Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Mustapha Musa Kaita

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Mustapha Musa Kaita

  Multi-Media Broadcast Journalist

  Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

  Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin.

  Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

 2. Shugaban Botswana ya ba matan aure damar mallakar gonaki a ƙasar

  ...

  Shugaban Botswana, Mokgweetsi Masis, ya bayyana cewa an yi gyara ga dokar ƙasar inda a halin yanzu matar aure na da 'yancin mallakar gona tare da mai gidanta.

  A baya dai, dokar ƙasar kan mallakar gonaki ta hana matan aure mallakar gona matuƙar mazajensu na da gona.

  Matan da ba su da aure ko kuma matan da mazan su ba su da gona ne kaɗai aka yarda su mallaki gonaki a baya kafin yanzu aka sauya dokar.

  Wannan bambancin da ake nunawa ya sa miliyoyin mata ba su da gonakin da za su zauna su yi aiki.

  Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi maraba da wannan sauyi inda suka ce dama ya kamata a ce tun tuni an yi wannan sauyi.

 3. Labarai da dumi-dumi'Yan bindiga sun harbe minista a Somalia

  Rahotanni daga Somalia na cewa wasu 'yan bindiga sun harbe ƙaramin minista na harkokin addini a Jowhar, babban birnin yankin Hirshabelle a daren yau.

  Gidan rediyon Risala a ƙasar ya ruwaito cewa wadanda suka aikata ɗanyen aikin sun tsere bayan harbe ministan.

  A watan Agustan da ya gabata ne 'yan bindigan suka aikata irin haka inda suka kashe Abdulkadir Abukar Karani, wanda shi ne ministan aikin gona na yankin Hirshabelle inda shi ma aka kashe shi a Jowhar.

  Babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai harin, sai dai ƙungiyar al-Shabab, mai alaƙa da ƙungiyar IS ce ta fi yawan kai hare-hare ƙasar ta Somalia.

 4. MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 17/09/2020

  Video content

  Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
 5. Buhari ya amince da sauya fasalin aikin 'yan sanda a Najeriya

  ...

  A yau ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaɓa hannu a dokar kawo sauye-sauye ga aikin ‘yan sanda a ƙasar.

  Dokar ta tanadi yadda rundunar ‘yan sandan za ta kasance mai ƙarin nagarta da kuma kyakkyawan tsari a aikinta, bisa manufofi na tabbatar da gaskiya da rikon amana a tafiyar da lamuranta da albarkatunta.

  Dokar kuma ta tanadi wani tsari na musamman da rundunar za ta rinƙa samun tallafin kuɗi kamar yadda wasu manyan cibiyoyin gwamnati suke samu, haka kuma za a ƙara inganta aikin ta hanyar horo na musamman da za a rinƙa ba jami'an.

  Aikin 'yan sanda a Najeriya na daga cikin ayyukan da suka yi ƙaurin suna ta fannin cin hanci da rashawa, kuma ana zargin hakan ya samo asali ne sakamakon rashin kyakkyawan tsari da aka ɗora aikin tun a farko.

 6. Masu gwajin korona a Faransa sun shiga yajin aiki

  ...

  Ma'aikatan lafiya da ke gwajin cutar korona a Faransa, sun shiga yajin aiki, inda suke kokawa da rashin yanayi mai kyau na gudanar da aiki.

  Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ɗaruruwan ma'aikata ne daga ɗakunan gwajin cutar korona sun shiga wannan yajin aiki, wanda hakan ya haddasa tsaiko ga gwajin da ake yi a wasu garuruwa.

  Kungiyar ta bayyana cewa za a ci gaba da wannan yajin aikin mudddun shugabannin ɗakunan gwaje-gwajen suka ƙi magance koke-koken da ma'aikatan ke yi na ƙarancin ma'aikata da kuma albashi.

