Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Umaymah Sani Abdulmumin da Awwal Ahmad Janyau

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Nan za mu rufe wannan shafin da muka shafe yinin Alhamis muna kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya.

  Da fatan za ku kasance da mu gobe Juma'a domin ci gaba da kawo labarai kai-tsaye kan abubuwan da za su faru a Najeriya da sassan duniya.

 2. Matar Netanyahu ta ‘saɓa’ dokokin kullen korona

  Matar Firaministan Isra’ila, Sara Netanyahu, an bayar da rahoton cewa ta saɓa dokokin kullen korona a ƙasar bayan ta kira wata mai gyaran gashi a gidanta a makon da ya gabata.

  A ƙarƙashin dokokin kullen korona a Isra’ila ba a amince wani ya yi tafiyar da ta zarta kilomita ɗaya ba zuwa gidan wani, kuma ba amince wani ya kai ziyara gidan wani ba.

  Wasu majiyoyi da na kusa da uwar gidan Netanyahu da jaridun Isra’ila suka ruwaito sun ce ta yi tunanin tana da damar da za a iya yi mata gyran gashi a gida kamar wani fim da aka yi na faɗakarwa da ke bayani kan muhimmanci sanya takunkumi.

 3. Amurka ta ƙaƙaba wa Iran sabbin takunkumi

  Shugaban Iran Rouhani

  Amurka ta kakaba wa Iran wasu sabbin takunkumi - a wannan karon kan manyan bankunanta yayin da gwamnatin Trump ke ci gaba da matsawa kasar lamba.

  Ma'aikatar Baitul MalinAmurka ta ce ta ware wasu bankunan Iran 28 a wani mataki na ƙara taɓarɓarawar tattalin arzikin Iran da yake cikin mawuyacin hali.

  Jami'an Amurka sun ce dalilin a takunkumin shi ne tilasta wa Iran ta kawo ƙarshen goyon bayan da take bai wa ta'addanci da kuma shirinta na nukiliya da gwamnatin Amurka ke ganin zai kai ga mallakar makaman nukiliya.

  Sakataren Baitul malin Steven Mnuchin ya ce takunkuman za su ba da damar hada-hadar jin-kai don tallafa wa mutanen Iran.

  Amma Ministan Harkokin wajen Iran Javad Zarif ya wallafa wani martani cikin fushi a shafinsa na Tuwita inda ya ce Amurka na ƙoƙarin tarwatsa ragowar hanyoyin Iran na biyan kuɗin abinci da magunguna.

 4. Trump ya ce yana da maganin korona da zai raba kyauta

  Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana da maganin korona wanda ya sha ya warke bayan ya kamu da cutar

  Shugaban ya kuma ce zai raba maganin kyauta bayan tabbatar da ingancinsa ƙasa da mako ɗaya.

  "Muna da maganin korona wanda na sha na warke – kuma yana da karfi"

  "Ba da dade wa ba za mu samar da shi, kuma muna da hukumar da za ta tabbatar da ingancinsa cikin gaggawa."

  "Abin da zai ɗauki shekara uku zuwa hudu, amma ni cikin mako ɗaya ko ƙasa da haka ma zan yi," in ji Trump.

  Shugaban na Amurka ya kuma ce gwamnatinsa tana samun ci gaba da yaƙi da korona - "Muna samun ci gaba akan wannan cutar da ta addabe mu wadda China ta yada muna"

  View more on twitter
 5. Yadda bene mai hawa 33 ya kama da wuta

  Iska mai ƙarfi ya taimaka wajen yaɗuwar wutar,
  Image caption: Rahotanni sun ce Iska mai ƙarfi ya taimaka wajen yaɗuwar wutar.

  Gobarar wuta ta kama wani bene mai hawa 33 a garin Ulsan da ke yankin kudancin Koriya ta Kudu

  Bidiyon gobarar ya nuna yadda wutar ta watsu a sassan benen da ake kira Samhwan Art Nouveau da ke ƙunshe da kantina da kuma gidajen mutane.

  Ɗaruruwan mutane ne aka kwashe da cikin benen da suka ƙunshi har da waɗanda ke ƙololuwar benen, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Yonhap ya ruwaito.

  Wutar ta fara ci ne misalin ƙarfe biyu agogon GMT, kuma cikin lokaci ƙanƙani ta yaɗu zuwa sassan ginin.

  Wutar ta soma ne daga hara na 8 da 12 na ginin da ke da gidaje kusan 120 da rukunin shaguna.

