Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Mustapha Musa Kaita da Halima Umar Saleh

time_stated_uk

 1. Rufewa

  Masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo karshen labarai da rahotannin wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya a yau.

  Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

  Sai ku koma ƙasa don karanta labaran da aka wllafa tun safe.

  Mu kwana lafiya cikin alherin Allah.

 2. Coronavirus ta hallaka mutum miliyan 2 a duniya zuwa yanzu

  Coronavirus

  Fiye da mutum miliyan biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar korona tun bayan ɓullar cutar shekara ɗaya da ta gabata.

  Adadin mutanen ya ninka waɗanda suka mutu sakamakon cutar HIV da maleriya da mura da kuma amai da gudawa idan aka haɗa wajen guda.

  Har yanzu Amurka ce ƙasar da cutar ta fi ƙamari -- inda kusan mutum dubu 390 suka mutu -- sannan sai Brazil da Indiya.

  A Turai kuwa, Birtaniya da Italiya ne aka fi samun yawan mace-mace fiye da kowace ƙasa a yankin.

  A yanzu ana fatan yi wa fiye da mutum miliyan 10 allurar riga-kafin cutar zai taimaka wajen rage yawan mace-mace da kuma adadin mutanen da ake kwantarwa a asibiti.

  A Isra'ila, kasar da aka fi yi wa mutane allurar riga-kafin idan aka kwatanta da yawan mutane ƙasashe, an fara ganin kyakkyawan sakamako kan mutanen da ake kwatarwa a asibiti musamman waɗanda suka haura shekara 60.

 3. Nancy Pelosi ta bukaci wani tsohon janar na soji ya yi nazarin yadda magoya bayan Trump suka kutsa majalisa

  Nancy Pelosi

  Shugabar majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta ce ta bukaci wani tsohon janar na soji mai mutuncin gaske, wato janar Russel Honoré da ya sake nazarin yadda aka yi har magoya bayan Shugaba Trump suka samu kutsawa zauren majalisar, inda suka far wa ƴan majalisar a makon jiya.

  Ta ce "dole ne mu miƙa wannan zauren a duba shi ciki-da-bai, ganin abin da ya faru, ga kuma bikin rantsarwa da ke tafe."

  Ana sa ran janar Russel Honoré ya kammala aikinsa na da kwana biyar masu zuwa, kafin a rantsar da shugaba mai jiran-gado, Joe Biden.

  Nancy Pelosi ta yi na'am da shirin Mista Biden na riga-kafin korona da kuma farfado da tattalin arzikin kasa, tana cewa lallai “taimako na tafe.”

 4. Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗi kan riga-kafin korona na jabu

  Riga-kafin korona

  Hukumomin Najeriya sun yi gargaɗi kan wani riga-kafin korona na jabu dake yawo a faɗin ƙasar.

  Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna NAFDAC ta ce ba ta amince da ko wane riga-kafi ba.

  Shugabar hukumar Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa ta tashi tsaye haiƙan wajen hana shigar riga-kafin na jabu hannun jama'a ba.

  A baya-bayannan hukumomi sun ce suna fatan yi wa kaso 40 cikin ɗari na ƴan kasar riga-kafin a 2021.

  Yayin da ake fuskantar ƙaruwar masu kamuwa da cutar ta korona, akwai fargabar cewa wasu miyagu ko ƙungiyoyi za su iya amfani da halin da ake ciki su samar da riga-kafin da ba a amince da shi ba a kasuwannin bayan fage.

  A ranar Alhamis cutar ta kashe mutum 23 a Najeriya, wanda shi ne mafi yawa tun bayan da korona ta ɓulla a Najeriya, kuma adadin waɗanda suka kamu ya kai 105,478 a cikin wata goma sha ɗaya.

 5. Yau sojojin Amurka za su kammala fita daga Somaliya

  Dakarun Amurka

  A yau ne ake sa ran kusan baki dayan sojojin Amurka za su kammala fita daga kasar Somalia.

  Rundunar sojin Amurka dai ba ta yi bayani a kan janye zaratan sojojin nata su dari bakwai ba…amma ta ce ta duƙufa wajen kare kasar Somalia…kuma za ta ci gaba da sa ido a kan kungiyar Al-shabab.

  A shekara ta 2007 ne Amurka ta kai daukin sojoji na baya-baya a Somalia, wadanda suke horar da sojojin gwamnatin tarayya.

  Sai dai sojojin Amurkan sun kashe mayakan al-shabab da dama ta hanyar kai musu hari da makami mai linzami da kuma jirage marasa matuƙa.

