Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bin mu a wannan shafi na BBChausa.com a nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotanni kai tsaye na abubuwan da suka dinga faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

  A Najeriyar dai a yau bikin murnar shekra 60 da samun ƴancin kan ƙasar daga Turawan Mulkin Mallaka ne ya mamaye komai.

  Ga wasu daga cikin labaran da za ku iya karantawa idan sun wuce ku:

  Nigeria @60: Ana gudanar da fareti a Dandalin Eagle

  Nigeria @60: Muhimman abubuwa biyar da Buhari ya ce yayin jawabinsa

  Nigeria @60: Wasu 'yan Najeriya sun fito zanga-zanga

  Baƙin halittu za su mamaye wasu wuraren da babu mutane a duniya

  An yi wa ginin da ya fi tsayi a duniya na Dubai adon taya Najeriya murna

  Atletico Madrid ta taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 60 da samun ƴancin kai

  Turkiyya za ta kafa wasu tsauraran sharudda kan kafafen sada zumunta

  Za a buɗe makarantu a Kano daga 11 ga watan Oktoba

  Sai ku biyo mu gobe da safe don ɗorawa daga inda muka tsaya. Halima Umar Saleh ce ke fatan Allah Ya sada mu da alkhairanSa.

 2. An kama fiye da mutum 500 a Habasha 'masu ƙoƙarin tayar da rikici'

  Hukumomi a jihar Oromia da ta fi yawan jama'a a Ethiopia sun kama mutane sama da dari biyar, wadanda suka yi zargin cewa suna shirin tayar da husuma a lokacin wasu bukukuwan al'ada na shekara shekara.

  'Yan sanda sun ce an kama makamai da kuma nakiyoyi.

  Ranar Asabar da Lahadi ne za ayi bukukuwan a Adis Ababa, babban birnin kasar, da sauran yankuna na Oromia.

 3. Shugaban Turkiyya ya yi watsi da kiraye-kirayen kasashen duniya na kawo karshen fada tsakanin Armeniya da Azarbaijan

  Recep

  Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi watsi da kiraye-kirayen wasu kasashen duniya na kawo karshen fada tsakanin Armeniya da Azarbaijan a yankin Nagorno-Karabakh da ake takadama kansa.

  Mr Erdogan ya ce za a samu zaman lafiya ne kawai idan Armeniya ta janye dakarunta daga yankin, wanda ya ɓalle, wanda kuma a hukumance ɓangare ne na Azarbaijan, amma kuma 'yan ƙabilar Armeniyawa ne ke mulkinsa.

  Rasha da Faransa da kuma Amurka duk sun buƙaci a gaggauta dakatar da kai hare-hare a kwana na biyar na yaki a yankin na Nagorno- Karabakh.

 4. Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na bana na UEFA

  Lewandowski

  Dan wasan Bayern Munich ɗan kasar Poland Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na bana na hukumar kwallon kafar Turai UEFA.

  Lewandowski mai shekara 32 ya yi nasara a kan Manuel Neuer da suke ƙungiya ɗaya da kuma Kevin de Bruyne na Manchester City wajen lashe kyautar.

  Lewandowski ya ci ƙwallaye 55 a wasa 47 a kakar bara inda Bayern ta lashe Gasar Zakarun Turai da ta Bundesliga da kuma German Cup.

  Ya ci ƙwallo 16 fiye da duk wani ɗan wasa a manyan lig-lig biyar na Turai a dukkan gasar da aka yi a kakar 2019-20.

  Hukumar ta bayar da kyautar mata ga Pernille Harder yar kasar Denmark mai buga ma Chelsea wasa.

  Dama ta taɓa lashe kyautar shekaru biyu da suka wuce.

  A jadawalin rukunin gasar zakarun kulob na Turan na bana, an hada Bayern Munich da Atletico Madrid a rukuni guda.

  Juventus kuma da Barcelona a wani rukunin, inda hakan ke nuna cewa za a gwada yar ƙashi tsakanin Cristiano Ronaldo da Lionel Messi.

 5. Ku saurari labaran duniya cikin minti ɗaya da BBC Hausa

  Video content

  Video caption: Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 01/10/2020
 6. Shugaban Ghana ya ja kunnen ‘yan aware cewa jami’an tsaro za su yi maganinsu

  Nana Akufo

  Shugaba Nana Akufo Addo na kasar Ghana ya yi wa ‘yan aware masu rajin ɓallewa daga kasar kashedi cewa jami’an tsaron kasar za su yi maganinsu.

