Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Fauziyya Tukur da Nasidi Adamu Yahaya

time_stated_uk

  1. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku a wannan shafin. Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu inda za mu zo muku da sabbin labarai da rahotanni.

    Kuna iya ci gaba da bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara inda za ku iya tafka muhawara da bayyana ra'ayoyinku.

    Mu kwana laifya.

  2. 'Yan bindiga sun kashe mutum 23 a Kaduna

    View more on twitter

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce 'yan bindiga sun kashe akalla mutum 23 a hare-haren da suka kai kananan hukumomi biyar cikin awa 24.

    Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a sakon da ya wallafa a shafin Tuwita na ma'aikatarsa.

    Ya kara da cewa "gwamnatin Kaduna ta samu rahotanni daga jami'an tsaro game da kisan mutum 23 a hare-haren da aka kai wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi da Kauru."

    A cewarsa, a Birnin Gwari 'yan bindiga sun kashe mutum 10, yayin da a Igabi da Giwa aka kashe mutum dai-dai, sai kuma a Kauru suka kashe mutum biyar.

    Ya ce an kashe mutum shida a Chikun kodayake ya kara da cewa an kashe dan bindiga daya a yayin da mazauna yankin suka mayar da martani.

    Mr Aruwan ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka mutu sannan ya sha alwashin ci gaba da yin aiki tukuru domin tabbatar da tsaro a jihar.

  3. Shugaban Tanzania 'ba zai nemi ta-zarce karo na uku ba'

    Magufuli

    Jam'iyyar da ke mulki a Tanzania ta yi watsi da kiraye-kirayen da 'yan majalisar dokokinta suke yi wa shugaban kasar John Magufuli ya tsawaita zamansa a kan mulki.

    Shugaban mai shekara 61, wanda ya yi nasara a zabe a watan Oktoba, a yanzu haka yana cikin wa'adinsa na biyu na shekara biyar din karshe a ofis.

    Humphrey Polepole, kakakin jam'iyyar CCM da ke mulki, ya shaida wa 'yan majalisar cewa Mr Magufuli ba shi da niyyar zama a kan mulki fiye da ka'idar da kundin tsarin mulki ya ba shi.

    Wasu daga cikin 'yan majalisar sun yi ta neman a sauya kundin tsarin mulkin domin ya samu damar tsayawa takara a karo na uku.

    “Shugaba Magufuli ba shi da niyyar ci gaba da zama a kan mulki," in ji Mr Polepole.

  4. Luiz Suarez ya doke tarihin cin kwallon Ronaldo a La Liga

    Suarez

    Ranar Litinin Atletico Madrid ta tashi wasa 2-2 da Celta Vigo a karawar mako na 22 a gasar La Liga.

    Tsohon dan wasan Liverpool da Barcelona, Luis Suarez shi ne ya ci mata kwallayen.

    Kwallon da ya ci ya sa ya haura tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo a lokacin da ya taka leda a Sifaniya.

    Kawo yanzu Luis Suarez ya ci kwallo 16 a wasa 17 da ya buga a kakar bana ta La Liga tun bayan da ya koma kungiyar daga Barcelona.

    Tsohon dan wasan Ajax da Liverpool shi ne na farko da ya ci kwallo 16 a wasa 17 a La Liga a kani na 21.

    Karanta cikakken labarin a nan.

  5. Tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC Barry Burgess ya rasu

    Barry Burgess

    Muna alhinin sanar da ku rasuwar tsohon shugaban Sashen Hausa na BBC, Mista Barry Burgess.

    Barry ya rasu a ranar Asabar din da ta wuce a gidansa da ke birnin Birmingham a Birtaniya yana da shekara 72 a duniya.

    Maragayin ya rasu ne ba tare da ya yi jinya ba.

    Ya soma aiki da BBC a shekarar 1974 a matsayin mai hada shiri a Sashen Hausa sannan ya bar BBC a matsayin shugaban sashen a shekarar 1999.

