Daga Awwal Ahmad Janyau, Halima Umar Saleh da Mustapha Musa Kaita
time_stated_uk
Rufewa
Mustapha Musa Kaita
Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kansu.
An fara bincike kan gobarar da ta tashi a wurin ajiye abincin agaji a Lebanon
EPACopyright: EPA
Jami'ai a Beirut babban birnin Lebanon, sun ƙaddamar da bincike kan sanadin gobarar da ta tashi a birnin a ranar Alhamis
Gobarar ta tashi a tashar jiragen ruwan Lebanon da ke Beirut ta kuma dangana da inda aka ajiye abincin agajin da ake samu - wanda hakan zai ƙara jefa aikin ba da agaji a birnin cikin wani hali.
Wutar ta tashi ne kusa da inda aka samu mummunar fashewar wasu sinadarai a watan jiya.
Masu kashe gobara da kuma jami'an soji sun shafe sa'o'i suna ƙoƙarin kashe wannan gobara, inda suke amfani da jirgin helkwafta domin fesa wa wutar ruwa kafin aka samu ta tsahirta.
Babu wanda aka ce ya samu rauni ko mutuwa sakamakon gobarar, babu kuma wani cikakken bayani dangane da abin da ya jawo wutar.
Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 10/09/2020
Video content
Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaranLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
Ana yunƙurin sake kutse ta intanet ga zaɓen Amurka – Microsoft
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Masu kutse ta intanet da ke da alaƙa da Rasha da China da kuma Iran na ƙoƙarin sake leƙen asiri ga mutanen da ke da ruwa da tsaki a zaɓen Amurka na 2020, inji kamfanin Microsoft.
Wata ƙungiyar masu kutsen ta Rasha wadda ta yi kutse a yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar Democrats a 2016, a halin yanzu ta fara yin katsalandan da kutse-kutse, inji kamfanin na Microsoft.
Kamfanin ya ce: "A bayyana take wasu ƙungiyoyi na waje sun ƙara matsa ƙaimi domin kai hari ga zaɓen."
Ana harin duka yaƙin neman zaɓen Mista Trump na Jam'iyyar Republican da kuma Mista Biden na Jam'iyyar Democrats.
Likitoci a Najeriya sun janye yajin aiki
BRYAN CHRISTENSENCopyright: BRYAN CHRISTENSEN
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa sun janye yajin aikin da suka soma a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.
Jaridar DailyTrust a Najeriya ta ruwaito cewa Shugaban ƙungiyar ta NARD Dakta Sokomba Aliyu ne ya tabbatar musu da hakan ta wayar tarho a ranar Alhamis.
Ya bayyana wa jaridar cewa ƙungiyar za ta fitar da sanarwa ta musamman da ke ƙunshe da bayanai kan janyewar yajin aikin.
A jiya ne dai Ministan Lafiya na ƙasar Osagie Ehanire ya shaida wa likitocin cewa dole ne su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya, kuma a cewarsa, bai dace likitocin su tafi wannan yajin aikin a daidai irin wannan lokaci ba.
Likitocin dai sun koka ne kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu musamman alawus-alawus na haɗarin aiki a lokacin cutar korona.
Ko a watan Yunin wannan shekarar ma sai da likitocin suka tsunduma irin wannan yajin aiki.
Sashen kiwon lafiya na Najeriya na daga cikin ɓangarorin da ake kokawa kan taɓarɓarewarsu a ƙasar.
An kashe mutum 58 a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo
ReutersCopyright: Reuters
Jami'ai a gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, sun bayyana cewa akalla mutum 58 aka kashe a wasu hare-hare biyu da wata ƙungiyar 'yan tawaye ta kai mai suna ADF.
An kashe mutum 23 ne a garin Irumu da ke kudancin lardin Ituri a ranar Talata.
Sauran 35 ɗin kuma an kashe su ne a garin dai na Irumu amma kuma a ranar Alhamis.
Jami'ai a kasar sun bayyana cewa akwai mutum 17 da suka yi ɓatar dabo, kuma ana zargin ƙungiyar 'yan tawayen ce ta sace su.
