Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Bayan shafe yinin Alhamis muna kawo labarai da rahotanni kai-tsaye a wannan shafin, a nan za mu dakata sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu inda za mu shafe yinin Juma'a muna kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sassan duniya.

  Da fatan za ku kasance da mu.

 2. Hotunan Buhari a Guinea Bissau

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya halarci bikin ranar samun ƴancin kan ƙasar Guinea Bissau da aka gudanar ranar 24 ga watan Satumba.

  Shugaban na Najeriya ya kaddamar da wata sabuwar hanya da aka raɗa wa sunansa yayin bikin na Guinea Bissau da aka gudanar ranar Alhamis.

  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
  Hotunan Buhari a Guinea Bissau
 3. Amurka ta ba Najeriya tallafin korona dala miliyan biyu

  Amurka ta ce ta tallafa wa Nijeriya da kudi sama da dala miliyan biyu don kyautata fahimtar tsananin yaduwar da cutar korona ta yi a ƙasar.

  Ta ce gwamnatinsu ta samar da wannan tallafi ne ta hannun Hukumar Taƙaita Yaɗuwar cutuka ta Amurka, da nufin gudanar da wani binciken gida-gida a jihohin Gombe da Nasarawa da kuma Enugu.

  Ta ce binciken zai ƙara fahimtar da ake da ita kan yaduwar cutar korona, da kuma tasirin hakan a cikin jihohin uku, domin sanin ɗaukin da ya kamata gwamnati da ƙawayenta su kai.

  Ku saurari rahoton Mukhtari Adamu Bawa

  Video content

  Video caption: Amurka ta ba Najeriya tallafin korona dala miliyan biyu
 4. Ina karanta littafin wani Bature kan zaben sabon Sarkin Zazzau - El-Rufa'i

  Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce yayin da ya ke jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani tsohon littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.

  A shafinsa na Twitter, El-Rufa'i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken "Gwamnati a Zazzau." wanda aka buga a 1960.

  Gwamna El- Rufa'i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau.

  View more on twitter
 5. An kama tsoffin kwaroron roba 320,000 da ake mayar wa sabbi

  Ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar.
  Image caption: Ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar.

  Ƴan sanda a Vietnam sun ce sun kama kwaroron roba sama da 320,000 da aka yi amfani da su kuma ake sayar wa ba bisa ka’ida ba ga masu buƙata.

  An nuna hotunan kwaroron da dama da nauyinsu ya kai 360kg a wani babban wurin ajiye kaya wanda a kwanan baya aka kai wa samame a kudancin lardin Binh Doung.

  An kama matar da ake tunanin ita ke da wurin ajiye kayan.

  Rahotanni sun ce ana wanke kwaroron ne a gyara sannan a sake mayar da su kamar sabbi a sayar.

  Matar ta ce akwai kuɗi da ake biyanta kan ko wane kwaroron roba.

  Babu dai tabbaci kan yawan waɗanda aka sayar a kasuwa.

 6. Yadda Amurkawa suka yi wa Trump ihun 'ba ma yi'

  Dandazon jama'a a harabar Kotun Ƙolin Amurka sun yi ta yi wa Shugaba Donald Trump ihu da sowar ''kar ku zaɓe shi.''

  Shugaban ya ziyarci kotun ne a ranar Alhamis da safe don nuna girmamawarsa ta bakwana ga marigayiya mai shari'a Ruth Bader Ginsburg.

  Trump ya ƙagara ya maye gurbin Ginsburg kafin zaɓen 3 ga watan Nuwamba na shugaban ƙasa - abin da ƴan Democrats ba sa so.

  Video content

  Video caption: Amurkawa sun yi wa Trump ihun "ba ma so" a kotun koli
 7. Abin da ya faru a Mali zai iya faruwa a Nijar – Hama Amadou

  Jagoran adawar Nijar Hama Amadou

  Jagoran adawa a Nijar Hama Amadou ya yi gargadin cewa rikicin siyasa da ya faru a Mali zai iya faruwa a Nijar idan har koton kundin tsarin mulki ta ki amincewa da takararsa.

  Tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar ya faɗi haka ne a wani taron manema labarai da ya gabatar, kamar yadda jaridar ActuNiger ta ruwaito.

  A cewar jaridar, Hama ya ce abin da gamayyar ƴan adawar Mali suka yi zai iya faruwa a Nijar.

  Ya ce duk matakin da kotun kundin tsarin mulki ta ɗauka za a iya soke shi idan mutane sun so. Ya ce wannan kira ne yake yi ga jama’arsa.

  “Wannan mataki ne na sauya abubuwa ba za a bari su ci gaba da ɗorewa ba,” in ji shi.

  Hama Amadou wanda sau biyu yana shan kaye a zaben shugaban ƙasa, a makon da ya gabata ne jam’iyyarsa ta sanar da shi a matsayin ɗan takararta a zaɓen shugaban kasa da za a yi watan Disamba.

  Ana tunanin zai fuskanci ƙalubale kan takararsa bayan shafe tsawon shekara ɗaya a gidn yari kan batun safarar jarirai.

 8. Gobarar tankar gas a Legas ta kone gidaje da motoci

  Hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas LASEMA ta ce wata tanka da keɗauke da gas ta fashe bayan ta yi hatsari a daidai wurin ɗaukar fasinja a Iju Ishaga.

  Hukumar ta ce gidaje da motoci da dama ne suka ƙone sakamakon gobarar da tankar ta haddasa.

  Sannan mutane da dama ne suka samu rauni, waɗanda aka garzaya da su zuwa asibiti.

  View more on twitter

  Wasu rahotanni sun ce kusan mutum 50 suka ji rauni sakamakon gobarar.

  Hukumar LASEMA ta jihar Legas ta wallafa bidiyo a Twitter da ke nuna girman ɓarnar da gobarar ta haifar

  View more on twitter

  Ga hotunan girman ɓarnar gobarar a Legas

  Hotunan gobarar Legas
  Hotunan gobarar Legas
  Hotunan gobarar Legas
  Hotunan gobarar Legas
 9. 'Sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan Boko Haram da dama a Malam-Fatori'

  Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar hallaka manyan mayakan kungiyar Boko Haram da dama tare da lalata sansanoninsu a garin Malamfatori da ke yankin arewacin Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

  Ta kuma ce a wani artabu na daban, daya daga cikin kwamandojin kungiyar ya mika kan sa tare da matansa hudu ga sojojin Najeriyar.

  Rundunar sojin Najeriyar ta jima a yankin suna artabu da mayakan a yankin arewa maso gabashin kasar.

  Kwamanda Abdussalam Sani jami’in hulɗa jama’a a cibiyar samar da bayanai a rundunar sojin Najeriya, ya kuma yi wa Bilkisu Babangida karin bayani ta wayar tarho.

  Ku latsa lasifikar da ke ƙasa don sauraron hirar:

  Video content

  Video caption: Hirar Bilkisu Babangida da Kwamanda Abdussalam Sani
 10. An samu fashewar wani abu a Legas

  Fashewar gas

  A yau Alhamis da rana ne aka samu wata fashewa a yankin Iju da ke Legas.

  Ba a san abin da ya jawo fashewar ba amma mutane da dama na zargin gas ne.

  Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe uku na rana a kusa da tashar bas ta Cele a Ajuwon.

  Ajuwon wani yanki ne da ke tsakanin iyakar jihar Legas da Ogun. Mutanen da ke zaune a yankin sun yi ta gudu ta kai ta kai don ceton rnsu.

  Yankin Iju da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Ikeja yanki ne da ke cike da cunkoson jama'a.

  A ƙalla an samu manyan fashewar gas a Legas sau uku tun shiga shekarar nan ta 2020, waɗanda suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.