 7. Ƙungiyar IS ce 'ta kashe Faransawa shida a Nijar'

  ..
  Image caption: An ga wannan motar a kusa da inda aka kai harin a watan Agusta

  Ƙungiyar IS da ke iƙirarin jihadi ta ɗauki nauyin wani hari da aka kai a Jamhuriyyar Nijar inda aka kashe ma'aikatan Faransa shida da kuma wani direba da kuma ɗan jagoransu waɗandan 'yan asalin Jamhuriyyar Nijar ne.

  An wallafa sanarwar da ƙungiyar ta fitar a shafin intanet na wata ƙungiya ta Amurka da ke tattara bayanan sirri da kuma sa ido kan rikice-rikice masu tsanani.

  An kashe mutum takwas ɗin ne yayin da suke kan hanyar su domin zuwa su ga wasu raƙuman dawa da ke gandun dabbobi na Koure.

  Rahotanni a lokacin sun bayyana cewa wasu mutane ne da suka zo kan babura suka kai harin.

  Ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya irin su Boko Haram na kai hare-hare a yankin, kuma ana yawan samun hare-hare da ƙungiyar IS ke kai wa a yankin na Sahel.

 8. Amurka ta saka takunkumi ga wasu kamfanoni

  ..

  Amurka ta saka takunkumi kan wasu kamfanoni biyu da take zargin Iran ta yi amfani da su wurin kutse ta intanet.

  Amurkar ta ce kamfanonin sun kai hari ne ga gwamnatocin wasu ƙasashe da kuma wasu masu adawa da ƙasar.

  Ma'aikatar kuɗi ta Amurka ta yi zargin cewa ma'aikatar tattara bayanan sirri ta Iran ta yi amfani da kamfanonin wurin yin kutse da cin mutunci da kuma bin diddiƙin mutane da kuma ma'aikatu da take kallo a matsayin barazana a gareta.

  Kamfanonin da take kallo a matsayin barazana na a ƙasashe kusan talatin, kamfanoni 15 daga ciki a Amurka suke.

 9. Mozambique na asarar miliyan $60 sakamakon kamun kifi ba bisa ƙa'ida ba

  ..

  Ma'aikatar kula da kamun kifi a Mozambique ta bayyana cewa ƙasar na asarar kusan dala miliyan 60 a duk shekara sakamakon kamun kifi da ake yi ba bisa ƙa'ida ba.

  Ma'aikatar ta bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon kamun kifin da ake yi a boye, kuma akasari jiragen ruwan wata ƙasa ne ke yin hakan.

  Ministar kula da harkokin kifaye a ƙasar Augusta Maita, ta bayyana cewa akasarin jiragen ruwan da aka ƙwace sakamakon kamun kifi ba bisa ƙa'ida ba, suna da rajista ne daga ƙasashe kamar Panama da Seychelles da Rasha.

  Ms Maita ta ce za a fara amfani da wani tauraron ɗan adam da za a rinƙa amfani da shi wurin sa ido kan ayyukan kamun kifi, wanda hakan zai rage kamun kifi ba bisa ƙa'ida ba.

 10. Thiago Alcantara: Liverpool ta kulla yarjejniya da dan wasan Bayern Munich kan £25m

  Thiago Alcantara ya lashe Champions league a Bayern Munich a kakar data gabata

  Liverpool ta yarda ta sayi dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara daga Bayern Munich a kan fan miliyan £20, da kuma miliyan £5 na tsarabe-tsarabe a kwangilar shekara hudu.

  Thiago mai shekara 29 ya je Bayern ne daga Barcelona a 2013 kuma ya yi mata wasa a wasan karshe na cin Kofin Zakarun Turai da suka yi nasara kan Paris St-Germain a kakar da ta kare.

  Zai sanya rigar wasa mai lamba 6 a Anfield.

  Thiago zai zama ɗan wasa na biyu da Liverpool ta saya a wannan bazarar, bayan dan bayan kasar Girka Kostas Tsimikas

  Liverpool za ta biya miliyan £20 da farko, sai kuma fam miliyan 5 da zai ta'alaka kan lashe kofin firimiya da kuma Zaarun Turai.