Ƙungiyar ADF ta kashe ɗaruruwan farar hula tun bayan da rundunar sojin Congo ta ƙaddamar da wani shiri na daƙile 'yan tawaye a makwaftan arewacin lardin Kivu a Nuwambar bara.
Jami'ar Imo ta fara binciken bidiyon da ake zargin malami na lalata da ɗaliba
Jami'ar jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yadda wasu ɓata garin malaman jami'o'i ke buƙatar lalata da ɗalibansu mata domin ba su maki.
Hakan ya faru ne bayan wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna an kama wani malamin jami'ar rabi tsirara yayin ƙoƙarin lalata da wata ɗaliba.
Wani bidiyon kuma ya nuna wani malamin na wasa da al'aurarsa bayan zargin yin lalata da wata ɗalibarsa.
Kafofin watsa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa ɗaliban ne tare da taimakon jami'an tsaro suka naɗi bidiyon malaman.
Ko a kwanakin baya sai da sashen BBC mai binciken ƙwaƙwaf ya fallasa yadda wasu malaman jami'o'i ke neman yin lalata da ɗalibai domin ba su maki.
Matan da suka tara kuɗi suka sayi motar kai mata haihuwa asibiti a Jigawa
BBCCopyright: BBC
Matan wani kauye da ake kira Bordo a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa a Najeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna-biyu zuwa asibiti domin haihuwa.
Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan buƙatar hakan ta taso musamman ma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin.
Ƙasar Jamus ta bayyana cewa an sake samun murar aladu tattare da wani alade da ke kusa da iyakar ƙasar da Poland.
A yanzu haka dai an killace kusan kilomita 15 na inda aka samu murar ta aladu a yankin.
Cutar dai ba ta da wata illa ga bil adama, amma tana da illa matuƙa ga aladu.
Ɓullar cutar babbar barazana ce ga fitar da naman aladen da Jamus ɗin ke yi zuwa Koriya Ta Kudu da China - wadda ita ce kasuwarta mafi girma a wajen Tarayyar Turai.
Tuni dai Koriya Ta Kudun ta haramta shiga da naman aladen da aka yi dakonsa daga Jamus.
Babu wani martani dai da Chinar ta mayar, wadda ta sawo naman alade na fiye da dala miliyan 500 a watanni huɗu na farkon shekarar nan.
Jamus dai ta gina wani bango mai tsawon kilomita ɗaruruwa kan iyakarta da ƙasar Poland a yunƙurinta na daƙile cutar daga yaɗuwa.
Muna kama mata mabarata 416 a Kano – Hukumar Hisbah
Video content
Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron wannan rahotonLatsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron wannan rahoton
Hukumar Hisabh ta jihar Kano ta ce ta kama mabarata
da almajirai 648 da ke barace-barace a wasu daga cikin titunan jihar.
Shugaban hukumar ta Hisbah a jihar Kano, Sheik Muhammad Haroon Ibn Sina, ya shaida wa BBC cewa sun kama almajirai mata sama da 400, da maza kimanin 200.
Ya ce an yi kamen ne cikin watanni uku zuwa huɗu, kuma a cewarsa, almajiran da ke jihar adadinsu na da matuƙar yawa.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin Kano ta haramta bara a jihar, tare da kuma ƙaddamar da shirin ilimi kyauta kuma dole.
China za ta fara shirin wayar da kai ga ma'aurata
GETTY IMAGESCopyright: GETTY IMAGES
Ƙasar China za ta fara wani shiri na musamman domin bayar da shawarwari ga ango da amarya da ke shirin aure, a yunƙurin ƙasar na kawo ƙarshen rabuwar aure da ake yawan samu a ƙasar.
A shekarar da ta gabata, sama da aure miliyan huɗu ya mutu a China, ana kuma zargin hakan zai ninka sau uku nan da shekara 20 masu zuwa.
Ana sa ran waɗannan shawarwari za su ƙara wayar wa ma'aurata kai kan rayuwar aure da kuma yadda za su yi haƙuri da juna.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke shirin waiwayar dokarta ta haihuwar ɗa ɗaya a ƙasar domin yi wa dokar gyara.