 6. Shekara 55 da kashe Tafawa Balewa da Ahmadu Bello

  Yau Juma'a 15 ga watan Janairu ce ranar da ake tuna wa da yin juyin mulkin soji na farko a Najeriya, kuma a ranar ne aka karkashe wasu daga cikin shuagabannin kasar da suka karbo mata ‘yancin kai.

  Daga cikinsu akwai firaministan farko na kasar Sir Abubakar Tafawa Balewa da FirimiyanJihar Arewa Sir Ahmadu Bello.

  Ga wasu hotunan tunawa da su da muka wallafa da za ku iya gani idan kun latsa nan.

 7. Mutum 34 sun mutu a girgizar ƙasa

  Indonesia Earthquake

  Masu aikin ceto na lalube a cikin ɓaraguzan wani asibiti da wani ɓangarensa ya rushe bayan girgizar ƙasar da ta afkawa tsibirin Sulawesi, inda ta kashe aƙalla mutum 34.

  Girgizar ƙasar mai girman 6.2 a ma'auni ta afku ne da safiyar Juma'a sa'o'i bayan an yi wata ƴar ƙaramar girgizar ƙasa.

  Ɗaruruwan mutane sun samu raunuka yayin da dubbai suka rasa muhallansu a girgizar ƙasar.

  Indonesia na da tarihin girgizar ƙasa da tsunami masu muni inda sama da mutum 2,000 ne suka rasa rayukansu a girgizar ƙasar Sulawesi ta shekarar 2018.

  Mutum takwas sun mutu lokacin da wani ɓangare na asibitin Mitra Manakarra mai bene hawa biyar ya ruguzo, in ji jami'ai.

  An samu tseratar da mutum 60 daga asibitin.

  Wani ɗan sanda ya sanar da BBC cewa lamarin ya janyo ɗaukewar wutar lantarki.

  Hukumomi na fargabar yawan mutanen da suka mutu zai ƙaru yayin da ake ci gaba da ceto mutane.

  Masu aikin ceton na fuskantar ƙalubalen rashin wutar lantarki da sabis ɗin waya.

 8. Mutum 15 sun mutu a haɗarin mota a Maiduguri - hukumar kare hadura

  BBC
  Image caption: 'Hadarin ya hadar da maza bakwai da mata takwas'

  A kalla mutum 15 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da su a kan titin Maiduguri zuwa Damaturu a ranar Juma’a.

  Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamnadan hukumar kiyaye hadura ta Najeriya da ke lura da shiyyar Borno Mista Sanusi Ibrahim ne ya tabbatar da faruwar al’amarin ga kamfanin dillancin labarai na kasar a Maiduguri.

  Ibrahim ya ce hadarin ya faru ne kusa da kauyen Mainok da ke karamar hukumar Kaga, kuma tuni aka garzaya da gawarwakin zuwa babban asibitin Benesheik.

  “Na samu rahoton hadarin ne daga sashenmu na Benesheik cewa wasu motoci biyu kirar Sharon dauke da fasinjoji 15 har da direbobinsu sun yi taho mu gama kuma duka su 15 babu wanda ya tsira.

  Hadarin ya hadar da maza bakwai da mata takwas,” kamar yadda Mista Ibrahim ya bayyana.

  Ya ce tayar motar direba daya ce ta fashe abin da yakai ga wannan mummunan hadari kenan.

 9. Amurka ta janye dakarunta daga Afghanistan da Iraƙi

  AFP
  Image caption: Shugaba mai barin gado Donald Trump ya nemi ciki alkawarinsa na lokacin yakin neman zabe, na ganin an kawo karshen yake-yaken da aka fara tun bayan harin 9/11

  Rundunar sojin Amurka ta rage adadin sojojinta a Afghanistan da Iraki zuwa 2,550 a ko wacce kasa, wannan ne adadi mafi ƙaranci da rundunar ta taba bari tun da aka fara yake-yake a kasashen cikin kusan shekara 20, kamar yadda ma’aikatar tsaron Amurka ta bayyana a ranar Juma’a.

  Shugaba mai barin gado Donald Trump ya nemi ciki alkawarinsa na lokacin yakin neman zabe, na ganin an kawo karshen yake-yaken da aka fara tun bayan harin 9/11, shi ne ya ba da umarnin a rage yawan dakarun kasar zuwa 15 ga watan Janairu.

  Mukaddashin sakataren tsaro Chris Miller ya ce ci gaban da ake samu a tattaunawar sulhun da ake yi a kasashen biyu zai ba da damar janye dakarun Amurka da na takwarorinta.

  Za a kara rage yawan sojin bisa nasarar da aka samu tsakanin jami’an Afghanistan da na Taliban kan tattaunawar sulhun da suke yi a Doha babban birnin Qatar.

