Akalla ma’aikatan
kamfanin lantarki na (TCN) biyu ne suka samu munanan rauni lokacin da motarsu
ta taka wata nakiya da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa a
Mainok da ke karamar Hukumar Kaga a Jihar Borno.
PRNigeria ta
ruwaito cewa fashewar ta faru ne bayan da tawagar injiniyoyin kamfanin TCN da
na kamfanin da ke raba wutar lantarki a Yola YEDC suka taka nakiyar a kan
hanyarsu ta zuwa gyaran wutar lantarki a Maiduguri da kewaye.
Jaridar ta ce an
kwashi ma’aikatan zuwa asibitin koyarwa ta Jami’ar Maiduguri domin kula da
lafiyarsu.
Hare-haren wuce
gona da iri da ƴan ta’adda ke kai wa na
kawo cikas ga samar da wutar a Maiduguri da wasu sassan jihar Borno.
Gwamnatin Kano ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya
Gwamnatin Kano ta sanar da rufe wasu makarantun koyar da
kiwon lafiya na jihar saboda barazanar tsaro.
Makarantun sun hada da ta Bebeji (School of Health
Technology Bebeji) da ta ma’aitan jinya a Madobi (School of Nursing Madobi), da kuma ta ungozoma (Schools of Midwifery) a
Gwarzo da Gezawa da Dambatta, kamar yadda sanarwar da ma’aikatar lafiya ta
jihar ta bayyana.
Sanarwar ta buƙaci iyaye su je su kwashe ƴaƴansu
daga makarantun.
Gwamnatin Kano kuma ta ce an yi tanadin yadda ɗaliban za
su ci gaba da karatunsu, ba tare da yin cikakken bayani ba kan tanadin da kuma
tsarin ci gaba da karatun ɗaliban.
Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro kan sako ɗaliban Kagara
PresidencyCopyright: Presidency
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina hukumomin tsaro da na leken
asirin kasar da kuma gwamnatin jihar Neja kan rawar da suka taka wajen sako daliban
Kagara da ƴan bindiga suka sace
A wata sanarwa da
fadar shugaban ta fitar bayan sako ɗaliban a ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce: "Muna farin ciki da
aka sake su".
Ya kuma tausaya wa ma’aikata da
ɗaliban da iyayensu kan abin da ya same su.
Ya yi gargadin cewa al'umma ba za ta ci
gaba da fuskantar waɗannan hare-hare ba sannan ya umarci jami'an tsaro su shiga
farautar ƴan bindigar tare da gurfanar
da su a gaban shari'a.
Barcelona ta samu sa'ar Sevilla a La Liga
Barcelona ta doke Sevilla 2-0 a fafatawar da suka yi a Camp Nou a ranar Asabar.
Messi ne ya ci ƙwallo ta biyu kuma ya ba Dembele ya ci ta farko, yanzu maki biyu ne ya raba Barcelona da Atletico Madrid da ke jan ragamar teburin La liga.
Sai dai Atletico tana da kwantan wasa biyu kuma idan ta cinye wasannin zai kasance maki 8 ta ba Barcelona.
Barcelona za ta sake karawa da Sevilla a Copa de Raey a ranar Laraba, sai dai Sevilla ce ta cinye karawar farko ci 2-0.
ReutersCopyright: Reuters
Man City ta buga wasa 27 ba a doke ta ba
Manchester City ta ci gaba da samun nasara a wasanninta da take buga wa a gasar Premier inda ta buga wasa 20 tana lashe wasa.
Yanzu City da ke saman reburin Premier tazarar maki 13 ta ba Manchester United bayan ta doke West Ham United 2-1.
Yanzu kuma ta buga wasa 27 ba a doke ta ba, inda za ta iya maimaita tarihin da ta kafa idan ba ta yi ɓarin maki ba a karawarta da Wolves a ranar Talata.
Getty ImagesCopyright: Getty Images
An kama ɗaruruwan masu zanga-zanga a Myanmar
Hukumomi a Myanmar na ci
gaba da kama jama'a ba ji ba gani, a wani yunkuri na dakile ci gaba da boren
adawa da gwamnati soji.