  Ya yi wadannan kalaman ne bayan hare-haren da aka kai wa wasu chaji ofis biyu a yakin Volta da ke kudu maso yammacin Ghana.

  Mutane 34 ne dai aka kama bias zarginsu da hannu a kai harin.

 7. Tsohon shugaban Saliyo Bai Koroma ya musanta zargin da ake masa na almundahana

  Bai Koroma

  Tsohon shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma ya musanta zargin da ake masa na almundahana, yana cewa dalilai na siyasa ne kawai suka sa aka kitsa su.

  Wani rahoto dake binciken cin rashawa a zamanin mulkin Mr Koroma na shekaru goma ya gano mutane sama da dari da ake son yi ma tambayoyi.

  Binciken na nuna cewa miliyoyin daloli ne suka bace. A sakamakon haka, gwamnati ta sa takunkumin hana tafiye tafiye ga tsohon shugaban kasar, da kuma sairan jami'ai.

  A makon gobe ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Saliyo zata gana da Mr Koroman.

 8. Mutane biyu sun mutu bayan sake bude gidajen giya a Kenya

  Uhuru

  Mutane biyu ne suka rasa rayukansu kwana daya kacal da sake bude gudajen shan barasa a kasar Kenya, mutanen sun mutu ne bayan sun ba hammata iska a wani gidan giya a Nairobi babban birnin kasar ta Kenya,

  A ranar Laraba ne sakataren ma'aikatar lafiya ta kasar Rashid Aman ya ce dole ne masu gidajen giya su rika bin dokokin da aka gundaya wajen kiyaye yaduwar cutar Corona.

  Ya bayyana mutuwar a matsayin '' abin takaici'' kana ya ce lamarin '' abin bakin ciki ne fargaba''.

  An dai amincewa giidajen shan barasar da su rika kasancewa a bude har zuwa karfe goma na dare, sa'a daya kafin dokar hana fitar dare da fara aiki.

  A ranar Talata ne bayan da aka amince gidajen giyar su sake budewa, masu sheke aya suka makare gidajen shan barasar, kana giudajen talabijin suka rika nuna dandazon mutane a gidajen giya daban-daban.

  Kasar Kenya na da adadin masu dauke da cutar Corona kimanin 38,529 , da suka hada da mutuwar mutane 71.

 9. Baƙin halittu za su mamaye wasu wuraren da babu mutane a duniya

  Aliens

  Masu bincike sun ce yawan baƙin halittun da ke mamaye wuraren da mutane ba su fiye zama ba a duniya na ƙara ƙaruwa da kusan fiye da rubu'i a cikin tsakiyar ƙarni tun daga matakin shekara ta 2005.

  Sun ce nahiyar Turai za ta fi fuskantar wannan matsala, da kusan kimanin baƙin halittu 2,500 da ake sa ran za su yi kaka-gida a yankin sammai da ƙassai da kuma ruwa.

  Burtaniya kadai kan kashe fiye da dala miliyan dari biyu a duk shekara wajen kokarin kawar da nau'in baƙin halittu da aka yi wa lakabi da ''Japanese Knotweed''.

  Masana kimiyya sun ce tsaurara dokokin cinikayya zai taimaka wajen rage yaduwar irin wadannan halittu masu mamaya.

 10. An yi wa ginin da ya fi tsayi a duniya na Dubai adon taya Najeriya murna

  Burj Khalifa

  Kamfanin jiragen sama na Emirates na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya taya Najeriya murnar shekara 60 da samun ƴancin kai.

  Shafin Emirate na Facebook ya wallafa hoton ginin da ya fi kowanne tsayi a duniya da ke Dubai wato Burj Khalifa wanda aka yi masa ado da launukan tutar Najeriya don taya ƙasar murna.

 11. Jagoran ƴan adawar Rasha ya ce Putin ne ya saka masa guba

  Navalny

  Jagoran 'yan adawar kasar Russian mai fafutika Alexei Navalny ya ce ya yi amanna Shugaba Vladimir Putin na da hannu wajen saka masa guba.

  "Na tabbata cewa Putin na da hannu wajen aikata haka, ba ni da wani karin bayani da zan kara yi,'' ya shaida wa mujallar Der Spiegel ta kasar Jamus a wata tattaunawa.

  Kasar Jamus din, inda Mr Navalny ke ci gaba da murmurewa a can, ta ce an saka masa gubar ne ta hanyar sinadarin Novichok.

