Got a TV Licence?

You need one to watch live TV on any channel or device, and BBC programmes on iPlayer. It’s the law.

Find out more
I don’t have a TV Licence.

Rahoto kai-tsaye

Daga Fauziyya Tukur da Umar Mikail

time_stated_uk

 1. Mu kwana lafiya

  Rahotanni a wannan shafin sun zo ƙarshe.

  Sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya.

  Umar Mikail ne ke muku fatan asuba ta gari.

 2. An kama mutum 70 da zargin sayar da ruwan gishiri a matsayin rigakafin cutar korona

  Korona

  China ta ce ta murkushe wani kasuwancin cinikin rigakafin cutar korona na bogi tare da cafke mutane da dama.

  Hukumomi sun ce daga cikin waɗanda aka kama ɗin har da waɗnda suka ci ribar miliyoyin dala ta wannan hanyar.

  Wakilin BBC ya ce 'yan sanda a ƙasar sun ce sun kama mutum 70 da ake zargi da aikata laifuka 21 daban-na cinikin rigakafin korona na jabu.

  Wata kafar yaɗa labaran kasar ta ce cikin wadanda aka cafke akwai masu hada ruwan gishiri suna sayarwa a matsayin rigakafi.

  Kazalika, an rika kai irin waɗanan jabun rigakafin wasu asibitoci da ke cikin bukatar gaggawa. Haka nan, ana sayar da irin wannan jabun rigakafin har a kasashen katare.

 3. Abin fashewa ya kashe yara shida a Jihar Zamfara

  'Yan sandan Najeriya

  Wani abin fashewa ya kashe aƙalla yara guda shida tare da jikkata wasu a ƙauyen Magamin-Diddi na Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ranar Lahadi.

  Rukunin yaran da ya ƙunshi maza da mata 'yan shekara takwas zuwa 12, sun zaci ƙarfe ne kawai a lokacin da suka ga abin fashewar yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗebo kara.

  Huɗu daga cikinsu 'yan gida ɗaya ne.

  Kwamishinan Tsaro na Zamfara, Abubakar Dauran, ya ce akwai yiwuwar jami'an tsaro ne suka jefa abin fashewar yayin wani hari da suke kaiwa kan 'yan fashin daji da suka addabi jihar.

  Tuni aka yi jana'izar yaran kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a cewar Abubakar Dauran.

  Iyayen yaran sun shaida wa BBC cewa lamarin ya girgiza su sosai.

 4. An tura 'yan sandan kwantar da tarzoma zuwa Jihar Oyo

  'Yan sandan Najeriya

  Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin gaggawa na tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa Jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

  Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sadan Najeriya, Frank Mba, ya sanya wa hannu a yau Litinin domin dawo da zaman lafiya a rikicin da aka yi a ranakun Juma'a da Asabar.

  Mista Mba ya ce an tura dakarun ne domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da doka da oda a wuraren da aka yi rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa a ƙarshen mako.

  Hausawa aƙalla 10 aka kashe da kuma Bayarabe ɗaya yayin rikicin.

  "Dakarun waɗanda akasari suka ƙunshi masu tattara bayanan sirri da kuma na fagen daga, sun ƙunshi ɓangare huɗu na 'yan sanda; dakarun kwantar da tarzoma, ƙwararru wurin tattara baynai, jirgin helikwafta na sashen 'yan sandan sama," a cewar sanarwar.

 5. Labarai cikin minti ɗaya

  Video content

  Video caption: Minti Ɗaya da BBC na Yammacin 15/02/2021
  • An tabbatar da Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugabar kungiyar kasuwanci ta duniya, wadda za ta zama mace ta farko kuma bakar fatar Afirka da za ta rike mukamin. Shugaba Muhammadu Buhari ya taya tsohuwar ministar kudin Najeriyar murna bayan shafe kusan wata shida ana ja-in-ja.
  • Sojojin da ke mulki a Mynmar sun yi wa masu zanga-zanga barazanar hukuncin shekara 20 a gidan yari idan aka kama mutum da laifin yi wa dakarun kasar zagon kasa, yayin da ake ci gaba da nuna adawa da juyin mulkin da suka yi. Kazalika, za a ci mutum tara me tsoka ga wadanda aka samu da haddasa kiyayya da ko kuma kawo wargi ga shugabannin, a cewar gwamnati.
  • A bangaren wasanni kuma – Chelsea za ta barje gumi da Newcastle a wasan mako na 24 na gasar Premier a filin wasa na Stamford Bridge, sai kuma West Ham da Sheff. United. Ita kuwa Bayern Munich ta gasar Bundesligar Jamus za ta yi nata wasan da Arminia Bilefefeld a mako na 21.
 6. An kashe manoma uku a Jihar Ogun

  Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe manoma uku a jihar Ogun 'yan sa'o'i bayan tawagar gwamnatin jihar ta ziyarci yankin.

  Babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda ya ce sun fara gudanar da bincike.

  Rahotanni sun ce maharan sun mamaye Agbon-Ojodu da ke a yankin Eselu, inda suka ƙona wasu gidaje tare da kashe manoman.

  Wata tawagar manyan jami'an gwamnatin jihar da ta ziyarci yankin Hausawan jihar, ta tabbatar da cewa gwamnati na yunƙurin samar da zaman lafiya ne domin kauuce wa tashe-tashen hankali da ke faruwa a kwanan nan na korar Fulani da ake yi daga wasu yankunan ƙasar Yarabawa.

 7. Matsalar zubar da shara na damun mazauna Yamai

  Video content

  Video caption: Latsa hoton sama ku saurari rahoton Tchima Illa Issoufou daga Yamai

  A birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, matsalar zubar da shara ce ke damun mazauna Unguwar Bukoki ta biyu a cewar mazauna unguwar.

  Mazauna yankin na cewa sharar da ake zubarwa tana komawa kuma ta haifar musu da matsalolin da suka hada da rashin lafiya da sauransu.

  Wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou ta ziyarci unguwar don gane wa idonta girman matsalar da ke damun mutanen.

 8. Buhari ya taya Ngozi murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya

  Buhari da Ngozi

  Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Ngozi Okonjo Iweala murnar zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya, World Trade Organisation (WTO).

  A yau Litinin ne aka tabbatar da tsohuwar ministar kuɗin ta Najeriya a matsayin mace kuma 'yar Afirka ta farko da za ta jagoranci ƙungiyar bayan kusan wata shida ana ja-in-in-ja.

  "A madadin Gwamnatin Tarayya da dukkanin 'yan Najeriya, Buhari na taya tsohuwar ministar kuɗi, Dr Ngozi Okonjo-Iweala, murnar zaɓenta a matsayin shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya," a cewar sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.

  Buhari ya ce ta jawo wa Najeriya "kwarjini da girmamwa", yana mai cewa ta aiwatar da sauye-sauye masu yawa lokacin da take ministar kuɗi da kuma ministar harkokin waje.

  Ngozi ta samu shugabancin ne bisa samun goyon bayan gwamnatin Amurka ƙarƙashin shugabancin Joe Biden kasancewar Donald Trump bai goyi bayanta ba.

 9. Gwamnatin Jihar Ogun na tattaunawar gina zaman lafiya tsakanin Hausawa da Yarabawa

  Ogun

  Gwamnatin Jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta fara wani yaunƙurin gina zaman lafiya tsakanin Hausawa da Yarabawa a jihar.

  Wata tawagar manyan jami'an gwamnatin jihar da ta ziyarci yankin Hausawan jihar, ta tabbatar da cea gwamnati na wannan yunƙuri ne domin kauuce wa tashe-tashen hankali da ke faruwa a kwanan nan na korar Fulani da ake yi daga wasu yankunan ƙasar Yarabawa.

  Da yake magana a fadar Olu na Masarautar Ilaro, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Afolabi Afuape, ya ce suna yin aikin ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

  "Duk da cewa rikicin makiyaya da manoma matsalar ƙasa ce baki ɗaya, gwamnatin jiha na ƙoƙarin kamo bakin zaren matsalar saboda ba ta jin daɗin abin da ke faruwa a yankin," in ji shi.

  Mai bai wa gwamna shawara kan ƙabilu, Hadi Sani wanda ya yi magana cikin Hausa da Yarabanci, shi ma ya yi kira ga al'umma da su zauna lafiya "saboda babu wani ci gaba da za a samu idan babu zaman lafiya".

  View more on twitter
 10. Kotu a Indiya na zargin masu fafutuka da haɗa kai da ƙasashen waje don tayar da rikici

  Wata kotu a Indiya ta aike da sammaci kan masu fafutika biyu yayin da take ci gaba da bincike kan zargin hada baki da kasashen ketare wajen haddasa husuma ko rikici a India.

  Ƴan sanda Delhi na binciker Nikita Jacob da Shantanu da hannu a wasu takardu da aka rinƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta kan yadda za a taimaka wa manoma a Indiya kan wasu sabbin dokokin noma.

  Ms Jacob ta nemi kariya daga wata kotu a Mumbai domin hana a cafke ta.