Za a yi gyara ga dokar ne sakamakon yawan tsofaffi da ke ƙasar na neman rinjayar na matasa.
Shahararriyar 'yar wasan fina-finan nan ta Hollywood, Dame Diana ta mutu a yau inda take da shekaru 82.
Ta fito a matsayin Olenna Tyrell a fim ɗin nan na zango-zango wato Game Of Thrones.
'Yarta Rachael Stirling, ta bayyana cewa mahaifiyarta ta mutu ne sakamakon ciwon dajin da ta yi fama da shi.
Dame Diana ce mace guda tak da ta taɓa fitowa a matsayin matar James Bond.
Ta fito ne a matsayin Tracy cikin fim ɗin On Her Majesty's Secret wanda aka yi a 1969.
Netherlands za ta biya diyya ga mutumin da sojojinta suka kashe iyalansa a Iraƙi
Ƙasar Netherlands ta ce za ta biya diyya ga wani farar hula da
ya rasa iyalansa sakamakon harin sojin sama da sojojin ƙasar suka kai a Iraƙi.
Sojojin sun kashe wa Bassim
Razzo matarsa da ƴarsa da wasu ƴan uwansa biyu a harin da suka kai ta sama a
garin Mosul shekaru biyar da suka gabata.
Sojojin sama na Netherlands
sun yi kurkuren kai hari ne a wasu gidaje biyu da suka yi tunanin na mayaƙan IS
ne.
Akwai mutane da dama
da ke son Netherlands da ke cikin ƙawancen Amurka a yaƙi da IS ta biya su diyya a wani hari da aka kai inda
aka kashe mutum 70.
Buhari na taro kan samarwa ƴan Najeriya abinci
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taro kan samar da abinci a ƙasar.
Taron na zuwa a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kuka kan tsadar farashin kayayyaki.
Shugaban ya ce sun lura da mummunan tasirin ambaliyar ruwa da ta yi ɓarna ga manoma.
A kwanakin da suka gabata ne gwamnati ta yi ƙarin farashin fetur da kuma lantarki, matakin da ƴan Najeriya ke ganin zai ƙara haifar da tsadar kayayyaki.
Gwamnatin Buhari ta bayyana abu uku da ta ce su suka janyo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.
Dalilan da gwamnatin ta bayar sun haɗa da tsirin annobar korona da kuma ƴan kasuwa da gwamnatin ta zarga da ɓoye abinci.
Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da sarakunan arewa kan korona
@UNICEF_NigeriaCopyright: @UNICEF_Nigeria
Kwamitin shugaban kasa kan yaƙi da cutar korona a Najeriya na tattaunawa da sarakunan gargajiya na yankin arewacin ƙasar kan yadda za a daƙile yaduwar cutar tsakanin al'umma.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da Sarkin musulmi Abubakar Sa'ad na uku da kuma sauran manyan sarakunan jihohin arewa.

Har yanzu a kullum ana samun ƙaruwar masu cutar a Najeriya, duk da dadin na raguwa.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta shafa a ƙasar sun kai 55,632.
Amma yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 43,610, yayin da kuma cutar ta kashe mutum 1,070.
‘Ƴan tawayen Houthi sun cilla wa Saudiyya makami mai linzami’
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Ƴan tawayen Houthi a Yemen sun yi ikirarin cewa sun harba makami mai
linzami a wani yanki na Riyadh
Rahotanni sun ambato kakakin ƴan tawayen Yahya al-Sarea, na cewa sun kai harin ne a
wani muhimmin wuri a Riyadh domin mayar da martani ga hare-haren da Saudiyya ke
jagoranta a Yemen.
Babu dai wata sanarwa daga hukumomin Saudiyya game da ikirarin na ƴan
Houthi.
Amma tun da farko kafar talabijin ta Saudiyya Al Arabiya ta bayar da
rahoton cewa Saudiyya ta kakkabo wani Jirgin ƴan Houthi marar matuki a kudancin birnin Jazan.
Wannan na zuwa bayan ƴan tawayen Houthi sun yi barazanar ci gaba da kai wa
Saudiyya hare-hare.