  Dakunan binciken kasashen Faransa da Sweden ne suka tabbatar sakamakon.

  Fadar Kremlin din ta musanta cewa tana da hannu.

  Yayin da yake mayar da martani a wata tattana wa a ranar Alhamis, mai magana da yawun Mr Putin ya ce babu wata shaida da ta nuna cewa an saka wa Mr Navalny guba, kana ya ce jami'an hukumar binciken laifuka ta CIA na aiki ne tare da jagoran adawar.

 12. Atletico Madrid ta taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 60 da samun ƴancin kai

  Ƙungiyar ƙwallon ƙafa a Spaniya ta Atletico Madrid, ta taya ƴan Najeriya murnar cika shekara 60 da samun ƴancin kai.

  A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Tuwita a ranar Alhamis ƙungiyar ta ce: ''Muna taya magoya bayanmu ƴan Najeriya murnar cika shkera 60 samun ƴancin kai.''

  View more on twitter
 13. Turkiyya za ta kafa wasu tsauraran sharudda kan kafafen sada zumunta

  Turkey president

  Turkiyya za ta kafa wasu tsauraran sharudda kan kafafen sada zumunta na zamani, matakin da masu sharhi ke cewa zai takura wa 'yan adawa, ya kuma kawo karshen 'yancin fadin albarkacin baki a kasar.

  A sharuddan, tilas ne duk wani dandalin sada zumunta da mutane sama da miliyan guda ke amfani da shi a kullum, ya bude ofis a Turkiyya, domin aiki da umurnin kotun kasar na cire wasu abubuwan da suka wallafa na cin zarafi, cikin kwanaki biyu.

  Kuma wajibi ne su taskace dukkan wasu abubuwan da ake wallafawa a Turkiyyar.

  Idan kamfanoni irin su Facebook da Instagram da Twitter suka ƙi aiki da wannan umurni suna iya fuskantar tara mai ɗumbin yawa da rage masu ƙarfi a cikin kasar, lamarin da zai sa a kasa amfani da su.

  Jami'in kare hakkin jama'a na Facebook, Ian Levine ya ce sabin sharuɗɗan kokari ne na takaita yada labarai ta intanet da ba taba ganin irinsa ba.

 14. Za a buɗe makarantu a Kano daga 11 ga watan Oktoba

  Ganduje

  Gwamnatin Kano ta amince da a bude makarantu a jahar Kano inda za a buɗe su daga 11 ga watan Oktoba.

  Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sunusi Muhammad Kiru ne ya sanar da haka a yayin ganawa da BBC.

  Ya bayyana cewa 'yan ajji shida da biyar na firamare za su koma makaranata a ranar 11 ga watan Oktoban 2020.

  Yan aji ɗaya da biyu za su rinƙa zuwa makaranta a ranakun Litinin da Talata kawai, inda za su fara daga 12 ga watan Oktoba.

  Sai kuma 'yan aji uku da huɗu da biyar na makarantun firamare su ma za su rinƙa zuwa Laraba da Alhamis da Juma’a inda za su koma 12 ga watan Oktoba.

 15. Lebanon da Isra'ila za su tattauna kan iyakar ruwa

  ..

  Ƙasashen Lebanon da Isra'ila za su gudanar da tattaunawa ta musamman a yunƙurinsu na kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu kan batun iyaka ta ruwa.

  Kakakin Majalisar Lebanon ya bayyana cewa an amince kan batun da ƙasashen za su tattauna a kai, inda za a yi tattaunawar da taimakon Majalisar Ɗinkin Duniya.

  Ministan makamashi na Isra'ila ya bayyana cewa za a fara tattaunawar a tsakiyar watan Oktoba.

  Amurka dai ta kira wannan tattaunawar da za a yi matsayin wani abu na tarihi bayan an shafe kusan shekara uku ana neman haɗa wannan tattaunawa.

  Isra'ila da Lebanon sun fara rikici ne tun tsakanin 1948-1949 a lokacin yaƙin ƙasashen Larabawa da Isara'ila.

 16. Najeriya @60: Hotunan bikin cikar Najeriya shekara 60

  ..
  ..
  ...
 17. Ɗan sanda ya fasa wa ɗan jarida kai a wurin zanga-zanga

  ..

  'Yan sanda a jihar Legas sun cafke wasu da suka fito zanga-zanga a jihar a yau inda har wani ɗan sanda ya fasa wa wani ɗan jarida kai da kulki, a daidai lokacin da ƙasar ke murnar cika shekara 60 da samun 'yancin kai.

