya tantance fasinjan ba da ke ciki ba daga tsibirin na Girka da suka kamu da korona bayan gano wasunsu na ɗauke da korona.

  Kamfanin jirgin ya ce ya sanar da hukumomin lafiya, waɗanda ke da alhakin tuntuɓar fasinjojin 204 da ke cikin jirgin.

  Tsibirin Crete
 19. Na damu da tsadar rayuwar da ake fuskanta - Buhari

  Shugaba Buhari

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan tsadar kayayyakin abinci da ƴan kasar ke kuka da gwamnatinsa.

  Sanarwar da mai taimakawa shugaban kan harakokin watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce gwamnatinsa ta damu a tsadar kayayyakin a daidai lokacin kullen korona ya ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani hali.

  Shugaban ya ce duk da matsalar ta shafi duniya baki ɗaya amma gwamnatinsa ta fara bin matakan shawo kan matsalar.

  Sanarwar ta ce shugaban ya bayar da umurnin fitar da abinci kusan ton 30,000 na masara ga masu samar da abincin dabbobi domin sauƙake farashi. Ya ce yanayin da aka shiga zai zo ya wuce

 20. Za a daidaita albashin 'yan kwallo maza da mata a Brazil

  Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil ta sanar da cewa yanzu haka ta daidaita albashin mata da maza a manyan kungiyoyin kwallon kafar kasar.

  Dukkanin kudaden yau da kullun da ladan samun nasarar lashe lambar yabo da ake bawa mata da maza da ke halartar gasar wasannin Olympics sun zama kai da kai.

  Har zuwa 1979 doka ta haramtawa mata a Brazil buga kwallon kafa, ana kallon wasan matsayin wahala, da bai kamaci mata ba.

  Masu sharhi sun ce ganin yadda Brazil ta yi shuhura a fagen wasan kwallon kafa a duniya, matakin da ta dauka a yanzu ishara ce mai girma ga sauran kasashen duniya.