    Bayan ya bar BBC, Barry Burgess ya koma koyar da harshen Hausa a tsangayar Nazarin Afrika da Gabashin Duniya da ke Jami'ar London.

    An haifi Barry Burgess ne a ranar 8 ga watan Oktoban 1948.

  6. Gwamna El-Rufai ya sabunta rijistarsa ta jam'iyyar APC

    View more on twitter

    Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-Rufai, ya bi sahun 'yan jam'iyyar APC wajen sabunta rijistarsa ta jam'iyyar.

    A farkon watan Fabrairu ne jam'iyyar ta APC ta soma sabunta katin mambobinta wanda ta ce hakan zai inganta yadda ake tafiyar da sha'anin jam'iyyar.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Talata, Gwamna El-Rufai ya ce ya sabunta katinsa na jam'iyyar APC a rumfar zabe ta Ungwan Sarki da ke birnin Kaduna.

    Gwamnan yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar ta APC.

    A makon jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari shi ma ya sabunta katinsa na jam'iyyar a mazabar Sarkin Yara da ke Daura.

  7. Ba daga ɗakin gwaji cutar korona ta samo asali ba - WHO

    Tawagar WHO

    Wata tawagar ƙwararru da ke bincike kan inda cutar korona ta samo asali sun yi watsi da wani batu da ke cewa ƙwayar cutar ta samo asali ne daga wani ɗakin gwaji.

    Peter Ben Embarek, shigaban binciken na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ya ce zai yi matuƙar wahala a ce ƙwayar cutar ta fito ne daga wani ɗakin gwaji a birnin Wuhan na China.

    Sai dai ya ce akwai buƙatar ƙarin gwaje-gwaje don gano asalin cutar.

    Wuhan, da ke lardin Hubei a yammacin China, shi ne birni na farko a duniya da aka fara ganin cutar. Tun bayan nan sama da mutane miliyan 106 ne suka kamu da ita kuma mutum miliyan 2.3 sun mutu dalilinta.

    Dr Embarek ya shaida wa manema labarai cewar bincikensu ya gani sabbin bayanai kan cutar amma ba su da muhimmancin da za su sauya yadda ake kallon annobar.

    Ƙwararru na ganin cewa ƙwayar cutar ta samo asali ne daga dabbobi kafin daga baya ta yadu zuwa mutane, amma babu tabbas kan yadda hakan ya faru.

  8. Habasha na shirin rufe sansanonin ƴan gudun hijira a Tigray

    Faɗa ya ɓarke a Tigra a watan Nuwamba
    Image caption: Faɗa ya ɓarke a Tigra a watan Nuwamba

    Habasha na shirin rufe sansanonin ƴan gudun hijirar da faɗa ya ritsa da su a Tigray da ke arewacin ƙasar, a cewar hukumar da ke kula da ƴan gudun hijira ta ƙasar.

    A lokacin da yake magana da ƴan jarida ranar Talata, shugaban Hukumar Tesfaye Gobezay ya ce kusancin iyakokin Eritrea da yanayin yankin su ne dalilan da suka sa za a rufe sansanonin.

    Ƴan gudun hijirar Eritrea kusan 100,000 ne ke rayuwa a sansanoni huɗu a Tigray kafin faɗan ya ɓarke a farkon watan Nuwamba.

    Biyu daga cikin sansanonin - Shimbela da Hitsats - da ke da ƴan gudun hijira sama da 20,000 sun jima ba sa samun agaji daga ƙungiyoyi.

    Mista Gobezay ya ce za a mayar da ƴan gudun hijirar wasu sansanonin ko kuma a shigar da su cikin al'umma.

  9. Saurari labarai cikin Minti Daya da BBC Na Rana 09/02/2021

    Video content

    Video caption: Minti Daya da BBC Hausa Na Rana 09/02/2021
  10. Buhari ya ƙaddamar da aikin shimfiɗa titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Maraɗi

    Muhammadu BUhari

    Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya ƙaddamar da titin jirgin ƙasa da zai taso daga Kano ya ratsa Katsina da Jibiya ya tsaya a Maraɗi cikin jamhuriyar Nijar.