Ana saran an tsare daruruwa kuma a wasu wuraren an samu
taho mugama a tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda, inda
jami'an tsaro suka rika amfani da harsashen roba wurin tarwatsa taruka.
Sojojin da suka kwace mulki hannun farar hula sun sanar
da korar wakilin Myanmar a majalisar dinkin duniya Kyaw Moe Tun, wanda a ranar
Juma'a ya yi kira ga kasashen duniya da kar su kulla hulda da sojojin.
Amnesty ta yi Allah wadai da kama Salihu Yakasai kan faɗin albarkacin bakinsa
Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kama Salihu Tanko Yakasai mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai.
Salihu Tanko Yakasai wanda gwamnatin Kano ta sanar da tuɓe shi daga muƙaminsa bayan ya soki gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari, mahaifinsa Alhaji Tanko Yakasai ya ce jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kama ɗansa.
Sai dai shugaban 'yan sandan DSS na Kano, Alhassan Mohammed, ya musanta kama shi, yana mai cewa "ba mu ma san da kalaman da ake cewa Salihun ya yi ba".
Ɗan takarar adawa a zaɓen shugaban ƙasa a Nijar Mahamane Ousmane ya buƙaci a saki magoya bayansa da hukumomi suka yi.
Tsohon shugaban na Nijar ya yi ƙorafi a shafinsa na Twitter da ba ta tantance cewa "kama shugabannin adawa da masu fafutika ba bisa ka'ida ba da kuma toshe intanet ba shi da wani tasiri ga tabbatar da zaɓin jama'a."
Tun bayan sanar da sakamakon zaɓe zagaye na biyu na wuccin gadi da hukumar zaɓe ta CENI ta yi rikici ya ɓarke a Nijar.
Mahamane Ousmane ya yi watsi da sakamakon inda yake ikirarin lashe zaɓen. Rahotanni sun ce Hama Amadou madugurun adawar ƙasar wanda ya mara wa takarar Mahamane Ousmane baya ya miƙa kansa ga hukumomi domin jin dalilin zarginsa da ake na tunzura jama'a.
Ministar ma’aikatar jin-ƙai da kare afkuwar bala'i
ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ta ce ta shafe yini tana yi wa ɗalibai mata na makarantar Jangebe da ƴan
bindiga suka sace a jihar Zamfara addu'a.
Ministar wadda ƴar
asalin jihar Zamfara ce, cikin jerin saƙwanni da ta wallafa a shafinta na
Twitter ta ce: “na shafe mafi kyawun yini ina addu’ar fatan jin labari mai daɗi
game da tashin hankalin da ke faruwa a
jiha ta."
A ranar Juma’a aka wayi
gari a Najeriya da sace ɗalibai sama da 300 a makarantar sakandare ta mata a
garin Jangebe da ke cikin ƙaramar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara inda ƴan bindiga suka abka makarantar tsakar dare suka yi awon gaba da su
Sadiya ta yi Allah wadai da sace ɗaliban tana mai cewa
koma-baya ne ga ilimi da ci gaba.
A yaƙi 'yan fashi kuma a tattauna da su - Ahmad Lawan
Video content
Video caption: Danna hoton sama ku saurari hira da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad LawanDanna hoton sama ku saurari hira da Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan
A Najeriya, ana ci gaba da tafka zazzafar mahawara kan batun matakan da ya kamata a bi wajen lalubo bakin zaren matsalar 'yan bindiga da ta addabi jihohi da dama na arewacin kasar.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya yi tsokaci kan batun da kuma wasu da suka shafi siyasar jam'iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya.
Editan Sashen Hausa na BBC Aliyu Abdullahi Tanko, shi ne ya jagoranci hirar.
Fursuna 400 sun tsere daga gidan yari a Haiti
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Fiye da fursuna 400 ne suka tsere a ƙasar Haiti bayan sun gudu daga wani gidan yari da ke wajen babban birnin kasar, Port-Prince, ranar Alhamis.