  Da aka tambayi kocin Liverpool Jurgen Klopp a kan sayen Thiago a satin da ya wuce, ya amsa cewa: “ ba zan iya cewa komai kan jita-jita ba tunda har yanzu kasuwar ciniki a bude take”.

 11. Hotunan yadda jirgin sama ke zagaye da minista Sadiya ta na duba ɓarnar ambaliya

  Sadiya Farouq

  Ministar jin-ƙai Sadiya Farouq na shawagi a cikin jirgi inda take duba irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta haddasa sakamakon ɓallewar madatsar kainji.

  Sadiya Farouq
  Sadiya Farouq
 12. An rage farautar giwa ba bisa ka'ida ba a Mozambique

  Giwaye

  Ministan kasa da Muhalli a Mozambique, Ivete Maibasse ta ce an samu ragi da kashi 70 cikin 100 na farautar giwa ba bisa ka'ida ba.

  Ta ce hakan baya rasa nasaba da irin matakan tsaro da aka inganta domin kare wurin da dabobbin ke rayuwa.

  "Kafin 2014, ana rasa giwaye 1,200 a shekara," a cewarta, ta kara da cewa adadin ya ragu zuwa 360 a shekara tsakanin 2015 zuwa 2019.

  Ministar ta ce Niassa Reserve, yanki mai tsaro mafi girma a kasar, babu giwa guda da aka yi farautar ta a cikin shekaru biyu da suka gabata.

 13. Cin zarafi 'bai sauya ba a Burundi duk da cewa anyi sabon shugaban ƙasa'

  Burundi

  Hukumar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce babu wani sauyi da aka samu a fanin kare haƙƙin bil adama a Burundi duk da zaɓen sabon shugaban ƙasa da aka yi.

  Masu binciken sun ce har yanzu dimokuradiyya ba ta samu wurin zama ba kamar yadda ya kamata, sannan ana samun wasu shafaffu da mai da ba a hukuntawa, bayan shugaba Eversite ya maye gurbin Pierre Nkurunziza.

  An naɗa ɗaiɗaikun mutanen da ya kamata su fuskanci hukunci kan manyan matsayi a gwamnatin Burundi.

  MDD ta ce tana da shaida kan yadda ake tsare mutane da yadda ake azabtar da su da kuma cin zarafinsu kafin da kuma bayan zaɓe a watan Mayu.

 14. Dan wasan gaba Gareth Bale ya shirya komawa Tottenham a matsayin dan aro

  Gareth Bale

  Dan wasan gaban Real Madrid Gareth Bale ya shirya tafiya ingila a ranar Juma’a domin kammala yarjejeniyar komawar sa Tottenham Hotspur.

  Har yanzu ana sasantawa kan yarjejeniyar da za a cimma da Bale mai shekara 31, wanda zai je Tottenham a matsayin ɗan aro daga Real Madrid.

  Ƙungiyoyin biyu har yanzu na kan tattauna wa wanda ake sa ran za su kammala nan bada jimawa ba, kafin tafiyar Bale Landan.

  Tun asali ɗan wasan na taka rawa ne a Tottenham bayan komawar sa ƙungiyar daga Southampton a 2007, sannan ya koma Real Madrid ne a 2013 kan miliyan £85.

  Ya zura wa Real Madrid ƙwallaye fiye da 100, sannan ya lashe mata kofin zakarun Turai sau hudu.

 15. Labaran duniya cikin Minti ɗaya na rana

  Video content

  Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana 17/09/2020
 16. Akwai yiwuwar a soma wahalar man fetur a Abuja da sauran jihohin arewacin Najeriya

  Man fetur

  Akwai yiwuwar a soma fuskantar ƙarancin man fetur sakamakon yajin aikin da ƙungiyar direbobin daƙon mai ta soma a yau Alhamis.