  A ranar Lahadi, Disha Ravi, wanda ta samar da wata kungiya kare muhalli a Indiya mai cibiya a Sweden, an cafketa a Bangalore, batun da ya tunzura mutane da dama musamman masu fafutika da yan siyasa.

 11. Wajibi ne a dakatar da zubar da jini a Sasa - Atiku

  Atiku Abubakar

  Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce "wajibi ne a kawo ƙarshen kashe-kashe" a kasuwar Sasa ta Jihar Oyo.

  Atiku na wannan batu ne bayan kashe Hausawa aƙalla 10 a kasuwar da ke birnin Ibadan na JIhar Oyo a rikicin ƙabilanci tsakaninsu da Yarabawa a ƙarshen mako.

  "Garin haihuwa na kowane ɗan Najeriya shi ne Najeriya. Najeriya ce ta haifar da garuruwan ba su ne suka haife ta ba. Kowace jiha a Najeriya wajibi ne ta zama 'yar Najeriya a kodayaushe," a cewarsa.

  Ya ƙara da cewa "saboda haka dole ne a dakatar da zubar da jini a Sasa da ko'ina".

  Rahotanni sun ce wani Bayarabe ɗaya ya ransa a rikicin, wanda ya samo asali daga wani ɗan dako Bahaushe da ya zubar da kayan da yake turawa a baro a gaban shagon wata Bayarabiya.

  View more on twitter
 12. Labarai da dumi-dumiAn naɗa Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya

  Ngozi

  Bayan shafe kimanin watanni shida ba tare da shugaba ba, yau Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO ta nada tsohuwar Ministar Kudi ta Najeriya a matsayin shugabarta mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko.

  Mrs Ngozi Okonjo-Iweala ta maya gurbin dan Brazil Alberto Azevedo wanda ya sauka daga mukamin a watan Augustan bara, gabanin cikar wa’adin mulkinsa.

  Bisa tsari dai, sai duka kasashe 164 mambobin kungiyar sun amince kafin nada shugaba – don haka lokacin da Amurka karkashin shugabancin Donald Trump ta ƙi amincewa da nada Ngozi Okonjo-Iweala aka shiga kiki-kaka, har sai da shugaba Joe Biden ya hau karagar mulki a watan Janairu, kana ya sauya matsayin na gwamnatin Trump.

  Ishaq Khalid ya duba mana kadan daga tarihin sabuwar shugabar ta Kungiyar Cinikayya ta Duniya, ga kuma rahotonsa.

  Video content

  Video caption: Rahoton Ishaq Khaid kan nadin Ngozi Okonjo-Iweala
 13. Matar Yarima Harry ta kusa haihuwa

  Meghan and Harry

  Yarima Harry da matarsa Meghan na dakon haihuwar ɗansu na biyu, a cewar kakakin mata da mijin.

  Harry da Meghan na shirye-shiryen tarbar ƙani ko ƙanwar ɗansu Archie Mountbatten-Windsor, wanda yake daf da cika shekara biyu.

  Kakakin nasu ya ce suna cikin matƙar farin ciki.

  Kazalika, kakakin Sarauniyar Ingila wato kakar Harry da mai gidanta da mahaifin Harry Charles da duka ƴan gidan sarautar na farin ciki da samun ƙaruwar.

  Harry da Meghan sun wallafa wani hotonsu inda Harry ke zaune a ƙarƙashin wata bishiya ita kuma mai ɗakin nasa na kwance ta ɗora kanta a saman cinyarsa sannan ta dafe cikinta.

  Wanann ɗan da za a haifa shi ne na 8 a jerin mutanen da za su iya zama sarki ko sarauniya.

  Ba a bayyana lokacin haihuwar Meghan ba amma cikinta ya fito a hoton.

 14. Jacob Zuma ya bijire wa umarnin kotu

  Jacob Zuma

  Tsohon shugaban Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya sake bijirewa umarni kotu na bayyana gaban hukumar bincike kan rashawa duk da cewa kotun kolin kasar ta umarci shi da yin hakan.

  Mista Zuma, wanda ya musanta aikata ba daidai ba, ya zargi hukumar na nuna son-kai da bukatar a sauya shugabanta.

  A shekara ta 2018 aka tilastawa Zuma yin murabus saboda badakalar rashawa.

  Badaƙalar ta ƙunshi zargin iyalin nan mai arzikin gaske na Gupta, waɗanda suka kasance abokan tsohon shugaban, inda ya yi amfani da alaƙarsa da su ya ba su kwangiloli na miliyoyin dala.