Mahukunta sun bayar da sanarwar nemansu, ta hanyar wallafa hotunansu a kafafen talabijin da jaridu da mujallu.
Wakilin BBC ya ce mahukunta sun ce lamarin ya janyo mutuwar mutum 25, ciki har da daraktan gidan yarin sannan yawancin wadanda abin ya shafa fararen hula ne wadanda rikicin ya rutsa da su.
Gwamnatin Haiti ta ce an kashe wani shugaban gungun masu aikata laifin mai suna Arnel Joseph, sa'o'i kaɗan bayan ya tsere.
An harbe shi ne da safiyar Juma'a a wani shingen bincike a arewacin kasar.
Joe Biden ya gargaɗi shugabannin Iran 'su taka a hankali'
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi shugabannin Iran da su taka a hankali.
Mista Biden na magana ne kwana daya bayan da jiragen yakin Amurka suka kai hari kan wasu wurare a gabashin Syria da ke karkashin ikon kungiyoyin 'yan Shi'a masu goyon bayan Iran.
Akalla mutum 17 aka bayar da rahoton an kashe yayin harin, wanda shi ne matakin soja na farko na Amurka tun lokacin da Biden ya hau mulki.
Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta kira harin a matsayin 'martanin da ya dace da harin rokar da mayakan suka kai wani sansanin sojin Amurka da ke Iraki, inda suka kashe mutum biyar.
Dole ne gwamnoni su daina saka wa 'yan fashi da kyautar kuɗi - Buhari
NG PresidencyCopyright: NG Presidency
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya gargaɗi gwamnonin ƙasar da su daina saka wa tubabbaun 'yan fashi da kuɗi da kuma motoci.
Buhari na wannan magana ce kwana ɗaya bayan 'yan fashin daji sun sace ɗalibai mata 317 daga makarantar kwana ta GGSS Jangebe da ke Jihar Zamfara.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya haƙiƙance cewa yin sulhu da 'yan fashin dajin da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane shi ne mafita wurin kawo ƙarshen matsalar.
"Wajibi ne gwamnonin jihohi su sake duba dabarunsu na saka wa 'yan fashi da kuɗi da kuma ababen hawa," in ji Buhari cikin wani jerin saƙonni da ya wallafa a Twitter.
Ya ƙara da cewa: "Irin wannan yunƙurin ka iya harfar da bal'ai mai girma. Dole ne jihohi da ƙananan hukumomi su zage dantse wurin samar da tsaro a yankunansu.
"Kar 'yan fashi da 'yan ta'adda su zaci cewa sun fi ƙarfin gwamnati ne. Kar su ɗauki sassautawar da muke yi a matsayin tsoro ko gazawa, muna yi ne domin kare rayukan waɗanda ba su ji ba su gani ba."
Martanin nasa ya biyo bayan koken da Gwamnan Neja Abububakar Bello ya yi ne, cewa "Gwamnatin Tarayya (ƙarƙashin Buhari) ba ta taimaka mana wurin ceto ɗaliban makarantar Kagara", waɗanda aka sace ranar 17 ga Fabarairu kuma aka sako su a yau Asabar.
Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan wasu ‘yan Saudiyya bayan wani rahoton leken asiri da aka gano cewa Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman ne ya ba da umarnin kamawa ko kashe ɗan jarida Jamal Khashoggi.
Matakan sun haɗa da hana biza da ƙwace kadarorinsu. Sai dai babu wani mataki da ƙasar ta sanar a kan yariman da kansa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce matakan ba sa nufin lalata alakar Amurka da Saudiyya.
An kashe Mista Khashoggi tare da gididdiba namansa a ƙaramin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istambul, babban birnin Turkiyya a shekarar 2018.
Amurka ta kuma sanar da wata sabuwar manufa da ta kira ''Albarkacin Khashoggi'' wadda za ta samar da kariya ga 'yan jarida yayin tsallaka iyakokin ƙasashen duniya.
An rufe makarantun kwana a Kano da Zamfara
BBCCopyright: BBC
Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rufe
makarantun kwana guda 13 har sai abin da hali ya yi saboda barazanar tsaro.