Gwamnati ta ƙarfafa tsaro a yankin rainon Ingila na Kamaru
Gwamnati
ta daɗa ƙarfafa tsaro a yankin rainon ingila, musamman ma a birnin Bamenda inda
dokar da hukumomi suka shimfuda na haramta zirga-zirgar babura na yin karo da
dokar da ‘yan aware suka kafa ta hana motoci yin zirga-zirga.
Rahotanni na cewa ɗaruruwan dakarun tsaro ne aka aika wannan birnin, inda suka mamaye tituna suna
gudanar da bincike gida-gida a wasu unguwanni, kuma suna tsare da wasu muhimman
wurare.
Har ila yau kuma babu motoci a kan tituna. Duk wasu harkoki kuma sun
tsaya cak, sakamakon haka.
Wata tambaya da kusan kowa da kowa yake yi ita ce,
ta yaya dokar da ‘yan aware suka kafa ta rinjayi ta Gwamnati wurin mutuntawa?
Amsar tambayar da Alhadji Amadoun Kaka wani mai yi sharhi ya bai wa Mohaman Babalala a hirar da suka yi.
Video content
Video caption: Hirar Alhadji Amadoun Kaka da Mohamman BabalalaHirar Alhadji Amadoun Kaka da Mohamman Babalala
Rahoto kai-tsaye
Daga Awwal Ahmad Janyau, Halima Umar Saleh da Mustapha Musa Kaita
time_stated_uk
Rufewa
Mustapha Musa Kaita
Multi-Media Broadcast Journalist
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan labaran da muka wallafa ko kuma tafka muhawara a kansu.
An fara bincike kan gobarar da ta tashi a wurin ajiye abincin agaji a Lebanon
Jami'ai a Beirut babban birnin Lebanon, sun ƙaddamar da bincike kan sanadin gobarar da ta tashi a birnin a ranar Alhamis
Gobarar ta tashi a tashar jiragen ruwan Lebanon da ke Beirut ta kuma dangana da inda aka ajiye abincin agajin da ake samu - wanda hakan zai ƙara jefa aikin ba da agaji a birnin cikin wani hali.
Wutar ta tashi ne kusa da inda aka samu mummunar fashewar wasu sinadarai a watan jiya.
Masu kashe gobara da kuma jami'an soji sun shafe sa'o'i suna ƙoƙarin kashe wannan gobara, inda suke amfani da jirgin helkwafta domin fesa wa wutar ruwa kafin aka samu ta tsahirta.
Babu wanda aka ce ya samu rauni ko mutuwa sakamakon gobarar, babu kuma wani cikakken bayani dangane da abin da ya jawo wutar.
Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 10/09/2020
Video content
Ana yunƙurin sake kutse ta intanet ga zaɓen Amurka – Microsoft
Masu kutse ta intanet da ke da alaƙa da Rasha da China da kuma Iran na ƙoƙarin sake leƙen asiri ga mutanen da ke da ruwa da tsaki a zaɓen Amurka na 2020, inji kamfanin Microsoft.
Wata ƙungiyar masu kutsen ta Rasha wadda ta yi kutse a yaƙin neman zaɓen Jam'iyyar Democrats a 2016, a halin yanzu ta fara yin katsalandan da kutse-kutse, inji kamfanin na Microsoft.
Kamfanin ya ce: "A bayyana take wasu ƙungiyoyi na waje sun ƙara matsa ƙaimi domin kai hari ga zaɓen."
Ana harin duka yaƙin neman zaɓen Mista Trump na Jam'iyyar Republican da kuma Mista Biden na Jam'iyyar Democrats.
Likitoci a Najeriya sun janye yajin aiki
Ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa sun janye yajin aikin da suka soma a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba.
Jaridar DailyTrust a Najeriya ta ruwaito cewa Shugaban ƙungiyar ta NARD Dakta Sokomba Aliyu ne ya tabbatar musu da hakan ta wayar tarho a ranar Alhamis.
Ya bayyana wa jaridar cewa ƙungiyar za ta fitar da sanarwa ta musamman da ke ƙunshe da bayanai kan janyewar yajin aikin.