 15. Labaran BBC cikin Minti Ɗaya na Rana

  Video content

  Video caption: MINTI ƊAYA DA BBC NA RANA 15/02/2021
 16. Akwai yiwuwar Faransa za ta janye dakarunta daga yankin Sahel

  Shugabannin ƙasashen da ke fama da tashin hankalin masu ikirarin jihadi a yankin Sahel na taro kan matsalar da yiwuwar janye dakarun Faransa daga yankunan.

  Shugaba Emmanuel Macron na halartar taron ƙolin ne da ke gudana a birnin Ndjamena na Chadi ta hanyar bidiyo a intanet.

  A bara ne Faransa ta ƙara yawan sojojinta 5,000 da ke yankin Sahel.

  Amma mutuwar gwamman sojojin ya sa an matsa wa gwamnatin Faransa lamba da a maido su gida.

  Sojojin Faransa da na sauran ƙasashen duniya sun gaza daƙile matsalar tsaron da ta addabi yankin.

  Sahel
 17. Gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya na taro kan matsalar tsaro a yankin

  Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro a Najeriya, Babagana Munguno da duka gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya bakwai na taro a Kaduna don lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

  A baya-bayan nan, ƴan bindiga sun addabi yankin kuma sun kashe ɗaruruwan mutane da raba wasu da muhallansu.

  Taron tsaro a Najeriya
  Taron tsaro a Najeriya
  Taron tsaro a Najeriya
  Taron tsaro a Najeriya
 18. An saka gasar kwaikwayon ɗaurin ɗankwalin Ngozi Okonjo-Iweala a Twitter

  Masu goyon bayan mace ta farko kuma ƴar Afrika ta farko da ake sa ran za ta zama shugabar Ƙungiyar Cinikayya ta Duniya, Ngozi Okonjo Iweala, na ci gaba da nuna alfaharinsu bisa nasarorinta, ta hanyar kwaikwayon ɗaurin ɗankwalinta.

  Wata mai amfani da shafin Twitter kuma ƴar kasuwa Temie Giwa-Tubosun ta yi alƙawarin N100,000 ga duk wanda ya kwaikwayi ɗaurin Ngozi Okonjo Iweala.

  Ms Giwa-Tubosun ta wallafa saƙon ne a shafinta na Twitter inda ta yi irin daurin na Misis Okonjo-Iweala kuma tana maganar tattalin arziƙi da samar da ayyuka, kamar yadda aka san Iweala da yi.

  View more on twitter
  View more on twitter
  View more on twitter
  View more on twitter
  View more on twitter
 19. Gwamnatin Ogun ta gudanar da taron lalubo hanyar zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a jihar

  Gwanatin jihar Ogun ta fara shirin samo zaman lafiya mai ɗorewa kan matsalar manoma da makiyaya a jihar.

  Gwamnatin jihar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Twitter inda ta ce ta tattara masu ruwa da tsaki, ciki har da manyan jami'an gwamnati da wakilan hukumomin tsaro ta tura su yankunan da rikicin ya fi shafa.

  A lokacin da ya ke magana a fadar Olu na Ilaro, kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da gargajiya ya ce Hon. Afolabi Afuape ya ce rikicin makiyaya da manoma matsala ce da ta shafi gaba ɗaya Najeriya.

  Ya ce don haka ne ma gwamnatin jihar ta Ogun ke neman mafita saboda ba ta jin daɗin abubuwan da ke faruwa.

  Wasu daga cikin jami'an da suka yi magana a taron sun yi kira da a bai wa manoma da amfanin gonarsu kariya.

  View more on twitter
 20. Ƴan bindiga sun kashe mutum uku a Jos

  NIGERIA POLICE

  Wasu ƴan bindiga sun kashe mutum uku a ƙaramar hukumar Bassa da ke jihar Filato.

  Jaridar Punch ta ruwaito cewa an harbe mutanen ne da yammacin ranar Lahadi a hanyarsu ta komawa gida.

  Shugaban ƙungiyar matasa ta Irigwe Youths Movement, Ezekiel Bini ya shaida wa jaridar Punch cewa mutanen da aka kashe na hanyar ne daga garin Ri-bakwa lokacin da ƴan bindigar suka mamaye su da misalin 7.30 na maraice.

  Ya ce mutum uku sun mutu nan take yayin da mutum daya ya samu manyan raunuka amma yana samun kulawa a asibiti.

  Eziekel ya ce bayan da suka harbe mutanen, ƴan bindigar sun shiga ƙauyen Zirshe inda suka kona wasu gidaje kafin suka tsere.

  Rundunar ƴan sanda jihar ta ce tana bincike kan lamarin kuma kwamishinan ƴan sanda ya kira taron masu ruwa da tsaki don nema mafita, a cewar jaridar Punch.