Gwamantin ta ce ta rufe makarantun ne biyo bayan sace ɗaliban makarantu a jihohin
Zamfara da Neja da aka yi a baya-bayan.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Sunusi Sa’id Kiru ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne kasancewar wasu daga cikin makarantun na kan hanya
sannan wasu kuma sun yi wajen gari.
Ya ƙara da cewa a baya-bayan ma an yi yunƙurin
shiga makarantar kwana da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa amma mutanen ba su samu nasara ba.
Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana biyo bayan sace ɗalibai mata 317 da aka yi ranar Juma'a a makarantar sakandare ta Jangebe.
Cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar ranar Juma'a da yamma, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tabbatar da isasshen tsaro a dukkan makarantun jihar.
Sai dai ba a san ranar da za a sake buɗe makarantun ba.
Cutar korona ta sake kashe mutum 11 a Najeriya
Getty ImagesCopyright: Getty Images
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 600 da suka kamu da cutar korona ranar Juma'a.
Kazalika, cutar ta sake kashe mutum 11, wanda jumillarsu ta zama 1,902 tun bayan ɓullar cutar a ƙasar a watan Fabarairun 2020.
Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 21 kuma Legas ce kan gaba da mutum 169, sai Taraba mai 92 da Ogun mai 65 da kuma Cross River mai 57.
Rahoto kai-tsaye
Daga Umar Mikail da Awwal Ahmad Janyau
time_stated_uk
A nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe.
An buɗe babbar gasar Legas ta Third Mainland Bridge
Gwamnatin Legas ta sanar da buɗe babban gadar Third Mainland Bridge bayan kammala aikin gyaran gadar.
Sanarwar da gwamnatin Legas ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce an buɗe hanyoyin gadar biyu na zuwa da dawo wa bayan kammala aikin.
Gadar da ta ratsa tekun Legas ita ce mafi tsawo a Afrika.
Ma’aikatan NEPA sun ‘taka nakiya’ a Borno
Akalla ma’aikatan kamfanin lantarki na (TCN) biyu ne suka samu munanan rauni lokacin da motarsu ta taka wata nakiya da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa a Mainok da ke karamar Hukumar Kaga a Jihar Borno.
PRNigeria ta ruwaito cewa fashewar ta faru ne bayan da tawagar injiniyoyin kamfanin TCN da na kamfanin da ke raba wutar lantarki a Yola YEDC suka taka nakiyar a kan hanyarsu ta zuwa gyaran wutar lantarki a Maiduguri da kewaye.
Jaridar ta ce an kwashi ma’aikatan zuwa asibitin koyarwa ta Jami’ar Maiduguri domin kula da lafiyarsu.
Hare-haren wuce gona da iri da ƴan ta’adda ke kai wa na kawo cikas ga samar da wutar a Maiduguri da wasu sassan jihar Borno.
Gwamnatin Kano ta rufe makarantun koyar da kiwon lafiya
Gwamnatin Kano ta sanar da rufe wasu makarantun koyar da kiwon lafiya na jihar saboda barazanar tsaro.
Makarantun sun hada da ta Bebeji (School of Health Technology Bebeji) da ta ma’aitan jinya a Madobi (School of Nursing Madobi), da kuma ta ungozoma (Schools of Midwifery) a Gwarzo da Gezawa da Dambatta, kamar yadda sanarwar da ma’aikatar lafiya ta jihar ta bayyana.
Sanarwar ta buƙaci iyaye su je su kwashe ƴaƴansu daga makarantun.
Gwamnatin Kano kuma ta ce an yi tanadin yadda ɗaliban za su ci gaba da karatunsu, ba tare da yin cikakken bayani ba kan tanadin da kuma tsarin ci gaba da karatun ɗaliban.
Buhari ya jinjina wa jami’an tsaro kan sako ɗaliban Kagara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina hukumomin tsaro da na leken asirin kasar da kuma gwamnatin jihar Neja kan rawar da suka taka wajen sako daliban Kagara da ƴan bindiga suka sace
A wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar bayan sako ɗaliban a ranar Asabar, Shugaba Buhari ya ce: "Muna farin ciki da aka sake su".