A jiya ne dai Ministan Lafiya na ƙasar Osagie Ehanire ya shaida wa likitocin cewa dole ne su ƙara haƙuri da gwamnatin tarayya, kuma a cewarsa, bai dace likitocin su tafi wannan yajin aikin a daidai irin wannan lokaci ba.
Likitocin dai sun koka ne kan rashin biyansu haƙƙoƙinsu musamman alawus-alawus na haɗarin aiki a lokacin cutar korona.
Ko a watan Yunin wannan shekarar ma sai da likitocin suka tsunduma irin wannan yajin aiki.
Sashen kiwon lafiya na Najeriya na daga cikin ɓangarorin da ake kokawa kan taɓarɓarewarsu a ƙasar.
An kashe mutum 58 a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo
Jami'ai a gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo, sun bayyana cewa akalla mutum 58 aka kashe a wasu hare-hare biyu da wata ƙungiyar 'yan tawaye ta kai mai suna ADF.
An kashe mutum 23 ne a garin Irumu da ke kudancin lardin Ituri a ranar Talata.
Sauran 35 ɗin kuma an kashe su ne a garin dai na Irumu amma kuma a ranar Alhamis.
Jami'ai a kasar sun bayyana cewa akwai mutum 17 da suka yi ɓatar dabo, kuma ana zargin ƙungiyar 'yan tawayen ce ta sace su.
Ƙungiyar ADF ta kashe ɗaruruwan farar hula tun bayan da rundunar sojin Congo ta ƙaddamar da wani shiri na daƙile 'yan tawaye a makwaftan arewacin lardin Kivu a Nuwambar bara.
Jami'ar Imo ta fara binciken bidiyon da ake zargin malami na lalata da ɗaliba
Jami'ar jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta ƙaddamar da bincike kan yadda wasu ɓata garin malaman jami'o'i ke buƙatar lalata da ɗalibansu mata domin ba su maki.
Hakan ya faru ne bayan wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna an kama wani malamin jami'ar rabi tsirara yayin ƙoƙarin lalata da wata ɗaliba.
Wani bidiyon kuma ya nuna wani malamin na wasa da al'aurarsa bayan zargin yin lalata da wata ɗalibarsa.
Kafofin watsa labarai na Najeriya sun ruwaito cewa ɗaliban ne tare da taimakon jami'an tsaro suka naɗi bidiyon malaman.
Ko a kwanakin baya sai da sashen BBC mai binciken ƙwaƙwaf ya fallasa yadda wasu malaman jami'o'i ke neman yin lalata da ɗalibai domin ba su maki.
Matan da suka tara kuɗi suka sayi motar kai mata haihuwa asibiti a Jigawa
Matan wani kauye da ake kira Bordo a karamar hukumar Jahun da ke jihar Jigawa a Najeriya sun yi karo-karon kudi inda suka sayo motar daukar mata masu juna-biyu zuwa asibiti domin haihuwa.
Matan sun samar da kudin ne inda aka sayi motar domin a rinka kai matan kauyen asibiti idan buƙatar hakan ta taso musamman ma haihuwa saboda matsalar sufuri da ake fuskanta a yankin.
Karanta cikakken labarin a nan:
An sake samun ɓullar murar aladu a Jamus
Ƙasar Jamus ta bayyana cewa an sake samun murar aladu tattare da wani alade da ke kusa da iyakar ƙasar da Poland.
A yanzu haka dai an killace kusan kilomita 15 na inda aka samu murar ta aladu a yankin.
Cutar dai ba ta da wata illa ga bil adama, amma tana da illa matuƙa ga aladu.
Ɓullar cutar babbar barazana ce ga fitar da naman aladen da Jamus ɗin ke yi zuwa Koriya Ta Kudu da China - wadda ita ce kasuwarta mafi girma a wajen Tarayyar Turai.
Tuni dai Koriya Ta Kudun ta haramta shiga da naman aladen da aka yi dakonsa daga Jamus.