 11. China ta gina cibiyoyi 400 domin tsare Musulmai - Australia

  Shugaban China

  Wani kwamitin ƙwararru na Australia ya ce China ta gina cibiyoyi kimanin 400 domin tsare Musulmai ‘yan ƙabilar Wiga marasa rinjaye da ke rayuwa a lardin Xinjiang, wato karin kashi 40 cikin dari kan adadin da aka yi hasashe a baya.

  Cibiyar tsare-tsare ta Australia ta ce, ta yi amfani da hotunan tauraron dan adam wajen gano sama da cibiyoyi 380 da ake zargin an gina.

  Akwai kuma gwammai da ake ci gaba da ginawa, duk da ikirarin gwamnatin na cewa tana amfani da cibiyoyin ne wajen sake horar da ma’aikata.

  Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan sahihin rahoton ya nuna cewa akwai miliyoyin musulmai ‘yan kabilar Wiga da ake tsare da su a sansanonin ba tare da shari’a ba, yayin da ake ci gaba da samun rahotannin azabtarwar da ake musu.

 12. Ƴan Republican sun ce za su karbi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa duk yadda ya fito

  Manyan 'yan jam'iyyar Republican sun bayyana cewa jam'iyyarsu za ta karbi sakamakon zaɓen shugaban ƙasa duk yadda ya fito.

  'Yan jam'iyyar sun bayyana hakan ne bayan da Donald Trump ya ƙi bayyana matsayarsa kan ko zai ika mulki cikin ruwan sanyi ko kuma akasin hakan.

  Shugaban Jam'iyyar Republican a Majalisar Dattawan Ƙasar Mitch McConnell ya bayyana cewa za a rantsar da wanda ya ci zaɓen a watan Janairu.

  Ya bayyana cewa za a bi tsari wurin rantsar da wanda ya ci zaɓen kamar yadda aka saba a duk bayan shekara huɗu, kamar yadda aka fara hakan tun a 1792.

  Trump
 13. Isra'ila ta saka wasu sabbin dokokin korona

  Netanyahu

  Isra’ila ta sanar da sanya wasu sabbin dokokin kullen annobar korona a yau, wadanda za su hada da kulle kusan duka wuraren aiki, da kuma takaita zuwa wuraren ibada da fita zanga-zanga.

  An takaita ‘yancin zanga-zanga – wanda ake ganin hakan zai iya kawo karshen zanga-zangar makonni ukun da ake yi kan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu.

  ‘Yan hamayyar kasar dai na zargin Firaiministan da daukar wannan mataki domin takura musu.

  An sanya dokar kullen makonnin uku a fadin kasar ne tun ranar Juma’ar da ta gabata – inda shugabannin ‘yan adawa ke zargin gwamnati da gazawa wajen yaki da cutar ta korona.

 14. Covid-19: Za a gurfanar da manyan jami'an gwamnati a Kenya kan zargin almubazaranci

  ...

  Masu bincike a Kenya za su gurfanar da aƙalla manyan jami'an gwamnati 15 da 'yan kasuwa gaban kotu, sakamakon zarginsu da almubazarancin miliyoyin daloli da aka ware domin sayen magungunan korona.

  A binciken da aka gudanar, an gano wasu takardu da ke nuna yadda aka bai wa jami'an da 'yan siyasa kwangilar.

  Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin a gudanar da bincike sakamakon kiraye-kirayen da al'ummar ƙasar ke yi.

  Kuɗin da ake zargi sun karɓa sun kai kusan dala biliyan biyu

 15. Zlatan Ibrahimovic ya kamu da cutar korona

  Zlatan Ibrahimovic

  Dan wasan AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya kamu da cutar korona.

  Dan kasar ta Sweden mai shekara 38 ya killace kansa a gida, a cewar kungiyar.