Ya kuma tausaya wa ma’aikata da ɗaliban da iyayensu kan abin da ya same su.
Ya yi gargadin cewa al'umma ba za ta ci gaba da fuskantar waɗannan hare-hare ba sannan ya umarci jami'an tsaro su shiga farautar ƴan bindigar tare da gurfanar da su a gaban shari'a.
Barcelona ta samu sa'ar Sevilla a La Liga
Barcelona ta doke Sevilla 2-0 a fafatawar da suka yi a Camp Nou a ranar Asabar.
Messi ne ya ci ƙwallo ta biyu kuma ya ba Dembele ya ci ta farko, yanzu maki biyu ne ya raba Barcelona da Atletico Madrid da ke jan ragamar teburin La liga.
Sai dai Atletico tana da kwantan wasa biyu kuma idan ta cinye wasannin zai kasance maki 8 ta ba Barcelona.
Barcelona za ta sake karawa da Sevilla a Copa de Raey a ranar Laraba, sai dai Sevilla ce ta cinye karawar farko ci 2-0.
Man City ta buga wasa 27 ba a doke ta ba
Manchester City ta ci gaba da samun nasara a wasanninta da take buga wa a gasar Premier inda ta buga wasa 20 tana lashe wasa.
Yanzu City da ke saman reburin Premier tazarar maki 13 ta ba Manchester United bayan ta doke West Ham United 2-1.
Yanzu kuma ta buga wasa 27 ba a doke ta ba, inda za ta iya maimaita tarihin da ta kafa idan ba ta yi ɓarin maki ba a karawarta da Wolves a ranar Talata.
An kama ɗaruruwan masu zanga-zanga a Myanmar
Hukumomi a Myanmar na ci gaba da kama jama'a ba ji ba gani, a wani yunkuri na dakile ci gaba da boren adawa da gwamnati soji.
Ana saran an tsare daruruwa kuma a wasu wuraren an samu taho mugama a tsakanin masu zanga zanga da ‘yan sanda, inda jami'an tsaro suka rika amfani da harsashen roba wurin tarwatsa taruka.
Sojojin da suka kwace mulki hannun farar hula sun sanar da korar wakilin Myanmar a majalisar dinkin duniya Kyaw Moe Tun, wanda a ranar Juma'a ya yi kira ga kasashen duniya da kar su kulla hulda da sojojin.
Amnesty ta yi Allah wadai da kama Salihu Yakasai kan faɗin albarkacin bakinsa
Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kama Salihu Tanko Yakasai mai ba gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai.
Salihu Tanko Yakasai wanda gwamnatin Kano ta sanar da tuɓe shi daga muƙaminsa bayan ya soki gwamnatin APC ta Muhammadu Buhari, mahaifinsa Alhaji Tanko Yakasai ya ce jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kama ɗansa.
Sai dai shugaban 'yan sandan DSS na Kano, Alhassan Mohammed, ya musanta kama shi, yana mai cewa "ba mu ma san da kalaman da ake cewa Salihun ya yi ba".
Mahamane Ousmane ya buƙaci a saki magoya bayansa
Ɗan takarar adawa a zaɓen shugaban ƙasa a Nijar Mahamane Ousmane ya buƙaci a saki magoya bayansa da hukumomi suka yi.
Tsohon shugaban na Nijar ya yi ƙorafi a shafinsa na Twitter da ba ta tantance cewa "kama shugabannin adawa da masu fafutika ba bisa ka'ida ba da kuma toshe intanet ba shi da wani tasiri ga tabbatar da zaɓin jama'a."
Tun bayan sanar da sakamakon zaɓe zagaye na biyu na wuccin gadi da hukumar zaɓe ta CENI ta yi rikici ya ɓarke a Nijar.
Mahamane Ousmane ya yi watsi da sakamakon inda yake ikirarin lashe zaɓen. Rahotanni sun ce Hama Amadou madugurun adawar ƙasar wanda ya mara wa takarar Mahamane Ousmane baya ya miƙa kansa ga hukumomi domin jin dalilin zarginsa da ake na tunzura jama'a.