  Iska mai ƙarfi ya taimaka wajen yaɗuwar wutar, Rahotanni sun ce jami'an kashe gobara na ƙoƙarin gano mutane da dama da ake tunanin suna cikin ginin.

 6. 'Ɗaya bisa huɗu na al'ummar duniya na rayuwa ƙasa da dala uku'

  Bankin Duniya ya ce kusan ɗaya bisa huɗu na al'ummar duniya na rayuwa ne ƙasa da dala uku.

  Rahoton na Bankin Duniya ya ce kusan rabin al'ummar duniya kuma na rayuwa ne ƙasa da dala biyar.

  Rahoton ya ce talauci tsakanin al'umma ya ƙaru bayan ya ragu a shekarun baya.

  View more on twitter
 7. Atiku ya jagoranci taron gyara PDP

  Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya jagoranci wani taron tattauna gyara jam'iyyar PDP, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

  Atiku wanda ya yi wa jam'iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2019, ya ce ya jagoranci kwamitin sasantawa na jam'iyyar domin haɗin kan jam'iyyar.

  Ya kuma ce ya bayyana wa ƴan jam'iyyar burinsa na gyara jam'iyyar PDP.

  View more on twitter
 8. Covid 19: Za a buɗe babban dakin karatun Masallacin Makkah

  Makkah

  Hukumomin Saudiyya sun sanar da ranar buɗe babban dakin karatun Masallacin Haram na Makkah bayan rufe shi tsawon watanni takwas saboda annobar korona.

  Kafar yaɗa labaran gwamnatin Saudiyya ta Al Arabiya ta ce za a buɗe dakin karatun a ranar 1 ga Rabi’ul Awwal daidai da 18 ga watan Oktoba.

  Ɗakin karatun shi ne babban cibiyar musulunci da ke na ƙunshe littafai na addini da shari’a inda ɗalibai daga sassan duniya ke ziyarta.

  Sai dai an yi tanadin matakai na tsabta ga duk masu shiga ɗakin kararun domin bincike.

  Matakin buɗe ɗakin karatun na zuwa bayan dawo da aikin Umrah a ranar 4 ga Oktoba.

  Kafar Al Arabiya ta ce ɗakin karatun na ɗauke da litattafai 70,000.

  Kuma hukumomin ɗakin karatun sun ce sun shirya karɓar baki 30 a duk sa’a ɗaya.

 9. Da gaske korona ta kama ƴan wasan Super Eagles?

  Hukumar kwallon ƙafar Najeriya ta ƙaryata labarin da wasu jaridun ƙasar suka buga cewa wasu ƴan wasa huɗu daga cikin tawagar Super Eagles sun kamu da korona kafin wasan sada zumunci da za su yi da Algeria ranar Juma'a.

  Hukumar ta ce labarin ƙarya ne, kamar yadda ta wallafa a Twitter.

  View more on twitter

  A labarin da Sahara Reporters ta buga a shafinta ta ce kocin Super Eagles yayin ganawa da manema labarai ne ya sanar da cewa ƴan wasa huɗu sun kamu da korona, ba tare da ya bayyana sunayen ƴan wasan ba.

  Amma hukumar NFF ta ce ba a fahimci bayanin kocin Super Eagles Gernot Rohr ba, inda hukumar ta ce kocin yana nufin tun ɓarkewar annobar korona ƴan wasa huɗu ne suka kamu da cutar.

  "Amma dukkaninsu sun warke," in ji NFF

  View more on twitter

  Hakan dai na nufin ƴan wasan sun warke bayan sun kamu da korona.

  Hukumar NFF ta ce tana jiran sakamakon gwajin da aka yi wa ƴan wasan kafin karawar da za su yi da Algeria.

 10. Karon farko mace za ta jagoranci ƙungiyar cinikayya ta duniya WTO

  Ngozi

  A karon farko mace za ta jagoranci ƙungiyar cinikayya ta duniya WTO bayan ƴar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da kuma ƴar Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee sun kasance ƴan takara biyu da suka rage da ke naman kujerar ungiyar inda suka tsallake zuwa zagayen ƙarshe.

  Al’ummar Afirka za su yi fatan Ngozi Okonjo-Iweala ta yi nasara, a matsayin ƴar Afirka ta farko da ta shugabanci hukumar.

  A watan Agustan bara ne shugaban hukumar Roberto Azevedo ya yi murabus kafin cikar wa’adinsa.

  Da farko mutum takwas ne ke takarar maye gurbinsa amma yanzu sun dawo tsakanin Ngozi Okonjo-Iweala ta Najeriya da kuma ƴar Koriya Yoo Myung-hee.