  An tabbatar ya kamu da cutar ne bayan ya yi gwaji na biyu kuma bayan dan wasan baya Leo Duarte ya kamu da cutar ranar Laraba, sannan sakamakon gwajin da aka yi wa sauran 'yan wasa da ma'aikatan kungiyar ya nuna cewa ba sa dauje da cutar.

  'Yan wasan biyu ba za su buga zagaye na uku na wasan neman cancantar shiga gasar Europa da Bodo/Glimt ranar Alhamis ba.

  Ibrahimovic ya zura kwallaye biyun da Milan ta doke Bologna ranar Litinin.

  A watan jiya ne ya tsawaita zamansa a kungiyar da shekara.

 16. Sojojin Koriya Ta Arewa sun harbe tare da ƙona jami'in Koriya Ta Kudu

  ..

  Ma'aikatar tsaro ta Koriya Ta Kudu ta bayyana cewa dakarun Koriya Ta Arewa sun harbe wani jami'in ƙasarta sa'annan suka ƙona shi.

  Ma'aikatar ta nuna rashin jin daɗinta dangane da lamarin.

  Koriya Ta Kudu ta bayyana cewa jami'in da aka kashe ya kasance ma'aikacin hukumar kula da harkokin kifi, kuma ya yi ɓatar dabo daga wani jirgin ruwa da ke sintiri kusa da iyakar ƙasashen biyu, wanda daga baya aka ga gawarsa cikin ruwan Koriya Ta Arewa.

  A martanin da ma'aikatar tsaron Koriya Ta Kudu ta mayar, ta yi zargin cewa sojojin Koriya Ta Arewa ne suka harbe shi, suka saka masa mai a jikinsa, sa'annan kuma suka ƙona shi.

  Har yanzu dai Koriya Ta Arewar ba ta mayar da martani ba kan batun.

 17. MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA - 24/09/2020

  Video content

  Video caption: Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren labaran
 18. Me ya sa Saurez yake yawon jawo ce-ce-ku-ce?

  A cikin wannan bidiyon, dalibi da ke sanin makamar aiki tare da BBC Hausa, Abdulrazak Bello Kumo ya yi mana nazari kan abin da ya sa ɗan wasan ƙwallo Saurez yake yawon jawo ce-ce-ku-ce.

  Video content

  Video caption: Me ya sa Saurez yake yawon jawo ce-ce-ku-ce?
 19. An yanke wa wasu mawaƙa hukuncin ɗaurin watanni biyu a Sudan

  Wata kotu a Sudan ta tura wasu mawaƙa shida zaman gidan yari na watanni biyu bayan samunsu da laifin neman haddasa fitina.

  Ko a makon da ya gabata ma sai da aka yanke wa wasu mawaƙan irin wannan hukuncin.

  Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da wani mai shirya fina-finai, Hajooj Kuka. An kama su ne tun a watan Agusta bayan wasu mahara waɗanda ba a kama su ba suka nemi hargitsa wasan da suke yi a wani fagen wasanni.

  Wasu sun bayyana cewa jami'an Sudan ne waɗanda ke adawa da tsare-tsaren gwamnati tun bayan hamɓare shugaba al-Bashir ne suka ƙulla wa mawaƙan makirci.

 20. Najeriya za ta yi gwanjon jirgin shugaban ƙasa

  ..

  Gwamnatin Najeriya ta saka ɗaya daga cikin jiragen shugaban ƙasar a kasuwa domin yin gwanjonsa.

  Wasu jaridun Najeriya a ranar Laraba sun wallafa tallar Jirgin mai suna, Hawker 4000, mai lamba kamar haka: 5N-FGX/: RC 066 a shafukansu.

  Tallar jirgin ta ce gwamnatin Najeriyar ta fara amfani da jirgin ne tun a 2011, kuma yana ɗaukar fasinjoji tara, da ma'aikatan jirgi uku.

  Ko a kwanakin baya ma sai dai gwamnatin ƙasar ta yi gwanjon wasu jiragenta guda biyu domin rage nauyin da ke kanta na kula da jiragen.