Sadiya Farouq ta yi wa Zamfara addu'a
Ministar ma’aikatar jin-ƙai da kare afkuwar bala'i ta gwamnatin Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ta ce ta shafe yini tana yi wa ɗalibai mata na makarantar Jangebe da ƴan bindiga suka sace a jihar Zamfara addu'a.
Ministar wadda ƴar asalin jihar Zamfara ce, cikin jerin saƙwanni da ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce: “na shafe mafi kyawun yini ina addu’ar fatan jin labari mai daɗi game da tashin hankalin da ke faruwa a jiha ta."
A ranar Juma’a aka wayi gari a Najeriya da sace ɗalibai sama da 300 a makarantar sakandare ta mata a garin Jangebe da ke cikin ƙaramar hukumar Talatar Mafara a jihar Zamfara inda ƴan bindiga suka abka makarantar tsakar dare suka yi awon gaba da su
Sadiya ta yi Allah wadai da sace ɗaliban tana mai cewa koma-baya ne ga ilimi da ci gaba.
A yaƙi 'yan fashi kuma a tattauna da su - Ahmad Lawan
Video content
A Najeriya, ana ci gaba da tafka zazzafar mahawara kan batun matakan da ya kamata a bi wajen lalubo bakin zaren matsalar 'yan bindiga da ta addabi jihohi da dama na arewacin kasar.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan makon, Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Lawan, ya yi tsokaci kan batun da kuma wasu da suka shafi siyasar jam'iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya.
Editan Sashen Hausa na BBC Aliyu Abdullahi Tanko, shi ne ya jagoranci hirar.
Fursuna 400 sun tsere daga gidan yari a Haiti
Fiye da fursuna 400 ne suka tsere a ƙasar Haiti bayan sun gudu daga wani gidan yari da ke wajen babban birnin kasar, Port-Prince, ranar Alhamis.
Mahukunta sun bayar da sanarwar nemansu, ta hanyar wallafa hotunansu a kafafen talabijin da jaridu da mujallu.
Wakilin BBC ya ce mahukunta sun ce lamarin ya janyo mutuwar mutum 25, ciki har da daraktan gidan yarin sannan yawancin wadanda abin ya shafa fararen hula ne wadanda rikicin ya rutsa da su.
Gwamnatin Haiti ta ce an kashe wani shugaban gungun masu aikata laifin mai suna Arnel Joseph, sa'o'i kaɗan bayan ya tsere.
An harbe shi ne da safiyar Juma'a a wani shingen bincike a arewacin kasar.
Joe Biden ya gargaɗi shugabannin Iran 'su taka a hankali'
Shugaban Amurka Joe Biden ya gargadi shugabannin Iran da su taka a hankali.
Mista Biden na magana ne kwana daya bayan da jiragen yakin Amurka suka kai hari kan wasu wurare a gabashin Syria da ke karkashin ikon kungiyoyin 'yan Shi'a masu goyon bayan Iran.
Akalla mutum 17 aka bayar da rahoton an kashe yayin harin, wanda shi ne matakin soja na farko na Amurka tun lokacin da Biden ya hau mulki.
Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta kira harin a matsayin 'martanin da ya dace da harin rokar da mayakan suka kai wani sansanin sojin Amurka da ke Iraki, inda suka kashe mutum biyar.
Dole ne gwamnoni su daina saka wa 'yan fashi da kyautar kuɗi - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ya gargaɗi gwamnonin ƙasar da su daina saka wa tubabbaun 'yan fashi da kuɗi da kuma motoci.
Buhari na wannan magana ce kwana ɗaya bayan 'yan fashin daji sun sace ɗalibai mata 317 daga makarantar kwana ta GGSS Jangebe da ke Jihar Zamfara.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya haƙiƙance cewa yin sulhu da 'yan fashin dajin da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane shi ne mafita wurin kawo ƙarshen matsalar.
"Wajibi ne gwamnonin jihohi su sake duba dabarunsu na saka wa 'yan fashi da kuɗi da kuma ababen hawa," in ji Buhari cikin wani jerin saƙonni da ya wallafa a Twitter.