Babu wani martani dai da Chinar ta mayar, wadda ta sawo naman alade na fiye da dala miliyan 500 a watanni huɗu na farkon shekarar nan.
Jamus dai ta gina wani bango mai tsawon kilomita ɗaruruwa kan iyakarta da ƙasar Poland a yunƙurinta na daƙile cutar daga yaɗuwa.
Muna kama mata mabarata 416 a Kano – Hukumar Hisbah
Video content
Hukumar Hisabh ta jihar Kano ta ce ta kama mabarata da almajirai 648 da ke barace-barace a wasu daga cikin titunan jihar.
Shugaban hukumar ta Hisbah a jihar Kano, Sheik Muhammad Haroon Ibn Sina, ya shaida wa BBC cewa sun kama almajirai mata sama da 400, da maza kimanin 200.
Ya ce an yi kamen ne cikin watanni uku zuwa huɗu, kuma a cewarsa, almajiran da ke jihar adadinsu na da matuƙar yawa.
A kwanakin baya ne dai gwamnatin Kano ta haramta bara a jihar, tare da kuma ƙaddamar da shirin ilimi kyauta kuma dole.
China za ta fara shirin wayar da kai ga ma'aurata
Ƙasar China za ta fara wani shiri na musamman domin bayar da shawarwari ga ango da amarya da ke shirin aure, a yunƙurin ƙasar na kawo ƙarshen rabuwar aure da ake yawan samu a ƙasar.
A shekarar da ta gabata, sama da aure miliyan huɗu ya mutu a China, ana kuma zargin hakan zai ninka sau uku nan da shekara 20 masu zuwa.
Ana sa ran waɗannan shawarwari za su ƙara wayar wa ma'aurata kai kan rayuwar aure da kuma yadda za su yi haƙuri da juna.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke shirin waiwayar dokarta ta haihuwar ɗa ɗaya a ƙasar domin yi wa dokar gyara.
Za a yi gyara ga dokar ne sakamakon yawan tsofaffi da ke ƙasar na neman rinjayar na matasa.
Rarara ya gindaya wa masoya Buhari sharaɗi
Dame Diana ta fim ɗin Game Of Thrones ta mutu
Shahararriyar 'yar wasan fina-finan nan ta Hollywood, Dame Diana ta mutu a yau inda take da shekaru 82.
Ta fito a matsayin Olenna Tyrell a fim ɗin nan na zango-zango wato Game Of Thrones.
'Yarta Rachael Stirling, ta bayyana cewa mahaifiyarta ta mutu ne sakamakon ciwon dajin da ta yi fama da shi.
Dame Diana ce mace guda tak da ta taɓa fitowa a matsayin matar James Bond.
Ta fito ne a matsayin Tracy cikin fim ɗin On Her Majesty's Secret wanda aka yi a 1969.
Netherlands za ta biya diyya ga mutumin da sojojinta suka kashe iyalansa a Iraƙi
Ƙasar Netherlands ta ce za ta biya diyya ga wani farar hula da ya rasa iyalansa sakamakon harin sojin sama da sojojin ƙasar suka kai a Iraƙi.
Sojojin sun kashe wa Bassim Razzo matarsa da ƴarsa da wasu ƴan uwansa biyu a harin da suka kai ta sama a garin Mosul shekaru biyar da suka gabata.
Sojojin sama na Netherlands sun yi kurkuren kai hari ne a wasu gidaje biyu da suka yi tunanin na mayaƙan IS ne.
Akwai mutane da dama da ke son Netherlands da ke cikin ƙawancen Amurka a yaƙi da IS ta biya su diyya a wani hari da aka kai inda aka kashe mutum 70.
Buhari na taro kan samarwa ƴan Najeriya abinci
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na jagorantar taro kan samar da abinci a ƙasar.
Taron na zuwa a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kuka kan tsadar farashin kayayyaki.
Shugaban ya ce sun lura da mummunan tasirin ambaliyar ruwa da ta yi ɓarna ga manoma.
A kwanakin da suka gabata ne gwamnati ta yi ƙarin farashin fetur da kuma lantarki, matakin da ƴan Najeriya ke ganin zai ƙara haifar da tsadar kayayyaki.