  Masu zanga-zangar sun fito ne domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda al'amura ke tafiya a Najeriya.

  Rahotanni sun bayyana cewa tun da farko dai masu zanga-zangar sun fito sun yi ta a cikin lumana tare da sa idon 'yan sanda.

  Bayan masu zanga-zangar sun kammala tattakinsu, sai wasu rukunin 'yan sanda kuma suka zo inda suka fara kama masu zanga-zangar da kuma cin zarafin 'yan jarida.

  Ɗaya daga cikin 'yan sandan ya yi amfani da kulki inda ya rantama wa ɗan jaridar Punch.

  Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas ya bayyana cewa tuni aka ɗauki ɗan jaridar zuwa asibiti domin yi masa magani.

  Ɗaruruwan mutane ne dai suka fito zanga-zangar a biranen Legas da Abuja da Benin City da Kogi da wasu biranen yayin da ƙasar ke cika shekara 60 da samun 'yancin kai.

  Cikin waɗanda suka fito zanga-zangar har da Omoyele Sowore, Babban Editan Jaridar Sahara Reporters, da kuma Aisha Yessufu, ɗaya daga cikin masu gwagwarmaya a ƙasar.

 18. Ambaliyar ruwa ta saka ƴan Sudan a halin yunwa

  Sudan Flood

  Hukumar abincin da ayyukan noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mummunar ambaliyar ruwan Sudan ta shafi kusan kashi daya cikin uku na amfanin gonar da aka shuka, da kuma gidaje kimanin 600,000.

  Sama da tan miliyan guda na hatsi ne ya lalace, musaman dawa, wadda ita ce aka fi amfani da ita, lamarin da ya sa iyalai da dama sau daya suke iya cin abinci a rana.

  Ambaliyar ta halaka mutum sama da 100. Haka nan lamarin ya shafi wasu daga cikin kayan amfanin gonar da ake nomawa don samun kudin shiga irin su ayaba da kuma mangwaro.

 19. An kama shugabannin jam'iyyar adawa a Indiya a hanyar zuwa ta'aziyyar budurwar da aka yi fyaɗe

  Indiya

  An kama wasu shugabannin jam'iyyar adawa ta Congress a Indiya, a wajen birnin Delhi, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa don gana wa da iyayen wata budurwa da ta rasu sakamakon fyaɗen da aka yi mata na taron dangi.

  An tsayar da Rahul Gandhi da ƙanwarsa Priyanka ne lokacin da suka yi ƙoƙarin takawa a ƙasa zuwa kauyen da yarinyar ta fito a jihar Uttar Pradesh.

  Hotunan talabijin sun nuna Mr Gandhi ya faɗi ƙasa a lokacin hayaniyar.

  Hukumomin jihar dai sun taƙaita taruwar jama'a a ƙauyen su yarinyar wadda ta rasu ranar Talata, makonni bayan cin zarafin nata.

 20. Ƴan majalisar dokoki sun ƙi karɓar gudunmowar kwaroron roba 200,000 da aka ba su

  Malawi parliament

  Ƴan majalisar dokokin Malawi sun ƙi karɓar gudunmowar fiye da kwaroron roba 200,000 daga gidauniyar agaji ta Aids Health Foundation.

  An bayar da kwaroron robar ne don a ajiye su a banɗakunan da ke cikin ginin majalisar.

  Shugaban marasa rinjaye na majalisar Richard Chimwendo, ya ce mambobin majalisar ba sa buƙatar irin wannan taimakon don kuwa za su iya sayen kwaroron robar da kuɗinsu.

  An bayar da gudunmowar ce ta hannun shugabar kwamitin lafiyar jiki Maggie Chinsinga.

  Mr Chimwendo ya ce wani rahoto da wata jaridar ƙasar ta wallafa kan gudunmowar - cin mutunci ne ga ƴan majalisar.

  Rahoton ya ambato Ms Chinsinga tana cewa majalisar dokokin tana bayar da kusan kwaroron roba 10,000 a kowane wata, kuma a wasu lokutan ''har sukan ƙare mata,'' kamar yadda jaridar gwamnatin Malawi ta ruwaito.

  Mataimakin kakakin majalisar Madaliotso Kazombo, ya ce hakan ba gaskiya ba ne kuma ya nemi jaridar ta bayar da haƙuri.