Fasalin jerin duniyoyin a kan tsarin duniyar rana, da ya fara da wadanda suka fi kusa da rana har ya zuwa nesa da ita sun hada da duniyoyin: Mercury da Venus da Earth da Mars da Saturn da Uranus da Neptune da kuma duniya ta tara da aka dade ana tababa a kai, wato Pluto.
Rahoto kai-tsaye
Daga Fauziyya Kabir Tukur
time_stated_uk
Kotun Malaysia ta amince kiristoci su yi amfani da sunan ‘Allah’ a rubutunsu
Kotun Koli a Malaysia ta kawo karshen taƙaddama ta tsawon shekaru 13 inda ta zartar da hukuncin da ya ba Kiristoci damar yin amfani da kalmar "Allah" a rubuce-rubucensu.
Shari’ar ta shafi wata mata ce daga 'yan asalin ƙasar Malaysia bayan ƴan sanda sun ƙwace kaset kaset na CD na addini a 2008 da ke cewa haramun ne a gare tamallaki abubuwan da ke ɗauke da sunan Allah a Larabci.
Gwamnatin ƙasar kullum tana jaddada cewa kalmar ‘Allah’ Musulmai ne kawai ya kamata su yi amfani da ita, tana mai cewa saɓa ma hakan ga wani addini zai iya sauya tunani da kuma jirkita tunaninsu zuwa wasu addinai idan aka yi amfani da sunan wanda zai saba wa addinin.
A shekarar 2013, wata kotun ɗaukaka ƙara a kasar Malaysia ta yanke hukuncin haramta wa wata jaridar mabiya Katolika a ƙasar amfani da kalmar Larabci "Allah" a cikin fassararta ta Malay a rubutunta game da addinin Kirista ba, wani lamari da ya haifar da hare-hare a wuraren ibada uku shekarun baya.
Buhari ya kaddamar da shirin shinfiɗa layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya ƙaddamar da shirin manyan ayyukan ci gaban ƙasa guda uku.
Shugaban ya bayyana ayyukan a shafinsa na Twitter da suka haɗa da aikin shimfiɗa sabon layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri.
Da babbar tashar jirgin ruwa ta Bonny a jihar Rivers da kuma babbar tashar jirgin ƙasa da za a dinga jigilar kayyakin da aka samar a cikin gida.
Buhari ya ce layin dogo daga Fatakwal - Maiduguri, zai zama hanyar jigilar kayayyaki da samar da bunƙasa sufuri a cikin gida da kuma fitar wada shigo daga kaya zuwa waje.
Bauchi ta karɓi kasonta na allurar rigakafin korona
Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin kasar ta karɓi nata kason rigakafin korona.
Za a dai fara yi wa ma'aikatan lafiya, da manyan jami'an gwamnati da sarakunan gargajiya da shuwagabannin addinai allurar domin karfafa gwiwar jama'a kan ingancin rigakafin.
Tun a ranar Litinin gwamnatin tarayya ke ci gaba da aika wa jihohi kasonsu na farko na alluran rigakafin cutar korona.
Mataimakin gwamnan jihar ta Bauchi kuma shugaban kwamitin yaki da annobar korona a jihar, Sanata Baba Tela, ya shaida wa BBC cewa sun shirya wa aikin fara rigakafin a jihar.
Madugun adawar Tanzania na son sanin halin da John Magufuli yake ciki
Madugun adawa a Tanzania ya bukaci gwamnati ta yi bayanin inda shugaba John Magufuli yake, bayan shafe mako biyu ba a ji duriyarsa ba a kasar.
Tundu Lissu ya ce sanin halin da shugaban ke ciki na da muhimmanci sosai ga yan kasar.
Gwamnatin Tanzania dai ta gargadi kafofin yada labarai kan yada labarai game da lafiyar shugaba Magufuli.
Wata jarida a Kenya ta bayar da rahoton cewa wani shugaba kasar Afirka na kwance a asibitin Nairobi saboda kamuwa da annobar korona sai dai ba a tabbatar da labarin ba.
Mr Magafuli ya sha musanta cewa annobar korona matsala ce, inda yake karfafa gwiwar a yi addu'a a matsayin hanyar yakar cutar.
Yadda aka yi wa Gwamnan Badaru allurar rigakafin korona
An yi wa Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar allurar rigakafin korona a ranar Laraba.
An yi masa rigakafin ne ta AstraZenica a asibitin gidan gwamnatin jihar a Dutse.
Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sadarwa na intanet ya nuna yadda aka yi wa gwamnan rigakafin.
Jigawa na cikin jihohin da suka karɓi kason allurar rigakafin daga cikin miliyan hudu da aka ba Najeriya
Video content
An kusan yi wa Ganduje allurar rigakafin korona
Gwamnan Kano Abdullahi Umar ganduje ya ce a gobe Alhamis za a yi masaallurar rigakafin korona a matsayin na shugaba a jihar
Sai bayan an yi wa ma'aikatan lafiya a jahar za a yi wa gwamna Ganduje da mataimakinsa
A ranar Talata negwamnatin jihar Kano ta karɓi allurar rigakafin korona fiye da dubu 200 daga cikin rigakafi sama da miliyan hudu da aka kawo Najeriya.