    A bikin ƙaddamar da aikin titin, wanda shugaban ya halarta ta intanet, ya ce titin zai bi ta manyan cibiyoyin kasuwanci kamar Kazaure da Daura da Katsina da Maraɗi.

    Buhari ya ce wannan aiki mai muhimmanci zai tabbatar da ci gaban kasuwanci tsakanin Najeriya da Nijar.

    Haka kuma ya ce hakan zai inganta hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasashen biyu.

    Kamfanin Messrs Mota-Engil Nigeria Limited ne ke aikin shimfida titin, kuma zai gina wata makarantar koyon kimiyyar sufuri da titin jirgin ƙasa.

    Shugaba Buhari ya yi kira ga masu zuba jari su sa hannu don ganin an samu ci gaba a fannin tattalin arziƙi.

  11. Kamfanin BUA ya mayar wa CACOVID martani kan sayen riga-kafin korona

    AbdusSamad Rabiu

    Kamfanin BUA ya soki martanin da kwamitin nan mai yaƙi da cutar korona a Najeriya na CACOVID ya yi kan sayen riga-kafin cutar da kamfanin na BUA ya yi.

    Ranar Litinin ne kamfanin BUA Group ya sanar da sayen riga-kafin AstraZeneca miliyan ɗaya don raba wa ƴan Najeriya kyauta.

    Kamfanin na BUA ya ce ya yi mamakin watsi da CACOVID ya yi da sanarwar sayen riga-kafin, inda kwamitin ya ce babu wani mutum da zai iya sayen riga-kafin kamar yadda kamfanin BUA ya yi.

    A wani mataki na tabbatar wa da al'umma sayen riga-kafin, kamfanin BUA ya fitar da wasu bayanai a shafinsa na Twitter.

    Bayanan bayyana abin da ya faru a wani taro tsakanin shugabannin CACOVID inda Shugaban Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin Afrexim ya bai wa kwamitin damar sayen riga-kafin miliya 1. .

    Sai dai akwai sharaɗin biyan kuɗin riga-kafin a jiya Litinin ko yau Talata - kuma idan ba a biya ba a wadannan ranaku, za a rasa damar samun riga-kafin a mako mai zuwa.

    A cewar kamfanin BUA, bayan tsawon lokaci ana tattaunawa an gaza cimma matsaya kuma babu wanda ya amince ya biya kuɗin riga-kafin.

    Kamfanin ya ce ya ɗauki nauyin sayen alluran guda miliyan 1 a kan dalar Amurka 3.45 wanda gaba ɗaya ya kama Dala miliyan 3,450,000 wanda ya kama Naira biliyan 1.311.

  12. Sabon shugaban sojin Mozambique ya mutu sakamakon cutar korona

    Sabon shugaban rundunar soji a Mozambique, Eugénio Ussene Mussa, ya rasu bayan kamuwa da cutar korona.

    Ya rasu a asibiti mafi girma a Mozambique Maputo Central Hospital, inda ya yi jinya.

    Bai yi wata ɗaya da fara sabon muƙaminsa ba inda ya sha rantsuwa ranar 20 ga Janairu.

    Kafin hawansa mulki, shi ne mai kula da ayyukan soji na yaƙi da masu iƙirarin jihadi a yankin Cabo Delgado mai arziƙin mai.

    Mai baiwa Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya shawara a Mozambique, Mirko Manzoni, ya aika saƙon ta'aziyya ga Shugaba Filipe Nyusi da al'umar Mozambique bisa rashin.

  13. An tsare mutum sama da 200 kan saɓa dokokin korona a Kano

    Abdullahi Umar Ganduje

    Kwamitin da ke sa ido kan cutar korona a jihar Kano ya ce ya kama mutum sama da 200 a wani yunkuri na tabbatar da bin dokokin hana yaɗuwar cutar a jihar.