Ya ƙara da cewa: "Irin wannan yunƙurin ka iya harfar da bal'ai mai girma. Dole ne jihohi da ƙananan hukumomi su zage dantse wurin samar da tsaro a yankunansu.
"Kar 'yan fashi da 'yan ta'adda su zaci cewa sun fi ƙarfin gwamnati ne. Kar su ɗauki sassautawar da muke yi a matsayin tsoro ko gazawa, muna yi ne domin kare rayukan waɗanda ba su ji ba su gani ba."
Martanin nasa ya biyo bayan koken da Gwamnan Neja Abububakar Bello ya yi ne, cewa "Gwamnatin Tarayya (ƙarƙashin Buhari) ba ta taimaka mana wurin ceto ɗaliban makarantar Kagara", waɗanda aka sace ranar 17 ga Fabarairu kuma aka sako su a yau Asabar.
Amurka ta ƙaƙaba wa wasu 'yan Saudiyya takunkumi
Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan wasu ‘yan Saudiyya bayan wani rahoton leken asiri da aka gano cewa Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman ne ya ba da umarnin kamawa ko kashe ɗan jarida Jamal Khashoggi.
Matakan sun haɗa da hana biza da ƙwace kadarorinsu. Sai dai babu wani mataki da ƙasar ta sanar a kan yariman da kansa.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce matakan ba sa nufin lalata alakar Amurka da Saudiyya.
An kashe Mista Khashoggi tare da gididdiba namansa a ƙaramin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istambul, babban birnin Turkiyya a shekarar 2018.
Amurka ta kuma sanar da wata sabuwar manufa da ta kira ''Albarkacin Khashoggi'' wadda za ta samar da kariya ga 'yan jarida yayin tsallaka iyakokin ƙasashen duniya.
An rufe makarantun kwana a Kano da Zamfara
Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta rufe makarantun kwana guda 13 har sai abin da hali ya yi saboda barazanar tsaro.
Gwamantin ta ce ta rufe makarantun ne biyo bayan sace ɗaliban makarantu a jihohin Zamfara da Neja da aka yi a baya-bayan.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Sunusi Sa’id Kiru ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki matakin ne kasancewar wasu daga cikin makarantun na kan hanya sannan wasu kuma sun yi wajen gari.
Ya ƙara da cewa a baya-bayan ma an yi yunƙurin shiga makarantar kwana da ke Ƙaramar Hukumar Gabasawa amma mutanen ba su samu nasara ba.
Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kwana biyo bayan sace ɗalibai mata 317 da aka yi ranar Juma'a a makarantar sakandare ta Jangebe.
Cikin wani jawabi da ya yi wa al'ummar jihar ranar Juma'a da yamma, Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa na ƙoƙarin tabbatar da isasshen tsaro a dukkan makarantun jihar.
Sai dai ba a san ranar da za a sake buɗe makarantun ba.
Cutar korona ta sake kashe mutum 11 a Najeriya
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 600 da suka kamu da cutar korona ranar Juma'a.
Kazalika, cutar ta sake kashe mutum 11, wanda jumillarsu ta zama 1,902 tun bayan ɓullar cutar a ƙasar a watan Fabarairun 2020.
Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 21 kuma Legas ce kan gaba da mutum 169, sai Taraba mai 92 da Ogun mai 65 da kuma Cross River mai 57.
Sauran su ne: Abuja (38), Rivers (28), Kwara (26), Akwa Ibom (25), Osun (21), Plateau (12), Borno (9), Gombe (9), Abia (8), Ebonyi (8), Ekiti (7), Kano (7), Delta (6), Oyo (6), Bauchi (3), Nasarawa (3), Sokoto (1).
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 155,076 ne suka kamu da cutar a Najeriya, sai kuma 132,544 da aka sallama bayan sun warke.
Assalamu Alaikum
Barkanmu da hantsin Asabar. Sannunmu da sake hauwa a shafin labarai kai-tsaye.
Ku biyo ni Umar Mikail domin sanin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.