  Duk wadda ta lashe zaɓen a ranar bakwai ga watan Nuwamba – za ta fuskanci ƙalubalen taɓarɓarewar tattalin arziki da annobar korona ta haddasa wa ƙasashe.

  A zagaye na biyu aka yi waje da Amina Mohamed ta Kenya da kuma Mohammad al-Turaiji da ke neman kujerar.

  Afirka na da babban burin cewa ya kamata a ce ɗan Afirka ya zama shugaban ƙungiyar.

  Ba'amurke ne ya yi ta shugabancin Bankin Duniya sannan kuma Bature ne ya yi ta shugabancin Asusun Bayar da Lamuni na Duniya, ɗan Afirka bai taɓa shugabanci a makamancin waɗannan cibiyoyi ba.

  Amma idan Ngozi Okonjo-Iweala ta Najeriya ta zama shugaba, Nahiyar Afirka za ta ji cewa lallai tana da rawar takawa a harkar kasuwancin duniya.

 11. Za mu yi gaggawar amincewa da kasafin kudin 2021 - Gbajabiamila

  Shugabannin majalisar tarayyar Najeriya

  Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya bayar da tabbacin cewa majalisar za ta yi nazari sosai tare da amincewada kasafin kuɗin 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar wa majalisar a ranar Alhamis.

  Ya ce majalisar ta tara za ta cika alkawalin da ta ɗauka na mayar da kasafin kuɗin tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.

  Mista Gbajabiamil ya ce za su yi aiki tare da hukumomin gwamnati da abin ya shafa domin tabbatar da cewa kasafin kuɗin ya shafi dukkanin buƙatun ƴan Najeriya.

 12. Louise Glück ta lashe lambar yabo ta Nobel

  Louise Glück

  An bai wa ‘yar Amurka Louise Glück da ta shahara a rubutattun wakoki lambar yabo ta Nobel.

  Cibiyar Nazari ta kasar Sweden ta yaba wa matar kan yadda take sarrafa muryarta.

  Glück ta buga jerin rubutattun wakokinta na farko cikin shekarar 1968 kuma wakokin da ta rubuta masu taken Wild Iris da Triumph of Achilles ne suka fito da ita.

  Wakokinta galibi kan tarihin rayuwarta na da suke mai da hankali kan rashi da damuwa.

 13. Ɗalibai a Netherlands sun Ƙirƙiri mota daga shara

  Luca

  Ɗalibai a Netherlands sun ƙaddamar da wata sabuwar motar da suka ƙirƙira daga shara.

  Motar ta tsere sun yi mata laƙabi da Luca.

  Mafi yawan robobin da suka yi amfani da su wajen ƙera motar sun samo ne daga teku.

  An yi amfani da wata leda ne wajen yi wa motar fenti mai kalar rawaya da ke da matuƙar daukar hankali a maimakon fenti na ruwa kuma an cusa gashin doki da ɓawon itacen kwakwa cikin kujerun.

  Sauran robobin kuma sun samo ne daga cikin kayan wasan yara da kayan talbijin.

  Motar dai na iya gudun kilomita 90 cikin sa’a ɗaya. Nauyin motar da batirinta kuma sun kai kilo dari hudu da ashirin.

 14. Facebook zai dakatar da tallan siyasa bayan zaɓen Amurka

  Facebook

  Kamfanin Facebook ya ce zai daina nuna talla musamman na siyasa bayan zaɓen Amurka da ke tafe ranar 3 ga watan Nuwamba.

  Kamfanin ya ce matakin na wucin-gadi ne domin rage "damar da ake amfani da ita wajen haifar da ruɗani da cin zarafi" kafin fitowar sakamakon zaɓen.

  Tuni dai Facebook din ya haramta tallan da ke bayyana wanda zai yi nasara a zaɓen.

  Sai dai masu fafutika sun ce hakan ba zai "kawo sauyi ko warware matsalolin da ke ƙasa ba".

 15. Gobara ta tashi a rumbun ajiyar makamai a Rasha

  Rasha

  An kwashe mutane daga kauyuka 14 da rufe manyan tittuna sakamakon wata gobara da ta tashe a rumbun ajiyar makamai da ke kudu maso gabashin birnin Moscow, na Rasha.

  Akalla mutum shida suka jikkata, wasu biyar kuma na kwance a asibiti.

  Rumbun da ke yankin Ryazan anan ake ajiyar makamai masu linzami da sauran abubuwa fashe da makaman artilary.