    Cikin mutum 200 da aka kama an kai 25 gidan gyara-halinka.

    Kafar yaɗa labarai ta The Authority a Najeriya ta ruwaito cewa kotunan tafi da gidanka 21 da aka ƙaddamar a jihar na kewayawa tare da shugaban kwamitin Honorobul Baffa Babba Danagundi.

    Haka kuma jaridar ta ce shugaban kwamitin ya tabbatar da cewa an samu mutum 102 da laifin saba doka kuma sai da aka ci tarar ko wannensu Naira 5000.

  14. Rundunar sojin Najeriya ta naɗa sabon kakakinta

    MM Yerima

    Rundunar sojin Najeriya ta sanar da Burgediya Janar Mohammed M. Yerima a matsayin sabon kakakinta, kamar yadda wasu kafofin yaɗa labaran kasar suka ruwaito.

    Yerima zai maye gurbin Burgediya Janar Sagir Musa wanda ya riƙe muƙamin a shekaru biyun da suka gabata.

    Kafar yaɗa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito cewa wannan ne na farko cikin sabbin naɗe-naɗe da sabon hafson sojin ƙasar Majo Janar Ibrahim Attahiru zai yi.

    Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Brig Janar Yerima mutumin ƙaramar hukumar Bade ne a jihar Yobe.

    Ya yi karatun kimiyyar Siyasa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria sannan a shekarar 1989 ya shiga aikin soja.

  15. Ana aikin ceto mutum 35 da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasa a Indiya

    Makekekiyar ƙanƙarar ta faɗo cikin rafin ne sannan ta auka cikin madatsar ruwa ta Rishiganga
    Image caption: Makekekiyar ƙanƙarar ta faɗo cikin rafin ne sannan ta auka cikin madatsar ruwa ta Rishiganga

    Ma'aikatan agaji na aiki tuƙuru don ganin sun ceto mutane 35 da ake zaton sun maƙale a wata hanyar ruwa ta ƙarƙashin ƙasa a arewacin Indiya.

    Hanyar ruwan mai nisan kilomita 8 ta toshe ne bayan ambaliyar ruwa a jihar Uttarakhand ranar Lahadi inda mutane 28 suka mutu kuma kusan 150 suka ɓace.

    Ana zaton wani ɓantaren ƙanƙara daga Himalayas ya faɗa cikin wani rafi ya janyo ambaliyar.

    Da alama mutane sun maƙale a ciki lokacin da ruwan mai tsananin sanyi ya gangaro ɗauke da manyan duwatsu da ƙasa da gudun gaske.

    Sai suka toshe hanyoyin ruwan.

    An ceto ma'aikata 12 daga wata ƙaramar hanyar ruwa da ta hadu da babbar amma gwamnan jihar Trivendra Singh Rawat ya ce kusan mutum 35 na nan a maƙale cikin hanyar.

  16. An shiga rana ta huɗu ta zanga-zanga a Myanmar

    Myanmar Protests

    Ƴan sanda a Myanmar sun harba wa masu zanga-zanga harsasan roba don tarwatsa su a Nay Pyi Taw babban birnin ƙasar.

    Haka kuma, an yi amfani da ruwan zafi da hayaƙi mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar da ek buƙatar a dawo da dimokuraɗiyya bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

    BBC ta gano cewa a ƙalla mutum biyu ne suka samu munanan raunuka.

    Ana ci gaba da zanga-zangar a kwana na huɗu duk da sabbin dokokin da aka sa a ƙasar.

    An sa dokokin hana taro da na hana fita a wasu biranen ƙasar.

    Masu zanga-zangar dai na neman a sako shugabarsu da suka zaɓa Aung San Suu Kyi tare da sauran shugabannin jam'iyyarta ta National League for Democracy (NLD).