Gwamnatin Buhari ta bayyana abu uku da ta ce su suka janyo halin tsadar kayayyaki da ake fuskanta amma batun rufe iyakokin kasar ba ya daga cikinsu.
Dalilan da gwamnatin ta bayar sun haɗa da tsirin annobar korona da kuma ƴan kasuwa da gwamnatin ta zarga da ɓoye abinci.
Za ku samu ƙarin bayani game da dalilan a nan
Fiye da mutum miliyan biyu suka kamu da korona a Gabas Ta Tsakiya
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce fiye da mutum miliyan biyu cutar korona ta shafa a sassan yankin Gabas Ta Tsakiya – daga Morocco zuwa Pakistan.
Hukumar ta ce adadin ya lunka a ƙasashe 21 na yankin tun daga farkon watan Yuli.
Daga cikin ƙasashen da cutar ta shafa sun haɗa da Iran da Iraƙi da Saudiyya.
WHO ta ce ƙasashe da dama sun yi ƙoƙarin rage yaɗuwar cutar kamar Jordan da Tunisia da adadin ke raguwa.
Majalisar Kaduna ta amince da dokar dandaƙa ga masu fyade
Majalisar jihar Kaduna ta amince da kudirin dokar da ke son a dinga yi wa masu dandaƙa.
Majalisar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an amince da dokar a ranar Laraba a zaman da majalisar ta yi.
Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da sarakunan arewa kan korona
Kwamitin shugaban kasa kan yaƙi da cutar korona a Najeriya na tattaunawa da sarakunan gargajiya na yankin arewacin ƙasar kan yadda za a daƙile yaduwar cutar tsakanin al'umma.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron har da Sarkin musulmi Abubakar Sa'ad na uku da kuma sauran manyan sarakunan jihohin arewa.
Har yanzu a kullum ana samun ƙaruwar masu cutar a Najeriya, duk da dadin na raguwa.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce adadin mutanen da annobar korona ta shafa a ƙasar sun kai 55,632.
Amma yawan mutanen da suka warke kuma aka sallame su daga asibiti ya kai 43,610, yayin da kuma cutar ta kashe mutum 1,070.
‘Ƴan tawayen Houthi sun cilla wa Saudiyya makami mai linzami’
Ƴan tawayen Houthi a Yemen sun yi ikirarin cewa sun harba makami mai linzami a wani yanki na Riyadh
Rahotanni sun ambato kakakin ƴan tawayen Yahya al-Sarea, na cewa sun kai harin ne a wani muhimmin wuri a Riyadh domin mayar da martani ga hare-haren da Saudiyya ke jagoranta a Yemen.
Babu dai wata sanarwa daga hukumomin Saudiyya game da ikirarin na ƴan Houthi.
Amma tun da farko kafar talabijin ta Saudiyya Al Arabiya ta bayar da rahoton cewa Saudiyya ta kakkabo wani Jirgin ƴan Houthi marar matuki a kudancin birnin Jazan.
Wannan na zuwa bayan ƴan tawayen Houthi sun yi barazanar ci gaba da kai wa Saudiyya hare-hare.
Gwamnati ta ƙarfafa tsaro a yankin rainon Ingila na Kamaru
Gwamnati ta daɗa ƙarfafa tsaro a yankin rainon ingila, musamman ma a birnin Bamenda inda dokar da hukumomi suka shimfuda na haramta zirga-zirgar babura na yin karo da dokar da ‘yan aware suka kafa ta hana motoci yin zirga-zirga.
Rahotanni na cewa ɗaruruwan dakarun tsaro ne aka aika wannan birnin, inda suka mamaye tituna suna gudanar da bincike gida-gida a wasu unguwanni, kuma suna tsare da wasu muhimman wurare.
Har ila yau kuma babu motoci a kan tituna. Duk wasu harkoki kuma sun tsaya cak, sakamakon haka.
Wata tambaya da kusan kowa da kowa yake yi ita ce, ta yaya dokar da ‘yan aware suka kafa ta rinjayi ta Gwamnati wurin mutuntawa?