  A wata sanawar da ta fitar jiya Laraba shugaban ƙungiyar na ƙasa, Otuba Salimon Oladiti, ya ce matakin ya zama dole saboda umarni da gwamnatin Neja ta bayar na hana manyan motoci ratsawa ta titunan jihar.

  A cewar Otuba, daga ranar 15 ga watan Satumba jihar Neja ta sanar da cewa babu wata babbar mota da za ta amince ta sake ratsa Jihar.

  "Mun dau wannan matakin ne sakamakon datse hanya da gwamnatin Neja ta yi ga manyan motoci ciki har da mu da ke ratsawa ta jihar idan mun dauko mai daga Legas zuwa arewacin ƙasa.

  "Hanyar da ta rage mana motar ba ta iya bi. Hanyar Bida -Agai - Lambata, ta lalace baki-daya, kuma hadari ne a gare mu."

 17. New Zealand ta faɗa cikin matsin tattalin arziki

  New Zealand ta faɗa cikin matsin tattalin arziki a karon farko tun bayan saka dokar kullen korona.

  Shi ne karon farko da ta fuskanci irin wannan matsi a cikin shekaru sha daya.

  Duk da cewa mutum 25 korona ta kashe a ƙasar, annobar ta yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikin ta musamman fannin yawon buɗe ido.

  A wata mai zuwa za a gudanar da babban zaɓe a ƙasar, kuma jam'iyya mai mulki ta Labour na fatan ganin bayan annobar da kuma cike giɓin da ta yi wa tattalin arzikin ƙasar.

 18. 'Wani babban al'amari na faruwa' WHO ta yi gargadi

  Alkaluman duk mako da ake samu na masu kamuwa da cutar korona ya zarce wanda aka rinka bada rahotaninsu lokacin da annobar ta soma kai wa kololuwa a Turai a watan Maris, hukumar lafiya ta WHO ta yi gargadi.

  "Wani babban al'amari na faruwa a kan cutar," a cewar daraktan hukumar na Turai a lokacin wani taron manema labarai yau Alhamis.

  Hans Kluge ya kara cewa alkaluman da ake samu a watan Satumba su kasance abin "jan hankali" ga gwamnatocin Turai, yayinda masu kamuwa da cutar suka kai wa dubu 300 a makon da ya gabata.

 19. Gwamnatin Kano ta yi watsi da bukatar MDD kan wanda ya yi ɓatanci

  Kano

  Gwamnatin Kano ta ce ba za ta sauya matsayinta ko na kotun shari'a ba, kan hukuncin da aka yankewa yaron nan Omar Faruk kan laifin kalaman ɓatanci kan annabi, tare da cewa shekarun sa 16.

  Asusun kula da ilimin kananan yara na Unicef ya bukaci gwamnatin tarayya ta taka rawa wajen ganin gwamnatin Kano ta gaggauta janye hukunci da sake nazarin shari'ar da ta yi wa yaron mai shekara 13.

  A ranar 10 ga watan Agusta ne wata kotun shari'ar musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin shekara 10 kan yaron da aiki mai sassauci.

  Unicef a wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba a Abuja ta ce hukuncin ya ci karo da dokokinta na kare haƙƙin yara na 1991, da Najeriya ta aminta da shi.

 20. Ƴan bindiga sun kai wa ƴan sanda hari a Sokoto 'sun kashe DPO'

  Sokoto

  Wasu ƴan bindiga sun kai hari a garin Gidan Madi da ke karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto.

  Maharan sun kai harin ne a ofishin ƴan sanda a tsakar dare kuma har sun kashe DPO a garin, kamar yadda wasu mazauna garin suka shaida wa BBC.

  Wani mazauni garin ya ce suna bacci suka ji ƙarar harbe-harben bindiga wanda ya tayar da su daga bacci.

  Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar wa BBC da harin, amma kakakin ƴan sandan jihar, ASP Muhammad Sadiq bai yi ƙarin haske ba musamman game da kashe DPO da ƴan bindigar suka yi.

  Latsa nan don karanta karin bayyani