  Rumbun ya kama da wuta ne a ranar Laraba sakamakon wutar kona ciyaya da iska ta yaɗa zuwa wajen ajiyar a cewar mahukunta.

  An ƙaddamar da dokar ta baci a yankin

 16. Ƙungiyoyin farar hula sun mayar da martani kan haramta musu taron gangamin

  A jamhuriyar Nijar kungiyoyin farar hula ne suka fara mayar da martani kan haramcin da ofishin shugaban da'irar birnin Yamai ya yi masu na taron gangamin da suka kudiri shiryawa gobe Juma'a.

  Cikin wata takarda ce shugaban ya haramta masu wannan taro, yana mai cewa gudanar da taron tamkar taka wasu dokoki ne.

  Sai dai 'yan farar hular na ganin ana nuna masu bambanci ganin yadda 'yan siyasa ke cin karensu babu babbaka ba' a hana su.

 17. Annoba ta haifar da 'koma baya ga haɓakar tattalin arzikin Afirka'

  ANNOBA

  Bankin Duniya ya ca annobar cutar korona ta haifar da koma baya a ci gaban tattalin arziki da ƙasar ta samu a cikin shekaru wanda hakan ya sauya haɓakar da ake hasashe a 2020.

  Amma bankin ya yi hasashen cewa haɓakar na iya sake farfado wa a shekara mai zuwa.

  Afirka ta tsallake hasashen da aka rinka yi mafi muni na yada annobar za ta shafeta, alkaluman masu kamuwa da cutar ba su kai yadda aka yi tsanmani ba a nahiyar.

  Sai dai dokar kulle da ta rage yaduwar cutar ta taka rawa waje jefa ƙasashen cikin matsin tattalin arziki, kamar a Afirka ta kudu, ƙasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki.

  Bankin ya yi gargadin cewa mutum miliyan 40 na iya tsunduma a cikin talauci.

 18. Ranar masu fama da lalurar gani ta duniya

  Yau ce dai ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya MDD ta ware a matsayin ranar masu fama da larurar gani ta duniya.

  A cewar MDD akwai mutum kusan biliyan daya da ke fama da matsalar rashin gani, wanda da dama daga ciki ba su ma san suna fama da wannan matsala ba bare su magance ta.

  Wani dattijo mai shekaru kusan 60 a duniya, mai suna Umar Mohammad wanda tsohon ma'aikacin banki ne, da ya rasa idonsa shekara 10 da suka gaba, a lokacin da wani hatsari ya rutsa da shi a yayin wata ziyara da ya kai ƙauye.

  Duk da wannan lalura Malam Umar Muhammad ya ce har yanzu bai fitar da ran sake sa iyalansa a ido ba, da fatan ci gaba da harkokinsa yadda ya saba a baya kafin ya sami wannan larura.

 19. Trump ya ce ba zai yi muhawarar takarar shugaban ƙasa ta intanet ba

  Trump

  Muhawara ta biyu ta zaben Amurka da aka shirya yi a mako mai zuwa, za a gudanar da ita ne ta intanet.

  Hukumar da ke tsara muhawarar ta ce za ta dauki salon taron karawa juna sani inda ‘yan takarar za su shiga muhawarar daga wurare daban-daban.

  Sai dai Mista Trump ya ce ba zai gudanar da mahawarar ba ta intanet.

  Wanda zai jagoranci mahawarar Steve Scully da mahalarta muhawarar za su kasance a wata cibiyar zane-zane da ke Miami a Florida.

  Rabon da a ga shugaba Donald Trump a bainar jama’a tun ranar Litinin bayan ya dawo daga asibitin sojoji inda ya yi jinyar cutar korona.

  A daren jiya ne Mike Pence da Kamala Harrissuka fafata a tasu mahawarar ta ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa game da batun annobar korona da sauran batutuwa.

 20. An yi kutse a wayar minista a Kamaru

  Kutse

  Ministan Ma'adinai a Kamaru, Gabriel Dodo Ndoké, ya ce an yi masa kutse a cikin wayarsa.

  Ministan ya yi gargadi ga mutanen da ke da lambarsa da kada su tanka duk wani sako da ya shiga wayar su na neman kuɗi da sunansa.

  Mr Ndoké ya ce mahukunta na bincike domin shawo kan matsalar da kuma maido masa da lambarsa.

  Ministoci a Kamaru na yawaita fuskantar barazana daga masu kutse da ƴan damfara da ke amfani da sunansu wajen kirkirar shafukan jabu da sunansu suna damfarar mutane, a cewar jaridar Journal du Cameroun.