  17. Ɗaya daga cikin ƴan bindigar da suka sace Ɗaliban Ƙanƙara ya tuba

    Repentant Kidnapper

    Wani shahararren ɗan bindiga a Zamfara, Awwalun Daudawa ya miƙa kansa ga hukumomi tare da tuba daga ayyukan ta da ƙayar baya.

    Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Abubakar Muhammad Dauran ne wa shaida BBC haka.

    Ya ce Awwalun Daudawa na cikin ƴan bindigar da suka yi garkuwa da ɗaliban nan sama da 300 daga makarantar Ƙankara a jihar Katsina a cikin watan Disambar 2020.

    Repentant Kidnapper

    Jihar Zamfara da Katsina na daga cikin johohin arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.

    Repentant Kidnapper

    A watan Disambar 2020 ne wasu ƴan bindiga suka afkawa wata makarantar kwana ta maza suka yi awon gaba da ɗalibai sama da 300.

    Sai dai an sako daliban bayan ƴan kwanaki, inda aka daidaita tsakanin ƴan bindigar da gwamnati.

  18. Za a fara zaman sauraren ƙarar tsige Donald Trump a karo na biyu

    Donald Trump

    A yau Talata ake fara zaman sauraren ƙarar tsige Donald Trump a karo na biyu, inda shugabannin majalisar Dattawa suka amince yi a gaggauce.

    Ana tuhumar tsohon shugaban ne da "tunzura tashin hankali" a wani jawabi da ya yi ga magoya bayansa kafin mummunar zanga-zangar da aka yi a Majalisar Dokokin ƙasar ranar 6 ga Janairu.

    Ƴan Demokrat sun ce suna da hujja mai ƙarfi da ke nuna rashin gaskiyarsa yayin da tawagar lauyoyin da ke kare shi suka ce masu zanga-zangar sun yi gaban kansu ne.

    Mista Trump ne shugaban Amurka na farko a tarihi da aka taɓa tsigewa sau iyu kuma shugaba ɗaya cikin shugabanni uku da aka taɓa tsigewa.

  19. Burtaniya ta ce sau biyu masu shiga ƙasar za su yi gwajin korona a lokacin da su ke killace

    Coronavirus

    Daga yanzu duk masu shiga Burtaniya za su yi gwajin cutar korona biyu a lokacin da suke killace kansu, a wni yunƙuri na hana sabbin nau'ukan korona shiga ƙasar.

    Ana so masu shiga ƙasar su yi gwaji kwana biyu bayan shiga da kuma rana ta takwas a kwanaki 10 na killace kansu.

    Ma'aikatar Lafiya ta ce matakin zai samar da ƙarin kariya, wanda bayar da damar gano sabbin masu dauke da cutar yadda ya kamata.

    Sakataren Lafiya, Matt Hancock zai bayar da ƙarin bayani a gaban majalisar nan gaba.

    Ana buƙatar a yi gwajin cikin sa'o'i 72 kafin shiga ƙasar, kuma duk wanda zai shiga ba tare da sakamakon gwajin na fuskantar tarar Fam 500.

  20. Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar musaya BVN da lambar dan ƙasa, NIN

    ISA ALI PANTAMI

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa ministan sadarwar Najeriya Dakta Isa Pantami ya ce gwamnatin tarayya na shirin sa NIN a madadin BVN.

    Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a lokacin da ya kai ziyara inda ake yi wa wasu ƴan ƙasar rajistar NIN a Abuja.

    Ya ce ya gabatar da wannan manufa ga Kwamitin Ci Gaban Tattalin Arzikin Kasa kuma ya jawo hankalin Babban Bankin Najeriya kan buƙatar amfani da NIN a madadin BVN.

    A cewarsa, BVN manufar masu sa ido ce yayin NIN kuwa dokar ƙasa ce, kamar yadda Punch ta ruwaito.

    Ministan ya ce BVN na iya aiki ne kawai ga mutanen da ke da asusun ajiya a banki yayin da NIN kuwa na ko wane ɗan ƙasa ne.