Ga karin bayanin da Gwamna Ganduje ya yi wa wakilin mu na Kano Khalifa Shehu Dokaji.
Video content
An yi wa gwamna Elrufa'i allurar rigakafin korona
Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya karɓi allurar rigakafin korona a ranar Laraba.
Haka ma an yi wa mataimakiyarsa Dr Hadiza Balarabe allurar.
A ranar Talata ne gwamnatin Kaduna ta ce ta karɓi allurar 180,000 kasonta na rigakafin korona daga cikin miliyan hudu da gwamnatin Najeriya ta karɓa.
Mahukunta soji a Myanmar sun soma korar iyalan ma'aikatan jirgin kasa daga gidajensu
Mahukunta soji a Myanmar sun soma korar iyalan ma'aikatan jirgin kasa daga gidajensu, a wani kokari na tarwatsa yajin aikin gama gari da kungiyoyin kwadago ke yi domin adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi a watan da ya gabata.
Daruruwan sojoji da yansanda suka kai samame gidajen ma'aikatan da ke Yangon.
Wakilin BBC ya ce An hango ma'aikatan da aka kora dauke da akwatina da taimakawa iyalansu ciki harda tsoffi domin ficewa, an fitar da bukatar kai musu agajin abinci da matsuguni.
Masu fafutika da suka daura hotuna da bidiyon yada ake korarsu a shafin Twitter sun ce sojojin Burma na kuma amfani da bindiga wajen tilastawa masu yajin aiki su koma bakin aikinsu.
Ƴan adawar Tanzania na son a gaya musu inda shugaban ƙasar ya shiga tsawon mako biyu
Madugun yan adawa a Tanzania ya bukaci gwamnati ta yi bayanin inda Shugaba John Magufuli yake, bayan shafe mako biyu ba a ji duriyarsa ba a kasar.
Tundu Lissu ya ce sanin halin da shugaban ke ciki na da muhimmanci sosai ga yan kasa.
Gwamnatin Tanzania dai ta gargadi kafofin yada labarai kan yada labaran da ba su bincike ba a kan lafiyar Shugaba Magufuli.
Wata jarida a Kenya dai ta ba da rahoton cewa wani shugaban kasar Afirka na kwance a asibitin Nairobi saboda kamuwa da annobar korona sai dai ba a tabbatar da labarin ba.
Mr Magafuli ya sha musanta cewa annobar korona matsala ce, inda yake karfafa gwiwar a yi addu'a da sirace a matsayin hanyar yakar cutar.
An kashe mutum ɗaya a zanga-zangar ɗalibai a Afirka Ta Kudu
Ƴan sanda a Afrika Ta Kudu sun harba harsasan roba domin tarwatsa ɗaliban jami'a da ke zanga-zanga kan kuɗin makaranta da kumja jinkiri wurin rijista.
An kashe mutum ɗaya, amma ba a tabbatar da ko ɗalibi ne ko kuma mai wucewa ba.
Ɗaliban jami'ar Witwatersrand da ke Johannesburg sun fara zanga-zanga ne tun a ranar Litinin inda suka tare hanyoyi da kuma tayar da zaune tsaye.
Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Rana 10/03/2021
Ku saurari Labarai Cikin Minti Ɗaya Da BBC Hausa Na Yamma 10/03/2021, wanda Halima Umar Saleh ta karanta.
Video content
China da Rasha sun sanar da gina tasha a duniyar wata
Hukumar binciken sararin samaniya ta Rasha ta ce ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da takwararta ta China don samar da cibiyoyin bincike a sararin duniyar wata.
Wata sanarwa daga hukumomin ƙasashen biyu ta ce sauran kasashen duniya ma na iya amfani da cibiyoyin binciken.
Wannan na zuwa ne a yayin da Rasha ke shirin yin bikin shekara 60 da ta fara tura mutum duniyar wata.
Tashar ƙasa da ƙasar ta duniyar wata za ta gudanar da jerin bincike kan watan, a cewar sanarwar.
Majalisar dokokin Najeriya ta ce kuɗin da Ibori ya sace na jihar Delta ne
Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da cewa Fam miliayn 4.2 da Burtaniya ta dawo wa da Najeriya na gwamnatin jihar Delta ne.
Jaridar vanguard ta ruwaito cewa majalisar ta bukaci ma'aikatar kuɗi ta gaggauta dakatar da aike kudin ga gwamnatin tarayya.
Majalisar ta yanke wannan shawarar ne bayan wani kudiri da yan majalisar su 9 ƴan jihar ta Delta suka miƙa wa shugaban marasa rinjaye Honarabul Ndudi Elumelu ranar laraba.
Haka kuma, majalisar ta buƙaci Ma'aikatar Kuɗi da Anto Janar na ƙasar su mika mata duk wasu bayanai da suka danagnci kuɗin na Ibori.