 10. Koriya ta Arewa ta fitar da sabon makami mai linzami

  Makaman Koriya ta Arewa

  Koriya ta Arewa ta gabatar da wani sabon makamai mai linzami na ƙarƙashin ruwa, wanda kafar yaɗa labarn ƙasar suka bayyana a matsayin "makami mafi ƙarfi a duniya".

  Makaman da yawa ne aka baje a lokacin wani fareti da Shugaba Kim Jong-un ya jagoranta, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito.

  Wannan matakin na zuwa ne kwanaki kafin rantsar da Joe Biden a matsayin shugaban Amurka.

  Haka kuma, ya biyo bayan wata ganawar siyasa da ba a saba gani ba inda Mista Kim ya ce Amurka ce babbar maƙiyar ƙasarsa.

  Hotunan da Koriya ta Arewa ta fitar ya nuna a ƙalla manyan makamai masu linzami huɗu ana tuƙasu a gaban ƴan ƙasar masu riƙe da tutoci.

 11. Tantabara ta auna arziki a Australia

  ..

  Wata tantabara, ta auna arziki, bayan mahukunta a ƙasar Australia sun fasa kashe ta.

  An dai yi zaton cewa tantabarar, mai suna Joe, ta yi ɓatan kai ne lokacin da suke gasar tsere, ta shiga cikin wani kaya da ke jirgin ruwa, har aka kai ta ƙasar Australia.

  Da farko gwamnatin ƙasar ta ce a kashe ta ne, gudun ko tana ɗauke da cuta mai yaɗuwa, musaman ma da aka ga sunan Joe a jikin wani zoben da ke ƙafarta, inda aka zaci cewa daga Amurka take.

  Amma mahukunta sai suka fasa kashe ta, bayan wata sanarwa da ƙungiyar da ke tsara gasar tseren tantabaru ta yi, cewa zoben da ke jikin tantabara na jabu ne.

 12. Gwamnatin Trump ta rage yawan sojojin Amurka a Iraƙi da Afghanistan

  Gwamnatin Shugaban Amurka mai barin gado, Donald Trump, ta rage yawan sojojin da ke Afghanistan zuwa 2,500 a Afghanistan da Iraƙi.

  Janye sojojin na daga cikin shirin shugaban ƙasar mai barin gado na rage yawan sojojin Amurka da ke ayyuka a wasu ƙasashe.

  Manyan jami'an sojojin ƙasar sun nuna shakku kan wannan yunƙuri musamman kan sojojin da za a janye daga Afghanistan.

  An bayyana cewa akwai yiwuwar janye sojojin zai iya jawo matsala ga gwamnatin Trump.

 13. Yau Juma'a kusan duka sojojin Amurka za su bar Somalia

  ..

  A yau Juma'a ake sa ran kusan duka sojojin Amurka da ke Somalia za su bar ƙasar.

  Rundunar sojin Amurka ta ƙi cewa komai kan batun sojoji 700 da za su bar Somalia, amma Amurkar ta ce ba za ta daina ba Somalia gudunmawa ba kuma za ta ci gaba da sa ido kan masu iƙirarin jihadi da suka addabi ƙasar.

  Amurka dai ta fara shirinta na wanzar da zaman lafiya a Somalia tun a 2007, kuma sojojin ƙasar sun taimaka matuƙa wurin horas da jami'an sojin ƙasar.

  Haka kuma dakarun na Amurka sun kashe manyan dakarun al-Shabab ta hanyar hare-haren sama da amfani da makaman roka.

 14. 'Mutum 60,000 suka gudu cikin mako guda daga Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika'

  Hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da rahoton samun ƙaruwa matuƙa a yawan ƴan gudun hijira da ke guduwa daga rikicin Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika.

  Mutum 60,000 suka bar ƙasar a makon da ya gabata - wanda adadin ya ninka na waɗanda suka bar ƙasar a tsakiyar watan Janairu.

  Akasarinsu na tsallakawa zuwa Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo ta Kogin Ubangui da ke kudu.

  A ranar Laraba ƴan tawaye suka kai hari Bangui babban birnin ƙasar a karon farko.

  Sai dai dakarun gwamnatin ƙasar da kuma sojojin haya daga Rasha da kuma sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya sun daƙile harin.

 15. Hotunan yadda aka gudanar da bikin tunawa da ƴan mazan jiya a Abuja

  .
  .
  .
  ..
 16. Cutar korona na ƙaruwa sosai a Ghana

  Cutar Korona

  Ƙungiyar Likitoci a Ghana ta yi gargaɗin akwai yiwuwar ƙaruwar masu cututar korona a ƙasar.