Bidiyon zanga-zangar lumana da Ƙungiyar Ƙwadagon Najeriya ta shirya
Video content
Kamaru ta mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya 5,000 gida
Hukumomin Kamaru karkashin jagorancin Minista Paul Atanga Nji, sun dawo da ƴan gudun hijirar Najeriyta 5,000 kuma sun miƙa su ga gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.
An miƙa mutanen ne ranar Litinin a unguwar Amchide da ke kan iyakar kasashen biyu.
Ƴan gudun hijirar na cikin dubban ƴan Najeriya da suka tsere daga Borno a shekarar 2014 zuwa sansanin ƴa gudun hijira na Minawao a Mokolo da ke yankin arewacin Kamaru don gujewa tashin hankalin Boko Haram.
Minista Paul Atanga Nji ya snaar da cewa Shugaba Paul Biya ya amince a bai wa ƴan gudun hijirar 5,000 tallafin kayan abinci da katifu da barguna.
Haka kuma, ministan ya yaba wa Gwamna Zulum kan gidajen da ya gina wa ƴan gudun hijirar inda za su fara sabuwar rayuwa.
Shi ma Gwamna Zulum ya raba wa mutanen kayan abinci da sauran kayan amfani.
Ya bai wa ko wane namiji mai iyali Naira 30,000 sannan aka ba ko wace mace Naira 10,000 da atampa.
Hotunan zanga-zangar lumana da Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta shirya a faɗin kasar
Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta shirya zanga-zangar lumana bisa matakin Majalisar Dokokin kasar sauya dokar mafi karancin albashi.
Ƙarin Bayani: Kungiyar ƙwadago a Najeriya za ta yi zanga-zanga
Ƙungiyar IS ta yi iƙirarin kashe sojoji 30 da kai harin ƙunar baƙin wake a Najeriya
Ƙungiyar IS ta ɗauki alhakin kashewa ko ji wa sojoji 30 rauni ran 8 ga watan Maris a arewa maso gabashin Najeriya lokacin wani faɗa da suka ce an kai harin kunar bakin wake.
Kungiyar ta masu ikirarin jihadi ta bayyana haka ne a wata sanarwa a shafinta na RocketChat. Sanarawar ta ce mayakan IS sun kori dakarun soji a kusa da garin Wulgo a jihar Borno.
Ta ce sun kara ne a lokacin da mayaan IS ɗin suka tada wasu abubuwan fashewa a cikin motoci, wanda ya yi sanadiyyar kashewa da yi wa sojoji 30 rauni.
Sun ambato sunayen yan kunar bakin waken Abubakar Siddiq da bana Jundallah.
Sai dai babu wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka yi dai-dai da bayanan sanarwar kungiyar.
Mutum 25 ƴan gida ɗaya sun mutu bayan sun ci ganyen wata itaciya
Mutum ashirin da biyar ƴan gida ɗaya sun mutu a arewacin Mozambique bayan da suka ci wasu ganyayyaki, a cewar hukumomi.
Jami'ai a yankin sun ce a baya-bayan nan an samu karuwar mutane masu cin kayan itatuwa da ganyayyakin da ba a san su ba a yankin.
Wani rahoton gidan talabijin ɗin kasar, TVM, ya ce mazauna yankin na daka gayayyakin daji su haɗa da garin masara su dafa fate.
Yankin dai na fuskantar ƙarancin abinci saboda ƙarancin ruwan sama.
Mutum 29 sun mutu a wani harin coci Ethiopia
A ƙalla mutum 29 aka kashe bayan da wasu ƴan bindiga suka kai hari wani cocin Orthodox a kudu maso yammacin jihar Oromia ran 5 ga watan Maris, kamar yadda shafin intanet na Addis standard ya ruwaito.
Wani shaida ya ce ƴan bindigar mambobin Oromo Liberation Army, OLA ne.
Mutanen da aka kashe sun haɗa sa mata 21 da jarirai wadanda maharan suka kai wani daji sannan suka harbe su.
Rahoton ya kara da cewa maharan sun shiga yankin ne bayan da dakaru na musamman na Oromia suka bar wurin. Dama dai an kai su yankin ne don yaki da yan bindigar OLA.
An kwashe tsawon shekaru ana rikicin kabilanci da na siyasa a jihar yankin Oromia amma abin ya karu a bara bayan kisan mai fafutuka kuma mawaƙi Hachalu Hundessa.
Masarautar Ingila na binciken zarge-zargen da surukar sarauniya ta yi na nuna wariyar launin fata
Masarautar Ingila ta ce tana ɗaukar zarge-zargen nuna wariyar launin fata da Gimbiyar Sussex ta yi a wata hira da aka yi da ita da matuƙar mahimmanci.
Wata sanarwa da aka fitar a madadin Sarauniyar Ingila ta ce baki ɗaya fadar ta yi baƙin ciki da irin ƙalubalen da Yarima Harry da Meghan suka fuskanta a ƴan shekarun da suka gabata.
Masarautar ta ce za ta yi wani abu kan lamarin cikin sirri.
Cikin hirar dai Meghan ta yi magana kan wani kalami da ta ce ɗaya daga cikin mambobin masarautar ya yi game da kalar fatar ɗansu na farko abin da ta ce ya sa ta ta yi tunanin kashe kanta.