  Kafin bukukuwan kirsimeti, masu fama da cutar ba su fi 800 amma a wannan watan kawai sun haura mutum 1000.

  Ƙungiyar ta ce karin mutanen da aka samu na da nasaba da rashin bin ƙa'idoji da watsi da dokokin cutar ta covid-19.

  Haka kuma, ƙungiyar ta ce ana samun ƙarin mutane da ke shigowa ƙasar daga ƙasashen waje ɗauke da cutar.

  Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ya ta bayyana cewa cibiyoyin kula da masu cutar sun cika maƙil musamman a babban birnin ƙasar da kewayensa.

  ƙungiyar ta ce ya kamata gwamnati ta ƙara yawan gwaje gwaje sannan a riƙa yin gwajin kyauta.

  A yau ne dai aka buɗe duka makarantu a faɗin kasar amma za a ci gaba da kulle gidajen rawa da shagunan sayar da barasa.

 17. An sanar da makoki na kwana uku a Malawi bayan mutuwar ministoci biyu

  Shugaban ƙasar Malawi, ya sanar da makoki na kwanaki uku bayan mutuwar ministocinsa biyu.

  A makon nan ne dai aka sanar da mutuwar ministan ƙananan hukumomi na ƙasar, Lingson Berekanyama da kuma ministan sufuri na ƙasar wato Sidik Mia wanda ya kasance mataimakin shugaban jam'iyya mai mulki ta ƙasar.

  An kuma bayyana cewa ministocin sun kamu da cutar korona bayan wani taron ministoci da aka yi a watan da ya gabata.

  An ƙara tabbatar wasu ministoci guda biyu da skan kamu da cutar inda tuni guda daga ciki ya samu lafiya.

  Ƙasar dai ta Malawai na tsananin yaƙi da cutar kuma Shugaban ƙasar, Lazarus Chakwera ya ce ƙasarsa har yanzu ba ta yi abin da ya kamata ba domin rage yaɗuwar cutar.

 18. Bobi Wine ya soma watsi da sakamakon farko-farko na zaɓen Uganda

  ..

  Ɗan takarar Uganda daga jam'iyyar adawa, Bobi Wine, ya yi watsi da sakamakon farko-farko da aka fara bayyanawa, inda ya fara kiran kansa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa duk da cewa har yanzu ana nan ana ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa.

  Bobi Wine, na zargin cewa zaɓen da aka yi a ranar Alhamis shi ne zaɓen da aka fi tafka maguɗi a tarihin ƙasar, duk da cewa bai bayar da cikakkiyar hujja ba.

  Ya kuma bayyana cewa yanzu ne aka fara gwagwarmaya.

  Bobi Wine, wanda sunansa na asali shi ne Robert Kyagulanyi, ya bayyana cewa zai yi wa ƴan jarida jawabi nan ba da daɗewa ba.

  Sakamako na farko da aka bayyana ya nuna cewa Museveni na kan gaba da kashi 60 cikin 100.

 19. Bidiyon Ku San Malamanku tare da Ustaz Husaini Zakariyya

  Video content

  Video caption: Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan shirin
 20. Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilanta na kwashe Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi

  ..

  Shugaban hukumar kula da ababan hawa da muhalli ta jihar Kaduna, KASTELEA wato Manjo Garba Yahaya Rimi, kuma shugaban kwamitin yaƙi da annobar korona a jihar ya bayyana cewa kai samamen na daga cikin matakan da suka fara ɗauka na daƙile annobar korona.

  A ranar Laraba ne gamayyar jami'an tsaro suka kutsa cikin gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, inda suka kwashe duka almajiran da ke kwance a tsakar gidan.

  Sai dai gwamnatin jihar ta ce wannan matakin ba wai ya tsaya bane kan makarantar Dahiru Bauchi kaɗai, inda ya ce ya shafi duka ƙananan hukumomi 23 ne na jihar.

  Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa ɗalibai 140 suka kwasa daga makarantar kuma an ajiye su sansanin alhazai na jihar Kaduna inda ake tantance su, inda ya ce akwai wasu daga cikin almajiran da suka fito daga ƙasashe kamar Nijar da Chadi.

  Gwamnatin ta ce idan aka gama tantance almajiran, waɗanda suka fito daga wasu jihohi za a miƙa su ga gwamnonin jihohinsu, na jihar Kaduna kuma za a miƙa su ga ciyamomi na ƙanan hukumomi, ɗaliban ƙasar waje kuma za a miƙa su ga hukumar shige da fice ta Najeriya.

  Ko a bara sai da gwamnatin jihar ta mayar da wasu almajirai garuruwansu, inda ta zarge su da yaɗa korona.